Showing 39001 words to 42000 words out of 137802 words

Chapter 14 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

jikinka sai ya cuce ka ba tare da na waje ya yi ba."
Ga mamakinta sai ta ga yana hawaye. Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi ta zauna a gefen gado tare da ciro wayarta a jaka ta da take neman agaji ganin Hajiya Turai ce ya sa ta ɗauka da sauri haɗe da sallama.
"Hello, uwa ba da mama."
"Na am Hajiya Turai ina jinki."
"Yarinyar nan da kika tura ni ƙauyensu na je amma akwai matsala."Kafin ta ce komai ta ci gaba da cewa,
"Mijinta ya hau dokin na ƙi, kan babu inda za a kai masa mata, kuma kamar harda goyon bayan iyayenta, don sun kafe maganin gida za su yi. Ga shi yarinyar tana cikin mawuyacin hali, mun kaɗa mun raya amma sun ƙi yarda harfa tsutsa ya fara cin ƙafafunta, da wuya ba yanke ƙafar za a yi ba."
Shiru ta yi tana nazari na 'yan daƙiƙa."Kai wai me ke damun mutanenmu na daji, ƙaya aka ce mini ta coke ta har ya ja mata wannan sanadin, amma ba za su hankalta ba su bari a nemar mata magani."
Tsaki ta yi." Bari na nemi Umar soja kamar in aka je da shi za mu yi nasara.
"To uwa ba da mama, don Allah ki dawo Ƙasarki domin tana buƙatar ki, duk da anan ɗin ma ba ki gaza ba."
"Shikenan, in sha Allah zan dawo. Allah ya rufa mana asiri."
"Amin, in sha Allahu sai kin ci zaɓen nan."
Ƙoƙarin kashe wayar ta yi bayan ta amsa amma sai ta ji ta ce "Yauwa na manta sati uku kenan, wata mata na zuwa ofishin mu nemanki, mun yi munyi da ita ta sanar mana buƙatarta, domin daga gani tana neman temako ne, amma ta ƙi burinta ku haɗu da juna. Kuma mun gaya mata cewar kina Ƙasar waje amma sai ta ce za ta jira ki dawo tun da za ki yi zaɓe ko yaushe ne za ta jira. Ni wallahi na yi tunanin mahaukaciya ce ma."
"Mahaukaciya?!" Ta yi tambayar da sigar mamaki.
"Eh, ba za ki gane hakan ba sai kin ganta, amma fa da hankalinta don cikin natsuwa take magana. Wahala ce ya mai da ta haka. Sai dai, ta nuna ba ta son taimakonmu ta fi son ganinki."
"To shikenan, Allah ya kaimu." Ta faɗa da sauri tare da gitse wayar a ranta tana tunanin wace mata ce da duk da ta san bai wuce taimako ta zo nema kuma ko ba ta nan za a yi mata.
Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin bayan ta ja ƙofar.


NIGERIA
Anty Nahlin ce ta shigo ɗakin Hajiya Baaba riƙe da waya tana ihun murna.
"Oh little sis sleeping, wake up let's celebrate." Tana dariya cikin farin ciki.
Miƙewa ta yi tana goge ido domin ta yi nisa sosai a cikin baccin.
"For God sake, za ki tashe ni kaina ke ciki ciwo."
"Ayya sorry, I can't wait ne. Guess what?" Ta ce cikin tsananin murna.
Ganin haka ya sa ta tashi ta zauna tna fuskantarta.
"Anty Nahlin what's going on? Please tell me, you know I'm not good in guessing."
Ɗage kafaɗa ta yi tare da ɓoye wayar da take ƙoƙarin ƙwace don ta gane albishirin da za ta nuna mata yana wayar."No, sis you most guess."
Ɓata fuska ta yi."Ok, to shikenan in ba za ki gaya mini ba, let me give it a try. You are engaged?" Ta ce da sauri cikin tsokana.
Binta da gudu ta yi suka fara zagaye dakin,
"Common, ya za yi na yi aure ya Ajmal bai yi ba. Duba ki ga abin farin cikin da ya same mu a family dinmu. Your mom za ta fito takarar Minister, and soon she will be back to Nigeria."
Da sauri ta saki wayar da take nuna mata hotonta wanda ta yi kyau sosai, ganin haka ya sa ta yi sauri ta rike wayar kafin ta kai kasa tana kallonta cikin tsananin mamaki.
"What happened? Why are you frustrated?"










Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K








KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 11-12*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"I hate her. My mom is so selfishness. Za ta dawo Nigeria saboda she wants to be a politician? Or my God! I can't imagine this. Bayan ta ki dawowa saboda umurinin mijinta da ni. Allah ban taba ganin maiyar kuɗi ba irinta. So take ta kwashi kuɗin gwamna..."
"Haba Jannah, duk waɗannan mugayen kalamai ga mahaifiyaki kike furtawa. Wannan fa cigaban ahalinmu baki ɗaya ne, ke da za ki yi murna za ta dawo kusa dake."
"No, I won't go. Na fi son na zauna a gidan, amma babu inda za ni don ba ta da lokacina. So am happy here."
Hararar sakin mata tare da miƙewa" You know what? I can't deal with your shit right now, and is this attitude of you that annoyed me."
"You don't know everything. You don't know her shi ya sa kike faɗin haka.
"Then disclose it to me, kinga.."
"No I don't have that time, abin da kawai na sani ba ta sona." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
Hajiya Baaba ta fito daga ɗakinta ta balla mata harara,"Ke dai wallahi anyi 'yar baƙinciki. Ni ban taɓa ganin yar da take wa uwarta hassada ba sai ke. To ta Allah ba ta ki ba, mahaifin na ki da kike so ya fi ta ba haka Allah ya so ba, sai dai ki mutu.
Miƙewa ta yi ta tura baki tare da zabga mata harara kamar idanun za su faɗo ƙasa.
Ɗaki ta ruga tare da kulle ƙofa tana kuka sosai. Numbar dad ta kira wanda bugu ɗaya ya ɗauka,
"Helle dad, is it true that mom wants to come back to Nigeria because of politics?"
Shiru ya yi kamar ba zai amsa tambayar ba har sai da ta kara maimatawa cikin ƙaraji.
"Oh yes but understand her."
"Haba dad, supporting her all the time, you don't have right in your house. Na tabbata in har ta fara siyasa, sai kayi watanni ba ka ganta ba. Please ka rabu da ita ka dawo Nigeria ka yi aure mu yi zamanmu da matarka, ta haifa mini ƙanni, saboda ita mom neman kuɗi ya sa ta ƙi haihuwa. Ni ɗaya kawai ta haifa kamar mayya."
Wani irin abu ya daki kansa mai kama da guduma. Ko kaɗan bai taɓa tunanin za ta yi ƙorafi game da rashin haihuwar mom ba. Idanunsa ya rintse yana jin anya in ta ji shine sanadin hakan za ta yafe masa. Take zufa ya keto masa har yana ɗiga a jikinsa.
"Haba Jannah, ya kamata.."
Ɗif ta kashe wayar tare da jifa da ita."Na rasa wane irin so yake mata ba wanda ya kasa yin wani abu a gidansa. Anya ba asiri ta yi masa ba, don ta juya shi son ranta." Ta tambayi kanta cikin ruɗu.
Har ta danna numbarta za ta kira sai kuma ta ga rashin alfanun hakan, domin tunda ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta.
"Rayuwarta ne ta je ta yi kowa yana da ikon zaɓa ma kansa abin da yake so. Kamar yadda take rayuwara son ranta ni ma ba ta isa ta ba ni umurni na bi ba." Ta faɗa a hasale


Don haka ta cire abin a ranta tunna shi kansa wanda yake da iko da ita ya kasa komai ballantana ita da ba ta bata mahimmanci a rayuwarta ba.


