Showing 81001 words to 84000 words out of 137802 words

Chapter 28 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

da take tsaye tana magana cikin tsananin fushi.




"Har kana da bakin faɗin haka? Bayan kaine sanadin da ya sa na baro Ƙasata nake rayuwa cikin kewa da ƙunci. And now you have the audacity to say that to me?" Ta dasa aya da tambayar haka sai kuma ta ja tsuka ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki.




"Please am sorry, I exceeded my boundaries. Perdon me, I couldn't do it again, but you know the way we raised her wasn't the right way, we should have inculcated good morals to her."




"Is fine ya wuce, amma yanzu bai kamata mu tsaya wannan maganar ba, mun riga mun yi kuskure. Maganar auren ta ya ke damuna, I really don't know what to say."






Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093








KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 22-23*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM





"Ina ga we have to sleep on it. Kin san ta don haka mu yi gaggawar komaw.."




Bai ƙarashe maganar ba kiran Jannah ya shigo wayarsa, sai suka kalli juna a tare. Zuciyar mom cike da jin daɗin ba ita ta kira ba, domin ta san sai ta gaya mata maganar da za ta kasa bacci da kuka.




"Hajiya Baaba ta kira mana ruwa fa." Ya faɗi daidai lokacin da mom ta yi hanyar ɗakinta da sauri tana faɗin,




"Ba ri na shiga ɗakina sai ku ƙarata can ba zan iya da rigimarta ba."




Cikin sanyin jiki ya sanya wayar a kunninsa bayan ya yi sallama. wanda ko sallamar ba ta amsa ba ta fara faɗin,




"Dad, could you imagined wai ni Hajiya Baaba, said that she will gonna give my hand in marriage to Ya Ajmal, as young as I'm, wallahi I really hate him cus he is not civilized at all." Ta ƙarasa maganar tana ƙuta.




Shiru ya yi don ya rasa me ze ce mata sai ya tsinci kansa da faɗin,"Never and impossible! Sam ba zan taɓa miki auren dole ba, kuma ba za ki yi aure yanzu ba sai kin cika burinki."




"Haba! I wander, ai dama na san wasa take yi mini domin ba za ka taɓa yadda ba, amma sai ta ce mini wai you are so greedy you most agreed." Ta katse shi tana faɗin haka.



Maganar ta soke shi har sai da ya rintse idanunsa, yana jin zafi a ransa ba tun yau ba ya san ta tsane shi ba ta son shi, musamman lokacin da lamarin ya faru abubuwa suka rikice."




"Kar ki damu ki kwantar da hankali ki saurari dawowarmu, muna dawowa za mu koma gidammu."




"Ai dama ban damu ba, kawai she is pestering me, shi ya sa na ga I have to give you a call, duk da na san shi doesn't has authority on me. Please dad take care you of youself I love you." Ta kashe wayar tana murmushi.




Kalmar da ta faɗi suka rinƙa masa kuwwa a kunninsa sai ya dafe kansa cikin jin tausayinta.




"Ba ki san wace ce Hajiya Baaba ba, domin ba ki da mafita da ya wuce auren nan."






Jannah ta sauke wayar tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi ta kalli Nahlin da Ummu da suka yi zugum ta ce,"Da ma na gaya muku wallahi ba ta isa ba. Haba ita ɗin wa, don kawai ta haifi mom sai ta ce za ta juya kowa."




Miƙewa suka yi suka kalli junansu sannan suka shige ɗaki ba su ce mata komai ba, wanda ganin haka ya sa ta taɓe bakinta ta nufi sashin Hajiya Baba fuskarta a ɗaure babu ko walwala.




A falo tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinta daidai lokacin da ta fito daga bayin falon da abu ƙulle a baƙin leda da ƙatuwar roba a hannunta.




"Yauwa Jannahtu zo nan, dama yanzu zan sanya a yi mini kiranki, saboda tun yau zan fara miki wankan lalli saboda babu lokacin, don zamaninmu biki tun yana kusan wata bakwai ake farawa wa, ga shi ke duka ba za a sanya da nisa ba don ba zai wuce wata uku ba, don haka gara mu fara tun yanzu."




Har ta murɗa ƙofa za ta shige ɗakinta duk da ta ji kiran amma kuma sai ta fasa jin abin da ta ce.




Idanunta ta waro mata cikin ɓacin rai daidai lokacin da ta ƙaraso gabanta tana juya ruwan lallin da hannunta.




