Showing 9001 words to 12000 words out of 137802 words
Chapter 4 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
ce, "Ma’am, lunch is ready."
Yamutsa fuska ta yi tare da ɗan jan tsuka ta ɗauki wayarta tana duba time. "What’s for lunch?"
"Supaghetti." Ta ba ta amsa.
"May be I will eat later, as I’ve lost me appetite." Ta ce ba tare da ta kalle ta ba, sai ma ɗaukar wayarta da ta yi ta kwanta a kan gado.
"Please, you know your condition; you hav.."
"I said I will eat later! So please excuse me." Ta daka mata tsawar da ba ta san ta yi ba, domin Rose tamkar uba take a gurin ta don kular da take mata sam ba ta samun sa daga mom.
"I’m sorry, Ma’am!"
Ta faɗa cikin girmamawa tare da juya wa ta fice da sauri har tana haɗawa da gudu, sai kuma ta ji sam ba ta kyau ta ba.
Mikewa ta yi daga inda take ta buɗe wardrobe ɗinta tare da ɓalle Amitriptyline ta watsa a bakinta tare da komawa ta kwanta tana jin yadda kanta yake juyawa tamkar ana murza sitiyarin motar da a ka ƙure mata maleji take shararar gudu a saman titi.
A hankali ta fara jin kanta na saituwa zuwan can, maganin ya fara aiki wani irin ɗauyayyar bacci ya ɗauke ta.
Rose ba ta ji gargaɗin da ta yi mata ba kamar yadda ta saba, bayan ta ba ta ɗau lokaci ta shigo. Ganin ta kwance rigingine ta ɗora filo a fuskarta, sai ta yi matuƙar ba ta tausayi.
A hankali ta isa gare ta tare da gyara mata kwanciya, yayin da ta ji hawayen tausayinta na bin ƙuncinta. Ita kam ba ta taɓa ganin mace wacce ta fifita neman kuɗi da taimakon al'umma a rayuwarta ba. Tsananin tausayinta ya ƙara kamata domin ta san she is depressed. Hannunta ta sa ta janye mata gashinta da ya zubo a fuskarta. Mikewa ta yi da sauri ganin ta juya tuna gargaɗin da ta yi mata, amma sai ta ga ta kama hannunta ta riƙe tare da faɗin, "Momiii." Cikin magagin bacci.
Ba ta tashi ba sai bayan kiran magariba sannan ta miƙe. Wanka ta yi ta fita neman abinci ba tare da ta damu da sallah ba don yunwa take ji matuƙa don haka ta bari sai cikin dare in ta tashi karatu ta yi sallah har da isha'i.
Sai bakwai saura ta shigo cikin gidan da waya a kunninta tana waya. Dad da ya rigata dawowa ya shiga ɗakin Jannah sai ya ga tana bacci don haka ya zauna a falo bayan ya ci abinci ya kunna news.
Ɗaga masa hannu kawai ta yi lokacin da take cire takalminta da gyalenta, wanda Rose ta karasa kan kujerar da sauri ta haɗa da laptop ɗinta da ta karɓa.
Ido kawai ya bita da shi har ta shige ɗakinta. Duk yunwar da take ƙwaƙaƙularta kasa cin abincin ta yi, wanka kawai ta yi sallah sai bacci.
Ba ta tashi ba sai goma da rabi a lokacin Jannah har ta ci abinci tana zaune da littafi tana karatu wanda ya zamar mata ƙa'ida kafin ta kwanta. “Jannah, ya kike, kin ci abinci?"
Sai ta kalle ta sheƙeƙe cikin tsananin mamakin kalaman da ta furta wanda ta tabbata subutar kalami ne. "Oh please, Mom! since when do you care whether I eat or not? Da ma dai karatu kika tambaya as usual."
Kauda tambayar ta yi ta hanyar komawa ta zauna a gefen Dad tare da ɗaukar laptop wanda hakan ya ƙara baƙanta ransu matuƙa da sauri Jannah ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta dad ya kalle ta da takaici ya ɗauki wayarsa ya nufi nasa ɗakin. Tsayawa ta yi da aikin da take yi, ta raka su da ido har suka shige, sannan ta maida hankalinta kan aikinta tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi.
