Showing 57001 words to 60000 words out of 137802 words

Chapter 20 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

san shi ne kawai zai iya watsa mana ruwa. Don Allah ka yi haƙuri."
Ta furta cikin rawar murya tana shirin kuka.
"Rufe mini baki ja'ira, kin dai ɗauka ni ce marainiyar wayonki."
Bulala ya zuga mata wanda yasa ta canyar ƙara tare da miƙewa da sauri tana sosa bayanta va tare da ta damu da kayan da ke jikinta ba.
Ummu kuwa har ta fara kuka don ta san yau sai buzunta.
Ganin kayan da yake jikinta ya sa ya saki bulalar yana faɗin,"Ma za ku shirya ku same ni a falo, marasa jin magana kawai." Ya fice cikin ɓacin rai. Hajiya Baaba ta bi shi tana ƙara zuga shi, don ita ba haka ta so ba.
"Wai yau Allah ya taimake mu kayan bacci sun yi ceto." Cewar Ummu da ta miƙe ta nufi bayi.
Da sauri ta sanya key a ɗakin ta dawo ta zauna,"Wannan jarabben ba zai barmu mu huta ba duk da yabar gidan."
"Au zama kika yi kin manta yana jiranmu ko?" Da sauri ta miƙe jin abin da ta ce.
Cikin ikon Allah results ɗinsu ya fito kum duk sun cinye. Baƙaramin murna Aby ya yi ba ganin sun fito da sakamako mai kyau.
Washegari da safe suna Hajiya Babaa ta fito daga kicin tana faɗin,"Ani ma zaku raka ni gidan Adamuu, amaryarsa ta zo har sau biyu ban je ba.
"Ni dai ba zani ba, ku dai je ke da ita."
"Iko wallahi ba ki isa sai kin je, don haka ku shirya zamu je."
Kan dole ta shirya ba don tana so ba. Sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu.
"Hajiya bari na karɓo key gurin Musa direba na tuƙa motar." Ta faɗa cikin tsokana.
"Ke dakata, tsaya na ce ko!" Ta furata cikin ƙaraji tare da ɗorawa,"Ce miki akai na gaji da duniyar, ko mutuwa nake son na yi? Don haka ki bari na mutu maza su kaini ba mata ba. Ni da nake son ganin har jikokinki."
Dariya suka kwashe da shi duka ganin yadda ta firgice.
"Su Hajiya akwai dogon buri na kusa da ƙasa ana hangen gaba."
Uban tsaki ta yi ba ta ce komai ba ta shiga motar tare da kamewa a gidan gaba.
"Wow! gaskiya gidan Ya Ajmal ya tsaru. Ina mishi kallon ɗan ƙauye ashe ya san me yake yi. A rayuwarsa gidansa ne kawai ya burge ni." Ta furta tana kallon gidan cikin mamaki d sha'awa.
"A gida kam ya yi sai dai fatan rai ya mora. Adamuu ya yi ƙoƙari sosai, Allah ya yi masa albarka. Da ina shiri da maigidan nan kwana nan wuni."
"Taɓ!" Ummu ta ce a ranta domin za ta iya rantse yau ce ranar da ta ji ta sa mishi albarka.
Jannah da Ummu suka ciro wayarsu ana ɗaukar hoto da bidiyo za a yi posting, har da yi wa Hajiya Baaba bidiyo da take ta kare fuskarta tana zaginsu wai ta zo kwaɗayi.
"Gafara masu gida." Hajiya Baaba ta ce da ƙarfi.
Dariya suka kwashe mata da shi."Hajiya wa zai ji maganarki a irin wanann gidan."
Hannu ta kai ta danna ring bell wanda ya fargar da Mushiirat da ke tsaye da kaskon wuta a hannunta tana turare falon da shi.


