Showing 78001 words to 81000 words out of 137802 words
Chapter 27 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
Tsaki ta yi ta zauna tana faɗin,"Ko me za ka faɗa a taron oho, bayan na riga na yanke magana kuma babu fashi."
Ajmal ya ɗago idanunsa yana kallonta ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ma ya huta, domin da ya san in ya dawo abin da zai faru kenan, da ya tabbata acan har duniya ta naɗe in ya so matarsa ta bi shi can. Tun yana yaro take shigar masa hanci da ƙudundune ga shi ba ta sake zani ba, rana tsaka tana ƙoƙarin shigo masa da wata aba can, wanda ko a tarihin mafarkinsa bai taɓa tunanin rayuwa da ita ba, ballantana a zahirce, don haka a ransa ya sanya ayi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma, ai maganarta ba ta Allah ba ce.
"Kai ina ba za ta taɓa yiwu ba bindiga a ruwa. Da wane ido zan kalli abokanaina da mutane na nuna ta amatsayin matata ina matsayin malami, sai ta nemi aura mini 'yar tasha. Yariyar da ko Kur'ani ba ta sauke ba ballantana aje maganar hadda da manyan littafai." Ya furta a cikin ransa zuciyarsa a dagule.
Ummu ta ɗago tana kallon Jannah da ba ta wani damu ba, domin ta ɗauki maganar kamar wasa gani take ba ta da right ɗin da za ta yi mata auren dole.
Tausayinta da na Huzaifah suka sanya hawaye taruwa a gefen idanunta, musamman Huzaifah da ya mutu akan sonta, ba shi da buri sai dai maganar aurensu.
Kallon tausayi ta ƙara mata lokacin da ta ga sai danna wayarta take ba tare da damuwa ko da yake za ta iya mata uzuri don ba ta san wace ce Hajiya Baaba ba, don in har ba'ayi auren ba za ta iya iƙirarin tsinewa iyayensu wanda ba za su so hakan ba. Ba tare da ta sani ba hawaye suka fara shatata a fuskarta.
"Kai this is absolutely impossible! Auren nan ba zai taɓa yiwu ba. Huzaifah shi ya dace da ita kuma yana matuƙar ƙaunarta, don Allah Hajiya Baaba ki tausaya rayuwarsu."
Cikin zafin nama ta yi kanta za ta zabga mata mari. "To don uwarki sai ki hana in kin isa ba wai ki tsaya kina zagina da turanci ba don kin ga ban yi boko ba. Akan me gida bai ƙoshi ba za a bawa dawa."
Da sauri ta matsa bayan Ajmal ta ɓoye domin ita ba ta san maganar zuci ta fito fili ba.
Miƙewa ta yi tana gyara zaninta."Wallahi kun ji na rantse in har ni na haifi Muhammadu sai an yi aure nan, don haka ban ga amfanin taron nan ba, in dai ba so ake na sanya fitinar dole a ɗaura a yau ba."
Ta ja numfashi tana girgiza tare da balla ma Jannah harara da ta ɗago ido tana kallonta tana dariya domin har yanzu ba ta ɗauka da gaske take yi ba. Ba tare da ta kula da bidiyon da take mata ba ta ci gaba da cewa,
"Idan Jannah ba ta da hali da tarbiya ni ina sonta a haka, kuma in bai rufa mata asiri ya aureta ba wa zai aure ta. Kai Muhammadu a gabana kake nuna ba ka son haɗa zuriya da 'yar ƙanwarka wanda kuka rage mini ku biyu tal a duniya, sai na ce sam ba ka yi wa Halimatuu adalci ba. Ka ƙi aminta da auren 'yarta ɗaya tal aduniya."
