Showing 69001 words to 72000 words out of 137802 words
Chapter 24 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
karatu." Jannah ta furta tare da shigewa bayi.
"A lallai wuyanki ya isa yanka ƙaramar mara kunya. Ai sai kije ki gaya masa." Cewar Nahlin.
Dariya Ummu ta yi." Ke da ya aiko ke za ki gaya masa, haka kawai duk kin bi kin takurawa rayuwarmu."
"Kan ku ake ji." Ta bata amsa tare da harararta ta fice.
Taba fita daidai lokacin da ta fito daga bayin."Wai a ƙwato ni daga ɓata, wato na kafurta kenan na shiga ɓata? Gani 'yar jujal jikar sheɗan." Ta ce cikin ɓacin rai.
Sai kuma ta sa kuka tana faɗin,"Wallahi Allah ya isa kuɗin da na biya, ni ba ma wannan ba yadda zan ita tsefe gashin nan in just one hour? Imagined."
Ummu ba ta ce komai ba ta fara tsifar don ta ga surutun cinye lokacin da ya ba su yake yi.
Ganin haka ta ɗauki masilla ta yi tare da ƙwala wa Talatu da Atine kira da su ta ya.
"Ya rinƙa wani behaving as if he is the most ethical and the most decent person in the world, bayan yaudaren kansa yake ɗan ƙauye kawai. We are in twenty first century he should have known that."
Kan dole babu yadda za su yi suka hau tsifar wanda kamar yadda ya basu awa ɗaya ba ta cika ba sai dai suka gama. Tsabar haushi ko lunch ba ta ci ba sai cika take tana batsewa.
Bayan sun gama suka je suka kwaso kayansu duka.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 19-20*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
LONDON
Mom zaune akan kujera da wayarta tana waya, oder take bayar wa na kalan furnitures ɗin da za a sanya mata a gidanta.
Dad ya fito daga ɗakin cikin shirin fita yayin da jakarsa sagale a kafaɗunsa sai ƙamshi yake yi.
Ɗagowa ta yi ta kalle shi tare da mai da kanta ta ci gaba da wayarta. Tsayawa ya yi tamkar gunki har sai da ta kammala ta kashe wayar sannan ta juyi ta kalle shi, bayan ta ije wayar akan kujera.
"Ranki ya daɗe na fito zan kai tsaƙon nan airport and daga nan I will heading to office."
"Ok, but amh. Mun yi magana da Governor I think we must go back to Nigeria within two weeks, because of the campaign and I can't go may be you will go on behalf of me an.."
"No way Halima." Ya ce tare da ɗaure fuska sannan ya ɗora da cewa,"You know I do not support you in to politics ina ganin it should be better ki bar maganar na..."
"Oh please stop Injiniya, will you represent me or not?" Ta tambaye shi cikin ɗaga murya.
"I will not cus am not you errand boy am you husband."
"Ok, fine." Ta kwashi tarkacenta ta shige ɗakinta daidai lokacin da ya saki tsaki ya fice daga gidan zuciyarsa a jagule.
NIGERIA
Nahlin ta tashi da asuba bayan ta yi wa su Adal karatu ta zauna tana ɗan gyangyaɗi tana jiran shigowarsu, amma har ta gaji ba ta ga ƙeyar su ba.
"Kai ni kam waɗannan yaran sun ishe ni, Ya Ajmal ya ɗora mini wahala. Miƙewa ta yi ta nufi sashin Hajiya Baaba.
Turus ta yi bayan ta buɗe ɗakin ganin har yanzu babu wacce ta farka da alama ko sallah ba su yi ba.
"Lailai yaranan ba su da hankali sun raina Yaya wallahi."
Duka ta kai musu tana faɗin,"Ku tashi marasa mutunci ayi ta maimata muku magana ɗaya, sai ka ce wasu kurame haba."
"Wallahi an takurawa rayuwarmu wai baccin safen mutum ba shi da ikon yi. Da hostel ne in bamu da lecture sai mu kai ƙarfe sha biyu muna bacci." Cewar Jannah.
"Aiko an yi asara." Ta ba su amsa sannan ta ɗora da cewa,
"Ba wannan ya kawo ni ba don ina da abin yi. Za ku yi karatun ko na kira shi."
"Taɓ! Allah na tuba, ai da wuya na haddace ko aya biyu gara Ummu na ga ta yi karatu kafin ta kwanta, kuma ta tashi da daddare."
