Showing 123001 words to 126000 words out of 137802 words
Chapter 42 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
damu da ita ba. Matsalarta ɗaya rashin kunyarta da sangarta wanda ita kuma babu haƙuri take tunzurata.
"Saboda kun raina ni bani da mutunci shiyasa kuka daina kula ni don na haɗa auren da ba ku so ko? To wallahi bari kuji na gaya muku sai dai ku mutu. Ke Hafsatuu, ki yi addu'ar saurayinki ba tsotse ƙwallon mangwaro ya yi ya yar don ya huta da ƙuda ba, don yana wuce lokacin da ya iba babu neman shawara sai dai a lulluɓe ki a kaiki gidan duk wanda na aura miki. Ke kuwa Ummu-Kursumu da babu mashinshini, sai aukin iyayi da kininibi ki zuba idanu ki gani kar ki daina biye wa wannan shashashar, da ba ta san inda ke mata ciwo ba, wallahi kin jin rantse miki da Musa direba zan haɗa ki."
Wani irin ƙara suka saka saki hadda Jannah da ta ci magani jin abin da ta ce, wanda ya sa suka juya cikin sauri suna kallon Muda direba da yake goge motar Abby da sun bar shi yana shiri zai fita, yana ta washe naki jin abin da Hajiya Baaba ta ce duk da ya san da kamar wuya auren gurguwa nesa, don ya san ta faɗa ne don ta ƙuntata mishi, amma ina shi ga auren wannan zuƙeƙiya zankaɗaziya mai kama da matan aljanna, kuma da hakan zai faru ai sai ya ce tsuntsu daga sama gasshshe.
Ummu ta ƙara juwawa ta kalle shi taga yadda yake washe haƙora da suke gantso sai kawai ta sa kuka ta nufi shashin su.
Duk damuwar da Jannah take ciki sai da ta kwashe da dariya, a zuciyarta tana tabbatar da Hajiya Baaba, ta ƙai maƙura gurin rashin mutunci tun da ta haɗa ta da Musa direba, domin da ita ne ta tabbata sai ta kwana amai da ƙyanƙyani saboda muninsa.
Harara ta zabga mata tare da ɗaure fuska sosai ta bi Nahlin da ta koma rarrashin Ummu ganin tana kallonta, wanda Hajiya ba ta ce mata komai ba sai ido da ta bita da shi tana mamakin ramar da yi, ganin yadada ta koma kamar waccce mayu suka kama.
"Innalillahi! Dubi yadda ta koma sai kace ƙashi. Oh ni jikar mai gishiri, wanann rama haka to mai angon zai samu anan dama ba auki ba? Ga shi mara mutunci ne da na haɗa mata abubuwanda za ta cika kafin bikin."
Duk ita kaɗai take tunanin zuci har suka fito suka wuce wanda ƙarar buga get ɗin gidan ya fargar da ita.
Miƙewa ta yi ta ɗauki kujerarta ta koma ciki ganin ta isar da abin da take son faɗi, domin shi ya sanya ta zauna kawai don ta jira fitowarsu.
Ganin da gaske bikin za a yi mom ta kama siyayyan kaya na hauka, domin zuwa lokacin komai an siya hatta kayan furnitures ta siya masu kyau da tsada.
Dad, shi ma ya yi nasa bajintar sosai don kuɗi maƙudai ya bawa mom duk da ta nuna bata so, amma ya kafe saboda yana son ya yi mata bajinta.
Ta fannin ango kuwa har ya manta da wani maganar biki, domin tun da Aby ya rararshe shi kan cewar zai samo matifa, ya manta komai ya ci gaba da sabgoginsa don haka babu wani shiri da yake yi.
Jannah ma ba ta ƙara maganar auren duba ga yadda Hajiya Baaba, ta fita daga sabgarta kan maganar bikin burinta a koma makaranta su ci gaba da karatunta, wanda take ganin a yanzu ba ta da abin da yafi karatun duba ga yadda iyayenta suka yi watsin karan mahaukaciya da ita.
Hajiya Baaba, babu zama an saci zanin ɓarawo, saboda kullum ranar duniya sai ta je kasuwa ta yi siyayya, domin kashe kuɗi sosai take kan maganar auren. Maganarta kullum dole ta yi abin bajinta da gyarata saboda gidan kishiya za ta. Sai dai, duk abubuwan da take yi, ta kasa yi wa amaryar maganar ta zo a gyarata sai rara gefe take yi, amma babu fuska wanda ganin haka ya sanya ta bari sai mom ta zo.
Lokaci dai baya ƙarya domin a yadda aka sanya ranar ya rage saura wata ɗaya cif.
A ranar da ya rage wata Hajiya Baba, ta sa rigima tun da asuba ta fara magana cikin ɓacin rai.
"Ai wallahi, Muhammadu, ka bani matuƙar mamaki saboda karka manta Jannatuu, yar Halima ce. Kana bin uwarta a gindi-gindi, amma na bawa ɗanka 'yarta ka ƙi maida hankali akan maganar bikin, saboda ita uwarta samu kake da ita, ita kuwa ɗanka hidima zai yi da yarta."
