Showing 18001 words to 21000 words out of 137802 words

Chapter 7 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

Tana gama faɗar haka ta shige cikin ɗakin da ta nuna mallakin ta don kar ta kara ce mata komai.
Ajmal bai shigo gidan ba, sai misalin goma da rabi na dare, don ya san a wanann lokacin yar rigimar ta yi bacci. Ko da Hamir ya so ya shigo da shi har ciki, amma sai ya bukaci ya yi parking a waje ya sauka.
Cikin sanɗa ya shigo zai ije mata hura da nonon da ya zame ƙa'ida kullum sai ta sha sai ka ce magani.
"Munafikin Allah! Ina za ka dawo ma za dawo na ce. Ai na ji karar bude get, labarai nake sauraro na yi ma za na kashe don na san haka zai faru. To dawo dan ubanka. "
Takaici da haushi suka cika shi, ji ya yi kamar ya wuya ya shake mata makogaro, domin ta saka shi a gaba. Ko iyayensa ba sa zagin sa, amma sai ita haka take tamkar jikar maguzawa.
Kamar ba zai juya ba sai kuma ya jiya ya watsa mata kallo yana ƙoƙarin barin wurin
"Ka dawo na ce Adamuuu ka na jima ko? Wallahi in ka tafi sai fushin nan ya shafi kowa, don gobe ba wanda zai karya ta daɗi. Ta shi zan yi tun asuba na fara masifa da bala'i. "
"Hajiya Babaa, na ce ki dena ce mini Adamuu! I really hate the way you pronounce it. Tun da kin ka sa kiran Ajmal please call me Adam."
Ya ƙarashe maganar cikin ƙunar rai da ɓacin rai.
"Umm, aikin bit in ji tusa. Da ba'a san asalin angulu ba, sai ta ce daga Ƙasar misrah ta ke. Inji uban ka da ga ƙauye ya fito ɗan kauye ne na gidi. Wallahi lokacin da ya fito birni komai bai iya ba. "Sai kuma ta sa kuka ta ci gaba da faɗin,
"Wallahi Allah ya isa tsakanina da ƙanina Hamisu. Haka kawai ka saka finitina ka gudo mini da yaya birni ga shi nan, zuriyana ba su da maraba da iyalan arna.
"Iyalan arna kika ce Babaa! "Ya tambaye cikin tsananin mamakin abin da ta furta.
"Ina maraban dabbe da faɗa? Bakiɗaya kun ɗauki ɗabi'ar yahudu da nasara kun ɗora ma kan ku. Ni wannan turancin ma da kuke yi shi ya fi ci mini tuwo a ƙwarya. Ƙiri-ƙiri ina gani ku zage ni ba ni da ta cewa. Ina ji ranar nan cewa ka yi ko myh God. Da ga ji zagi ne. Allah shi zai saka mini, don wallahi uwarka ka zaga na ni ba.
Takaici da dariya sun hana ya shi ce mata komai ganin ta yi shiru tana zare ido.
"Allah ya ba ki hakuri. Bar na je na kwanta bacci na ke ji. "Ya ce, tare da ƙoƙarin ficewa.
"Kan ka ake ji. Mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce "Kan ku ake ji ni wankana nake yi. "
"Hmmm. Sai da safe." Ya ce yana ƙoƙarin ficewa.
Ƙunƙunai ta yi wanda bai ji me ta fadi ba, don haka ya fara ƙoƙarin ficewa a ransa yana addu'ar Allah ya sa kar ta ƙara ɗago wata maganar kamar yadda ta saba, gamakin sa sai ya ji ta mike da sauri ta nufo gurin sa da yake ƙoƙarin fita.
"Ai na manta ni jikar mantau. Dawo maza Adamuu. Zo ga yar'uwar bakuwar turai ma za shiga ku gaisa. "
Ajmal ya tsaya da takaicin abin da ta ce. "Haba da tsawon dare nan, zaki ce na gaisa da ita? Dare ya yi ki bari sai gobe. Ba ni da lokacin ta. "
"To sannu agogo sarkin ƙa'ida. Ai dama na san ba'a abin arzikin da kai. Yar gidan Anty ka Halimatuu ne fa. Kar ka manta duk da bazarta kuke rawa, shi kan shi uban na ka da wa yake taƙama in ba da ita. Arzikin ta ka ci na daina fadarda nake maka, tana hutun gajiya bana son na tashe ta." Ta dasa aya cikin murya mai raɗa kamar wacce ta shinfiɗar da jaririn goye.
Ajmal ya yi tsaye sororo. Tabbas ya saba da gorin Hajiya Baaba, amma na yau da ban ne. Yarinya ƙarama take son ya je ya gaisar? Haba wuce nan. Shine har da yi masa gorin ba. Take ya ji wani tsanar Jannah ya kama shi matuƙa.
"Ki san kalaman da za ki furta mini, kuma wallahi kika sa ta raina ni, karya ƙasusuwanta zan yi kin san ban ɗaukar raini." Yana fadin haka ya fice daga ɗakin har yana haɗawa da gudu, yana jin lokacin da take fadin,
"To sannu ubana ko mijina. Ai gidan nan duk wanda ya so zaman lafiya dole ya yi wa Jannatuu biyayya."
Komawa ta yi ta zauna tana bambamin ta tare da kunna rediyon.
"Su kuma waɗannan 'yan rashin mutuncin cigaba da labaren su ka yi ba su jira ni ba."Ta faɗi tare sa kallon agogo, inda ta ga sha ɗaya da rabi.
"Oh ni jikar maigishiri! Haka lokaci ya tafi wancan mara mutuncin ya tsare ni da surutu zai ja mini makara gobe, ga shi ina da tashin asuba na badawa shalele girki, koda yar gwadashin ba dole ta ci ba. Miƙewa ta yi tare da kashe wutan falon ta fara tofe-tofen addu'a wanda ya zame mata ƙa'ida.


