Showing 48001 words to 51000 words out of 137802 words

Chapter 17 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

jin tana karatun sallah daidai, don duk lokacin da na takura mata sai ta yi ta motsa bakinta, wai ba ta iya karatu a bayyane ba."
" Please! Ni fa gaskiya ki daina kirana da Jahil.."
"Rufe mini baki banza kawai! Ƙarya na yi? Ai ni wallahi na ga sakarcin Halimatuu, da ta yi rainon ki kamar na tunkiyoyi, babu abin da kika sani sai fitsara da rashin kunya."
Ta buɗe baki za ta yi magana jin abin da ta ce ya daka mata tsawa ta yi shiru sai ruwan hawaye dake tsiyaya. Ta fakaici idanunshi ta zabga mata harara.
"Ban ga ana hararata ba sai idanu sun faɗi ƙasa." Ta ce tana jijjiga ƙafafunta ta ci gaba da jan carbinta.
Cikin ɓacin rai ta fara karanta suratul Amma da baƙinta da bai gama zaunawa a bakinta ba.


Kwashe da dariya 'yan ɗakin suka yi ban da Hajiya Baaba da Ajmal
"Inna lillahi! Anty Jannah, da ma ba ki iya karatun akur'ani ba, ƙatuwa da ke? Ko ni na izifina ishirinnda biyar?"
"Kai rufe mini baki banza kawai." Ta ce masa tare da kai masa duka.
"Wallahi kika ƙara dukansa sai na haɗa ki da gini ai gaskiya y faɗa. Jahilar banza kawai. Babu abin da kika sani sai iyayi da taƙama." Cewar Hajiya Baaba.
"Kin dai gani ko Hajiya, kin ga wacce kike karewa har kika tsaya don kar na bige ta?" Ya faɗa cikin takaici da mamaki.
"Tashi zan yi ni kam yanzu. Ka koya mata karatun, in ta ƙi ka yi mata dukan mutuwa ka ga tafiyata." Ta fice daga sashin.
"Ke kam kin ji haushi da auren mace irin ki gara zama gwauro. Ke Nahlin ki ɗauko mata bagadadi ki rinƙa koya mata. Na ba ta wata biyu ta gama. Duk ranar da ba ta yi ba, just inform me I will just seize her phone.
Kuka sosai ta saka harda su share majina ko tari ba ta yi ba ganin wacce take goyon bayanta ta kware mata.
Tsawar da ya daka mata ya sa ta yi shiru ta bi Nahlin da taje ɗauko bagadadi don ta koya mata.
Wunin ranar babu wanda ta kalla don ɗakinta ta kulle ta yi zamanta. Ko abincin rana ƙinci ta yi, babu abin da ya fi ƙona mata rai irin dariyar da suka yi mata. Ga shi ko da ta dawo haka ta sata a gaba da habaici da waƙe-waƙe.
Ta kira wayar dad ya fi sau nawa amma bai ɗaga ba, don haushi ko kallon numbar mom ba ta yi ba, don tana ganin duk ita ta ja mata wannan tozarcin.
Duk irin gargaɗin da ya yi mata ba ta ji. Ko da Nahlin ta fara koya mata ganin hankalinta ba shi gare ta share ta kama aikinta, wanda hakan ya yi mata daɗi ta ci gana da kallonta.
Washegari da asuba Nanlin ta zo ta tashe ta ko sallah ba ta yi ba suka tafi cewar inta dawo za ta yi. Ko da ta je babu abin da ta iya sai zare ido wanda hakan ya baƙanta ransa.
Bulala biyar ya yi mata sannan ya ce," Ma za ki shiga ɗakina ki gyara mini, it is you funishment."
"Ban iya ba." Ta ba shi amsa ba tare da shakku ba tana sosa inda ya duke ta.
"Allah ya isa mugu azzalimi, in sha Allahu sai an rama mini akan yaranka." Ta faɗa a hankali yadda ba zai ji ba.
"Je ki koya mata sannan ta gyara ɗakin da kyau. Kuma wallahi gobe in ba ki iya ba sai na lahira yafi ki jin daɗi."
"Ni fa gyaran ne I can't cus I don't know how to do chores."
"Ok." Ya bata amsa yana kallonta domin ya gama fahimtar 'yar rainin wayo ce.
"If that is the case then you will collect another cane." Ya ce yana ƙoƙarin ɗaga bulalar.
Da gudu ta ruga ta ɓoye bayan Nahlin ta ce,"I will don Allah kar ka ƙara dukana." Sai ta bi bayan hanlin da ta riga ta shiga ɗakin domin tare za su yi.