"Ashsha! Don Allah mai ya kawo maganar nan? Na ga an riga an saka rana, to mene ne na ƙorafi akai?"
"Babu Muhammdu, mai zai san ya na yi ƙorafi kan maganar auren babu ai ko? Sai dai, in dai ƙorafin da na saba, domin na sani a gidan nan, kowa kirana yake da jarababbiya."
Dafe kansa ya yi ya rasa bakin magana saboda shi kansa bai san me zai faɗi ba. Yana matuƙar tsoron wannan haɗin aure da za ta yi, amma ya rasa inda zai ɓullo, saboda hatta Ajmal tsoron yi masa maganar auren yake yi, kuma ga dukkan alamu mom ta yi na'am da auren duba da ba ta taɓa masa ƙorafi ba sai ma kiransa da ta yi kan maganar shirin bikin.
"Hajiya Baaba, in kika ce za ki ci gaba da irin waɗannan maganganun za ki iya raba zumuncin dake tsakaninmu musamman ta wurin yaran."
"Na lura kamar so kake kace kowa ya kama harkar gabanshi a dalilin auren nan ko Muhammadu?"
"Ba haka nake nufi ba ina dai tunatar miki maganganunki zai iya kawo naƙasu a zumunci."
"To ina ruwana domin in baku yi ba kwayi shi a ƙiyama."
"Yanzu mai kike so game da auren?" Ya tambayeta cikin takaici yana ƙoƙarin ɓoye damuwarshi.
"Na ga ai Jannatun ba kaza ba ce da har yanzu ba a fara shirye-shiyen aurenta ba, a lokacin da zai yi wancan uren saura wata ɗaya da kwanaki gidanan ya far kacamewa, amma ita saboda ba kwa sonta babu maganar akwati da hidimar biki, kamar wanda za a aura masa yar baben roba."
"Ki yi haƙuri yau za a fara kuma zamu yi maganar da Ajmal yau in sha Allahu."
"Ka kira shi yanzu ka gaya masa ko na je har gidansa mu yi maganar a gaban matarsa, kuma ka san halina in yaso sai ta yi tsirensa."
Wayarsa ya ɗauko ya danna numbobinsa."Bari na yi masa bayani Hajiya Baaba, don Allah ki bar ni na shiga ciki mu yi magana ta hankali." Y ace cikin marairaice fuska.
"Kun dai ba ni wallahi ku haifi yaya da cikinku kuna jin tsoronsu." Ta ce tare da sakin tsuka ta bar gurin wanda ya yi sororo tamkar mutum mutuni.
"Hello Aby, mun tashi lafiya?" Ajmal ya furta cikin girmamamawa, bayan ya ɗauki wayar wanda ya tunatar da shi kan kira yake.
"Ajmal, in har nina haifeka ka aminta da auren Jannah, kuma ka fara shirye-shiye saura wata ɗaya."
Jikinsa ne ya mutu murus ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi yana tunanin abin da zai ce masa, amma sai ya ji ya kashe wayar cikin huci, wanda hankalinsa ya maƙurar tashi domin ya san in Aby ya yi fushi ya gaya masa magana cikin fushi dole ya bi.
Zama ya yi cikin motarsa yana jinjina lamarin, yayin da damuwa suka haɗu suka yi masa rubdugu har ya rasa ta inda zai fara saboda ba zai iya kallon Mushirat ya samar mata da auren sa ba, haka zalika ba zai taɓa kallon Jannah a matsayin matar aurensa ba.
Wani irin juya ya ji yana ƙoƙarin kamasa wanda ya yi sauri ya zauna tare da dafe kai, domin ya san cewa da ga ranar da aka aura masa ita ya yi bankwana da farinciki a rayuwarsa.
Wata dubara ta faɗo masa wanda da sauri ya ɗauki wayarsa da ya sanya caji a cikin mota ya fara ƙoƙarin neman numbar mom, duk da ya san cewar alfarmar da zai tambaya tana da matuƙar tsauri da rashin kirki, domin ko wace uwa ba za ta ji daɗi namiji kamarsa mai haiba ya kira ta ya sanar mata da baya ƙaunar 'yarta tare da roƙon alfarmar a janye auren ba, amma domin farincikinsa dole ya yi hakan don ba shi da zaɓin da ya wuce wannan.
Ringin biyu ta ɗauka cikin sakin fuska tana jin wani irin girmarsa da nauyinsa ya kamasa.
"Hello Ajmal, kamar ka san ina son kiranka yau ɗin nan fa."
Gabansa ya buga jin tana buƙatar kiransa wanda bai san akan mene ne ba.
"Barka da safiya Mom." Ya ce cikin rashin karsashi yayin da yake ƙoƙarin nemo kalmomin da zai yi magana da su a bakinsa, amma sai ya ji tamkar bai iya magana ba, domin ji ya yi kalamansa sun ɗauke ɗif."