__________
NIGERIA
A hankali ya ƙarasa gaban madubin dake gabansa, ya ɗauko wani sanyayar tureren da tun kafin ya buɗe wani irin sihirtaccen ƙamshi yake tasowa daga cikin kwabar. Sai da ya kusan daƙiƙa talatin yana riƙe da kwalbar tureren yana shaƙa idanunsa a lumshe, a rayuwarsa babu abin da ya fi so irin turaren apple, shi ya sa ko da ya je ƙasar cairo raka Daddy, babu tsarabar da ya yi wa kansa sai kwalaben turaren.
Bayan ya gama shaƙar ƙamshi ba don ya ishe shi ba, sai dakin babu lokacin da zai ta shaƙar ƙamshin, sakamakon fita shi da amininsa Ridwan da zai raka shi gurin buduwarsa.
Ɗan ƙaramin tsaki ya ja tare da janye yarfe hannunsa ya zauna akan saman madubin yana ƙarewa ƙawataccen ɗakinsa kallo. Kusan kimanin daƙiƙa bakwai ya ɗauke idanunsa tare da tsuka mai sauti.
"Na rasa mai yaran nan suka raina ni." Ya yi maganar tamkar wanda ya ke tambayar kansa da tsabar takaici ƙarara a fuskarsa.
A zafafe ya miƙe ba tare da ya ɗauki wayarsa da take kan gado ba zai fice, sai dai kiran da ya shigo cikin wayar ya sanya shi dawowa da sauri ya ɗauki wayar domin ya manta da ita.
A tunaninsa amininsa ne ya gaji da kiran sa, amma jin kiran wayar ya tabbatar masa da wannan natacacciyar tsohuwar ce, wacce ta ƙi mutuwa mu ci gumba kamar yadda yake tsokanarta. Ya san uzurin ta ne ya tashi ya sanya ta kira shi, don haka ya ƙi ɗaukar wayar ya juya cikin ɗakinsa don ya rufe sashinsa ya fice ba tare da ta sani ba, ballantana ta ɓata masa lokaci da suruntunta na marasa kan gado.
Lokaci guda ya ji ransa ya ɓaci a dalilin kiranta, duk da cewar shashinta ya yi ninyar zuwa domin ya shuka wa yaran gidan rashin mutunci don ya yi ninyar dukannin su sai ya yi musu wanka da ruwar sanyi duk da irin hunturun da ake yi, amma da ya tuna ba kanwar lasa bace domin zai ita cewa a tarihin rayuwarsa bai taɓa ganin mace mafaɗaciya ba irin Hajiya Babaa, in tana faɗa har wani girgiza take kamanninta na canzawa.
Don haka ya fasa ɗaukar motarsa ya fice gidan cikin sanɗa ba tare da ya bari kowa ya gan shi, duk da cewar bai sai Ammy ɗinsa na tsaye a gefen windon ɗakinta tana kallon fitarsa, duk da cewar ba za ta yi masa magana ba. Murmushi kawai ta yi tare da sakin labulen tana girgiza kai don ta san dawan garin.
Hajiya Babaa da take ta famar kiran Ajmal baya ɗauka, tsaki ta ja ta janyo farin gilashin dake cikin gidansa ta maƙala a yar takurarriyar fuskarta da ta fara nuna tsufa da manyanta, sai dai daular da take ciki ya hana bayyana hakan ƙararar.
"Ɗan ƙwal’uba! Ja'iri wanda bai yi gado abin kirki ba sai tsiya da muskilanci irin na wancan mara mutuncin uwar tasa, mai kama da tsinƙe ana bata abinci, amma babu amfani. Dama ina zai ɗaga wayata ya raina ni bani da amfani a gurin sa. Ke Nahlin kike ko Hahl."
Ta ja tsuka ta ɗora cikin ɗaga murya. "Ku yi ta saka wa kanku sunaye masu wahala da sunan wayewa, ƙila sunan aljanu aka saka miki, domin tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin sunayen nan ba, ko acan karkararmu."
Ta ƙarashe maganar tare da ɗauko robar lacasera da take sha, sannan ta ɗauko ɓallin goran da ke kan gefen kujerar da take zaune, ta gutsira tare da jefawa a bakinta.
Hakan ya sa Nahlin ta ji cikinta ya yamutse wani irin amai ta ji zaizo mata, tun tana yarinya ta tsana sai dai babu yadda zata yi, domin ko da ta ƙauracewa shashin kan dole ta dawo, saboda ƙorafin da Hajiya Baaba ta kai wa daddy cewar yaran suna ƙyamarta. A dalilin haja Aby ya yi faɗa tamkar zai zane su. Don haka ta kauda kanta tana jin wani irin amai na taso mata.
