Showing 21001 words to 24000 words out of 137802 words

Chapter 8 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt


"Mom said you should join us breafask. "
"Ok. "Ta miƙe tsunbul dama cikin ta karyawa yake sai dai ba ta ga yadda za ta yi ta sha koko a cikin ta ba.
"Ke Jannatuu ina za ki? "Ta tambaya ganin sun miƙe.
"Please Hajiyata Jannah. Ki daina ce mini Jannnatuu kamar wata 'yar ƙauye. "
"Ikon Allah! Ka kawo mu zamanin da 'ya'ya suke gudun sunayen su, sai ƙalƙalar banza.
Da sauri suka fice ba tare da sun damu da kiran da take musu ba.
"Hajiya is so dramatic! Kuma haka kuke zama da ita? " Ta tambaye ta cikin dariya.
"Tab! You never see anything, sai ta haɗu da Yaya Ajmal. "Ta ce mata dai-dai lokacin da suka shiga cikin falon.
"Good morning Dad. "Ta ce mishi tare da zuwa gafen sa ta tsaya. Shafa kanta ya yi cikin murna yana amsawa.
"Ya kika kwana da Hajiya da fatan ba ta takura miki ba? Na ɗauka tare da Nahlin za ku zauna. "
"No, bata ta kura mini ba. I slept like a baby."
"Masha Allah. "
Ajmal ne ya yi tsallama ya shigo fuskarsa a ɗaure sai dai ganin iyayen nasa ya sa ya saki fuskar tare da neman kujera ya zauna.
"Ina kwana Abby. Ammi mun tashi lafiya."Ya haɗa musu gaisuwar a jere.
Abby ya harare shi sannan ya ce,
"Jiya Alhaji bashir ya kira ni, ba ka je aiki ba, sai 10 kuma you took few minutes ka fita masallaci. "
"Eh Abby, na gaya maka zan je gurin aminina mahaifiyar sa ta dawo daga ummara na je gaishe ta. "
Ya giddira masa wannan karyar yana mamakin sa, domin ya san gurin sahibarsa ya wuni.
"You have to engaged, committed and be productive. Ka san kaine babba a gurin aiki so kome ya faru the blame will be on you. "
"I will Abby. "
Ya faɗa a gajarce don ya tsani a yi masa fada a gaban kanninsa.
"Oh na manta little sis na ka, na gurin ƙanwata Halimatu, da nace ka ɗauko ta ka ce ba ka da lokaci. She has arrived. "
"Ok. "
Kawai ya ce tare da ɗaukar filet zai yi saving ɗin kan sa ganin Nahlin ba ta da ninya, kuma ya fi ƙarfin ya yi mata magana, wanda ganin hakan da saurin ta ta shi tare da karbar filet ɗin.
Sai ya miƙa mata tare da mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake ta kira ta whatsapp duk da ya san mai kiran, ya dai ki ɗauka ne don ta faye nacin kira at many times.
Haka kawai tun jiya da Hajiya Baaba ta ce mishi ya ci albarkacin ta ya ji ya tsane ta. Kowa a gidan ba ta dafa masa kafa, amma daga zuwan ta har yaci albarkacin ta, ga shi babu abin da ya tsana face ya ci albarkacin wani.


"Jannah ki gaida ɗan'uwan ki mana Ajmal." Cewar Aby yana kallonta.
"Ina kwana. "Ta furta cikin muryar da ba su da tabbacin ya ji.
Kansa kawai ya ɗaga mata, ya ci gaba da cin abinsa ba tare da ya kalle ta ba. Sai dinning ya yi shiru sai ƙarar cokula.
Jannah duk sai ta ji ta muzanta sakamakon rashin sabo. Ta rinƙa juya cokali har Abby ya gaji ya ce,
"Ki ci abinci, kar ya yi sanyi. "
"Toh. "
Kaɗan ta ci abincin ta ture. Ajmal ne ya fara miƙewa daga dinning din Abby, Ammi sai na dawo. Bai jira abin da za su ce ba ya fice.
"Ka tabbatar ka gaida Hajiya. "
Ya faɗi dai-dai lokacin da yake ƙarashe fita daga falon. Don shi ne kawai sai ya gama dama yake zuwa, amma kowa na gidan yana gama sallar asuba zai je tana amsawa a hamsheƙe tamkar wata sarauniya.
Sai dai ko kallon shashinta bai yi ba ya yi wa maigadi umurnin ya buɗe masa get. Hajiya Baaba na jin tashin motarsa ta rugo da gudu har zanin ta na shirin faɗuwa ƙasa, ta yi maza ta rike tana faɗi,
"Adamuu! Adamuu!! Wato wuyan ka ya isa yanka har ka isa ka fita gidan nan ba tare da ka zo shashina ba? "Taƙaraso harabar gidan tana faɗin hakan.


