Showing 45001 words to 48000 words out of 137802 words

Chapter 16 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

Baaba ita da me aikinta da ke shirin tafiya. Ba ta ce mata komai ta bi ta gabanta ta wuce fuskarta kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa.
"Ki kika sani kije kuma wallahi ko namanki gunduwa-gunduwa aka kawo mini ba zan ce komai ba, sai dai ma na yi murnar an raba ni da fitsara da rashin kunya.
Tana jin abin da ta furta amma ba ta ce komai ba saboda ba ta da lokacin ta. Tunaninta yadda za ta kalli 'yan islamiyar wataƙila su yi mata dariya, wanda ta ɗauki alwashinnsai ta fasa musu baki.
A harabar gidan suka same shi zaune yana jiran ya ga fitowarta ko za ta ƙi. Sam a zuciyarsa bai yi tunanin za ta fito ba, ga mamakinsa sai ya ga ta fito tana kubbure-kubbure, wanda hakan ya ƙarfafa masa gwuiwa, domin tun safe yake tunanin in ba ta fito ba ya zai yi da rigimammiyar tsohuwar da ko gaisuwarsa ba ta amsawa tunda abin ya faru.
Ganin za su fita ya daka mata tsawa yana faɗin,"Ke dan ubanki, ina kayan islamiyarki, ko ba'a ba ta bane?" Ya ƙarashe maganar yana kallon Nahlin, wacce ta fara magana cikin tsoro tamkar ita ake tuhuma.
"Tun ranar da aka kai ta, na ba ta ta sanya, sai ta ce sun yi mata girma." Cewar Nahlin tana zare ido. Ita kuwa ko a jikinta ta nuna, duk da cewar ta yi matuƙar tsorata da shi, kasancewar har yanzu ba ta manta zafin dukan da ta ji ba.
"Yanzu suna ina?" Ya tambaye ta. "Ɗakin Ummu-Kursum." Ta ba shi amsa. "Ma za je ki ɗauko mata ta sanya, kuma gobe in Allah ya kaimu zamu koma karatun asuba, sai ku shirya."
Ɗaga masa kai ta yi ta juya cikin sauri, ganin har sun fara latti saboda tsayawa jiran ta da ta yi.
Kan dole ba don ta so ba ta juya don ta karɓi kayan ta saka ganin babu fuskar wargi."Jarababbe kawai! Na ga wanda ya isa ya tursasa ni na je." Ta furta tan wurga masa harara a fakaice wanda har ya shige sashinsa.
Kayan sun yi matuƙar yi mata kyau tare da amsar fatar jikinta, duk da cewar ita ba ta ga hakan ba sai cika take tana batsewa akan an yi mata dole.
Fakan idanunsa ta yi ta zabga masa harara tana turo bakinta wanda kamar zai taɓo gini.
" Mugu azzalumi jarabbe kawai!" Ta ce tare da jan tsuka mai ƙarfi. Sai kuma tsananin baƙinciki ya ƙara rufe ta."Mom, duk ke kika ja mini wannan bala'in don da kin dawo babu wanda ya isa ya biyo ni ya duke ni." Ta ce tana jin tsanarta na ƙara shigarta mai tsanani.
Ganin yana ƙoƙarin ciro belt ɗinsa ya sa ta ruga da gudu hanyar fita da sauri har tana buge kanta da get wanda ta ji zafi sosai.
A islamiyar ma, ba wani mai da hankali ta yi ba, abin da aka hana ta shi ta cigaba wato danna waya, don har aka gama karatun aka tashi, ba ta motsa ko da bakinta da ninyar yin karatu ba.
A hanya sun taso za su dawo gida. Nahlin ta kama hannunta tana dariya ganin yadda take shan kunu.
"Haba 'yar gidan hajiya Baaba, ki saki ranki mana ko laifin ya shafe ni?"
