Showing 42001 words to 45000 words out of 137802 words
Chapter 15 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
"Na shiga uku, na lalace an kwaso mini dangin jaraba! Kai kan Muhammadu sam ba ka yi sa'ar zuriya ba. Jama'a ku kawo mini ɗauki."
Ammi da ta fito daga sashinta da makullin mota tana sauri domin ta yi latti ta ji abin da take faɗi wanda ya sa ta yarda makullin tare da rugawa sashin cikin tsanin tashin hankali.
Wasu irin zafafan mari ta sauke masa."Ashe ba ka da hankali 'yar'uwarka za ka kama da duka haka saboda ga jaka ko?" Ta ce cikin zafi.
"Ai ko yau za'a yi ta a gidanan, wallahi sai ka yi sana-sanin dukanta." Cewar Hajiya.
Wani irin ƙululu ya ji ya taso masa cikin tsananin ɓacin rai ya kalli Hajiya Baaba yana faɗin,
"Kin yi kuskuren fifitata da kika yi akanmu, ki sani in ban yi ajalinta ba to sai na naƙasata." Ya juya zai fice daidai lokacin da ta ce,
"Za ka iya, ai zuciyarka kamar ta fir'auna take."
Jannah da ta ji duka rungume ta ta yi."Na shiga uku! Don Allah ki kira mom ta yi mini viser na koma ma London, if not he gonna kill me."
"Babu inda za ki, sai dai mu bar musu gidan. Shakuruminki shalele." Ta ba ta masa tana shafa bayanta.
Aby da ya shigo cikin falon a lokacin da zai fice wanda hakan ya sa ya fasa yana ajiyar zuciya a kai a kai.
"Yauwa, ma za shigo, ai sai da na gaya maka ka ja mana layi a tsakaninmu kaƙi, ga shi yanzu zai kashe mini shalele. Dole mu bar gidan nan, daɗin abin mahaifiyarta za ta iya siya mana duk irin gidan da muke so mu zauna ko a ketare ne."
Lamarin sai ya rikita kansa ya rasa ta ina zai fara." Tashin hankalin da kake so ka ja mini kenan Ajmal da sunan gyara? Kana jin mahaifiyata za ta bar gidana saboda kai."
Takaici sun na shi magana juya wa ya yi ya fice daga falon ba tare da ya ce komai ba, domin matuƙar ya ci gaba da kallonta, ƙila nan da minti uku, sai dai ayi maganar kai jana'izar gawarta . Zuciyarsa ta ɓace tsananin tsanarta ya ƙara shiga ransa sosai.
"Tashin hankali na nawa? Ai aikin gama ya gama. Barin gida ya zamar mini dole, ko kwana ba zan ƙara yi ba a gidannan."
Jannnah da ta ji duka ƙwaƙwarar motsi wahla yake mata. Ta kwantar da kanta kafaɗar Hajiyan Baaba da ko zama ta kasa yi, sai famar jijjiga take yi.
"Ya zama dole ka ɗauki mataki in ba haka ba, watarana sai ya jawo mana tashin hankalinn da ba mu yi tsammann.."
"Rufe mana baki! Munafukar Allah. Ai duk tarbiyarki ce, da kika raini 'ya'yanki sakaka kamar kashi, ba kya iya tsawata musu. Ni da na isa da ɗana, kin ga ina ije kara ya tsallake? Ai ni an haɗa mana jini da jaraba." Ta ƙatse Ammy da take maganar.
"Ki yi haƙuri Hajiya maganar ba ta kai haka ba." Cewar Aby. Harara ta gallah masa."Ta ma wuce." Ta ba shi amsa.
Kamata ta yi suka nufi ɗaki tana faɗin,"Shakuruminki kin ji shalele, babu inda za ki. Sai na ga uban da ya isa ya kai ki islamiyar."
Ganin ta ɗauki waya tana neman numba ya yi saurin shan gabanta."Don Allah, kar ki kira Halima. Ni ma ina da iko a kanta, kar ki manta ciki ɗaya muka fito."
"Sai na bari ya kashe ta ina gani ko?" Ta tambaye shi cikin ɓacin rai tare da shigewa ciki ta banko ƙofar da ƙarfi.
Dafe kansa ya yi, yana dana-sanin gaya masa, domin gashi yanzu ya ɓata goma biyar ba ta gyaru ba. Juyawa ya yi ya fita ganin kowa ya tafi ya barshi shi kaɗai.
