Showing 30001 words to 33000 words out of 137802 words
Chapter 11 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
Ummu Kursumu za'a gwada ki."
Turo baki ta yi tana kallon kayanta wulaƙance."Allah ya tsare ni. Ni na lura you are trying to deprive me."
"Jannah ina matsayin kakarki na yi miki kyauta ki ce ba kya so? To wallahi uban kuturu ya yi kaɗan."
Ta zauna tare da gutsirar goro ta saka a bakinta kana ta ci gaba da cewa,
A hannuna a ka bar mini amanarki, ni ce na ke da ikon zaɓa miki abin da na ke so a rayuwarki. Zan fara koya miki girki da kula da kanki komai da komai zan koya miki, kar ki yi aure mijin ya ga mun cuce shi, duk da cewar tare za mu yi zaman auren."
"Allah ya ba ki sa'a, na ga wanda za ki koya wa, don na gaya wa 'yarki masu aiki za ta ɗauko mini kuma ta amince."
"A ina? Amma ba dai a gidan nan ba, kuma ina raye ko. Ai ni mamakin Halimatuu na ke, wallahi albasa ba ta yi halin ruwa ba."
"Rigima kike ji in ban da rigimar ki mai zan yi da kayan tsoffafi ai kalar ki ce kayan, ko ba ki san wace ce mahaifiyata."
"Dallah rufe mini baki! Na haifi 'yar da cikina? Ai ni ce mai ƙashin ar'azikin, in da ba ɓan haife ta ba a gidan uban wa za ta haife ki. Ai wallahi na iya haihuwa. Kin ga kuwa ƙauyenmu har gori aka yi mini cewar ni da arziƙi sai dai in a jahannama ana yi, sai ga shi Allah ya nuna musu ishira tun duniya ya fara nuna musu ni 'yar aljannah ce. Mata nawa suka ci arzikin haihuwa da maza a karkarkarramu. Shi ya sa na ke shuka musu barbaɗar rashin mutunci.
"Huhm daga ganin ki Hajiya kin shuka rashin mutunci da kuruciyar.."
"Ubanki na ce"?! Tantiriya kawai ni kike faɗa ma haka."
Ɗakinta ta ruga tana faɗin, "Ashe ke muka gado." Ta shige ɗakin ba tare da ji me ta faɗa ba.
Hajiya ta ce." Allah ya kyauta gayyar arna a idi. Waɗancan fitsararrun kenan ni suka gado? Ƙarya kike yi, ga dai waɗanda suka gado ni nan sun zamo jigo ga al'umma.
Wanka ta yi sannan ta nufi sashin su Nahlin ta same tana zaune a falo tana tsefe wa Ummita kitso.
"Don Allah, Anty Nahlin za ki raka ni shopping? Dad ya tura mini da 3000k" Ta ƙarashe tambayar tana zama a gefenta.
Murmushi ta yi tare da ware idanunta."Iyye dad's pet. 3 hundred thousand just like that! Ba ri na kammala mata tsifar, in yi girkin rana sai mu shirya, I hope by 4 pm is ok? kin ga sai ki ta ya ni girkin ko?"
"Tab, na dai ta ya ki hira, don ni wallahi I can even remember when last I enter kitchen. Komai na ke buƙata sai dai a kawo mini. And you know what? I enjoin that" Ta ce mata tana ƙoƙarin kunna data, ta kunna tiktok. Sai ta juyo ta kalle ta ta ce,
Girgiza kant ta yi a ranta tana tunanin anya mom ba ta yi kuskure ba da sunan gyara?
"Anty Nahlin kina ƙoƙari fa, na ga gidan nan masu aiki har biyu, amma kullum kina kicin girki?"
Dariya ta yi."Eh, tsarin Ammy ce. Ya Ajmal ba ya cin abincin masu aiki, na su suke girkawa da masu gadi, sai karnika."