A maimakon ta saki fuskar kamar yadda ta buƙata sai ta ƙara ɗaurewa tana faɗin,
"Please Anty, muje gida na tafi ɗakinki, I wanna sleep jiya ban yi bacci ba, ina kallon film ɗin nan da na tura miki Abyss. Kuma na san ba za ta barni ba, ganin magariba za ta ce sai na yi sallah, kawai zan bari inna tashi cikin dare na haɗa."
"Humh." Ta ce cikin ranta ba tare da ta san mai za ta faɗi ba, domin lamarinta ya girmi tunaninta. Ƙara gasganta maganar Ammy ta yi da akan tarbiyarta. "Kina da ƙoƙari, kin ga wannan da kika tura mini? I haven't watch episode three."
Cikin mamaki take kallonta."Lallai ba kallon za ki yi ba, don ni a kwana biyu na kaga kallon shi.
"Ina za ki haɗa kanki da ni Jannah, ke da rayuwarki gabakiɗaya ne, sai dai kici ki kwanta.
Sai ta yi dariya jin abin da ta ce tana gyara zaman wuyan hijabinta da take jin ya shaƙe ta."To waye ba ya son hutu Anty Nahlin?
Girgiza kanta ta yi alamun babu tan ƙoƙarin buɗe ƙofar get ɗin gidan don su shiga. "Yau am full of excitement. Kin san an kai kuɗin sadakin Yaya?" Ta ce lokacin da suka shiga cikin gidan.
"Ni kuwa am neither happy nor sadness." Wa kenan, aka kai kuɗin aurensa? Ta tambaya cikin rashin kula.
Duka ta kai mata tana dariya."Ba na son iskanci, wane Yaya muke da shi a gidan, kuma jibi Ummu Kursum za ta dawo?"
"Don Allah?" Ta tambaya yayin da fara'arta ya ƙaru."Aiko zan ji daɗi sosa, na yi murnan jin hakan."Sai ta canza maganar zuwa na aurensa."Ai gara ya yi auren ku huta. Ni dai ina gama secandary, na samu admission na huta."
"Allah kin yi wa Ya Ajmal, mummunar fahimta amma sam ba shi da matsala kawai dai ba ya son rashin kunya ne."
"Haka ma za ki ce Anty Nahlin? For goodness sake, mai na yi masa ya kama ni ya rinƙa duka kamar ya samu jaka, amma kike faɗin haka. Anyway, da ma haka danginku suke, komai babu wanda ya iya sai ku. Ku yi ta criticizing mutane, bayan kune on the wrong part. The same with mom, alway criticizing dad."
Dariya ta yi tare da kama hannunta sai kuma ta ɗaure fuska ta ce,"Let's change topic, before I loose my temfer akan abin da kike faɗi."
"You better not to do, because I said the truth." Cewar Jannah.
A maimakon ta tafi ɗakin Nahlin kamar yadda ta yi shawara, amma sai ta fasa ta wuce sashin Hajiya Baaba ta sanya key a ɗakin tare da kunna waƙa ta ƙure ƙarar ta yadda ko ta dame ta da bugun ƙofar ba za ta ji ba.
Washegari da asuba bayan Ajmal sun dawo daga massalaci. Yana shiga ɗakinsa ya zauna azkar ya yi, sannan ya ɗauko alkur'ani yana karanta suratul Tauba cikin muryarsa mai daɗi da fitar da ƙira'a.
Yaran gidan suka yi sallama suka shigo a tsanake ya karanta musu karatu sannan suka fice. Tun da Nahlin ta shigo take addu'a a cikin ranta da Allah ya sa kar ya tambayi Jannah, wanda cikin sa'a bai tambaye ta ba har suka kammala karatun.
A ƙalla sai da suka yi kwana biyu suna karatun, amma ko da wasa ba ta taɓa maganar ba ballantana da yi ra'ayin zuwa, haka Hajiya Baaba ba ta yi mata maganar ba, don har yanzu hushi take da shi ko gaisuwarsa sai ta cika ta mule take amsawa.