"Haba hajiya na gaya miki ki daina ce mini bani da tarbiya. Sai wani maganar aure aure kike yi, kin san babu yadda za a yi ni kamata ace wai zan auri ustazu kuma mara wayewa. Wallahi ko driver ba zan iya ɗaukarsa ba domin tuƙi zai rinƙa na rashin wayewa. Abin kunya ne na gaya wa frinds ɗina wai zan yi aure da mijin da zan aura. Wato irin rayuwar gidadancin da matarsa take yi kullum cikin ƙumbiya-ƙumbiya da hijabi da safa da niƙabi kike son na je na yi? I know values, noms, and dignity.."
"Rufe mini ba ki banza kawai! Kunyar gareki? Kamar kin ci ƙwadun ɗan akuya haka kike. Ga yi nan tun ba a je ko ina ba kin fara girban abin da kika shuka domin kan idonki ake nuna ba a son rayuwa dake, ko shi Huzaifah da kike cewa yana sonki, ba za ku daɗe ba zai wartakoki ki zama ƙaramar bazawara saboda rashin kunya da mugun hali irin na ki."
"Ai gara na yi rayuwar zawarci da rayuwa da wanda kike son haɗa ni da shi, ballantana na san Huzaifah yana mugun sona ba zai yi mini haka ba. Kune dai kuka ɗauki mace baiwa kuna ganin in har ba ta iya girki da kula da miji ba ba za ta iya zaman aure ba, amma shi kansa a waye yake ya san 'yanci da hutu." Ta ce ba tare da shakku ko kunyar wani daga cikinsu ba.
"Tsakanina dake fa duka kawai ya rage amma kin daɗe da zageni tatas, domin duk wanda ya ke mayar maka da wannan maganar watarana duka zai kai maka. Ai ni dai wallahi Halimatuu ta haifar mini jaraba."
Banza ta yi da ita ba ta ce komai ba sai kaɗa ƙafa take yi cikin tsantsar rashin kunya da fitsara.
Ajmal ya yi shiru ya ma ratsa mai zai ce domin rashin kunyar da take yi ji yake kamar ya maƙure ta. Allah ya gani shi mutum ne mai tsananin son girma da kamun kai sam baya ƙaunar rashin kunya. Ko Mushiirat da take matarsa akwai lokacin da baya sakin mata fuska, ballantana ita da Hajiya ke son jawo masa raini ta haɗa su aure. Ai da ya yi rayuwar aure da ita ya gwammace ya mutu ba tare da aure ba. Duk rashin kunyar da take zuba wa sai ya zuba mata idanu kawai, burinsa ta fahimci wacce take son haɗa rayuwarsa da ita. In kuma ta yi gigin haka watarana sai dai a kawo musu gawarta domin bugu ɗaya zai aika ta lahira.
Miƙewa ya yi zai fice sai ya tsaya gab da ita ya fara da cewa,"A haka kike faɗin na auri 'yar da ba ta ganin ki da gashi? A haka kike son na kwashe ta na kai gidana Hajiya Baaba? In har kika yi mini haka sam ba ki yi mini adalciba ni da matana da muke zaman lafiya. Ina roƙonki tun wuri ki janye maganar auren nan kafin na canza mafa kammanni na yi wa wanda za ta aura asara don ni ko da gida da mota ba zan karɓa ba, saboda na tsane ta bana son ta ko mai kalarta ba na son gani."
"Aikin banza na san dai mugun halinta ka tsana amma ba Jannah da take son kowa ƙin wanda ya rasa ba, don ta fi matarka mai kama da doya. In dai don halinta ne ai hannunka ba ga ruɓewa ka yanke ka yar."
Ya buɗe baki zai yi magana sai ya kasa ya girgiza kansa idanunsa suka kawo ruwa ya fice daga cikin gidan.
"Na riga na gama magana kowa ya fice mini daga ɗaki kuka yi mini tsuru-tsuru kamar wacce ta yi ƙarya ko sata, in kuma sata na yi sai a gaya mini abin da na sata na biya." Ta daka musu tsawa tana faɗin hakan daidai lokacin da Aby ya miƙe ya bi bayansa amma ina har ya tada motar ya figeta cikin tsananin fushi.