Ba tare da Hajiya Baaba ta damu ba, ta kauda kanta tana tauna goron duk da cewar ta ga yadda take wani yatsina, amma ta riga ta saba musamman Ajmal wanda ya sha amai akan hakan, sai dai babu yadda za su yi da ita, domin ta zaman musu ciwon ido nan gari nan bari.
Nahlin ta miƙe da sauri zata bar ɗakin amma sai Hajiya Baaba ta yi kiranta tare da cewar. "Iskancin ya tashi kenan ina kiransa ya ƙi ɗaukar wayata, Allah ya shigo da shi lafiya zai same ni har cikin ɗakina." Ta ƙarashe maganar tare da jefa sauran ɓallin goron a bakinta. Sai kuma ta kalli Nahlin dake riƙe da murfin ƙofar falon zata fice ba tare da tace maka ƙala ba.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
*KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 4-5*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ciikin ƙufula ta ce, "ke dalla ja'ira ki karɓi wayar nan kira mini ɗan banzan yaron nan ya siyo mini madarar shanu, yau ba ni da wanda zan sha fura, kuma Faɗuma bata kawo mini ba."
"Ni dai Hajiya Baaba in dai ba za ki iya kiran sunana daidai ba, ki faɗi ainihin sunana, haka kawai ki rinƙa ɓata mini suna." Bata amsa tare da juyowa da sauri, sakamakon da har ta saka ƙafarta a waje.
"Ungo nan! na ce ungo nan, mutuniyar banza kawai." Ta ja numfashi tare da gyara zaninta sannan ta ci gaba da cewa, "zagi na kike mara mutunci! Ni za ki yi wa rashin mutunci kan na zagi wannan uwar taki mai baƙin hali.”
Nahlin ta karɓi wayar cikin ƙunƙunai jin abin da tace. "Daɗin abin Ammy ba liability ba ce tana da abin yi, don haka rashin ƙibarta ba zai saka ya zama aibu ba, kin san ko babu Aby zata iya ɗaukar hidimar gidan nan har da ɗawainiyarki." Ta ce tare da ci gaba da ƙunƙunƙunanta.
"Barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe. Ai dama hali gado ne, amma ba ki gado ɗana ba, Allah dai ya raba mu da gadon baƙin hali. Ki gaya mini magana son ranki mahaifinki zai dawo." Shiru ta yi ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta miƙa mata wayar.
"Ƙin miƙa mini waya ba ki ce komai ba za ki fice ga jarababba ta fara ko? To maza dawo ki zauna yau sai mahaifinki ya dawo sai na ga in shi ya ɗaure miki gindi."
"Wayarsa a kashe yake."
Tsaki ta yi tare da galla mata harara da fici-ficin idanunta da suke cike da rigimar tsufa. "Babu komai tun da ba za ki yi mini ba, bari na kira uwarki daɗin abin uwarki ta yi karatun boko kin ga ba za ki yi mini rashin mutunci ba, don ban yi boko ba sai na sanya ita ko mai aiki ta yi mini kiranta ta kira mini mahaifinku."
Da sauri ta miƙe jin motar yaran gidan sun dawo daga islamiya ko banza ta huta da rigimarta na ɗan lokaci. Ta ƙarashe ficewa daidai lokacin da take faɗin, "Tunda ba za ki kira mini shi ba, ga su andal take ko dal ya kira mini shi."
Ba ta san lokacin da ta bushe da dariya ba tana faɗin, "Kya ji da shi fitininanniyar tsohuwa kawai. Ba ki iya faɗin suna ba, ki yi ta ɓata ma mutane suna kamar ance dole, ke dole sai kin shiga zamani."
Hajiya Baaba ta ja tsuka cikin ƙubula ta fara ƙoƙarin miƙewa tana salati, sai wani juyi take tamkar wacce zata yi wani aiki. Kusan minti uku tana ƙoƙarin miƙewa saboda ƙiba da ya yi mata yawa, wanda kullum Abby yake mata magana, akan ta rage cin kayan da zai saka ta ƙiba sakamakon ciwon jiki da take fama da shi, amma ta yi kunnen uwar shegu da shi. Sam bata da wani abinci sai waɗanda zasu sanya ta ƙiba da maiƙo. Tun yana mata faɗa har ya gaji ya ƙyale ta.