Ganin ta tsaya a gaban motarsa ya yi kamar zai buge ta aiko ta saka ihu da ƙara ta ce. "Dama ka sha faɗa mini na mutu ka ci gumba ashe da gaske kake. Jama'ar gidan nan, ku yi taimako wallahi kashe ni zai yi."
Dariya sosai ya yi ganin yadda ta ruɗe tamkar zata zare har zanin ta sai da ya faɗi saura siket.
Sai da ya ga ta firgice ya fice daga gidan dai-dai lokacin da mutanen gidan suka fito a razane.
"Fitinanniyar tsohuwa kawai! Ki ci zamanin ki ki ci na wasu." Ya ce yana dariya tare da ƙara wa motarsa wuta.
Gabaki ɗaya mutanen gidan suka yi turus! Ganin ta yi zaune tana nishin wahala.Aby ne ya ƙaraso da saurin tare da kama ta ya miƙar da ita tsaye.
"Subuhanallahi! Hajiya mai ya faru. "
"Wallahi ni da Adamuu a gidan sai dai no koshi. Ai dama na san baya ƙaunar ganina a gidan nan." Ta furta cikin muryar kuka.
Sai kuma ta ƙara sakin kukan tana ce wa,"Laifin ka ne ai, ka rasa sunan da za ka sa mishi saina wani can dangin dagiro wai siriki. Ga shi nan ya ɗauko mugun hali da bakin jini. Ya girma har ya fara tsufa, ko maganar aure ba'a yi na sa."
Ammy ta yi shiru ba ta ce komai ba, amma ta ji gashin abin da ta faɗa.
"Ki yi hakuri Hajiya, mu koma ciki zai dawo ya same ni, sai ya raina kansa. "
Wafce zanin ta ta yi da yake miƙa mata. "Ni ka kyale ni haka kawai an haifi mini jaraba 'ya'ya sun mai da ni tamkar maƙiyayar su kuma duk laifin matarka ne da ta ke musu huɗubar tsiya. "
Ammy dai ba ta ce ƙala ba sai ta juya ta tafi.
"In sha Allahu sai dana ya ƙara aure, a gayawa bokan ya yi kaɗan ina nan ina addu'a. "
Ba ta tanka ba ta ƙarasa shiga ciki a ranta tana addu'ar Allah ya sa ta gane. Haka kawai ta ɗauki tsana ta dora mata.
Jannah sai ta yi turus tamkar gunki a wurin. mamakin diramar da suke sha ya kamata. Ganin Hajiya ta shige ɗaki ta bita domin laifin ta take ganin saboda ta cika zaƙewa, don ko maigidan baya ikon da take yi.
"Kin ga ni da idon ki ko? Kina ganin cin mutuncin da ɗan matar nan ya yi mini. Kuma wallahi tsaya ki gani babu matakin da za su ɗauka. Sam! Matar nan ba ta iya tarbiya ba, domin ita kan ta tsoron yaranta take. Ni kuma na isa da ɗana sai abin da na ce a gidan nan. "
"Gaskiya Hajiya abin da kike yi is too bad. Hab, ya.. "
"Wayyo Allahna na shiga uku. Shi ya sa na ce wa Muhammad karya gayawa makirar matarsa zuwar jikallena, amma da yake baƙin sa ba shi da rufi, ya sanar mata ga shi tun kafin ta zo an kai sunan ta, ba ta ganin kowa sai su. Kai Muhammadu ka zo wallahi da sake a gidan. " Kuka wiwi ta shiga yi har da share hawaye da fyace majina tana kiran Abby da takaicin Ajmal ya ishe shi yana ta kiran wayarsa ya ki ɗagawa don ya san rigimar nan sai an yi sati ana yi.
"Tabbas ga inda mom ta kwaso rigimar ta. Barewa baza ta yi gudu dan ta ya yi rarrafe ba." Ta furta a ranta, amma a fili sai ta zauna a gefen kujera tana kallon ta yadda ta hakince tana neman numba a wayarta sai ka ce ta iya.
