Showing 60001 words to 63000 words out of 137802 words

Chapter 21 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

don Allah babu ruwanki da ita." Ta faɗa cikin marairaice fuska.


Ba ta yi magana ba suka fice. Jannah ita take jan motar, suna tafe suna hira har suka isa.


"Matar nan 'yar rainin wayo ce, kalle ta fa yadda ta ci uban kwallliya sai danna waya take wai ba ta da lafiya." Cewar Jannah da suka shiga kicin ta ɗane saman drowers na kicin ɗin.


"Ƙila jinyar ba sosai bane." Ta bata amsa a gajarce tare da sakale gyalenta a saman ƙofar ta fara tattara wanke-wanken dake kicin ɗin.


Ummu ta yi nisa da aiki Mushiirat ta shigo zata ɗauki ruwa. Ganinta a zaune sai kaɗa ƙafa take tana danna waya da drink a hannunta tana kurɓa wanda ta ɗauka a frij sai zuba surutu ya sa ta yi mata kallon uku sauran kwata.


"Ke kuma fa da kike zaune tana aiki?" Ta yi tambayar cikin gadara.


"Ba komai Anty Mushiirat na kusa gamawa ni na ce ta barshi, girki zan ɗaura." Cewar Ummu cikin sauri gabanta na faɗuwa.


"Ok, sannu da aiki. Amma in ba aiki za ta yi ba ban ga amfanin zuwanta ba, don banga uban da ya sa ta zo ba."


"Ɗan dakata daga nan! Why are you insulting my father, for what reason? Kuma kin ga na yi kama da 'yar aiki ne da zan zo gidanki na yi miki aiki? 'Yar uwata na rako kuma ni da gidan ɗan'uwana ba zan zo ba sai dab dalili? Ba ki san wace ce uwata ba?"


Saukar mari suka ji tas! A fuskar Jannah wanda ta ji matuƙar shigar shi har sai da ta ji ba ta ganin komai na 'yan daƙiƙu.


"Na lura baki da kunya zai saita miki tunaninki. Sai me don uwarki za ta zama minister, ni iyayena an gaya miki kwasan kashi suke yi?"


"Kika mare ni?" Ta furta cikin tsananinn mamaki tana jinjina kanta.


"Na mare ki ko za ki rama ne?" Ta bata masa cikin gadara.

"Anty Mushiirat, please stop, act matual. Don Allah karki biye mata." Ta faɗa tana riƙe ta tare da kallon Jannah da take cika tana kubbura.


"Ki bari sis, kin san Ya zai ɗauki hukunci mai za fi kar kiyi mata rashin kunya."


"Mai zai hana ba sai kin tambaye ni ba, domin bana bin bashi."Ta bawa Mushiirat amsa sannan ta ɗaga hannunta iya ƙarfinta ta kwasa mata mari, ba tare da ta damu da maganar da Ummu take mata ba.


Tas ta ji ta saukar mata da nata gigitacccen marin har saida ta ji kanta ya sara.


"Ni kika mara?" Ta tambayeta cikin tsananin mamaki.


"Ok, a tunaninki kin mari banza kenan?"

"Yau zan sauke miki fitsarar da ke damunki don sai na canza miki kamanni." Kamata ta yi ta shaƙe tana kai mata duka ta ko ina.


"Wayyo Allah na shig uku! Don Allah ku daina Anty Mushiirat, kar ki yi kisa." Ummu ta faɗa cikin muryar kuka.


Kasancewar ƙarfi ba ɗaya ba sai ta ci ƙarfinta. Sosai ta ji ta takura da shaƙar da ta yi mata. Duk ƙoƙarinta na son ta ƙwace amma ya faskara, ganin tana shirin kaita barzahu kawai ta kai hannu ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka mata a goshi iya ƙarfinta wanda ya sa ta sake ta da sauri tare da ƙwala razannane ƙara.


"Wayyo na shiga uku! Ummu kira mini Bab, wallahi yarinyar nan 'yar daba ce." Ta faɗa cikin ihu.