Ajmal yana shiga ɗakinsa ya shige bayi. Ba tare da tuɓe kayansa ba, ya buɗe ma kansa shower yana ƙoƙarin tuɓe kayan, ya yin da ransa yake zafi zuciyarsa ke tafarfasa kamar za ta yi tsalle ta fito waje.
A maimakom ya yi hushi ya ƙyaleta sai ya saka a ransa sai ya ƙuntata rayuwarta don ya baƙanta mata da Hajiya Baaba da ƙiri-ƙiri take fifita ta akansu. Idon don kuɗi ne, ko kuɗin da yake da shi ba na Aby ba ya isa ta daina yi musu gorin sun ci da arzikinta.
Yana fitowa ya saka milk colour na jallabiya tare da ƙarasawa frig ya rinƙa banka ma cikinsa ruwan sanyi ko ya ji salama, amma da ya tuna abin da ya faru sai ya ji komai ya zaman masa sabo.
Wayarsa dake ƙara tun da ya shiga wanka ya ɗauka cikin ɓacin rai."Kin dame ni." Ya furta tare da daka mata tsawa.
Da sauri ta kashe wayar saboda tsabar tsoro jikinta har rawa yake yi."Na shiga uku! Wa ya taɓa shi?" Ta furta cikin jimamin tsawar da ya daka mata.
"Allah ya ba ka haƙuri. Ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni." Ta ce tare da ije wayar ta ci gaba da kwaɓin cincin ɗin da take yi.
"Hello Halimatuu, kina jina?" Hajiya Baaba ta furta."Eh in jin ki, Allah ya sa lafiya? Don na ji muryarki ta canza." Ta ce kamar ba ta san abin da ya faru ba, don Aby ya yi mata text ɗin komai kafin ta kira wayar.
"Ina lafiya, an saci zanin mahaukaciya. Gida za ki canza mana ni da Janaatuu, wannan azzalimin yaron ya tashi..."
"Hajiya Baaba, na ce ki daina ce mini Jannatu. Kowa sai kin ɓata ɓasa suna?" Ta katseta cikin masifa cikin kaukausar murya.
Takaici ya kamata matsawa da wayar ta yi tana faɗin,"Ka ga mini ja'irar yarinya fitsarrariya! Ina neman miki mafita, amma sai kin nuna halinki, ai na gaya miki albarkacin 'yata kike ci da na bari ya miki dukan tsiya wallahi, na watsawa karnikan gidan ƙasusuwanki."
Murguɗa bakinta ta yi ta gyara kwanciyarta tare da ci gaba da kuka da ƙarfi da sheshsheƙa ta yadda mom za ta ji yo ta.
Mom da ke jin faɗan da suke yi sai ta shiga girgiza kanta a ranta tana tunanin za ta canza halinta na fitsara kuwa, ganin ko uwarta ba ta ragawa ba.
Tun lokacin da Aby ya sanar mata ta yi matuƙar murna da hamdala, domin ta fahimci tana buƙatar wanda zai gyara mata kuskuren da ta aikata, kasancewar ta gama raina su duka.
"Yauwa ki nema mana gida wanda zamu zauna daga ni sai ita."
Ajiyar zuciya ta saki tana jin yadda take shiga take fita da zage-zage da jawo masa jifa'i tamkar ba matsayinsu ɗaya ba a gurinta wanda hakan bai yi mata daɗi ba, don ko ita ta ji wani iri ina ga kuma shi da iyayensa.
"Kiyi haƙuri Hajiya, su ɗin duka matsayi ɗaya suke a gurinki, kar ki sanya tsana ko rabuwar zumuncin su. Zan yi magana da Aby sai..."
"Ban san ke shashasha ba ce Halimatuu! Anya kuwa nonona kika sha? 'Yarki ɗaya tal wacce Allah ya ba ki ake shirin kashewa shi ne sai kin yi shawara da ubansa? To shikenan, ki bari ya kashe ta, inya so kuɗin da kuɗin da kike tarawa, kinga sai ki bar ma duniya su..."
Fisge wayar ta yi daga kunninta don tana jin abin da take cewa.
"Na san ba kya ƙaunata. So I don't want you to prove it. You know? I'm not under age, and my dad has money so I can handle myself." Ta yanke kiran cikin ɓacin rai.
Baki ta buge mata."Ke kam ban san lokacin sa kika zama haka ba! Mahaifiyar taki kike wa tsawa tamkar 'yar cikinki?"