Suna shiga ta tsaya a ƙofar ɗakin tana toshe bakinta."I really hate this guy with my whole being. Had I know I will face this I should have not came back to Nigeria. Sam ba shi da imani, I know he has his intentions for threating me, and very soon zan bar gidan nan."
"Haba kar kice haka. Shi ɗin ɗan'uwan ki ne, kuma he is doing all for you onw good, you will enjoy it in the meantime. So please let's bare it ok?"
"Oh please don't change the topic. I beg you pardon for saying that. Believe me, he has his reasons. Ni wallahi na ƙosa ya yi auren mu huta."
Dariya Nahlin ta yi ta fara kakkabe Saman gadon tare da yaye bargon ganin ba ta da ninyar farawa.
Zama ta yi tare da ƙara toshe hancinta."Kai this smelling is awfull. Gaskiya ƙazami ne sosai, wari nake ji, wannan matar shi ta bani da ƙazanta Allah. Ji ɗakin is not well organized."
Tsananin mamakinta ya sa ta kasa cewa komai sai da ga baya ta ce," Kai anya na taɓa ganin 'yar rainin wayo kamar ki? Ƙamshin tsadaddan turaren na sa kike cewa wari."
"Eh ni dai wari yake mini, daga jin ƙamshin outdated ones ya ke amfani da shi."
in gyaran muryarsa kamar zai shigo yasa ta miƙe da sauri ta fara taya Nahlin gyaran. Kusan aikin ita ta yi don babu wani abin kirkin da ta yi.
"Na gama." Ta ce mishi tare da marairaice fuska ita a dole ta yi aiki ta gaji.
"Sai ki fita gobe in kin ga daɓa kar kiyi kayana na nan sai ki wanke, kin ga kuɗina ya huta. Daƙiƙiyar banza kawai." Fita ta yi cilin ɓacin rai tana ƙunƙunai
Tan shiga sashinta ta sa kuka." Wallahi na tsani zaman gidan nan, na ƙosa na gama kama hostel, ni gidan nan kowa haushinsa na ke ji."
Tsaki Hajiya Baaba ta yi tana faɗjn,"Ni ma na ƙosa ki tafi na huta da ala ƙaƙai da kunna mini waƙoƙin arna. Ke na fahimci iyayenki gajiya suka yi da jarabar ki suka tattaro ki suka kawo mini wahala." Jin abin da ta ce yasa ta ƙara sakin wani kukan.
"Allah duk mom ce ta janyo mini wannan musifar ba zan yafe miki ba."
"Kyaji da shi, shashashar banza uwar tanki ma ba ki darajata ba ballantana wani. In kin gama kukan shagwaɓar ga abincin ki can da aka gama barbaɗe shi an kawo miki kwaɗayayya kawai.
"Oh dai, ni dai ba zan ci wannan jagwalgwalon na ki ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar kwanon abinta ta shige ɗakinta.
Da ta tasa abincin kasa ci ta yi babu abin da ke mata yawo aka sai dariyar da suke mata da kalmar jahila da daƙiƙiya da suke ce mata sai maimaita kansu suke yi.
"Zan ba su mamaki sai na nuna musu ni ba jahila bace, zan dage na koyi karatu sai muga jahili a tsakaninmu, kamar ni da nake ɗaukar distinction a makaranta za su kira ni jahila."
Ɗakin Nahlin ta nufa inda ta same ta tana zaune a kan gadonta tana danna waya. Kaanciya ta yi kan gadon har sai da ta gama wayar sannan ta juyo ta kalle ta.
"Anty Najhlin please ki koya mini karatu, so na ke cikin wata ɗaya na iya karatu, zan nuna masa ba nahilci ba ne kawai bana son karatun ne."
"Ok, ba ki da matsala zan koya miki, kin ga Ummu ta ci gaba koya miki in ta dawo. You will like her she is outgoing and loquacious"
"Really." Ta ce tana murmushi wanda ta ɗaga maka kanta tare da miƙewa.
Dariya ta yi jin abin da take faɗi,"You really crack me up. Ni ma zan so hakan." Kin ga direba ya tafi ɗauko Ummu-Kursum, kuma na ji Aby yana faɗin kamar makarantarku zai mayar da ita saboda kidnappers sun kai ma makarantar su hari. Kin ga sai ta rinƙa koya miki. Ki shirya an jim in mun yi lunch ki raka ni makaranta zan je screening.
"Wow! I can't wait to see me in to tertiary, it will be like.. Cus I wanna chill. I Phone 15 zan rike."
"A lallai ba karatun za ki yi ba, kin san ni Jami'a ba baƙuwa bace a gare ni, saboda sai da na yi diploma, yanzu two hundrent level za ni."