Ta ije kaskon tare da nufar ƙofar tana takun yanga ta buɗe. Ganin Hajiya Baaba ce ya sa ta faɗaɗa fara'arta
"Barka da zuwa Hajiya ku shigo." Ta ce tana kallon su Jannah.
Ba su yi aune ba sai ji suka yi ta saki dariya ƙasa-ƙasa. Da sauri Mushiirat ta kalle ta sai dai ba ta ce komai ba ta rage fara'arta ta basu hanya suka shiga.
Jannah ta ci gaba da dariyarta ƙasa-ƙasa Ummu na ta zungurar ta da ƙafa amma ta ƙi, duk da cewar tana yi kamar ba da ita take ba, amma tasha jinin jininta domin ta ɗaure fuskarta.
"Don Allah kalli wani shiga da ta yi wai ita a dole amarya, ta yi wani cukus da it ko kyau. Haba ai ƙananan kaya ba su dace da ita ba. Wai 'yar lukuta kenan, dama na gaya miki ƙatuwa ce ki kalli ydda ta ƙara ƙiba. Allah matar Ya Ajmal in ta yi haihuwa ɗaya ba za ta ganu ba."
"Baki da kirki sis wannan ai cin fuska ne a gabanta in ta ji ki fa. Please ki bari." Ta furta daidai lokacin da Mushiirat ta shiga kicin don ta kawo musu ruwa.
"Ki barta 'yar banzan yarinya mai shegen ɗaukar magana, kin san halin maigidan ubanki zai ci. Muje gida saina farfasa miki baki, ai gara ita da kike kamar muciya."
"Ni fa ki daina zagin ubana dama dai uwar kika zaga ko a gyalena, amma dad bai yi miki komai ba."
Har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta yi shiru ganin Mushiirat ta fito daga kicin ɗauke da ƙaton tire da aka cika shi da abin motsa baki.
"Bismillah ban san za ku zo ba, yanzu zan ɗora muku abinci, bari na tashe shi yana bacci."
"Sannu ɗiyar albarka mun gode."






Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093










Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K














Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K


KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 16-17*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM










Murmushi ta yi idanunta na kan Jannah da sai zagaye falon take tana ɗaukar hoto da bidiyo, sai kuma ta miƙe.

"Bari na je na taso Sadauki bacci yake yi." Ta nufi sashinsa ba tare da ta ji mai za su faɗi ba.

Dariya ta ƙara kwashewa da shi sai kuma ta gimtse sakamakon wata uwar harara da Hajiya ta sakin mata.


"Aifa Sadauki inda babu sadaukan ba ina ruwan farakwas."


"Ke ko wallahi watarana bakin ki zai kai ki ga halaka ba kya ji ko?"


"Na nawa Hajiya." Cewar Ummu.


Harara ta zabga mata sai ta ɗauki filet ta zuba ferfesun kayan ciki."Umh, bari muci girki matar Ya Ajmal ɗan iyayi, Allah ya sa ta iya girkin."


"Oho, ko bai yi daɗi ba tafi wata da ko gas ba ta iya kunnawa ba." Hajiya ta amshe maganar.


Ba ta ce komai ba ta ibi ferfesun ta kai bakinta a wulaƙance sai kuma ta ƙara kai wa."Wallahi ya yi daɗi sosai." Ba ta saurari hajiya dake mata gori ba ta shiga aikawa cikinta tana lumshe ido.


Ya fito cikin farar jallabiya fara tas har ɗaukar ido take."Ah yau su Hajjaju ce a gidan?" Ya tambaya cikin raha da tsokana.


"Eh, na gaji da fushi da na yi na zo. Kamata ya yi kaje har gida ka ɗauko ni, na yi ko wata ne, amma da yake ba ka gayyata ba ka yi hakan ba."

Kauda zancen ya yi bayan ya amsa gaisuwar su Jannah yana faɗin,"Allah ya huci zuciyar kakata, daga yanzu sai kin gaji da zuwa."


"Rufa mini asiri matarka da bata da sakin jiki kamar ba ta murna da zuwana har na kwana?"