Sum-sum suka miƙe suka fice ban Jannah da ta dawo gabanta ta tsaya bayan ta ije wayarta akan kujera.
Kallon uku saura kwata ta yi mata tare da miƙe wa.
"Bari na je na yi sallah don na ga kamar rigima kike ji ko da yake sallar ba ta dame ki ba sai kin ga dama."
"Idan bana yi ma ba damuwarki ba ce Hajiya Baaba, tun da na ga ba tare za a rufe mu ba." Ta bata amsa tana girgiza ƙafa tare da ƙara shan gabanta bayan ta fara tafiya.
"Allah ya tsare ni da mutuwa a rufe mu tare, domin wallahi na san duka da suburbuɗa za ki sha a hannun walakiri, kin ga kuwa da a rufe mu ta shafe ni, gara a barwa tsutsotsi naman jikina suyi watanga da shi."
"Wannan kuma ke ya shafa ba ni ba ai, in kin so ki barwa Kuraye ko a kwalar rigata." Ta ce mata tana girgiza.
"Jannah ki fita idanuna domin kin san Allah in kika cika ni zan iya zane ki da carbin nan yanzu. Kin san ke kaɗai kike mini fitsara a gidan nan na shanye da wata ce da tuni na yi ƙulin kubura da ita, ke ɗin ma albarkacin uwarki kike ci duk da albasa ba ta yi halin ruwa ba."
"Ai wallahi fitsara yanzu na fara matuƙar kika ci gaba da haɗani da wancan bagidajen. Ina 'yar minister ki rinƙa haɗani da shi, ai ni sai dai na auri ɗan shugaban ƙasa ko gwamna."
"To shikenan, sai mu zuba ni da ake shege ka fasa. Ai da uba ake ado ba uwa ba, sai ki gaya mini me ubanki yake da shi? Shi kansa rakuɓewa ya yi jikin 'yata yana cin arziki, don haka baku da komai."
"Allah ya kyauta kuma ya fi ƙarfin ki kira shi makwaɗaicin tun da duk abin da yake samu a jikinta aiki yake mata da guminshi yake."
"Jannah ki matsa na yi sallah ga shi can an tada sallah kafin na fasa bakin rashin kunya."
Harara ta zabga mata jin me tace sai kuma ta ja gefe ta matsa tana huci.
"Ko da yake sam bai kamata na tada hankalina ba, domin dad shi yake da ikon aurar da ni, in kuma na ce bana so babu wanda ya isa ya yi mini dole, ko ita 'yar taki a ƙarƙashinsa take." Ta faɗa tana zauna wa a kan kujera.
"Au haka kika ce? To zan nuna miki wannan makwaɗaicin uban na ki ba shi da kataɓus 'yata ta mai da shi mijin-ta-ce ta shanye shi da kuɗinta.
"Dama tuntuni nake zargin da saka hannunki mom take yi wa dad wulaƙanci ga shi nan zargina ya tabbata."
"Ba dole ta yi mishi ba ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi a tashar wahala da ƙasƙanci zai sauka." Ta amshe maganar.
Haushin abin da ta faɗa ya sa ta saka kuka tare da ɗaukar wayarta ta fice daga falon ta yi sashin su Ummu tana jan majina.
"Wawiya wacce ba ta san me yake mata ciwa ba, har wani ƙarfi uban na ki yake da shi da za ki alfahari da shi. Ma gani Allah ya kaimu su dawo sai ya haɗa auren in zai iya." Ta shige bayi tare da kunna famfo.
LONDON
"Kai ni fa wallahi kaina ya ɗaure! Wai mai ke faruwa ne, mai ya sanya Hajiya Baaba za ta yanke wannan ɗanyen hukuncin? Gabaki ɗaya na shiga cikin ruɗani!" Ta furta tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar ana buga mata guduma, domin ji take kamar ta rufe ido ta ganta a Nigeria.