"Anty Nahlinnnnn!" Suka ji muryar Ummu da ta sheƙo zuwa ɗakin tana kiran sunan cikin ƙaraji.
Nahlin tankama hannun Jannah suka fito tana faɗin,"Oyoyo, yar'uwata."
Faɗawa jikinta ta yi suna juya cikin tsananin farin ciki." Am so happy to see you Antyna." Ta furta tare da juyawa tana kallon Jannah da ta sagale hannunta tana kallon su cikin sha'awa.
"Jannah kin fi kyau a bayyane, gaskiya kina da kyau sosai."
"Don Allah?" Ta ce mata tana murmushi.
"Wallahi, kuma irin sosai ɗin nan, please let's take pics."
Murmushi ta yi ba tace komai ba daidai lokacin da Ummu ta kama hannunta suka shiga ciki bayan sun gama ɗaukar hoton.
Ko cikakken minti goma ba ta yi da dawowar Ummu ba suka ɗinke tamkar irin ƙawayen da suka daɗe ba a haɗu ba, saboda Ummu mutum ce mai shegen surutun tsiya da tsokana. Ga ta da son wayewa da hutu da ƙarya, kusan dai halin su ya kusan zama ɗaya.
Abin da ya ƙara sa ta saki jiki da ita yadda ta ga shigar ta yi rolling gyalen abayar da ta saka ba kamar Anty Nahlin da kullum take cikin hijabi kamar matar liman ko ƙonannniya ba.
"Please sis, punch me your number. Hope you do Whatsapp, Facebook, Twitter, TikTok and Instagram?"
"Dariya ta ji jin abin da ta ce,"Including snap chat and telegram." Sai suka yi dariya mai shewa suka tafa.
"Wow! Ki ce kema you are so socialized. Please ki ba ni labarin London, ina ta addu'a Allah ya sa Ya Ajmal ya bar Aby ya kaini Ƙasar waje na yi karatu I like going outside Country."
"Kar ki damu sai kin gaji." Ta ce mata tana jin daɗin samun 'yar'uwa mai kalar rayuwarta.
A tare suka ci abinci suk yi sallah. Suka yi wanka sannan suka wuce sashin Hajiya Baaba a can suka wuni. Ko rakiyar da Jannah za ta yi wa Nahlin tare aka je da Ummu duk da gajiyar da ta kwaso jin Jannah za ta ta dage sai ta bisu.
Ba su kwanta ba sai misalin biyu da rabi. Tare suka yi kallo a wayar Jannah, bayan sun gama suka yi karatu sannan suka kwanta.
"Ashe kema ƙwararriyace gurin kallon Korian films?Anty Nahlin da na tura mata ta ƙyar ta kalli season one penthouse" Ta tambayeta cikin mamaki.
"Eh ina kallo ina zo hutu, kuma suna da daɗi, amma na fi kallon Nigerian film. Ai Anty Nahlin 'yar islamiya ce kuma matar ustazu, ba ki ji ba ta rasa wanda za ta so sai Malam Amir za ta aura ba"
Zare ido ta yi cikin tsananin mamaki."Don Allah da gaske!"
"Eh, sun daɗe tun kafin ta kammala diploma, har maganar ta shigo gida kuma naji kamar Aby yana cewa bayan na Ya Ajmal, babu jima wa za a yi maganar na ta, yana son ta ɗan yi nisa da boko ne."
"Innalillahi" Ta ce tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi."Amma ta sanya ni a kwana. Ranar ya buge ni a gabanta na gama zage shi tatas, har ina faɗin gemunsa ya yi kama da jikin bushiya."
Dariya ta kwashe dashi har tana faɗowa saman gado."To what did she say."
"You know what? She just smile and she didn't say a word."
"Ai ba za ta ce miki komai ba Anty Nahlin akwai kawaici. Aby ya yaba da shi sosai bokin Ya Ajmal ne tare suka yi koyarwa a islamiyarmu. Yanzu lecturer ne A.B.U department of geology."
"Tab! Ai ta ba ni mamaki. Sis mai zai hana ki dawo sashin Hajiya Baaba, mu rinƙa kwana zan sa mom ta gyara mana ɗakin sa mana kayan kiɗa."
"Sashin Hajiya Baaba, za ta barni? Ni fa ba na wani shiri da ita don ta cika takura."
"Ba dolen ta ba, ni kaina ai ban so zama a gurinta ba, amm ta dage. Na yi mamakin yadda akai ba ta zo ta tasa ƙeya ta ba. Mu gwada inta ƙi saina tattaro kayana na dawo nan."
"Ok, shikenan, mu gwada mu gani." Ta bata masa tare kwanci sakamakon jin idanunta sun fara zafi.


