Showing 117001 words to 120000 words out of 137802 words

Chapter 40 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

da ita, amma saboda kafiya ta ƙi amsa calls ɗinsa duk lokacin da ya kira.


Sai ya tsinci kansa da kallonsa yana mamakin irin ƙarfin hali na Hajiya da ta danganta ta da shi, wai a matsayin matarsa, saboda in banda rashin mutunci mai zai yi da ita kamar sanda wanda ko ƙirjinsa ya ɗora mata sai ya karairayata. Shi ya ma manta da ita da maganar aurensu soyyayyarsa kawai yake sha da amaryarsa, don sai ya yanzu da ya ganta.


Wani uban harara ta zabga mishi har da sakin siririn tsaki domin wani mugun haushinsa take ji.


Ransa ne ya ɓace ya buɗe baki zai yi magana amm so Ammy ta yi mishi nuni da kar ya kulata da idanunta, wanda ya sa kan dole ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma zuciyarsa na tafarfasa.


Jin duk 'yan ɗakin sun ji tsaki da hararar da ta gi masa sai ta miƙe ta shige ɗakinsu domin t ji kunya da suka gani musamman Ammy da take biye mata tana taɓararta yadda ta ga dama, don har kwanciya a jikinta take yi.


"Ammy, kina ganin abin da yarinyar nan ta yi mini, amma kika yi mini nuni da na ƙyale ta."


"To kasheta za ka yi Ajmal? na ganta amma dole haƙuri za ka yi, domin karka manta shiga sabgarta da kake yi duk ya janyo aka maƙala maka aurenta."


"To ina gani sai ta yi ta zuba rashin kunya da fitsara, yanzu ki gani kamar ni za ta harara ta yi mini tsaki. Wallahi in ta ƙara saina tattaka ta sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita kanta Hajiyar yanzu saboda fitsararta korenta fa ta yi, amma saboda ni ba ni da gata za ta laƙa mini, ina zaman lafiya da mamata ta kawo mini jaraba, ita kanta ta san bamu dace ba."


"Ba ka da abin yi ban da wanda ya wuce addu' da fatan Allah ya zaɓa abin da yafi alkhairi, domin tun da ta furta sai wani ikon Allah."


"Kin san Allah Ammy ina ji ina gani ba zan yarda ta kawo mini jaraba da matsifa gidana ba, in kuma ta tilasta aka ɗaura auren da kanta in ta gaji da zamanta za ta zo ta kwashi tsiyarta, saboda kallon banza ba za ta ishe ni ba."


"Akan me tana matsayin matarka kana malami haƙƙinta za ka ɗauka?" Cewar ta cikin ɓacin rai.


"Ba ni nace ina son auren ba dole za a yi mini." Ya ba ta amsa tare da miƙewa domin hirar ta gimshe shi.


"Ka dai yi abu da hankali ka rinƙa aunawa da mizanin hankalinka. Jannah yar'uwarka ce, ko babu aure akwai zumunci tsaka.."


"Ammy, zan wuce gida dama na zo kiyi mini addu'a akwai tafiyar da zan yi kuma khairan in sha Allah." Ya katseta yana faɗin hakan domin ya gaji da hirar.


"Ok, masha Allahu. Ina maka addu'a da neman buɗi da ɗaukaka a dukkan rayuwarka. Ko akan wananan maganar ce?" Ta ƙarashe maganar da tambaya.
"A,a ita ma tana kan hanya aci gaba da mana addu'a."


"Kullum babu dare babu rana muna yi fatan nasara."


"Amin." Ya amsa tare da ciro damin kuɗi ya ije kusa da ita.


"Ba ri na wuce anjima zan turo Kamal ya kawo muku kifi, saboda yau za a kwashe ba ki ga girman da suka yi ba, Mushiirat na ta mamaki don ba ta ɗauka za su yi wannan girman ba."


"Masha Allah muna jira, duk da wanda aka kawo mana ma bamu gaba amfani da su basuna frij, ai gaskiya hannunka na da kyan kiwo ji kajin da aka kwashe wancan satin."


"Sun yi girman mamaki, ai albarkan da kuka sa mana ne." Ya ce tare da fara tafiya.


"Ai ko zamu ci gaba ka gaida Mushirat, ka ce na gode da tsaƙo Allah ya yi mata albarka, karka manta ka shiga ka gaida Hajiya Baaba."


"To." Ya ce tare da ficewa amma kuma bai shiga ba wanda tana ganin motarsa, da shigarsa tashinta har ya gama abin da yake yi, ya fito ya fita har leƙensa ta yi yana ta hararar shashin ya fice.