"Ni ma bai zauna ba Allah." Cewar Ummu tana turo baki.
"Allah ya shirye ku wallahi. Yara sai kace kafuran farko, ko kafuran aljanu sun shiga jikinku. Ni kama bari na kira shi kun fi ƙarfina."
Riƙe hannunta suka Ummu ta ƙwace wayar tana faɗin,"Haba our unique Anty, it hasn't gotten to that. Yanzu zamu fito. A dai yi ma uren nan na ki mu huta."
"Allah ya sa ita ma ba kusa da gida za ta sanya a gina mata gida ba don ta takura mana."
Ta furta tana ƙoƙarin tuɓe rigar baccinta.
Dariya ta yi ta sa kai za ta wuce tana mamakin halin ƙanninnata da take matuƙar so sosai.
Bayan sun yi hadda suka dawo bacci suka koma sai gurin sha biyu suka tashi saboda jiya sai ƙarfe uku suka kwanta.
Suna zaune a falo suna kallo Nahlin ta ƙara shigo wa."Kenan kun sa zan rinƙa safa da marwa tsakanin sashin Hajiya da namu. Ku ba kwa tunanin sai an yi muku. Sai ku zo na koya muku abinci. Ina ga kawai mu yi shi a matsayin abincin rana."
"Lallai m Anty Nahlin, ɗan abincin da zamu koya wanda bai wuce na gwangwani biyu ba, shi ne za ki wahalar damu. Gaskiya ya haka Yaya ce ba."
"To shikenan, marasa son moriya ke Ummu wallahi kin shiga uku, da bakinki kike faɗin hakan. Na ji nice baiwa a gidan nan, mu je na koya muku kaɗan ni sai na yi abincin gidan. Mijina ya huta kuna ganin wahalar da kaina nake yi ko?"
"Mu ma na mu ai bai ce miki wahala zai sha ba tun da akwai restaurant Kuma da kuɗi." Jannah ta ce tare da canza tasha zuaa wanda suka ga ana kallo.
"Hmm, Allah ya kaimu lokaci zai nuna. Kun ɗauka zaman auren film ne, da daɗin bakin da suke muku ko."
Shiru suka yi ba su ce mata komai ba.
"Mu je kicin ɗin Hajiya Baaba ba sai mun je sashinku ba." Cewar ganin sun yi hanyar fita Jannah tare da nufar kicin ɗin.
"Kin san halin Hajiya Baaba kar ta samu da masifa."
"Muje mana ba iyayenmu suka tsiya ba? Ni wallahi ko kaɗan bana tsoronta." Bin bayanta suka yi suka nufi kicin ɗin
A kicin ɗin ta dage sai yi musu bayani take yi amma hankalinta ba shi a kanta yana wayarta da take duba chatts da Huzaifah ya yi mata.
"Jannah kina jina? Don na lura you mind isn't here." Nahlin ta furta.
Ije wayarta ta yi ta ce," Anty Nahlin stop waisting your time for the explanation. Kin san with the advanced of technology everything is easier. So you don't need to explain just give me the recipes."Ta ƙarashe maganar tana ɗora tukunya.
Baki Ummu ta buɗe cikin mamakin ƙarfin halinta."Uban me za ki dafa, wallahi kin san kika haɗawa Hajiya gobara ko kika ɓata mata kayan abinci za ki sani. You that when we were in hostel ba ta taɓa girki ba."
"Then wait and see, I will search everything on YouTube and watch. Yau za ki ci abincin da baki taɓa ci ba. Believe me sis, you will really enjoy it" Ta ce tare da balla mata harara.
Baki ta taɓe tana faɗin,"I see, yau mata za su yi girki. I can wait to see."
"To shikenan, if you insist. Bari Ummu sai muje sashinmu ta yi acan." Ta ce tana ƙoƙarin fita don ta ba ta haushi.
"Su waye a kicin ɗina ba na hana shiga ba don wallahi ban yadda da ku ba, saboda tun da kuka dawo ake mini satar nama. A da sai na yi sati da miyata cike da nama, amma yanzu ko kwana ɗaya ba ya yi."
"Allah ya kyauta mun fi ƙarfin satar naman miya sai dai muci."Ummu ta ba ta amsa lokacin da ta ƙaraso.
"Gaya mata sis." Ta ce lokacin da take ƙoƙarin kuna gas.
"A keee! Dakata karki haɗa mini gobara. Uban me za ki yi?"