Har sai da suka shafe tsawon wata suna karatun, babu wanda ya yi maganarta.
Da asuba suna tafe da Aby sun dawo daga masallaci. Aby ya kalle shi ya ce,
"Malamin su Jannah, ya yi mini ƙorafin sam ba ta mai da hankali, don bai taɓa ba ta hadda ta kawo masa ba. Sannan ba na tunanin yarinyar nan za ta iya karanta ko izifi biyar, wallahi rayuwarta a kwai gyara."
Tsananin mamaki ya kamasa jin abin da ya ke cewa,"Ka ce ƙasurgumar jahila ce? Haba! Da ma ai biri ya yi kama da mutum. Shi ya sa ta ke behaving without moral, because she is not religious. Wallahi duk wanda aka aurawa yarinyar nan an cuce shi."
Dariya ya yi jin abin da ya ce."Sam ba na ganin laifin yarinyar sai ta yar'uwata, haba don kawai kin je Ƙasar wasu sai ki manta addininki al'adarki." Ya ƙarashe maganar cikin damuwa.
"Jihadi za ka yi Ajmal, domin ita ɗin 'yar uwarka ne, kuma Halima ta gane kuskurenta.Ka ga ko dukan da ka yi mata ba ta ce komai ba. Don haka ka dubi zumunci ka rinƙa koya mata karatu, kamar yadda kake wa su Nahlin."
Gajeren tsaki ya yi."Damuwata Hajiya Baaba, kai ma kasan halinta. Bambanci take nuna wa tsakaninmu. Har yau da kyar take amsa gaisuwata, don kawai na yi hukuncin da ya kamata. Ba na son na shiga lamarinta ta ɓata mini rai, kuma ba kyaleta zan yi ba."
"A lailai Ajmal, wuyanka ya isa yanka. Uwar tawa kake gaya ma haka."
"Haba Aby kai ma ka san ina matuƙar haƙuri da 'yar tsohuwar nan, gabaki ɗaya ta addabi rayuwata."
"Haƙuri za mu yi da fatan gamawa da ita lafiya. Ka gode ma Allah ina ka yi aure sai ka zo za ta ganka."
"Shikenan, zan yi ƙoƙarin hakan. Ba ri na shig na yi karatu, kafin su zo."
"Af na manta ka ga an sanya ranar wata bakwai, sai ka yi ƙoƙari ka gama gininka duk da na ga an kusa. Ginin ne na ga ka iba da yawa. Ko kana da tsarin mata biyu ne?" Ya tambayesa cikin tsigar zolaya.
"Allah ya kyauta! Ɗayar ma da za'a iya raba ta gida biyu ina so, domin rigimar mata sai su, ko ita Mushiirat wani lokacin sai a hankali, kuma ni Aby ai gado zan yi mata ɗaya ta ishe ni."


"To lallai, ai dama kyan ɗa ya gaji ubansa. Matuƙar mutum ba zai iya adalci ba gara ya yi ɗayan."
"Haka ne, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar yana dariya da sosa kai tare da yin hanyar bangarensa.
Bayan ya biya Nahlin karatunta ya kalle ta lokacinnda take ƙoƙarin miƙewa ta tafi."Je ki kira Jannah ta fara karatu."
Jim ta yi kamar ba ta so aiken ba, sai kuma ta ije alkur'anin ta tafi sashin Hajiya Baaba.
Sallama tare da ƙwanƙwansa kofar ta yi."Uban mene ne za'a dame ni da sassafe?" Hajiya ta tambayeta ko gama wassakewa ban yi ba.
"Allah ya ba ki haƙuri, ina kwana."
"Da ban kwana ba za ki ganni, kinibibabbiya."
Cikin ƙubula ta kalle ta dama kamar ta san hakan zai faru shi ya sa ba ta so aiken ba."Ni fa bana son faɗa, Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu."