Jannah na kwance wayarta ta fara neman agaji. Ganin numbar mom ya sa ta yi tsaki ta koma ta kwanta.
Tunawa da motarta ya sa ta zabura daidai lokacin da wayar ta tsinke. Tana ƙoƙarin kira kiran ya ƙara shigowa.
"Hello Jannah, motarki ta iso. In sha Allahu gobe yayanki zai ɗauko miki ita." Ihun murna ta saki sosai tana tsalle.
Maganar mom ɗin da take yi yasa murnarta ta koma ciki."Haba mom, kan me za'a hana ni driving? Ni gaskiya ba zan yarda ba."
Sauke ajiyar zuciya ta yi tana faɗin,"Kafin ki gama sakandiri ne, amma da zarar kin gama za ki fara tuki, kin san Nigeria ba kamar London ba." Kashe wayar ta yi tana gunaguni.
Hajiya Baaba da take ƙoƙarin shiga ɗakinta ta ja ta tsaya jin tana ta magana ciki-ciki."To 'yar gidan fitsara, jikar marasa kunya. Uban wa kike zagi, in dai ba 'yata ba?" Harara ta banka mata ta miƙe ta shige cikin ɗakinta sai kawai ta sa kuka.
A mota Aby ke nuna w Ajmal motar da zai ɗauko wa Jannah a Abuja. Tsananin mamakin motar da kyauta da tsadarta yake yi.
"Yanzu Aby wancan ficiciyar yarinyar mom za ta siya wa mota, kuma ta yi driving da kanta?" Ya faɗa cikin tsantsar mamaki.
"Kar fa ka manta mahaifiyarta wace ce. Kuma ita kaɗai ta mallaka."
Jinjina kansa ya yi, bai ce komai ba, wanda ganin hakan Aby ya ci gaba da cewa,"Ka ji maganar an tsayar da ita takarar minister ko?" Kallonsa ya yi sai kuma ya mai da hankalinsa kan tuƙi.