"Kin ganshi lalli ne mai kyau daga barno aka kawo mini shi ina ƙunsawa, yanzu dole na yi waya a kawo mini buhu don sai ya ƙare kafin bikin." Ta sa aya tare da ibo ruwan lallin za ta goga mata a fuska, wanda ya sanya ta matsa da sauri tana kallon shi kamar kashi tare da toshe hanci.




"Kin san Allah Hajiya Baaba, kar ki kuskura ki watsa mini wannnan abu mai kama da kashi a jikina, kuma ki bar maganar auren nan you are hurting my feelings, bana so."




"Dukana za ki yi? Ke fa daɗina dake ba a miki abin arziki kina sane da gidan kishiya za ki sai kin sha gyara kar kije ki zama mowa."




"Na ga alama kin taɓu sai an kai ki gidan mahaukata, ƙila kuma aure kike son yi sai ki samo bazawari tsoho, na san su mom ba za su hana ki ba."




"Kiji mini tsiya ni kike faɗin ma haka? Aure ko a lahira na haƙura da shi in dai ba Aminu masoyina za a ba ni. Ki kalli tsabar idona kice mini na taɓu, bari na nuna miki haukar."




Kawai ta ibo ruwan lallin mai yawa ta watsa mata a jiki har da fuska, wanda sanyin ruwan lallin ya shigeta sai ta ƙwala ƙara da ƙarfinta har sai da gidan ya ɗauka, wanda ya sa duka mutanen gidan suka sheƙo.




"Mutane za ki tara mini don ubanki daga miki abin arziki?"Ta tambayeta tare da toshe kunninta domin ƙarar ya shige har ƙwaƙwalwarta.




"Wallahi sai Allah ya saka mini da kika ɓata mini rigar da Huzaifah ya ce tafi kowane kaya yi mini kyau." Ta ce daidai lokacin da mutanen gidan suka ƙaraso a guje.



Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru?" Aby ya tambayeta cikin tsananin razana yana kalon Jannah da ke kuka shaɓe-shaɓe.




Ba ta ba shi amsar tambayarsa ba ta buge mata baki tana faɗin,




"Da maganar wani a kanki kike kiran wani gardi? To me ya rage tun da na riga na tambaya masa kawai auren ya rage, ga sadaki a hannuna yanzu ma zan iya bayarwa"






Sai kuma ta kalle su da suka yi jugum-jugum suna kallonta.




"Au kuji mini ja'ira dama kin yi ne da biyu don ki tara mini mutane?" Sai ƙara kallon Aby da yake jin damuwar zuciyarsa ta fi ƙarfin ƙwaƙwalwarsa ta ce,




"Ni da wannan da ba a mata abun kirki don kawai zan fara mata wankan lalli, shi ne take ci mini mutunci har tana kirana da mahaukaciya shi ya sa na nuna mata ƙarshen haukar. Da yake ita shashasha ce, ba ta san inda ke mata ciwo ba, ai ban gyarata a kwai matsala, tunna gidan kishiya za ta amma tana mini rashin mutunci, ai dole na fara gyarata ta zama mowa ko?"




Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallonsa wanda takaici ya hana shi cewa komai sai dai ya ɗaga mata kansa kawai ya fice yayin da sauran suka rufa masa baya.






Jannah ta galla mata harara za ta bi bayansu wanda da sauri ta janyo rigarta ta dawo da gabanta tana faɗin," Da wo nan babu inda za ki aini da ke mutu ka raba don ko auren aka yi, mutane na watsewa zan tattara inawa-inawa na dawo gidan.




Hannunta ta fisge ta gallah mata harara ta yi cikin ɗakinta tare da bugo ƙofar kamar za ta ɓalla.




"Allah Sarki kofa, ba ita ta kar zomon ba rataya aka ba ta." Ta juya ta shige ɗakinta tana mita.



Cikin sanyin jiki yake tuƙa motar tamkar wanda aka zarewa lakka har y isa gida ya yi hon.



Maigadi ya taso ya buɗe masa yana jiran ya shigo da motar, amma sai ya fahimci ya yi nisan kiwo, domin bai san ya buɗe ba. Tunani ne barkatai a ranshi wanda ba shi da hanyar ɓullo musu.