"Kyale ni, Hajiya ba ta sona ban taɓa yin abu na burgeta ba."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 12-13*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
A can ɓangaren mom ajiyar zuciya ta yi cikin takaici."Yauwa, Alhamdulillahi! Allah ya kawo mini wanda zai kawo gyara a lamarinta."Dariya dad ya yi jin abin da ta ce.
"Lamarinta yana bani mamaki ko Hajiya ba raga ma wa ba ita kanta sonta ne ya rufe mata ido, amma ba ka ji yadda take daka mata tsawa ba. Gaskiya na yi sakaci a rayuwarta.
Wayarta ta ɗauka ta yi wa Ajmal transfer kuɗi naira dubu ɗari. Bayan ta tura mishi message akan ya sa kati.
"Mu yi mata addu'a watarana zata daina har da kuruciya. Ya faɗa daidai lokacin da kiranta ya shigo wayarsa.
"Ga kiran mutuniyar nan, ya shigo." Ya ce yana kallonta da murmushi a fuskarsa.
" Ka gaya mata yadda muka tsara." Jinjina mata kai ya yi.
"Hello dady, na ba ni na shiga uku! Wallahi dangin mom mugaye ne, ka mai da ni family ɗinku ko ka canza mini gida."
Murmushi ya yi jin abin da ta ce." Ba za ki iya zama a family ɗina ba, kiyi haƙuri har mu dawo kin ji."
"No" Ta ce da ƙarfi. " Ba zan zauna ba ana cin zalina sai dai ka kama mana haya ni da Hajiya Baaba." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ƙara har sai da ya kauda wayar a kunninsa.
"Ok, sorry I will." Ya faɗa ba tare da shiri ba. Jin abin da ya ce ya sa ta yi shiru sai shan majina take yi.
" Ki bari zan nemi gida mai kyau ku zauna, amma yanzu bari na tambaya ki ba ni zuwa anjima."
"Ok dad." Ta ce cikin zallar shagwaɓa tare da kashe wayar.
Kafin wani lokaci temperature na ta yi yi high sai rawar sanyi take yi, wanda hakan ya ƙara ɗaga hankalin Hajiya Baaba. Ta yi zagi har da kuka. Su Allah ya isa ya sha babu iyaka. Kowa sai dai ya toshe kunninsa.
Ganin yadda jikinta ya rikice Aby ya yi wa likita waya ya zo ya duba ta har sai da ya ɗaura mata drip tasha pain reliever sannan aka samu sausaucin kukan da koshi zai iya ja mata ciwon kai.
Ajmal na zaune a falonsa yana ƙoƙarin kiran Mushiirat don ya bata haƙurin tsawar da ya yi mata alert ya shigo. Ya yi matuƙar mamakin ganin kuɗin, wanda har sai da ya yi tunanin ko kuskure ta yi, don ya san Hajiya Baaba ta gaya mata ƙarya da gaskiya.
A lokacin da ya ɗaga waya zai kirata sai ya ji kunyar dukanta da ya yi, amma da ya tuna abin da ta yi masa sai ya yi watsi da hakan.
Tana ɗaga wayar bayan ya yi sallama ba ta bari ya yi magana ba ta ce,"
Ajmal, ka ga kuɗi ko?" Amsawa ya yi cikin jin kunya. "Na tura maka ne ka sa kati, ka ga sai ka kira surukata. Aby ya gaya mini har an je jin magana ko?" Cikin jin kunya ya amsa mata.
"Allah ya kulla alkhairi ni zan haɗa lefe. Ya yi muku albarka. bye."
A hankali ya sauke wayar da ta datse kiran. Ji ya yi gaba ki ɗaya jikinsa ya yi sanyi."Sam ba ta yi halin mahaifiyarta mai kirki da tausayi ba." Sai ya ƙara jin babu daɗi akan dukan da ya yi mata, duk da ya ga alamun hakan daɗi ya yi mata, wataƙila ita kanta ta addabe ta ne shi ya sa. Don haka ya sanya a ransa zai watsi da duniyar hajiya Baaba y taimaki rayuwarta ko don mahaifiyarta har ta zamo ta ƙwarai.
Yamma na yi ko jiransa ya kira ba ta yi ba ta rinƙa kwaɗa masa kira ba adadi, wanda bai ɗaga ba sakamakon meeting da suka shiga.