"Rose, please give bottle of water and paracetamol." Ta ƙwalawa Rose kira tana faɗin haka tare da dafe kanta tana kallon dad da ya kasa cewa komai sai karanta wasiƙar jaki yake tun bayan da ta kira wayar.
Karɓar maganin ta yi ta ɓalla ta watsa a bakinta ta kora da ruwa tare da shanye ruwan kofin tas, sannan ta ƙara miƙa mata akan ta siyaya mata, wanda sai da ta shanye duka, domin ji take bakinta ya bushe babu ko ɗigon miyau.
"Shin wane irin lamari ne take shirin ginginmo mana gabagaɗi babu shawara? Wani abu ta yi mata, ko kamata ta yi tana harkar banza."
"Never! Karki ƙara danganta 'yata da wannan." Ta ji muryar dad ya daka mata tsawa yana faɗin hakan.
Kallon shi ta yi ba ta ce komai ba ganin yadda yake tada jijiyan wuya.
"Na san wace ce 'yata, na san me zata aikata." Ya ƙara faɗi tare da komawa ya zauna.
Takowa ta yi zuwa inda yake zaune yana huci ta kama hannunsa tare da zama a gefen kujerar.
"Jannah fa 'yarmu duka kuma mafi soyuwa a garemu. Kawai na shiga ruɗu ne ya sa na faɗi hakan. Wataƙila ba ta gana sanin wace ce ita ba shi ya sa take son gingimo abin da zai sanya ta kasa zaman lafiya, domin mundin ta tursasa auren nan sai Jannah ta zamo sanadinyar wargaza zumuncinmu da Ya Muhammadu. Sam jannah ba matar da za a nema wa wani bane, don ko wanda take so ya aure ta sai ya yi matuƙar kai zuciya nesa zai iya zama da ita."
Saki ya yi ya kauda kansa bai ce mata komai ba domin duk laifin ta yake gani don ita ce ta ɓata komai kuma ta ruguza komai.
"Kai ina jin Hajiya Baaba wasa take mini, ko kuma ta yi hakanne don na dawo da tunna ta kasa ba sanar dani dalilin son aurar da ita.
Miƙewa ya yi bai ce mata komai ba zai shige ɗakinsa.
"Please injiniya, say something don't go." Ta kama hannunshi tare da marairaice fuska tana faɗin hakan kamar za ta yi kuka, wanda ya sa ya koma ya zauna tamkar umurni ta yi mishi amma bai ce komai ba zuwa can ya ce,
"I was very surprised Halima, ace kin iya buɗe baki kina faɗin 'yarmu doesn't has table manners."
Kanta ta dafe jin abin da ya ƙara faɗin tare da furta
"Ya salam! Please understand me, I didn't mean that."
"Even if you mean it, ai duk laifinki ne da kika kasa bata tarbiya, saboda rashin yafiya kika gudo da ita Ƙasar da take da bambanci da addininki da al'darki. I really regreted the day I came to stay with you." Ya ƙarashe maganar yana kallonta cikin ɓacin rai tare da ɗorawa da cewa,
" Na san wace ce Hajiya Baaba na san artabun da na sha da ita, in har ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta. Baba Bukar ne kuma ba shi a duniya. Sam ba zan ja da maganar ta ba, domin Jannah ta samu miji kamar Ajmal abin alfahari ne a gare ni, kuma sannan ina son ta auri ɗan ɗan'uwanki saboda za ki fi jin zafin rashin bata tarbiyar da ba k.."
"Enough injiniya, saboda na nemi shawarar ka sai ka fara gasa mini maganganu? Kuskure na riga na yi kuma ba zan iya gyarawa ba, don haka ban ga amfanin zama kana gasa mini magana kamar 'yarka ba."
Ta nisa tana share zufar da ya keto mata a goshinta tare da faɗawa kan kujera ta rintse idanunta, saɓanin