Ganin aika-aikar da ta yi sai jikinta ya ɗauki rawa, domin ita kanta tana tsoron jini.


Hanyar fita ta nufa amma sai riƙe ta mau." Ai yau sai na ga uban da ya tsaya miki."


Sosai Ummu ta sa kuka tare da ɗora hannu aka don duk yadda take ganin lamarin ya zarce tunaninta.


Waje ta ruga don ta kira maigadi sai kuma daidai lokacin motar Ajmal ta sawo kai.


Da gudu ta nufe shi tana kuka da kiran sunasu don ta rasa yadda za ta yi masa bayani ya fahimta.


"Me ke ya samu Mushiirat ɗin kuma me Jannah ta aikata." Ganin ta kasa mishi bayani sai kuka take ya sanya ya ruga zuwa cikin gidan domin ya ji wani ƙara da ta ƙwala jin motarsa.



"Innalilahi! Mai ya same ki? Kanki jini yake zuba."


"Wayyo bab, ashe gidanku da 'yar daba ba ka gaya mini ba, ka cuce ni ga shi yanzu ta illata ni." Sai kawai ta faɗi luuu ta suma.


Tsananin tashin hankali ya kamasa ya ruɗe iya ruɗewa ya kalle ta da ita kanta ta yi nadamar aikatawa.


Ya nufeta yana kiran sunanta tare da girgizata amma ba bu numfashi sai ya ruɗe matuƙar gaske.


Da gudu ya cicciɓeta zuwa mota kafin ta yi wani yunƙurin guduwa ya sanya key ya kulleta tare da yi wa ummu umurnin ta shiga mota.


Sai ta yi duru-duru tana kallon ƙofar falon da ya rufe ta kamar ba ta son zuwa. Tausayinta ya kamata sai ta ƙara sakin kuka tana tunanin halin da za ta kasance.


Wata uwar tsawa da ya daka mata ya sanya ta shiga motar babu shiri.


Ganin ya kulle ta sai hankalinta ya yi matuƙar tashi sosai. Wayarta ta ɗauko ta kira dad yana ɗauka ta saka masa kuka tare da zayyana masa abin da ya faru. Hankalinsa ya tashi sosai jin abin da ta aikata.


"Hana Jannah, ya za ki je har gidan mata kiyi mata haka? Wannan saɓa doka ce."


Kuka ta saka tana faɗin,"Na rasa yadda zan yi ne dad kashe ni ta so ta yi, sam ba ta da imani."


"Ok, ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru. Matsalar Abby kin san yana Chaina shi da mom."


Shiru ta yi ba ta ce komai ba ganin haka ya datse wayar hankalinsa a tashe.


"Wayyo Allahna! Bab, ka yi mana tsakani da yarinyar nan. Tun ranar da ta zo gidana na ga tana mini kallon banza." Ta ƙarashe maganar tana sakin ƙara don harda ƙara zuzuta lamarin take yi.


"Kar ki damu za ki ga abin da zan yi mata. Na rantse sai na canza mata kamanni ki jira ni ina zuwa. Ke Ummu tashi na kaiki gida." Miƙewa ta yi cikin rashin dabara.

Yana shiga gida ya buɗe falon ya kama dukanta iya ƙarfinsa har sai da ya gaji don kansa ba tare da ya ji tausayinta ba. Tun tana kuka har sai da ta kasa.


Can ɓangarensa ya kai ta tare da kaita library ɗinsa ya kullu yadda za ta yi ihu babu wanda zai ji ta. Kayan kwana biyu ya ɗauka ya fice daga gidan. Daga asibiti hotel ya kama musu akan na kwana biyu bayan ya kashe wayarsa.


Tsananin tashin hankali ya kama Hajiya Baaba jin abin da ya faru.


"Wallahi kin ji na gaya miki ya illata mini jika hukuma za ta raba mu, don da biyu kika tura su gidan."