"Lallai yarinyar nan, kin raina ni. Ki kalli tsabar idanuna kice mini mafaɗaciya? Ko da yake ba laifinki ba ne, na san maganin abun ku..."
Maganar ta maƙale tunawa da ƙarshen abin da ta faɗa."Kika ce Ajmal ya ce a kira wa?"
Cikin rashin shakku ta furta bayan ta gyara tsayuwarta."Jannah."
"Oh, dukan da ya yi mata bai ishe shi ba, sai ya tsiri koya mata karatu don ya kashe saboda ba shi da uwarsa ba su da asara ko? To kije kice babu buƙatar hakan, ai yasan ni ɗin ba jahila ba ce zan koya mata. Wuce ki bani guri shashasha kawai."Juyawa ta yi tana hararta.
"Ɗan banza mara ta ido kawai." Ta ce tare da mai da ƙofar ta rufe, amma ba ta sanya key ba.
"Ya Ajmal, Hajiya ta ce ba za ta zo ba."
Miƙewa ta yi yana faɗin,"Ok." Ya yi sashin na ta.
Murɗa ƙofar ya yi ya shiga daidai lokacin da ta fito tana banbami."Ke Hafsatu, wallahi ki fita idanuna kin ji na gaya miki, ƙae dawowa ki ka yi kenan?"
Turus ta yi ganin wanda yake ƙoƙarin shigewa ɗakin Jannah."Wata uwar harara ta zabga masa.
Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu."Ma za zo ka fita, tun muna sheda juna, kafin muyi uwar watsi da kai."
"Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar yana nufar ɗakinta.












Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 13-14*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar tare da kai wa ƙofar wata uwar duka.
Cikin tsanannin tsoro ta miƙe daga baccin da take yi tare da zabga uban ihu domin ita a tunaninta ɓarayi ne suka zo, jin muryar Hajiya Baaba tana bambami ya sa hankalinta ya kwanta.
"Na shiga uku! Ashe gari ya waye ban yi sallah ba." Da sauri ta ƙarasa ƙofar ta buɗe daga ita sai figigiyar rigar bacci. Miƙa ta yi tana faɗin,
"Ni wallahi kin takurawa rayuwa kuma, gashi na buɗe bari na yi salla.." Maganar ta maƙale mata ganin mutum tsaye gefen Hajiya yana kallonta da take ta tsiya.
Ganin haka sai ta tsaya cikin tsoro tana zare ido, sai kuma ta janyo hijabinta ta sanya daidai lokacin da ta kalleta tare da zabga salati tana tafa hannu.
"Oh ni jikar mai gishiri, dama ba ki yi sallah ba, duk tashin da na rinƙa miki, kuma haka kike kwana sirara, so kike aljanu su shiga jikinki?"
"Haba Hajiya, ta ya ya za ki ce tsirara ba ki ga rigar bacci a jikina ba" Ta ce cikin ɓacin rai tana tura baki.
"Dalla gafara can, ina maraban dabbe da faɗa. Wannan yadin ƙyallen tatar kike kira kaya? "
"Ma za ki canza kaya ki fito daga yau karatu za ki fara da asuba, kuma minti goma na baki. Ya ƙarashe maganar zai juya ba tare da ya damu da abin da Hajiya Baaba take faɗi ba.
Ɗago idanunta ta yi ta watsa mishi."Karatu kuma da asuba bayan na islamiya? Ni fa wallahi.."
"Ke shaye-shaye kike?"Ya tambaya cikin tsananin mamakin ganin yadda idanunta suka yi ja.
"iInna lillahi! Shaye-shaye kuma? Allah ba bu abin da na ke sha." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.
"A'a Jannatu, biri ya yi kama da mutum. Kalli idanunki kamar an zuba jar bula, ki faɗi gaskiya tun kafin na sa ya canza miki kammanni don ba zan zauna da yar nanaye a gidan ba."