"Ni kake ma wannan wulaƙancin saboda zanyi maka aure, za ku ci ƙaniyarku da ga kai har ita." Ta ce tare da ɗaga waya ta kira wayar Aby wanda cikin rashin sa a ba ta same shi ba.


Fita ta yi ta bawa Musa Direba kuɗi ta ce,"Ka je ka siyo mini goro da tabarmai masu kyau da tsada ko nawa ne karka damu."


"To Hajiya, yanzu kuwa." Ya karɓi kiɗin yana mamakin me za ta yi dasu.


Bai jima ba ya dawo wanda ta karɓa ta adana su tana ta maganganu da habaici a sashinta wanda babu wanda ya jita don Ammy kwanciya ta yi.


Da daddare Aby ya dawo Hajiya Baaba ta yi kiransa wanda duk ciwon kan da yake fama da shi dole yazo.


Ganin uban goro da tabarmi sai da gabansa ya faɗi.
"Ah, Hajiya Baaba, waɗannan kayan fa? Na san na gaya miki iyayen manemin Nahlin sun roƙi abar maganar aurenta zuwa yaron ya dawon London ƙaro karatu da gurin aikinsa suka tura shi."




"Ba na son iskanci Muhammadu, nufinka Nahlin ce kawai mace budurwa a gidannan sauran ƙwailoli ka ɗauke su?"


"A'a Hajiya, na ga dai ita ce da muka san da maganar ta wani yana nemanta." Harararsa ta yi.


"Ka manta da maganar auren Jannnatuu da Adamuu, ko ka ɗauka wasa nake?"


Ji ya yi gabansa ya ƙara faɗi."Na dai ɗauka kin yarda sai ita jannar ta yi nisa da karatunta shi kuma matarsa ta haihu ko ɗaya ne." Ya ce cikin rawr murya.




"Matarsa ta haihu aka ce maka haihuwar za ta yi, saboda inda haihuwar za ta yi da ko wata ɗaya ba za ta yi ba yi ba za ta fara laulaluyi, tun da yanzu amaren yanzu kamar da cikin suke shiga, sai ka ga aure bai yi shekara ba an haihu hu. Matarsa juya ce ba haihuwa za ta yi ba."


Ya kasa magana sai kallonta yake yana mamakin ƙarfin halinta da maganar da take faɗi sai ka ce ta san gaibu, wanda ganin hakan ya sa ta ci gaba da cewa,


"To ban amince ba ta zane shi ko ta kashe shi in za ta so."


Kansa ya dafe ya duƙa ƙasa da gwuiwowinsa."Hajiya Baaba, ki wa girman Allah ki bar maganar nan zuwa wani lokac.."


"Ka fita idanuna Muhammadu, ka daina dawo mini da hannun agogo baya domin uren nan babu fashi. Ga ka kayan sa ranar nan, ka san na gaya maka ni zan yi komai, ko ƙwandalarku ba na son ku kashe, dama kuɗin da nake tarawa ban san me zan yi dasu ba, gara na yi aikin lada na samu lada, na sani ƙila ma shi ne zai sa na shiga al'jannah."


Shiru ya yi yana kallon kayan don ya rasa me zai ce.


"Za ka yi magana ne Muhammadu, ko ka mai da ni taɓaɓɓiya. Ka gaya mini nawa ne sadakin sai na biya."


"Na yi tunanin sai an zauna da yaran da kuma iyayen Jannah, musamman mahaifinta don bai kamata mu yi abu gabagaɗi ba, saboda yana da haƙƙi, kin ga dole ya gaya mana wanda zai naɗa waliyin Jnanh mu ne mu aurenta."


"To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka haka."










Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093


















KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 32-33*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka kace ina zuwa." Waya ta ɗauka ta danna numbobin dad wanda yake zaune yana cin abinci.


"Hello Jabiru, maganar auren Jannah da Adamuu ne, waliyin da za ka na ɗa nake tambaya saboda ina son asa rana."


Shiru ya yi ya rasa me zai ce a ransa yana tunanin ta dai na ce sai an yi auren nan.


"Ka yi shiru ko ba ka jina ne?"


"Abby ya zama waliyinta na ba shi wannan damar."Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinta.


"Saboda iskanci ya kashe mini wayaa ina sirikarsa ya manta lokacin da ya yi mini ƙarfa-ƙarfa aka ɗaura masa aure da Halimatuu, ashe babu daɗi ramuwar gayya."