"Ingo kira mini Yaya Bala, shi zai yi sasanci a gidan. " Ta ce da ita fuska a murtuƙe.
Sai lamarin ta ya bawa Jannah mamaki matuƙa. Ta rasa mai za ta ce mata, don haka ta karɓi wayar ba tare da ta ce mata komai ba.
"Ki kira mini shi na ce Jannatuu. "
Ta faɗa cikin tsawa da ɗaga murwa wanda hakan ya ƙubular da ita, ta ije mata wayar ba tare da ta ce komai ba don ta tsani a yi mata shouting.
"Allah ka na gani, daga dawowarta an can za mata tunani. Bari ni ma dole na koma makaranta na iya karatun da, da ake mini rashin mutunci akai. Na san ƙwaƙwalwata ba daƙiƙiya ba ce. "
"Tab! Ana wata ga wata. An ya zan iya zama gidan nan kuwa? " Ta tambayi kanta cikin jimami. Lokaci guda nadamar dawowarta ya kamata, don haka ta wayarta don ta kira dad.
Kwana uku da dawowarta Nigeria ta yi matukar nadamar hakan, domin Hajiya ta hana ta sukuni. Abin da ya fi damun ta rashin barin ta isasshen bacci da ba ta barin ta yi, domin kiran farko na assalatu za ta ta she ta, wanda hakan ba karamin damunta yake yi ba.
Sannan inta tashi ba ta tsira ba domin dole sai ta buɗe ƙofarta sun yi azkar da karatun kur'ani. Anan tasha mamaki domin duk iskancin da Hajiya Baaba take yi da sani, saboda tana da ilmin ta daidai gwargwado. Domin in tana karatun kur'ani babu wanda zai raina mata, sai hakan ya bawa Jannah mamaki sosai.
Washegari da safe Hajiya Baaba tana zaune tana karatun kur'ani Jannah ta fito daga ɗakinta, ta zauna a gefenta tare da kunna datana ta hau online.
Tsaki Hajiya Baaba ta yi sai kuma ta daina karatun ta juyo tana kallonta ta ce,
"Tab! Aiko iyayen ki sun cuce ki. Ai wallahi duk wanda ya aure ki na tausaya mi shi. Ina amfanin mace ba ilmin addini? Ai gara sabar biredi dake, domin ban ga amfanin auren mace da babu ilmi ba. "
Ta ce tana kokarin miƙewa tsaye tare da rufe kur'nin ta bayan ta yi addu'ar gama karatun kur'ani.
Jannah kuka ta saka sosai ta ji zafin maganar da ta yaba mata.
"Hajiya ni kike kike gara sabar biredi da ni? Am illiterate? " Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.
"Ato 'karya na yi? Wannan ilmin nasarar da kike taƙama da shi zai cuce ci ranar lahira ne? Dole na sanya Muhamadu ya sanya ki a makaranta da wuri, don kar ayi zuwan zomo kasuwa, yadda mutuwa take wuf da mutane ta ɗauke ki. Shikenan halam kalam. "
Duk da cewar ba ta fahimci ƙarshen maganar ta amma sosai ta ji haushin ce mata gara sabar biredi da ita.
"Am not illiterate. I'm educated and am better than you that you can't even read names. "
"Dawo na ce dan uwarki dawo nan ja'ira. Zagina kike yi? Ai tun da kika ci bincin ta an gama dake. "
Jannah ta fice da gudu shashin Amy don ta yi bacci.
"Kyaci kanki haka kawai. Wai gara biredi da ni."