Jannah na kwance cikin bargo tana sharan bacci ba tare da ta san wainar da ake toyawa a falo ba, kasancewar tun takwas da ta shiga yin sallah ta yi mata sallama bacci take ji.
Yanayi garin ya yi mata daɗi sosai kasancewar duk da babu room heater a ɗakin amma yanayin ya yi mata dadi don babu irin sanyin London.
Ba ta tashi ba sai da aka kira sallah. Shi ma karar ƙwanƙwasa ƙofar Hajiya Baaba ya tashe ta.
"Ta shi ki yi sallah. Malalaci shi ne ya ke barin jam'i ta wuce shi."Ta ce tana buga kofar ɗakin da karfi.
Miƙa ta yi da salati tare da kunna wayarta. Karar tsakon mom ya shigo da ga kunnawa, wanda dalilin kiran da ta dame ta da shi tun a jirgi ya sa ta kashe wayar.
"Na tashi Hajiya Baaba! "Ta furta cikin murya kaukausa ganin kiran sallar farko ne ta tashe ta.
"Ma za ki yi nafila ki roki Allah ya ba ki miji na gari. "
Tsuka kawai ta yi jin abin da ta faɗa. Ta koma ta kwanta duk da ta san ba lallai ba ne ta koma baccin.
"Akan miji kika tashe ni cikin tsakar daren nan, sai kace ba ni da buri da ya wuce na aure. Ko guda nawa nake da za ki yi mini maganar miji oho. "
Komawa ta yi ta kwanta sai da ta ji limami ta tada sallah san ta janye bargo ta shige bayi tare da sauro alwala, bayan ta bata lokaci gurin wanka, don a lokacin har an sallame sallah.
Tana idar da sallah ba ta yi azkar ba ta ta koma ta yi kwanciyarta, tare da saka earpiece a kunnin ta don kar ta dame ta. Season na Korean film take kallo mai dadi mai suna penthouse.
Hajiya Baaba ta yi kiran duniya da ƙwanƙwasa kofa akan ta so ta karya ta ƙi fitowa har sai da ƙarfe goma da rabi ya yi.
Ranta ya yi matuƙar ɓaci don ita ta ɗauka bacci take yi. Tun asuba ta gama dama mata koko, kosai kuwa bakwai dai-dai Talatu kai nika an soya, amma sai watsa mata kasa a ido ba ta fito ba yanzu.
Tana murɗa kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya ta tasa a gaba tana kallo.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.












Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093














Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K












*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 6-7*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM








Tana murɗa kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya a gabanta.
"Ungo nan! Na ce ugo Jannatu. Uwarki kika yi wa banza ba ni ba."
Ƙarasowa ta yi ta zauna kusa da ita tare da rungumeta. "Haba tawan ni kaɗai, kin san bamu faɗa. "
Murmushi ta saki tare da kama hannunta. "Ke kaɗai na damu dake, amma kika wulakanta ni. Kusan awa ɗaya ina buga kofarki. "
"Hajiya bacci na ke yi fa. "Ta faɗa a sangarce cikin muryar shagwaɓa jin abin da ta ce.
"Kai dai rashin zaman Halimatu ya sa ta yi sakaci da koya miki addini? "Ta faɗa cikin razana da mamaki.
Sai ta ɗora da cewar, "Ko karatun kur'ani ban ji kin yi ba, kamar yadda muka saba a gidan nan, sai kika koma bacci kika rinka shafa bacci kamar rago. "
Haɗe rai ta yi jin abin da tace. A ranta take tunanin ina mom take da lokacin ta ballantana ta koya mata karatu, gara ma dad shine ma yake dan ƙoƙari har ta ita haɗa baki a gurin sa.
"Aiko da sake. Yaran gidan nan duk sun sauke kur'ani da hadda ke kina nan. "Sai kuma ta kaɗa kanta tana faɗin,
"Halima Allah ya yi mace mai taurin kai, ni da ubanta sam bamu da wannan zuciyar ta rashin yafiya. Haka kawai ki nisanta kan ki da kowa saboda wani kuskure da ya wuce."
Jin abin da ta ce hankalin Jannah ya koma kanta. "Yauwa Hajiyata. Don Allah ki gaya mini abin da ya faru tsakanin ta da dad wanda ya sa ta ki yafe masa. "
"Kiyi hakuri, sai da na ɗaukar mata alkawarin ba zan gaya miki ba, sannan ta yarda ki zauna a gidan nan, amma na san dole watarana su gaji da kumbiya-kumbiya su sanar miki. "
Taɓe bakinta ta yi "To koma dai mene ne su suka sani. Na yi nisa da su ta yarda bazan cigaba da ganin abin da ke faruwa tsakanin su ba. "
Janyo plaks din koko ta yi tana faɗin, "Manta da su shalele, can suka sani. Ma za janyo kofi musha koko da ƙosai da na yi mik... "
"Koko da ƙosai kuma Hajiya? "Ta tambaya cikin muryar mamaki.
"Eh koko da kosai fa wanda ada yake gararan iyayen ki shi na dama miki, a tunanina za ki yi murna da hakan tun da kin gaji da cin abincin nasara."
"Ni ban gaya miki na gaji ba. Kuma ruwan tea zan sha da soyayen dankali na fi karyawa sha biyu da rabi."
"Umh! Sannu haihuwar turawa. Yanzu nufin ki watsa mini kasa za ki yi kamar na jiya. Aiko in dai ni jikar mai gishiri ce bazan kara miki girki ba, sai dai kije duk inda za ki ci kici, ai dama na lura kin fi son cin na wancan kinibiyar salon a mallake mani ke kamar yadda aka yi wa ɗana. "
"Dama kin hutar da ran ki. "Ta furta a ranta a fili kuwa, shiru ta yi tana jin ta na bambami ba ta tanka ba, sai ta kwanta tare da daukar remote zata canza tasha.
"A'a, a'a bar mini tashana ina kallon al'adun Hausawa, ki canza mini da wani yaren banza. " Ta fadi tare da wafce remote ɗin a hannunta, yayin da ta yi fici-fici da ido tsabar masifa.
Dariya ta yi ta san duka haushin ta ki shan koko ne, sai ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta kunna kallon ta ci gaba da kallo.
A falon Ammi tana tsaye a gaban dining tana shirya abin karyawa ita da Nahlin. Yar autar ta Ummita ta fito daga bedroom ɗin su da alama lokacin ta tashi tana goge idanu.
Da sauri Nahlin ta ɗauke ta tana dariya tare da nufar bedroom na su don ta yi mata wanka. Bayan ta yi mata wanka ta shirya ta cikin rigar da siket na kanti, kasancewar weekend ne ba school.
Ammi ta sumbace ta tare da faɗin,
"Maza kije ki kira ƙanwar ki ta karya in Hajiya ta yarda. "
Miƙewa ta yi da sauri. "Ba dolen ta ba, ni wallahi ɗakina zan dawo da ita da ƙarfin tsiya don ba za ta ji daɗin zama da ita ba."
"Taɓ! Aiko kina da aiki in dai Hajiya ne. "Ta ba ta masa tana ƙoƙarin zama.