Da sauri suka kalli juna shi da ita wanda jin abin da tace ta ƙara ɗaure fuska, kuma dariyar da Jannah ta yi mata ne ya sanya hakan don ta fahimci 'yar rainin wayo ce.


"Kar ki yi mata mummunar fahimta har da rashin sabo amma ba ta da matsala."


"Ba wani nan Adamuu, kai ɗin ma ba wani kirki kake da shi ba, ina ga ka sanar mata da halina ne, ko da tazo gida gaishe ni ta yi ta fice, can sashin uwarka da take da iko da kai."


"Duk ba haka bane da kaina zan ɗauko ki sai kin gaji ki koma."


"Allah dai ya kaimu lokacin Jannah za ta yi aure, mahaifinku ku sai ya yi kewata can zan tare, kasan da yake ita sangartacciyace babu fus ba as dole ni zan rinka girki wa mijinta da rainon yaran."

"Wallahi ba na gayy.." Ta furta da sauri tuna Ajmal na wurin ya sa ta yi shiru tana zare ido.


"To rasa kunya ɓeran tanka kiyi magana yanzu in ban naushi bakinki sai na miki giɓi ba, ƙarya na faɗa."Ba ta ce komai ba saboda yana gurin.


"Allah ya kyauta! Aiko babu mace anan, ke Ummu ki rinƙa faɗa mata gaskiya, kuma saboda fitsara yarinyar nan saurayi ne da ita."


Gwalalo ido ta yi." Ni wallahi ba ni da saurayi."


"Ok, ƙarya na yi miki kenan, ranar bikina wane saurayi ne ya rinƙa miki mannin kuɗi?"

Ta yi shiru ta kasa cewa komai sai zare ido. Ganin haka ya juya tambayar ga Ummu da ta yi duru-duru.


"Huzaifah ne kuma ba soyayya muke yi ba, abokina ne."Ta fada a tsorace.


Hannu ta shiga tafawa tana salati."Ni kam yaran nan suna shayar dani ruwan mamaki, yanzu ke Jannatu har saurayi kike da shi?"


"Na ce miki ba saurayina bane, shi ɗin a.."


"Ke dallah can rufe mini baki! Ana wani abokantaka ne tsakanin mace da namiji."


Baki ta tura ba ta ce komai ba don ba ta ga amfanin maganar ba.


Miƙewa ya yi bayan ya gallah musu harara."Wallahi ku natsu ku kiyaye ni, kuna ƙanana babu macen da za ta rinƙa kula samari don duk wanda ya ɗauko carry over a makaranta sai na zane masa jiki.Hajiya, bari na shiga wanka zan fita." Ya ce yana tafiya daidai lokacin da ta miƙe tana wani yauƙi tabi bayansa.


"Ki koma gurin su. Na gaya miki matuƙar kika ga ƙannina ki daina mini wani salo da kwarkwasa, saboda ni mutum ne mara son raini. Rayuwar aurenmu ya zama sirri a tsakaninmu. Yanzu kayan da kika saka ya dace ki fita da su? Na yi miki maganar ki saka hijabi sai kika biyo ni haka. Ki sani matuƙar za ki saɓa umurnina, ki zama mara biyayya ba zan lamunta ba."

Fuska ta ɓata sosai kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce,"Ka yi haƙuri." Ta ɗauki hijabin ta saka.


"Amma bab, gaskiya ya kamata mu zauna muyi magana. Ina buƙatar mai aiki wacce za ta rinƙa taya ni aikin gida. Da kuɗina zan biyata. Gidan nan ya yi mini girk.."


"Look! Mushiirat, hakan ba zai yiwu ba daga ni sai ke a gidan nan, sai kin ɗauki mai aiki. Ina son sakewa a gidana ba in zan fito ba na rinƙa tunanin wata za ta ganni." Ya yi shiru ko za ta ce wani abu, amma sai bata ce komai ba don haka ya ɗora da cewa,


"Tarbiyarki da kamun kanki da son addininki ya sa na aure ki, don hak kici gaba da kula dasu domin kar zubewarsu su janyo miki matsala a gareni." Ya shige bayi ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Tsayawa ta yi jim kamar mai nazari sai kuma ta harari ƙofar bayin ta juya ta fita.