"To sai na wa kenan? Ya mai da ke baiwarsa kenan? In girkin daɗi ne ya girka da kansa mana. I believe ko ruwan zafi ba ya iya dafawa, amma zai takurawa rayuwarki. Ni da tun zuwan gidan nan, na gane ya ɗauki mace baiwa, saboda ko serving ɗin kansa ba ya iya wa, sai dai ki yi masa, sai ka ce cikinki zai kai bincin. I was like haba!"
Dariya ta kwashe da shi sai da ta yi mai isarta ta ce,
"Lallai kina da aiki kuwa. So what if kika auri miji irin Ya Ajmal mai son girkin matarsa?"
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 9-10*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Allah ya kyauta! Shi kansa ya san matar da zai aura ta yi masa girki. Kamar ni babban yarinya irina mai aji, kuma he will expect me to cook for him?" Ta ƙarashe maganar tana juya jikinta wanda hakan ya ƙara ba ta dariya sosai.
"Kin san Allah Anty Nahlin? Ni ko zan yi aure ba yanzu ba, sai na yi degree, master, and phd. If possible na fara aiki. Haihuwa kuwa, anya zan iya may be one."
"A tab! Lallai ko da yake yarinya ce ke, ƙuruciya ke damun ki. Amma dai ina gargaɗin ki da kar ƙi ɗauki ra'ayin riƙau, wato feminism da kuma iƙirarin da bature ya ke yi na. What a man can do, woman can do better. A ko da yaushe namiji shi ne a gaba. Kamar yadda littafin mu mai tsarki ya ce. So please ki cire wannan a ranki."
Taɓe baki ta yi ba ta ce mata komai ba tana skipping kallon da take yi. Ganin hakan ya sanya ta ci gaba da cewa,
"Ko mom da kika gani, a gidan aurenta ta samu wannan ɗaukakar, don haka ki cire wannan tunanin."
"Haba Anty Nahlin! It is just my ideation. Kuma planning to my future kike tada jijiyar wuya haka har da su kawo ya da wa'azi. Mutum fa na da ikon tsara wa kansa abin da yake so. Kum..."
"Ki gyara kalamanki domin mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba sai Allah, shi ne ya ke da ikon wannan Mudabbirul amri ne. Kin manta ko shi baturen cewa ya yi man proposed but Allah disposed?"
"Huhmm." Ta ce cikin guddurar kalamanta.
"It hasn't go to that. I just telling you as far as am concerned ne."
"Na lura sam ba kya son gaskiya halin ki ɗaya da Ummu Kursum ita ma ba ta son gaskiya. Ni kuma as World concerned na ke gaya miki."
"Anty Nahlin. You know what? Let me go to falo and watch film. Is like you don't need my accompany bye."
Dariya ta yi ta kama hannunta ta riƙe."Sorry sis, dawo ki zauna na daina."
Ba bu kunya ta zauna tana murmushi sai kuma ta fara zuba tana mata hirar celebrities wasu ko sanin su ba ta yi ba. A haka suka gama girkin bayan sun ci sun yi sallah, Jannah ta yi wanka tare da wucewa sashin Hajiya Baaba don ta canza kaya.Bayan ta gama suka ci abinci suka yi sallah.
Ta same ta zaune a falo tana shan fura. Gallah mata harara ta yi, tare da kai ludayin furan bakinta. Dariya ta yi tana faɗin,
Allah ya bar mini kakata." Sai da ta kammala shirya cikin riga da wando ta fito tana rolling ɗin ɗan siririn veil ɗinta.
"Hajiya zan je shopping me zan siyo miki?"
"Kin san an gaya miki, ki daina mini isakancin turancin nan na ki? Tun da ba ji na ke ba, in ba haka ba zan shuka miki rashin mutunci."
"Allah ya ba ki haƙuri. Siyayya za ni me kike so."
"Ban sani ba, umma ta gai da ashsha." Ta faɗa a ƙubule.
"To shikenan, sai mun dawo." A gajarce ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa.
Ganin da gaske take sai ta ƙwala mata kira ta ce."Dawo mana shalele, maimakon ki rarrashe ne sai ki tafi? Ni fa tsiyata da ke ba ki da kirki. Abu mai daɗi za ki siyo mini."