Yana fitowa ya ɗauki wayar."Dad, Im under the weather, ƙarin ruwa ake mini." Zare ido ya yi jin abin da ta ce wanda muryarta ta bayyanar da zafin ciwon da take ciki.
"Subuhanallahi! Abu ai ya kai ga haka." Sai ta jinjina masa kanta kamar yana ganin ta yayin da take nishi tamkar waccce za ta haihu, sai ya tsinci kansa da jin haushin dukan da ya yi mata ganin har da ciwo.
Ya yi ajiyan zuciya mai ƙarfi da ƙoƙarin danne hakan a ransa ya ce,"Mun yi magana da aminina, ya ba ni haƙuri kan kar na kama miki gida ko na saya. Kin san ke ɗin wace ce? Ga shi matsalar Nigeria insecurity. Don haka, a shawarce ya ce na bari ki zana jarrabawarki, in ya so sai ki zauna a hostel, kin ga kafin nan mun dawo lokacin hutu sai ki rinƙa zuwa gida Abuja. What you say?"
Sai ta saka mishi kuka tana faɗin,"No dad! I said no, I wanna leave this house as soon as possible. So I won't take excuses."
Da ma ya san zai sha jarfa da ita cikin dubura ya ce,"Ok, kina son kidnappers su kama ki ko? Kuma wallahi har raping suke yi wa mace ko su bawa namomin daji gangar jikinki bayan sun kas.."
Ƙara ta saka ta kauda wayar a kunninta lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa don shegen tsoro ne da ita."Stop saying this, and don't be pessimistic. I'm just curious to leave the house."
Murmushin samun nasara ya yi don ya san yadda ta tsorota da wuya ta ƙi amince wa.
"Shikenan, zan yi haƙuri ai na kusa fara exam." Ta faɗa a sangarce tana tura baki. Sai ta ga zaman ta gama exam ta samu admission would be better da zama gida ɗaya da Hajiya Baaba don takurawa rayuwarta za ta yi.
Duk suna kan wayar take wannan tunanin domin ita ta ɗauka ya katse ganin dogon lokacin da ta ɗauka, but to her suprised he was on the call sai ta ji ya ce,
"Ki rinƙa zuwa islamiyar da haddar kin ji. Yanzu zan tura miki kuɗi a account ɗinki."
Ba ta san lokacin da guntun murmushi ya suɓuce mata ba." To dad, I will as you suggested." Ya saki dariya."Good." Ya ce sannan ya kashe wayarsa.
"You can force a horse to the river, but you can't force it to drink the water. Zan je islamiyar in ya san wata ai bai san wata ba. Ba sai na ga damar yin karatun ba? Tun da ba uban wani zan yi wa ba." Ta ce tare da ije wayar a gefenta.
"Yanzu da yake ke shashasha ce kin haƙura za ki zauna ya yi ta dukanki kamar ya samu jaka? A maimakon ki ta da fitina dole sai an canza mana gida muci gashin kammu. Ashe fitinarki ba ta yi miki amfani ba."
"Mu ci gashin kammu, ko ki takurawa rayuwata? Hajiya rigimarki kawai ta isa tashin farko a makaranta na ganni under probation. Haka kawai, ki rinƙa kunyata ni a gaban ƙawayena. Matuƙar na amince hawan jini za ki ɗora mini, domin ba na tantama har da rigimarki, ya sa mom ta tsani zaman Nigeria."
Tsananin mamaki ya sa ta kasa cewa komai sai zuwa can ta ce,"Ko kaɗan ban yi mamaki ba, ai halinki ne butulci. Abin da za ki saka mini da shi kenan. Oh Allah ka cire mini raina akan wannan banzar yarinyar na huta. Wallahi kin ci sa'ar ƙarin ruwan da ake miki da sai na yi ƙasa-ƙasa da ke."Zuɓɓura ba ki ta yi tana harararta.
Ajmal da kanshi ya je har islamiyar ya bada haƙuri tare da yi musu alƙawarin hakan ba zai ƙara faruwa ba. Tare da roƙon su duk abin da ta yi su gaya masa zai yi maganinta.
Jannah sai ta ji babu daɗi komawarta islamiyar domin a ganinta ƙasƙanci zai jawo mata amma kasancewar babu yadda za ta yi, kan dole ta shirya cikin doguwar riga da gutun hijabi iya kafaɗarta, ko al'qur'ni ba ta ɗauka ba ta fito.
A falo ta samu Hajiya