Ta ƙarashe maganar tana kallon Aby da ya rasa bakin magana.


"Ai ka ji abin da ya ce ko sai na ƙra maimaita maka."


"A, a na ji ina son na kira abokina ya nema wa Ajmal auren."


"Shikenan, kira shi yanzu don ba zan tashi ba sai an saka rana ga sadaki da komai ayi mini kuɗin tsiya na biya, duk da mara kunyar ba tsada za ta yi ba saboda fitsararta, don duk wanda aka ba shi cutarsa ma aka yi, Adamun da yake ɗan gidane shi ya sa, saboda hannunka baya ruɓewa, ka yanke ka yar."


Shi dai baice komai ya ɗaga waya ya kira shi sannan ya kalle ta bayan ya kashe waya.


"Hajiya Baaba, ya ce ga shi nan zuwa, bari na je na sha magani na ci abinci kaina ke ciwo."


"Ka je ina? In kaga ka jirka an sanya ranar nan ne, bari na ɗauko maka maganin ciwon kan da abinci in da su. Yau abin da kafi so na girka gudun kurna, na gane wayon ka salon ka tafi a zuge ka ba."


Bai ce mata komai ya zauna har ta kawo masa abincin wanda ya kasa ci duk sonsa da gudun kurna sai dai ya sha maganin y koma ya zauna ya na tunanin lamarin.


Bai ɗauki tsawon lokaci ba Alhaji Umar ya shigo ya same su, zaune jugum-jugum babu mai magana sai Hajiya Baaba, da take kaɗa ƙafa fuskarnan babu ɗigon rahma, domin kamar ta fuskanci Aby ya yi masa text kan ya zo ya ba ta hakuri.


Jiki a saɓule ya samu guri zauna yana kallon Aby, da yake ƙyafta masa idon akan ya gwada sa arsa ganin yadda jikinsa ya yi sanyi.


Hajiya Baaba, ƙuta ta yi tana kallonsu ta gefen ido a ranta take faɗin,"Munafukai ku gama ina kallonku."


"Barka Hajiya Baaba, mun same ku lafiya."


"Alhamdulillahi, lafiya lau kamar yadda ka ganni, sai abokin na ka yake ciwon kai." Ta ce a daƙile ba tare da ta kalli inda yake ba.


"Ashsha! Allah ya kawo afuwa."


"Amin" Suka amsa da shi sai ta gyara zama ganin yana gyara baki da tunanin ind zai fara.


"Abokin na ka ya gaya maka komai ko. Maganar auren duk bana son ya wuce wata uku, saboda ni da za a yi cikin satin nan zanfi murna."




"Ki yi haƙuri dai abi sannu tun da ba sauri ake kuma, kuma Hajiya da kin ƙara duba lamarin."




"Dakata, na ce ka dakata wato kun haɗa baki ko? To babu ruwanka da shiga harkan zumunci, za ka sanya ranar ko ni na saka da kaina tun da uban 'ya ya amince."


"A'a ba za ayi haka ba, kai Umar sanya ranar kawai, amma don Allah ki yi haƙuri asa ta yadda Jannah za ta kai aji uku a makaranta."


"Wata uku na ke so kuma haka za a sa. Na ga kuɗaɗena za su yi ciwo ba na ka ba, don haka ina ruwanka don an saka ko gobe ne."


"To shikenan, Allah ya ba su zaman lafiya." Ya ce tare da kama hannun abokinsa suka fita daidai lokacin da Hajiya Baaba ta amsa da.




"Amin." Sai ta ci gaba da cewa,"In ma ba su zauna lafiya ba, za su gaji su zauna domin auren nan mutu ka raba... Sai dai, ina mutu ku raba su, kuma ina sha Allah ina duniya har sai na ga jikokinsu." Ta ƙarashe maganar tana hararar ƙofar da suka fita.




Wayarta ta ɗauka wanda bugu ɗaya Halima ta ɗauka saboda tun da ta tafi ba ta kirata ba, kuma ko ta kirata sai ta mula ta mulmule take amsawa shi ma iya gaisuwa ta katse wayarta


"Hello, uwata ta kaina macen da ta fi ko wace mace a duniya." Ta amsa tana mata wannan kirarin


"Ba kiranki na yi ki mini kirari da ƙarya da ƙarerayin da kuka saba na 'yan siyasa ba, wanda sai mun zaɓe ku ku fito da manufofinku na zalunci da yaudara."


Shiru ta yi tana jinjina abin da ta ce sai kuma ta gyara murya ta ce,"Amma kya yi mini fatan alkhairi na zamo ta ƙwarai na kuma banbanta da saur.."