Ranta ya ɓace sosai musamman da ta kira wayarsa a kashe sai ruwan bala'i take yi ta ƙi barin kowa ya huta, don kujera ta ɗauko ta zauna a harabar gidan tana masifa sai kuma tasa kuka.


"Allah ya isa tsakanina da kai Adamuu! Akan bare za ka nemi kashe yar uwarka? Wallahi ina yi ido biyu da kai hukuma za ta raba mu." Ta furta cikin kuka ganin har zuwa lokacin ba ta dawo ba ga shi dare ya yi.


Sallah ma cikin rashin hayyaci ta yi shi. Kuma ta rantse duk wanda ya yi girki a gidan sai ta hukunta shi, yadda Janaah za ta kwana ba ta ci ba haka kowa zai kwana, wanda babu yadda za su yi sai dai suka sha tea a ɓoye.


Ta yi kuka ta yi bala'i ta yi matsifa tun tana kiran wayarsa har sai da caji ya ƙare ta sanya a aji.


Ammy ita kanta tasha kuka ta ci alwashin matuƙar ta ganshi sai ta hukunta shi, saboda ya cutar da ita.


Tsananin tashin hankali ya ƙara kamata ganin goma har da rabi, babu ita kuma an neme shi ba'a samu ba.


A wanann lokacin ta tasa bala'i suka ƙara komawa gidansa, amma sun kaɗa sun juya maigadi ya sanar masa da babu ita a gidan, bisa gargaɗin maigidansa wanda ba zai iya karyawa ba don kar abincinsa ya ƙare, amma shi kansa ta ba shi tausayi don tuna tana kuka har ya daina jin kukanta.


Kan dole suka dawo gida suka zauna jugum-gujum. Ganin tashin hankalin da Ummu ta nuna ya sanya Hajiya Baaba ta ji tausayinta suka zauna a falonta suna jimamin lamarin.


Cikin dare bacci ya gagare su. Ummu zazzaɓi ya rufe ta tun tana kukan ta kasa sai dai ajiyar zuciya, domin ta san tana cikin mawuyacin hali ga shi Aby ba ya nan.


Shi kansa Aby Hajiya Baaba ba ta barshi ya rintsa ba, don ya gode wa Allah da ya sanya na shi a garin abin ya faru da bai san halin da zai shiga ba.


Dad ya shiga matuƙar damuwa sosai, musamman da in ya kira wayarta ta gama ringin ba za ta ɗauka ba, wanda ya san dole akwai abinnda ya faru da ita, don ko hushi ta yi da shi duk inda ya yi kira biyu ba ta ɗauka ba to ana uku za ta ɗauka tana mita, amma har kira wanda bai san adadi ba ba ta ɗaga ba.






Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093








Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K


KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 17-18*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM






Ɓai taɓa tunanin yana da ƙarfin da zai iya tunkarar mom ya yi mata masifa ba. Ya kuma rantse in har wani ya samu 'yarsa ba zai ƙyale ba. Shiru ta yi masa don a yanayin da take ciki ba ta da lokacin da za ta kula shi. Ta san Ajmal ba mahaukaci ba ne da zai cutar da ita. Ko kaɗan ba ta ji zafi sosai ba, domin ta tsallake iya ta shiga har gidan mata ta mareta kuma ta nemi kashe ta saboda tsaurin ido da rashin kunya irin nata.


Washegari dole Aby ya dawo gida ganin yadda gidan yake ciki hankalinsa ya ƙara tashi sosai, domin da Hajiya Baaba da Ummu sun kwanta ciwo reras.


Ko hutawa bai yi ba ya bazama neman Ajmal. Kamar yadda ya rantse sai da ta kwana ta wuni sannan ya suka dawo gidan


Yana buɗe ɗakin da ya kaita Mushiirat ta sa ihu." Innalillahi! Na shi uku bab. Kar fa ka jawo mini ƙiyayyar dangin miji, kalli halin da take ciki."


Shi kansa ya matuƙar tsorata domin ta ɗauke dif babu numfashi. Kamata ya yi ya sanya a mota sai asibiti.