"Eh na ji kuma ta amince?" Ya ƙarashe maganar da tambaya.
Abby ya ce,"Ta amince da ƙyar, amma dad bai bata goyon baga ba, sai dai ka san in har ta amince babu wanda ya isa ya canza mata. Cikin satinnan zan je India na wakilce ta kan kasuwancinta."
Ajmal ya kalle sa yana faɗin,"Tana burge ni mace ce kamar maza, samun ta a ahalinmu abin alkhairi ne. Sai dai 'yarta sam ba ta ɗauko ɗabi'unta ba. She doesn't have table manners and she is so cheeky. Ga shi hajiya ta ƙarashe sangarta ta."
Aby da ya ji an tsokano masa inda ke masa ƙaiƙaiyi ya gyara zama yana faɗin,
"Yauwa, dama na bari ka dawo ne. Ka san yarinyar nan, ta daina zuwa islamiya? Har makarantar ta je ta mari malamin don ya duke ta."
Shiru ya yi, a ransa ya ayyana da zata iya fiye da haka, amma a fili ya ce,"Kai Hajiya sai addu'a. To yanzu bata zuwa kenan?" Aby ya ce,
"Eh, ta dage sai dai a canza mata wata makarantar, ko a ɗauko mata malami a gida. Kuma wallahi mahaifiyarta ta roƙe ni akan na bata ilmin addini. Don Allah ka yi wani abu." Ya yi shiro ko zaice wani abu, amma sai ya ga bai ɗauki maganar da mahimmanci ba, sai bin karatun kur'anin da ya kunna yake yi, wanda ganin hakan ya ci gaba da cewa,
"Ba zai yiwu na zura mata idanu ba, mahaifiyarta amana ta ba ni. Don haka dole na kula da ilminta kamar yadda zan kula da naku, kuma ko Halimatu ba ta da rai ni me riƙe ta ne. Daga yau na ɗora maka kula da ita."
Da sauri ya kalle sa jin aikin da yake son ɗora masa."Ni fa sam bana son shiga lamarin su, kasan Hajiya, ni kaina ba ta barni ba, da na yi magata zata fara mini gori a gabanta salon ta raina ni."
"Ya za ka yi, hakanan zaka jure ka yi don Allah, ai wani lokacin tana shakkarka " Jinjina kansa ya yi, don ya san aiki ne a gabansa.
Kasancewar ranar Juma'a suka yi maganar, don har ya manta a ranar sati, sai da ya ga Nahlin ta fito da zubbulelen hijabinta za ta tafi hadda ya tuna, har ta wuce shi ya dawo da ita ta hanyar ƙwala mata kira.
"Na'am Yaya, barka da hutawa." Ta ce tana ƙoƙarin ƙarasawa inda yake.
"Ke Nahlin ma za ki ce wa Jannah ta fito kuje hadda." Ta ɗan yi jin sai kuma ta ce,
"To." Ta juya sashin Hajiya Baaba.
Ta same ta a ɗakinta ta kunna waƙa sai tiƙar rawa take yi.
"Ya Ajmal ya ce ki shirya muje hadda." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba da ita take yi ba. Tsawa ta daka mata wanda ya sa ta miƙe tare da tura baki.
"Haddar me? Babu inda zani." Ta ce cikin ƙunƙunai.
"Oho, ni dai tsaƙo aka aiko ni." Sai ta fara buga ƙafafunta tana faɗin,"Ni fa Allah ba zan koma islamiyar nan ba, wannan ai salon a raina ni ne, ina babban yarinya."
Mugun kallo ta yi mata sannan ta furta.
"Ki iya bakinki, wallahi Yaya ba sa'an yinki bane. Don haka ki natsu ki san wanda za ki yi wa, in ba haka ba sai ya canza miki halitta."
Ta turo baki."Tun da ga ubana ba." Jinjina kai kawai ta yi ta fice, tana mamakin tsaurin idanunta.
Tana isa gurin shi da yake ƙoƙarin shiga mota."Ya ta ce ba za ta je b.."
"What?" Ya katseta yana tambayarta da ƙarfi tare da daka mata tsawa wanda ya sa ta matsa cikin tsoro. Fitowa daga cikin motar ya yi ba tare da ya kashe ba."Lallai yrinyar nan ba ta da kunya zan koya mata hankali."
Buga ƙofar ya yi da ƙarfi ya shigo ga mamakinsa sai ya ganta a falo da remote a hannunta tana canza tasha, wanda ganinsa ta fara ƙunƙunai tana turo baki.
Ajmal ya tsaya cikin mamaki yana kallonta aransa ya ayyana da zaginsa take ganin yadda bakinta ke motsawa. Cikin fusata ya ce,
"Ke zagina kike yi don ubanki?" Mari ya kai mata a fuska tauu! Wanda ta ji shi har tsakiyar ƙwaƙwalwarta. Ta takura iya ƙarfinta ta canyara ƙara tare da kiran sunan Hajiya Baaba, wacce ta fito da gudu har tana tuntuɓe.
"Na shiga uku! Shalele, maciji ya sare ki, ko kunama?" Turus! Ta yi tana ƙarashe ɗaura zaninnta ganin wanda yake falon.
Da gudu ta koma bayanta ta ɓuya. "Hajiya Baaba, ya kashe ni mari hamsin ya yi mini. Wayyo na mutu! Dadddyyy."
Hajiya Baaba ita kanta ta san ƙarya take yi domin da haka ne wataƙila da wata maganar ake ba wannan ba, amma saboda rashin son gaskiya ta kurma salati da ihu tana faɗin,
"Kan uba, uban me ta yi maka da za ka fara dukanta kamar ka samu jaka?" Ta tamabaye sa cikin tsananin ɓacin rai tana girgiza.
"Gaya masa Hajiya Baaba, ko iyayena ba sa duka na ballantana wani ban.."
Ransa ne ya ɓace lokaci guda idanunsa suka canza zuwa wani kala, ganin tana shirin zaginsa a gaban Nahlin wacce ko magana yake ba ta iya kallon shi, sai kawai ya zare belt ɗinsa ya shiga zuba mata ta ko ina kuma iya ƙarfinsa.
Cikin azama Hajiya ta kai masa cakuma tana faɗin,"Ai ko yau sai na ga uban da ya tsaya maka da za ka duke ta."
Ture ta ya yi har ta buge da center table, amma ko kula ta bai yi ba, wanda ganin haka ya sa ta ɗora hannu aka ta yi tsakar gida tana ihu tare da faɗin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login