"Ka yi shiru are you on the call?" Ta ce jin shirun ya yi yawa.
"Eh mom."
"Ok, dama akan maganar auren ku ne da Janaah, ka san lokacin aurenka na farko na yi maka lefe haka na Jannah ma, sannan maganar ɗakin da za a sanya kaya na gama danki kawai ya rage."
Wani irin tashin hankali ya ƙara riskan shi jin yadda ta ɗauki auren domin zaƙewarta ya yi yawa sosai.
Take ya ji ya kasa iya roƙonta wanda kuma in har ya yi haka ya cutar da kansa, don haka ya yi namijin ƙoƙari ya buɗe bakinsa don kar ya cutar da kansa, wanda kamar ta san abin da yake shirin roƙo ta rigasa ta da cewa,
"Yauwa sai magana ta biyu Ajmal, kan aurenku ne, don Allah ku zauna lafiya ban damu da duk abin da za ka yi mata ba, matukar za ta zama na ƙwarai, saboda na san cewar na yi sakaci a rayuwarta, a ka ga abu uwa saɓanin hankalinka ka yi haƙuri la ladabtar da ita, domin zan so hakan ta gane rayuwa ba irin wacce take ciki ba."
Ta yi shiru ko zai ce wani abu amma si ta ji ya saki naunayar ajiyar zuciya ba tare da ya ce ƙala, domin ji yake maganar da take kamar ta ɗauki dutsen dala ta ɗora masa.
"Ba ka sonta na sani domin duk macen da yake da mace kamar matarka babu abin da zai iy da ita, kuma na san Hajiya Baaba, dole ta yi maka, amma ina roƙon don Allah ka aureta ka nuna mata rayuwa, a cikin rayuwarta babu wansa take tsoro sai kai na san nauyi zan ɗora maka, amma don Allah ka yi wallahi ko duka dunkiya kake so zan baka matukar watarana Jannah za ta fahimci gaskiya ta soni ta zama ta ƙwarai. Ta so ni ta nuna mini ƙauna ta gane nice wacce na fi ƙaunarta fiye da kowa a duniyar nan." Sai ta fashe masa da kuka soasai wanda ya karyar da duk wani karsashi da gabbobin jikinsa har ya ji shima ya na son ya rushe da kuka na ƙarfa-ƙarfa da ake ƙoƙarin yi wa rayuwarsa.
Ya kasa cewa komai kuma ya kasa rarrashinta da take kuka, tamkar ranta zai fita wanda jin haka ta kashe wayar tana ji a ranta bahu daɗi domin a yadda ya yi ta san cewa ba ya so kuma baya ƙaunarta.
Ya kasa tuƙi sai ya kifa kansa a saman sitiyarin yana jin yadda zuciyarsa take tafarfasa da zillo tamkar za ta fito waje.
"Innalilahi wa inna ilahir raju'un! Tabbas Hajiya Baaba, kin shiga rayuwata, domin ban san yadda zan yi na yi adalcin zama da wacce ba na ƙaunarta, bayan ina da macen ƙwarai wacce ta gama siye zuciyata har ma da gangar jikina. Ya Allah ka kawo mini ɗauki." Ya furta a bayyane tare da sakin wawan ajiyar zuciya mai ƙarfi, zuciyarsa cike da tunanin shikenan yanzu ba shi da zaɓin da ya wuce na aminta da auren?
"Jannah, daga yau za ta koma sashina domin kin san bikinta ya rage saura kwana talatin cip, ya kamata a fara gyarata ba sai lokaci ya ƙure ba." Hajiya Baaba ta furta ba tare da ta kalli Jannah da take zaune fuskarta a turbuɗe tun sallamar da ta yi.
"To shikenan, Hajiya Baaba, sai ta koma Allah ya taimaka." Ammy ta furta cikin muryar sanyi.
Harara ta doka mata ba ta ce komai ba tana kallon Jannah da take aika mata da na ta tamkar idanunta tamkar za su faɗo.
"Ke, ba na son iskanci ki wuce mu tafi tun kafin na sanya Musa direba ya zo ya yi miki ɗaukar dawa."
"Babu inda zani kuma ba zan sha komai ba. Ai ni da ɗakinki ba zan ƙara shig ba."
"Shikenan, ba zan yi miki dole ba bari uwarki ta zo in ta kasa saki dole kije kice baƙinciki zai kashe kina ji kina gani a fifita kishiyarki."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 34-35*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Shi ɗin banza da zan damu don ya so wata fiye da ni, dama an gaya miki na damu da ya so ni ne. In ya so ya haɗiyeta ko a kwalar rigata don da shi da banza duk ɗaya." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Ammy ba da take tsaye tana jinta wacce ba ta ce mata komai ba sai kallonta take.
Shiri gadan-gadan aka fara yi wanda ya ta da hankalinsu matuƙa, musamman Ajmal da ya rasa yadda zai yi ya sanar mata domin inya kalleta sai ta ba shi tausayi, ga shi bai san yadda za ta ɗauki zancen