Haushin maganar da ta faɗi ya sa ta saki kukan da take ƙoƙarin mayar wa.
"Na gaya miki ba na shan komai, energy drink ne fearless, don na rinƙa kallo da daddare saboda bacci ba ya barina kallo. Kuma ko Adal za'a tambaya don shi yake siyo mini."
"Wane irin kallo kike yi da har sai kin sha fearless, ke da kike shirin exam and do you know its side effects at this your age kina shan waɗannan abubuwan?"
"Me kenan take sha, ko dai kayan mayen ne? Su Jannah an yi kyan ɗan maciji."
"A'a ba kayan shaye-shaye ba ne sai dai wani abu take sha don ya hana bacci, kuma yana da matuƙar illa a jiki. Ma za ki ɗauko wayarki na ga irin kallon da kike yi." Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan.
"A nan dai, kare ta kawai kake yi amma ka fito fili ka gaya mini tana kodimo. Kuma kallon da take yi na wasu mutane ne, da suke faɗin kucauu-kucauu na rantse ko ita ban jin ta san me suke faɗi. Ta yi ta sheƙa dariya tsakar dare ta hama ni sukuni, don ko hira ba ta yi dani sai dai ta barni kamar mayya." Ta ƙarashe maganar tana addu'ar Allah ya sa ya ƙwace wayar.
Juyawa ta yi ta shiga ɗauko wayar tana zabga mata harara sai ta ɗauko wayar ta miƙa masa tana zuɓɓura baki.
"Korian films ne, kuma ina fahimta don akwai subtitle da.."
"Can't you shut that mouth of yours?" Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan." Bai karɓi wayar ba ya juya ya fita yana faɗin,
" Ki tabbatar kin goge duk wani afilms dake wayarki. Ma za ki zo."
"Taɓ! Sannu ubana. Aikin banza kawai to goge ka yi, ai wallahi saina ɗauko ba kuɗi ba kuɗi ke aiki ba. Wayyo Allah har na ji tsoro kar ya ga chatts ɗina da Bud, yau da na shiga uku.
Galla mata Hajiya Baaba harara ta yi wacce take tsaye kamar tana son karanta abin da take faɗi a ranta.
" To 'yar zuga to babu abin da ya yi mini, na lura gabaki ɗaya kin daina sona." Ta ce cikin ɓacin rai za ta shige ɗakinta.
"A kan me zan so wacce ba ta san ciwon kanta ba? Ko ji dake da na ke albarkacin son da nake wa mahaifiyarki ne ya jawo haka, don gani nake kamar ita ne a gabana."
Ba tace mata komai ba ta ruga bayi tuna minutes ɗin da ya bata. Wankan aguje ta yi sallar da ina aka tsareta ba za ta iya faɗin abin da ta karanta ba.
"Muje na raka ki, ba zan bari ya cutar mini dake ba amana ka bani."
Sai ta ji daɗin jin abin da ta ce don haka ba ce mata komai ba suka fice da ga falon.Guri ta nema ta zauna riƙe da jarbi tan ja.
"Ina kur'ninki?" Kallon shi ta yi jin abin da ya ce."
"Ba ni da shi, bari na ɗauko app ɗin a wayata." Ta ba shi amsa ciki-ciki.
Tsananin mamaki ya kamasa ganin tana musulma amma babu kur'ani ko ɗaya a wayarta.
"Anty Jannah, ga kur'anina kiyi karatun da shi." Cewar Adal yana miƙa mata. Ƙarɓa ta yi tare da riƙewa batare da ta buɗe ba.
"Ke wai ina wasa dake ne? Za ki buɗe inda kike ki karanta." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Ni gaskiya, it been long I recited Kur'an. So I can't, just recite it to me kawai." Ta ce cikin kunkunai
"Jannah fa ƙasurgumar jahila ce, bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login