Kai tsaye ɗakin Nahlin ta nufa inda ta same ta, tsaye gaban wadrop ɗinta tana jera kayanta, da aka kawo ɗaga gurin wanki. Kwanciya ta yi a kan gado, tare da cire wayarta a key ta shiga yanar gizo.
Jannah da ke kallo bacci ne ya kwashe ta, amma duk da hakan, ba ta kashe kallon ba, domin sabon ta ne haka, don sautari ba ta iya bacci ba tare da ta kunna waƙa ba.
Ganin an kira sallah ba ta tashi ba, Nahlin ta bubbuga bayanta sannan ta tashi.
"It is time of prayer so get up and pray."Ta ce mata tare da nufar hanyar bayi. Alwala ta ɗauro tare da shinfiɗa dadduma ta tayar da sallah.
Jannah kuwa sashin Hajiya Baaba ta wuce bayan ta yi alwala ta yi sallah. Tun tana sallar calls ke shigowa, wanda rabin hankalinta yana kan wayar ganin mi kiran.
Da sauri ta sallame sallar ta ɗauki wayarta don ta kira shi, amma sai kiran mom ya shigo, wanda saboda ɓacin rai ta yi jifa da wayar kan kujera, ta fasa kiran gabakiɗaya.


Hajiya Baaba da ke sallah bayan ta idar ta ji dirin motar Ajmal, tun kafin ya shigo ta fasa yin azkar na sallah ta miƙe tare fita.
"Ja'iri ma za fito daga motar nan, yau ni ko kai a gidan nan."
Ganin ta tsaye tana jijjiga ya dafe kansa."Kai wannan tsohuwar ta zame mini ƙadangaren bakin tulu." Ya ce, tare da ƙin fitowa daga motar.
"Ai wallahi ko kwana za ka yi, sai na jira ka ka fito. Ka gama tozarta ni, ka kwance mini zani a kasuwa. Na tabbata da iyayenka ne, ba za ka yi musu haka ba."
Hamdala ta yi jin hon ɗin motar Aby." Yauwa zo nan Muhammadu, gara da Allah ya kawo ka, daidai lokacin da ake buƙatar ka, sai a yi komai a gaban ka."
Ta ƙarashe maganar tana isa gurinsa da ko gama parking bai yi." Dube shi mara kunya, ya kasa fitowa. So na ke ka zana mini tsakani da shi, don ko mutuwa na yi kar ya zo kan gawata."
"Suhanallahi ashsha! Hajiya mai ya kawo wannan magamar ke da angon naki?" Ya ce, cikin tsigar tambaya.
"Allah ya tsare ni da uren miji mai baƙin hali irin na sa, ai da haka uban ku ya ke wallahi ko kaza ba zan haifa da shi ba." Ta ba shi amsa.
Ajmal tsaki ya yi, ya galla mata harara ji ya ke kamar ya shaƙe ta.












COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.












Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093












Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K










*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 7-8*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"Allah ya kyauta ni ko mutuwa zan yi ba aure ni ma gara na mutu, da na auri mace mai hali irin na ki." Ya furta a a ransa, sai kawai ya yi shahada ya buɗe ƙofar ya fito.
"Sannu da dawowa Aby, Hajiya barka da yamma." Ya furta tamkar babu abin da ya faru tsakaninsu.
"Riƙe gaisuwarka Adamuu, daga yau ba na so, in dai akanta ne za ka nemi kashe ni na haƙura. Kai ni ko atiti kar ka nuna ka sanni, inda na gode ma Allah, sam ba ka yi kama da ɗana ba, sai dangin dagiro."
Shiru kawai ya yi yana kallonta domin shi kansa Aby ya ka sa ce mata komai.
"Mu shiga ciki mu sasanta. Sam ba ka gudun fushina Ajmal, kullum ina gaya muku ku rinƙa kiyaye doka don a zauna lafiya, amma kai ne babba babban banza, ka na girma kana cin kashi, saboda kullum da ga gareka fitinar take tasowa."
Ya yi shiru ko zai ce wani abu, amma sai ya ƙi cewa komai, yayin da ransa ya ƙara ɓaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login