Jannah ta ɗago ido tana kallonta lokacin da take ƙoƙarin kashe wayarta."I like you sis, you are so easy going and approachable."
Sai ta yi dariya kawai ta ije wayarta da ta kashe tana faɗin,"I like you sis too, please sleep like a baby."
Murmushi suka yi ma junansu suka kwanta domin ko wannensu ya yaba da junansu.
Sosai ta ji daɗin zuwan Ummu sai take jin wani farin ciki na zagaye ta. Ta yi amfani da dawowarta ta dage ta koya mata karatu sai ga shi cikin 'yan kwanaki ta fara ba wa masu yi mata dariya mamaki.




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093




















Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K



KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 14-15*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM






Sosai ta ji daɗin zuwan Ummu sai take jin wani farin ciki na zagaye ta. Ta yi amfani da dawowarta ta dage ta koya mata karatu sai ga shi cikin 'yan kwanaki ta fara ba wa masu yi mata dariya mamaki.

Jannah ta dage tare da saka ɗamarar koyon karatun. Kullum cikin dare ba ta bacci sai da ta ga taniya haɗa baƙin sosai ya zauna a kanta. Haddar ne tasha matuƙar wahalansa saboda ko ta fara sai ta ji ta gaji, amma da ta jajirce sai ga shi cikin wata biyu ta basu matuƙar mamaki.
Washegari da safe, duk tashin da Hajiya Baaba ta yi musu ba su tashi ba, sai misalin bakwai saura minti goma. Jannah sallah ta yi wana tana sallame wa ta ɗauki bagadadi ta fara karatu, sakamakon ba su da karatun asuba saboda ya yi tafiya.
Ummu ta yi sallah bayan ta idar ta yi karatun alkur'ani da azkar sannan ta koma ta kwanta don har yanzu gajiya bai sake ta ba, ga shi ba su yi wani baccin kirki ba.
Cikin lokaci ƙalilan ta shayar da kowa ruwan mamaki, domin ta nuna musu sa kai ya fi bauta. Sosai ta iya karatun shi kansa Ajmal mamakinta yake yi, wanda ya gane iskanci ne da rashin mayar da hankali ta sanya wa rayuwarta, wanda ganin hakan ya fara mata harda daga baƙara, kuma tana ƙoƙarin kawo masa daidai iyawarta.
Dawowar Ummu sai ya ƙara mata jin daɗin zaman gidan. Kusan halayen su ɗaya, sai dai Ummu tana aiki kuma da don ita take yi wa kanta komai, saɓanin Jannah da sai dai ta ci tasha ta kwanta tana kallo ko ta hau ynar gizo.
Sun yi matuƙar shaƙuwa tamkar 'yan tagwaye suke. Ummu ta bata shekara ɗaya amma in ka gansu sai ka ɗauka shekarun sun fi haka, don ita tana da jiki, yayin da Jannah ba ta da wani jiki siririya ce sosai.
Tun Hajiya Baaba na kauda ido akansu har aka kai mizanin da ta kasa haƙura ganin shaƙuwarsu, don ba ta ƙaunar hakan wanda ya sanya ta fara ƙorafi. Duk lokacin da Jannah ta tafi sashin su za ta bita ta taso ƙeyarta bayan ta yi ƙorafi da zage-zage, amma kuma ba shi zai hana anjima ta koma ba, wanda har ta gaji ta zura musu ido domin daga baya sashinta suka koma da zama gabakiɗaya.
Ranar lahadi bayan sun taso hadda suna har suka iso cikin gidan. Kai tsaye sashin su Ummu suka nufa sakamakon yunwar da suka dawo da ita. Tsaki Ummu ta yi tana faɗin,"Kai na san Anty Nahlin ce, da wannan kinibibin tsiyar ta yi mana gudun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login