"Ke kika sani Halima, ai ni kin gama sire mini tun da kika yi mini haka. Maganar auren Jannah, an saka rana wata uku sai ki fara shiri." Ta ce tare da gimtse wayarta ba tare da ta jira abin da za ta ce ba.


"Ka ji wai har ansa rana wata uku fa? Kai Hajiya ta ɗauki lamarin nan da girma." Ta ce tana jinjina lamarin da tunanin halin da Jannah take.


"Humh, a rigimarta in ba an yi bikin nan ba ba za ta taɓa samun sukuni ba."


"Ina fatan ta ƙulla alkhairi."


"Amin, in sha Allahu." Cewar dad sai kuma ya ɗora da cewa," Ki ce zuwa Zariya rarrashi ya kama ni."


"Aiko dole don yanzu Allah kaɗai ya san halin da take ciku, kuma ga shi ko na kira wayarta ba za ta ɗaga ba. Ka ƙara gwadawa ko za ta ɗauka."


"Humh, kamar ba ki santa ba sai ta huce." Ya ce yana ɗaukar wayar sa kira amma har ta gama ringing ba ta ɗaga ba.


"Ni kam na rasa wane irin kaya zan yi mata domin so nake gidanta ya banbanta da sauran 'yayan duniya dole na kashe mata kuɗi."


Dariya ya yi jin abin da ta ce."Gaskiya ita ce ya ɗaya tilo wanda Allah ya bamu. Yanzu fa shikenan, girma ya kama ki za ki ɗauki suruki."


"Hararsa ta yi cikin wasa tana faɗin,"Ban gane ba ko ka barwa Ya Bala surukutan ne."


"A'a ni ai yanzu nake tashen kuriciyata, kin san zan iya aura mace budurwa ke kuma kwanannan za a fara ce miki kaka."


Dariya sosai ta yi jin abim da ya ce wanda har ya sa ta tashi da sauri zata kai mishi duka sai ya ruga ta bishi da filo yana maka masa.




"Allah ba ka da kirki, wato tsufata kawai kake hangowa ko injinjiya? Ko dayake in dai 'ya'yan Ajmal ne ina fatan ta haifa mini su da yawa domin zan yi alfahari da su, ban haihu da yawa ba ina son ta haifa harda nawa. Sai dai, kuma ganin yadda auren na su yake hakan zai faru?"


Ta ce cikin murya sanyi wanda ya sa ya rungumeta yana faɗin," In sha Allahu za su zauna lafiya auren nan sai mun yi alfahari da shi."


"Ina fatan hakan." Ta ce tare da ɗaukar wayarta tana faɗin,"Bari na fara kira na gayi sa ranar na kuma fara shiri."


"Ah amara kirjin biki. Akwai lokaci ba."


"A'a barni Injiniya mai zurfin ido da wuri yake fara kuka." Ta fara kiran ƙawayenta.


Aby na fita bayan sun ɗan tautauna da Alhaji Umar wanda ya ba shi baki, da ƙara tausasashi kan su ci gaba da neman zaɓin Allah, sannan ya yi masa sallama ya rakashi har ya shiga motarsa ya tafi.


Ɗakinsa ya koma ya kwanta sharf! Yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.
"Abby, jikin ne? Ko za mu je asibiti ko da yake bari na kira doctor Irfan."


"Karki kira shi na ji sauƙi don na sha magani a sahshin Hajiya."


"To me ya faru you look worry?" Ta ƙarashe maganar tara da dafa shi tana taɓa goshinsa.


"Akan maganar auren yaran yanzu Hajiya ta tursasa aka sanya rana wata uku."


"Sa rana?" Ta tambaya cikin tsananin mamaki da ruɗani.


"Eh, dad ya naɗa ni waliyin Jannah, Alhaji Umar da ya ƙara tsayawa a waliyinsa."

"Ikon Allah!" Ta ce tare da nisawa. Sai kuma ta saki numfashi ta ci gaba da cewa,

"Ajmal ɗin ya sani?"


"A'a da shi da ita babu wanda ya sani yanzu dai zan kira shi na sanar masa, Jannah ce ban san yadda zan yi ba you know how rude she is."


"You have to hurry, kafin ta kira su ta hargiza su ta yadda zamu kasa shawo kansu, domin ka san ba za ta gaya musu da dadi ba"


Wayarsa ya ciro da sauri don ya kamata tun tuni ya kira shi kafin ta kira don da biyu za ta gaya masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login