Dariya kawai ta yi ta fice sai da ta kai ƙofa ta ce.
"Sai jarabar faɗa da kwaɗayin tsiya."
"Abby ya fita da motarsa. Ammy kuma tana gurin aiki, sannan motar ya Ajmal ko da tana nan ta fi ƙarfinmu, nan ga ni, nan bari. Don haka dole mu shiga motar gida."
Kallon wulaƙanci ta yi wa motar tana yatsina fuska.
"Kai dole mom ta saya mini mota, ba zan iya wahala ba."
"Lallai aiko da wuya Ya Ajmal da Abby su yadda. Za ki shiga aji shida na sakandiri ne za ki rinƙa driving? Ki sani Nigeria ba kamar London ba ce."
Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarinn shiga cikin motar ganin Musa direba ya shiga ya kunna.
A shopping Mall sai da ta yi wa kanta ƙarƙaf sannan hankalinta ya kwanta don ta jido kaya masu tsananin kyau har Nahlin da Ummita ta siya wa sai Hajiya da ta siya mata ƙwalama.
Suna shirin fita daga mall ɗin ta hango wata doguwar riga mai tsananin kyau.
"Wow Anty Nahlin! Kalli wannan rigar ta tafi da ni, bari na duba app ɗina na palpay kamar ina da kuɗi na sayi rigar nan.
"Kai Jannah, na lura ke money monger ce, duk irin kayan da kika siya, amma ba su ishe ki ba?"
"Allah ta yi kyau ne." Ta ba ta amsa.
Hankalinta bai kwanta ba sai da ta sayi abayar suka je gurin biya. Tana ƙoƙarin transferring ɗin kuɗin ta ji muryar namiji ta bayanta ya na faɗin,
"Yauwa Mufid! Ma za ƙaraso yau Allah ya haɗa ni da ɓarauniyar da ta yi mini sata a filin jirgi." Ya faɗa yana tafa hannunsa cikin tsananin farin ciki tare da kallon abokinsa.
Da sauri ta waigo cikin tashin hankali take idanunta suka ciko da ƙwallah. Ba tare da ta san ta yarda rigar dake hannunta ba.
Kallonsa ta yi tana tunanin kamar sun taɓa haɗuwa don fuskarsa ya yi mata kama da wanda ta taɓa gani.
"Like I knew you before?" Ta furta cikin tantama.
Sai ya ɓata rai tare da kai key ɗin motarsa kusa da fuskarta kamar zai taɓa ta da shi.
"Ban sa ni ba, kin bar ni da tunaninki babu dare babu rana. Haka ma za ki ce mini? Alamun kin manta da ni." Ya ƙarashe maganar tare da ƙara ɓata fuskarsa.
War ta yi da idanunta domin ta gane saurayin da suka haɗu a filimg jirgi wanda yake yawan faɗo mata a ranta.
"Haba kyakykyawa understand me. I wanna build and development a health relationship between us.
A jiyar zuciya ta yi mai ƙarfi, domin tun haɗuwarsu ta lura da irin kallon da yake mata, amma ina sam ba ta shirya ba. " Na gane ka, buddy ne wanda muka haɗu a airport."
"Jannah ki zo mu tafi kin ga dare yana yi, kuma Ammy ta ce kar mu daɗe." Nahlin ta furta tare da kama hannunta suka shiga mota, ganin kamar zaƙewarta na kula shi ta yi yawa, duk da cewar ita ma ta gane shi.
"Jannah." Ya furta a hankali yana shafa gemunsa da wani irin tsadadden murmushi a fuskarsa. Ganin direba ya tada motar ya sanya ya rugo da gudu a gefen da take.
"Haba Jannah, kar ki zama mace mai son kanta. Tun da kika ga mun yi haɗuwa biyu tabbas a kwai ɓoyayyen lamari a tsakaninmu. Yanzu haka za ki tafi ba tare da na san inda zan gidanku ba?" Ya yi tambayar cikin marairaicewar fuska.