Gyara ɗaurin zaninta sannan ta shige ƙurya ɗakinta tana faɗin"Bari na kira Musa mai-gadi ya siyo mini da alama Faɗuma jikinta ya tsananta."
LONDON
A yau safiyar Monday aka tashi da hazo ya rufe gidaje, wanda sakamakon hakan ya ɗaga hankalin mom ƙwarai, domin ta san ba karamin ciwo Jannah za ta yi ba. Duk irin ɗumama ɗakin da room heater da ta yi, amma hakan bai yi wani tasiri ba.
Jannah kwance akan makeken gadonta wanda ta koma can gefe ta rukuɓe cikin blanket. Gabakiɗaya jikinta rawa yake haƙoran sai haɗuwa suke yi tamkar za su fasa fatar bakinta. Hannunta mom ta janyo tare da ɗorawa akan cinyarta lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ganin yadda take yi tamkar zata fasa gadon ta shige.
Ta miƙe tare da janyo ledar magani mai ɗauke da tambarin pharmacy ta ciro maganin da ta bata ba da jimawa ta ɗauki ruwa tare da hawa kan gadon.
"Please kar ki taɓa ni don Allah kar ki buɗe bargon nan, sanyin nan ba zai bar ni ba, domin kamar numfashina zai ɗauke." Ta faɗa cikin rawar sanyi tare da ƙara ƙuɗunɗune jikinta a cikin bargon, sannan ta riƙe shi sosai yadda ba zata ita janye wa daga jikinta ba.
Tsananin tausayin ƴar gudaliyarta ya cika mata zuciya. Miƙewa ta yi tare da jingina kanta da mirrow.
"Tabbas ya kamata na kawar mataki akan ciwon nan, ba zan iya ganin 'yata a cikin wannan halin ba, hakazalika ba na jin zan iya komawa Nigeria." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Dad ya yi sallama ya shigo tare da dosan kan gadon da take kwance ba tare da ya kalli in da take ba. Kan gadon ya zauna tare da janyo ta ta kwanta akan jikinshi yana shafa kanta, sai kawai ta fashe da kuka cikin muryar kuka tace.
"Daddddddddi." Ta ja fasali tare da cewa, "Sanyi nake ji!"
Ta ci gaba da kuka cikin muryar shagwaɓa. Shafa kanta ya yi, ya ɗaga idanunsa ya kalli mom da ta yi kamar ba ta san da shigowarsa ba ya ce,
"Jannah za ta koma Nigeria zuwa gobe in sha Allahu yau zan kammala mana visa sai ki fara shiri.Ya karasa maganar cikin ɗaga murya.
Wani irin kallon hadarin kaji ta yi ma sa tare da taku biyu ta isa gare shi, idanunta cikin na sa ta fara magana. "Ka san me kake faɗi Jabir?" Ta kira sunan shi ba tare da shakku ba, sannan ta ɗora da cewa,
"Umurni kake bani akan rayuwata kuma yata da na haifa wacce ba ni da kamarta?" Dariyar takaici ta yi tare da fara taku ta matsa nesa da shi ta tsaya.
"Idan har kana tunanin zan bi umurninka na koma gida, tabbbas ka yaudari kanka, domin hakan ba zai tama faruwa ba. Don haka ka daina wannan mafarki, domin ba zan koma ƙasar da zata zamo maƙabarta a dare ni ba.
"Halima!" Ya kira sunanta cikin ɗaga murya tare da daka mata tsawa, sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya bari ta furta komai ba.
"Ki sani daga yau ba zan ƙara lamuntar mugayen kalamai daga gare ki ba, ya isa iya wanda kika gaya mini. Ina jin zuciyata zata iya bugawa in har ban ɗauki mataki ba." Ya ɗan jinkirta tare da rage murya ya ƙara matsawa gareta. "Na gaji Halima ki sani mi mijinki ne, uban yarki, ina da ikon na ba ki umurni kuma ki bi, saboda duk matsayinki a ƙarƙashina kike, don haka ki iya kalamanki kar kiyi dana sani!"
Wani banzan kallo ta yi mishi lokaci guda idanunta suka fara zubar hawaye."Yanzu kake da bakin faɗa mini waɗannan kalamin, bayan ka ɓata rawarka da tsalle. Na ce ba zan