"Girkin da kullum kike mini gori zan fara daga yau, saboda bana son na yi aure ki bini gidan mijina ki rinƙa mini tereren ke kike wa mijina abinci."
"Au to rasai, amma ba da kayan abincina ba ko?" Ta tambayeta jin abin da ta ce.
"Kin ga Hajiya Baaba, ki ƙyale ni karki ki sanya na manta abin da na kalla kuma."
"Yau na ga lukutar matsifa, ke da ba ki iya ba shine za ki ce rana tsaka za ki koya? To bari mu gani in tusa na hura wuta, an gaya miki girkin wasan yara ne. Kuma kika ɓata mini kayan abinci aljihun uwarki zai yi kuka." Ta ce tare da juyawa ta koma falo.
Bayan fitarsu ta gama ƙarewa gas ɗin kallo amma ba ta ga inda zata kunna ba.
"Talatu." Ta yi kiranta cikin raɗa tare da yafito ta da hannu.
"Na'am ga ni Hajiya." Ta ce lokacin da ta shigo kicin ɗin bayan Janah ta rufe ƙofar.
"Ki kunna mini gas ɗin nan." Ta miƙa mata ashana.
"Ai ba da ashana ake kunnawa ba, ashanar na kunna gawayi ne da Hajiya Baaba ke sanya turare."
"Oho, kunna mini to." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Talatu da take mata wami irin kallo ba.
"Kin ga yadda za ki yi nan Hajiya, ya kamata ki koya ko don nan gaba."
"Please don't lecture me, cewa kawai na yi ki kunna mini. Ce miki akai kuku nake karanta. Zan nuna ma mutanen gidan nan ni ɗin na iya kawai ba na son na yi ne. Allah na tuba girki har wani wahala yake da shi. Na san is so simple as eating food. Dallah ni in kin kunna fita ki bani guri." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka.
"Allah ya ba ki haƙuri." Ta ce tare da ficewa da sauri.
Ba ta ce komai ba ta ɗaura tukunyar tana 'yan waƙe-waƙenta da rawa.
"Umh, kamar na ga fa ta soya kayan miya ko?" Ta yi wa kanta tambayar a bayyane. Gnain ba ta tuna ba ya sa ta ƙara kunna video.
"Wayyo Allah ta soya kuma wallahi ni kam ba zan tsaya jira ba saboda am eager to start watching queen of tears, ga wan can jarababben ya sa mu hadda."
Sai kawai ta diddila mangyaɗa iya son ranta tare da kayan miyar ta kwara ruwa.
"Bari na saka mangyaɗa da magi yawa saboda nawa yafi na Ummu daɗi." Ta ce tana rawa da ƙafarta. Ta zuba magi da yawa gishiri ne ba ta cika ba.
Ruwan na tausa ta ibi shinkafar da tafi ƙarfin ruwan ta zuba ta juya ta mayar ta rufe tana shaƙar ƙamshin girki da ya ji uban spices har da wanda tea Hajiya take haɗawa da shi.
Mintinan da ta ga wacce ta yi girki a yourtube ta bawa girkinta ta iba sannan ta kira Talatu ta kashe mata gas ɗin ba tare da ta duba girkin ba.
"Na shiga uku Hajiya Jannah, kar dai har kin gama."
Wata uwar harara ta banka mata."Ni fa na lura dake muguwar munafuka ne, don ina zargin ke kike ƙara haɗa ni da Hajiya Baaba a gidanan, saboda shekaranjiya a gabanki na ibi nama yanka tara."
"Innalillahi! Don Allah kiyi haƙuri wallahi ba ruwana. Sam ba na shiga sabgar 'yan gida. Na dai tambaye ki ne saboda na ga ko kifin da kika sa na wanke bai isa dahu ba, ballantana naman kayan ciki masu tauri."
"To sannu 'yar iya sai ki koya mini girki ni da na koya a yourtube, kuma awannin da ta yi amfani da shi da shi na yi nima. Ke da kike baƙauyiya dake ji be ki fa, har wani girki za ki koya mini."
"To ai gas ɗin kaɗan-kaɗan kika saka yake ci fa."
"Dallah ni fita kiban gurin tun da kin gama mini amfani." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka.
Bayan ta fita kuma sai dawo da ta hankalinta tare ta tuna yadda gas ɗin mi girkin yake ci. Da sauri ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe tana kallon shinkafar da ta tokare tukunya ta yi cikin shige ga mai shanana.