Kafin motar ta fara tafiya ta leƙo da kanta ta ce. "Jannah Jabir Ingawa." Ta ɗaga masa hannu tare da mayar masa da ƙayatatten murmushin da yake mata. Zuciyarta cike da tsananin farin cikin sake ganin buddy ɗinta.
"Jannah Jabir Ingawa da ma ita 'yar family ɗin ce?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki domin sai ya ce faɗuwa ta zo daidai da zama don a kwai abokinsa a family ɗin.
Sunan da ta faɗa mishi ya san ta faɗa masa ne akan ya yi searching ɗinta a social media don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ciro wayarsa tare da kunna data ya rubuta sunan wanda take ya fito masa har da ɗauke da hotonta tana riƙe da teddy.
Murmushi ya saki tare da rungume wayarsa domin shi kaɗai ya san tsananin farin cikin da yake ciki. A gurin ya tura mata da friend request wanda ko minti ɗaya bai yi ba, ta yi acceptin da tura mishi da stiker masu ɗauke da hoton abota. Sai ya ƙara sakin murmushin jin daɗi ya buɗe motarsa ya shiga tare da tada ta ya ja cikin farin ciki.
"Huzaifah." Ta furta sunan kamar yadda ta gani a rubuce. "Huhm! You are so humorous buddy."
Ganin murmushin ya ƙi ɓacewa daga fuskarta. Nahlin ta gyara maza tana kallonta. " Kamar shine saurayin da kuka haɗu a filin jirgi, kuma na ga kamar sonki yake? Ina gargaɗinki da karki faɗa tarkon namiji ki fara relationship at this age. Kin ga ko ni sai da na shiga Jami'a sannan ya Ajmal ya barni nake kula samari."
"Haba Anty Nahlin! Why all this questions and statements? Kar ki kai ni inda ban kai ba. Babu komai a tsakaninmu, shi ɗin abokina ɗauke shi."
"Humh." Ta ce sai kuma ta kalle ta tare da yin dariya. "Idan kin ɗauke shi ba aboki, shi ba'a haka ya ɗauke ki ba. Kin dai san soyayya ba ta ɓuy.."
"Then I will make him understand ok? Yawancin abokanan na maza ne. So banga komai ba."
"It is just a piece of advice." Cewar Nahlin.
"Thanks." Ta ce ta maida hankalinta kan wayarta tana reply ɗin messages ɗin da ya yi mata.
Mom zaune a kan kujera ta zabga tagumi yayin da idanunta suke cike da ƙwallah tana sauraren Fedris da take ta yi mata bayanin abubuwan da suke buƙata. Kuɗin Ƙasar ta ciro daga jakarta masu tarin yawa ta ije a kan teburin dake gabanta.
"Take this and if there is need of it, please contact me. I wanna leave this country tomorrow." Ta furta cikin muryarta mai sanyi tana gyara ɗaurin gyalenta. "Thank you ma'am and I wish you safe trip." Jinjina mata kanta ta yi sannan ta fice daga ofishin.
A ranar da ta dawo, sam ba ta fita ko ina ba tana hutun gajiya, har sai da ta yi kwana biyu. Sosai dad ya ji daɗin yadda ta dawo cikin farin ciki, domin ya samu sausauci a tsakaninsu, har da yi masa hira da ba shi labarin ɗubbin nasarar da ta samu, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba, ya rinƙa ji da ita.
Washegari da safe ta shirya zata fita tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta ya shigo ganin ta cikin shirin fita, ya sauya fuskarsa daga fara'a zuwa ɗaurewa.
"Haba Halima, kamata ya yi ace sai kin yi sati kafin ki fara fita, kina cika wa kanki aiki. Ki tausaya mini ni fa mijinki ne, kuma ina da haƙƙi mai girma akanki."
"Please Injiniya! Kar mu fara tun yanzu. Ba rayuwata ba ne? I have ambition and I want to do everything humanly to accomplish my goals." Lokaci guda fuskarta ta