Drips aka ɗaura mata wanda ko minti biyu bai yi da fara shiga ta buɗe ido." Wayyo Allah! Dad, mom, na shiga uku. Wallahi ya Ajmal ba shi da imani." Ta ƙarashe maganar tana sakin gigitccen kuka.



"Ke ma za koma ki kwanta. Da ga yau sai ki gane bakin rijiya ba gurin wasan yara bane, don matata ba sa'ar ki ba ce. Mara kunya kawai." Ya daka mata tsawar da sai da ta ji 'yan hanjinta sun kaɗa, wanda ba bu musu ta koma ta kwanta sai ruwan hawaye ta ke.


Wani irin mugun tsanarsa ya kamata ji ta yi tamkar ta saka mishi guba ya ci a abinci ya mutu.


Sai da ruwan ya ƙare ya siyo mata abinci ta ci wanda ya yi mata dole ta ci. Ganin ramar da ta yi ya sanya ya ƙi mayar da ita gida, domin ya san in har Hajiya ta gan ta sai ta yi bandar namansa.


"Hello Ajmal, kana ina wane hali Jannah take?" Ya jera mata tarin tambayinsa.


"Muna asibiti ana ƙara mata ruwa."


"Ka san Allah in wani abu ya faru da yarinyar nan, sai ranka ya ɓace. Kuna da manya mai ya saka za ka ɗauki hukunci da kanka?"


"Aby, ka yi haƙuri yarinyar ba da ta tarbiya, ba ka ga yadda ta fasa mata kai ba, har sai da aka yi ɗinki."


Shiru ya yi don ya rasa yadda zai ɓullo ma lamarin don haka ya kashe wayarsa ya miƙe.


"Muje asibiti tana can ana ƙara mata ruwa." Ya fice da sauri gurin mota yana jin Hajiya na faɗin,"Mugu azzalimi, idona idon shi sai ya raina kansa."


Ko da suka je sibitin ba su same shi ba sai doctor Irfan da ya nuna musu ɗakin da take.


Tana gainsu ta sanya kuka." Hajiya Baaba, kashe ni ya so ya yi, ba ki ga dukan da ya yi mini ba."


"Ki barshi da ni, daga yau babu ni ba bu har abada. Na tsani matarsa babu ruwana da shi. Dubi yadda kika rame da ke ma jiki ba."


Ummu ta rungumeta cikin muryar kuka, amma sai ta ture ta daga jikinta.


"Ni ƙyale ni, babu ruwana da ku. ba zan ƙara zama da ku ba, hostel zan koma."


"Haba shalele, don Allah kar ki gudu ki bar ni, ki tsaya kika matakin da zan ɗauka."


Turo bakinta ta yi ba ta ce komai ba amma daga yau ta gama zaman gidan.


"Hello Sham, zan yi squatting a ɗakinki kafin na samu nawa."


Cikin murna ta ce,"Are you saying the truth, za ki dawo hostel? Inda gaske ne sai kin zo, kuma akwai wata friend ɗina she is married woman, mijinta ya hana ta zaman hostel ya kama mata gida a gari, don haka zan yi mata magana duk da na san akwai waɗanda suka yi mata magana, amma ba za ta hana ni ba."


"Ok, ba ni da lafiya ana ƙara mini ruwa, kije ki tamabayeta sai na tura miki kuɗin." Ta kashe wayar.


Sai da ta yi kwana biyu sannan aka ba ta sallama. Duk yadda Hajiya Baaba ke rarrashinta kan ta yi haƙuri, amma ta ƙi ta tattara kayanta.


"Yanzu shalele guduwa za ki yi ki barni? Don Allah kiyi haƙuri ki bari kiga matakin da zan ɗauka."


"Kyale ni dama na gaji da zaman gidan zuwan Ummu ya sa na fasa, amma yanzu babu wanda ya isa ya hana ni."


Hajiya ta fusata ainun ganin tun safe take rarrashinta amma kamar tana tunzurata.


"To shikenan kifi ruwa gudu, Allah ya raka taki gona." Ta ce tare da balla mata harara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login