Nahlin ta fita hannunta riƙe da Ummita. Da sallama ta shiga falon. Jannah ce kawai ta amsa gaisuwar, amma Hajiya ko kallon inda take ba ta yi ba.
"Ina kwana Hajiya. "Ta faɗi ba tare da ta ji mai za ta ce ba.
Shiru kawai ta yi sai motsi da bakinta da ta yi, wanda ba za ka gane mai tace ba, don kamar motsin sakamakon goron da take tauna ne.
"Little sis, watching film? Ta faɗi tana leƙa wayar Jannah dake kwance.
Miƙewa ta yi tare da daga mata ido bayan ta kashe kallon tana kallon ta.
"Morning sis. "
"Morning my sis. Hope you sleep well? You know Nigerian weather doesn't like London and mosquitoes everywhere. "
A'a na yi bacci sosai, ai Hajiya ta sa maganin zauri. So I must say I enjoyed it. "
"Good. "
Ta faɗi tana kallon Hajiya da ta yi fiƙi-fiƙi da ido jin an ambaci sunan ta. Dariya ya so ya ƙwace mata amma ta dake.
"Allah ya sa ba yi dani ake ba eh! Don na fi ƙarfin mutum ya san da wanda zan yi. "Hajiya ta ce tare da ƙara ɗaure fuska.
Dukkanin su babu wanda ya amsa mata, sai Nahlin ta ɗauki wayar Jannah tare da kunna kallon film da take kallo.
"Korian film sis, you do like it? Ni ko they are not cup of my tea. Infact I don't have interest. "
"Really"Ta tambaye ta cikin mamaki sai ta ɗaga mata kai.
"Kin ga ni kuwa da ga su sai Nigerian film I'm fan of them, kuma sam Korea ba sa film mara ma'ana unlike to Hausa movies I didn't say all sometime they do try. "
"Allah ko? Ko na fara kallo ne? Kin ga dama admission na ke jira. "
"Gaskiya I recommend you should start, you will enjoy it. "Ta ba ta amsa tana kallon ta.
"I will sis, since the recommendation is from you. "
"Ok, lemme send penthouse. If you don't have interest discard them."
"Sure, why not."Ta karashe maganar tana mika mata tsadaddiyar wayarta.
"Here you are little sis. "
"You will gonna enjoin it."
Dariya suka yi sannan Jannah ta miƙa hannu ta na kiran Ummita da ke kallon ta.
Hajiya Baaba ta cika ta batse sai dai ba ta ce komai ba, sakamakon rabin hankalin ta na can gurin tunanin yadda za ta yi ta canza dabi'un Jannah, da ta fahimci akwai ƙaracin kula da ibada kuma ta koyi cin abincin gargajiya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login