Rintse idanunsa ya yi yana jin tsananin tsanarta yana ƙara samun matsuguni a jikinsa, don sai yanzu ya gane dalilin tsanarta da ya yi matuƙa, saboda tun da ta zo ya kalle ta kwata-kwata ba ta yi masa ba.
Ganin ya yi nisan kiwo ya sanya maigadi ya bubbuga gilashin motar wanda ya sanya ya yi firgigif kamar mai bacci.




A hankali ya shigo da motar kamar baya son shiga gidan daidai lokacin da Mushiirat ta fito da dogon hijabinta har ƙasa da carbi a hannunta tana ja.


Jim ta ɗan yi tana kallon yanayin fuskarsa kafin ta ƙarasa gurinsa.




Kamar yadda suka saba duk lokacin da ya dawo sai ya miƙo mata hannu sun yi sallama suna sakar ma junansu murmushi sannan ya yi hugging ɗinsa. Sai dai, yau ita ta fara miƙa masa tare da kwanciya a jikinsa.




"Barka habibina, you took more than the time you said." Ta ce cikin shagwaɓa tana shafa gefensa da ya sha gyara sai ɗaukar ido yake.




"Am sorry." Kalmar da ya iya furtawa kenan sai ya matsar da ita daga jikinsa zai shige cikin falon cikin rashin ƙwarin gwuiwa, saboda wani irin tausayi da ta ba shi.


Ta bishi da kallo har ya shige wanda hankalinta ya yi matuƙar tashi sosai take ta fara tambayar kanta lafiya, amma rashin masa ya sanya tabi bayansa lokacin da ya shige ɗakinsa.


"Bab, what's wrong, are you alright?" Ta tambaye shi lokacin da ta rufe ƙofar tana ƙarasowa gurinsa.


"Yes I'm, kamar kaina yake son ya yi ciwo bari na watsa ruwa. May be I will better." Ya ce tare da miƙewa zai shiga bayi ba tare da ya kalle ta.




"Oh no please, yaushe muka fara ɓoye abin da ke damunmu a tsakaninmu? Don Allah ka gaya mini na shiga damuwa." Ta ce tare da riƙe hannunsa.




"Na ce miki kaina yake ciwo." Ya faɗa murya a kausashe yana ƙoƙarin shigewa.




Da sauri ta tari gabansa tana kallon idanunsa."Gaskiya ni ba zan yafe wa kaina ba, matuƙar ban ɗauke maka damu.."




"Ke!" Ya daka mata tsawar da ta firgita ta, wanda ya sa ta saki hannunsa da sauri ta matsa gefe tana zare ido don har hawaye ya fara sauka fuskarta, saboda za ta iya rantse wa yau ne farko da ta ji ya daka mata tsawa.




"Haba na gaya miki babu komai, amma you keep asking let me be." Ya ce tare da ƙarasa shiga cikin bayin.




Sharaf ta zauna a gefen gadon tare da saka kuka, dama tun da take kiran wayarsa bai ɗaga ba ta san akwai abin da ke faruwa. Lokaci guda ta fara tunanin abin da zai iya ɓata masa rai haka ya kauda ɗoki da zaƙuwar da yake ta yi ya dawo sun kasance a tare.




Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin ta nufi na ta tare da mayar da ƙofar ta rufe. Bayi ta shige ta ɗauro alwala ta fito har ta zauna a ɗakin za ta fara karatun kur'ani, sai ta miƙe ta fasa karantawa a ɗaki ta koma falo.




Ganinsa zaune da kur'ani amma ya kasa karantawa ya sa ta ji matuƙar haushinsa, domin ya karya alƙawarin da ya yi mata na cewar duk abin da yake damun ɗayansu za su kashe su rufa.




Zama ta yi akan kujera maimakon inda yake zaune wanda ya ware don karatu wanda ya ke cike kur'anai da littafan addini.




Cikin murya mai sanyi ta shiga rera karatu da ƙira'ar hafsi, yayin da wani lokacin take satar kallonsa da ya riƙe kur'anin ya lula duniyar tunani.




Idanunsa suka canza tuna maganar auren da Hajiya Baaba take son ƙababa masa na yarinyar da sam ba ta dace da rayuwarsa ba. Da ya kalleta yadda ta kame tana karatu cikin natsuwa sai ta ba shi tausayi, domin ya san duk inda macen ƙwarai take ta kai saboda duk da kasancewarta nurse bai taɓa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login