Bayan ya yi wanka ya shirya zai fita sagale da jakarsa. A lokacin ta gama girkin suna zaune suna ci. Jannah sai surutu take tana zuba santi domin ita kanta ta sara mata.


"Hajiya Baaba, zan wuce ofis sai na shigo gidan."
"Allah ya kai ka lafiya." Ta ce tana kai loma.

Ba su wani jima ba suka miƙe za su tafi domin Mushiirat kicin ta shige tana ta ayyukanta, wanda Hajiya Baaba ta ji haushin hakan ta yi mata sallama suka miƙe za su tafi.


Ɗaki ta shiga bayan ta yi musu umurni da su jira ta. Leda biyu ta fito da shi mai ɗauke da turare da sabulai manya ta miƙa wa Hajiya Baaba. Ɗayan kuma mai ɗauke da kayan shafa da turare ta ba su Jannah suka yi mata sallama suka tafi.


Su Jannah an fara zuwa makaranta a Jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U.). Wanka suke yi iya wanka ga shi sun samu ɗaurin gindi gurin mom, don sai da ta sai wa kowace motar ta da tsadaddiyar waya Iphone 15.Tamkar 'yan biyu haka suke shigarsu, kayansu iri ɗaya komai nasu.


Jannah jin kanta take ta zama babba domin yadda take nunawa ya girmi jikinta, duk da cewar ba ta da ƙiba Ummu na da jiki amma ba can ba.


Maƙudan kuɗi take kashe ma jikinta tana siyen mayuka na gyaran jiki da sabulai masu kyau. Ba fara ba ce, amma duk wanda ya kalli kalle ta sai ya ƙara yadda take haske da sheƙi da ɗaukar ido.

In kansu suke a wata sabuwar rayuwa kuma girma ya zo musu. Sun ɗauki girman kai da jiji da ɗagawa sun ɗorawa kansu. Ba kamar Jannah da a class ɗinsu indai ba ta ga akwai alamun ƙumbar susa ba bata kula ka.


A ɗan zamansu kowa ya san ita 'yar wace ce, saboda ji da kanta da taƙama da an yi magana sai ta fara faɗin kasan ni ko yar waye.


Sabod girman kanta da nuna bata son hurɗa da marasa class sai ba ta cika ƙawaye ba. Da ga Zainab Zeey, wacce take 'yar Kaduna kuma mahaifinta yana da muƙami a gwamnati, sai Shamsiya suna kiranta da Sham, daga Kano mahaifinta ɗan Kasuwane, sai kuma Aisha ita kuma daga Kebbi take, amma ba ta cika shige musu ba, domin kamar ba su da shi kamar su.


Duk jan kunne da Nahlin ta yi musu kan babu ruwansu da kowa karatu ya kai su. Da fari sun ji amma da ga ƙarshe ko sati biyu ba ayi ba aka san su a ajin saboda shegen surutu da girmn kai da taƙama. Ko shigowa za su yi cikin ajin makullin mota riƙe a hannu ana karkaɗawa.


Lokaci guda suka yi suna harda yin abokai maza guda uku. Musa wanda suke kiransa da Scietics da Ahmad sai Sulaiman. Duk rashin jin su sai dai ba sa wasa da karatu don suna cikin masu ƙoƙarin ajin.


Ranar Talata Ajmal ya kira Ammy ya sanar mata da ta tura Nahlin gidansa Mushiiirat ba ta da lafiya, sai aka yi rashin sa'a Nahlin tana da lecture harda test, don haka ta tura Ummu bayan ta ja musu kunne sosai.


"Kin san ni sai dai na yi miki rakiya don ban yi wa kaina aiki ba ballantana wata."Ta ƙarasa maganar tana yafa siririn mayafinta.


"Eh, sis tafiyar ce bana son na yi mi kaɗai, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login