Showing 54001 words to 57000 words out of 137802 words

Chapter 19 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

kar mu yi latti, kuma su Huzaifah suna jira."
Ɗaga mata kanta ta yi sannan ta ɗauki agogonta ta ɗaura suka fita suna taku cikin yanga da kwarkwasa.
Da suka isa ƙofar gida inda Huzaifah yake sai ta tsinci kanta da jin kunyarsa, musamman gainin yadda ya kafe ta da ido.
Wow! You look gorgeous and marvelous. Kin zama tamkar wata tarwaɗa."
"You are a such Flatter and you are good in it" Cikin jin kunya ta faɗi haka.
Gaban motan ya buɗe mata yana faɗin,"No, gaskiya na faɗa." Ya kalli Ummu da ta tsaya tana murmushin sannan ya juya ya kalle ta da dake ƙoƙarin shiga mota ya ce,
"Ummu right?"
"Haba Huzaifah, nufin ka ba za ka gane ni ba?" Ummu ta amshi tambayar cikin nuna alamun damuwa.
"Sorry, na dai tambaya ne kawai, amma kin san hakan na iya faruwa saboda na tabbata ke din ce, kin san hoto ba zahiri bane, musamman da yanzu mata canza halittar su suke in za su yi hoto."
"Amm kuma mun sha yin video calls da kai, remember?" Ta faɗa tana kallonsa.
"Oh yes haka ne, am sorry." Ya ce tare da haɗa hannayensa.
"Kullum ba a barin kunnawana su samu natsuwa sai dai a cika su da labarinka. Yau dai na ganka kuma duk ka cancanci abin da take faɗa a game da kai."
Ta shiga bayan motar ta zauna tare da kulle motar sannan ta ci gaba da cewa,
" You know what? I have a ton of embarrassing story about Jannah, and it will be perfectly for marital blackmail."
"Ke he is my bud, as I said earlier on."
Jannah ta karɓe zancen tana faɗin haka da harararta wanda ya sa suka kwashe da dariya.
"Oh pardon me, I forgot, amma kin san soyayya ba ta ɓuya idanuwanku za su bamu amsa ko Mufid." Ta ƙarashe tambayar tana kallon Mufid da tun da suka gaisa bai ƙara tankawa.
"Exactly, a dai juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe." Dariya ta yi jin abin da ya faɗa.
"Da gaske ina son 'yar'uwarki fiye da yadda nake son kaina, amma tunaninta ba shi a kaina, amatsayin aboki kawai ta ɗauke ni. Don Allah ki karkato mini da hankalinta gare ni, na yi miki alƙawarin kula da ita har ƙarshen rayuwa." Ya faɗa daidai lokacin da ya tashi motar ya fara tafiya kamar baya son tuƙi yayin da fuskarsa ta canza kalar tausayi.
"Kyaleta ta gama kauce-kauce da zagaye-zageye amma indai mutum ba makaho bane ko ya kalle ta ai ya sam abin da ke ranta. So exercised patient she has fallen in love with you."
Dariyar jin daɗin abin da ta ce ya yi, yana kallonta da ta ɗaure fuska ba ta ce komai ba.
Suna tafe suna hira har suka isa. Gurin ya cik ya batse babu masaka tsinke. Ango da amarya sun sha gayu da ƙyale-ƙyali, ba kamar amaryar da angon yake jin kamar ya sace ta ya gudu don ta yi kyau sosai. Sai murmushi mai tsada suke sakin ma junansu.
Bayan sun zauna Jannah ta kara kuninta a na Ummu,
"Ina ta tunanin matar da za ta aure shi da ƙaton ƙirjinsa, ashe ita ma yar lukuta ce, amma gaskiya ba yarinya bace na ganta da jiki."
Dariya Ummu ta yi jin abin da ta ce,"Wato ke a jiki ake gane girma ko? Ba yarinya bace, don ta gama degree har da masters aiki fa take yi."
"Oh kice guzuma ya aura kuma sun dace, ba ki ga ita ma bagidajiya ce irinsa ji fa wani shiga da ta yi na rashin wayewa on her weeding day sai ta sanya rigar da Ƙaramin hijabin da zai rufe mata duka jiki. Kai Allah ya kai mu nawa auren."
Duka ta kai mata."Ban son iskanci, and stop being dramatic you know they are compatible. Kuma Yayan kike kira bagidaje, don kawai yana ahlul sunnah."
"Ke dai bari, wallahi rayuwarshi babu wayewa. Kullum cikin jallabiyoyi da wando baya kai mishi ƙafa. Ji fa ko rawar sun kasa sai wani sunne kai suke."
"Ba ki da dama, Allah ya sa yaji kina ce msa bagidaje kin san halinsa. Duk wani events da aka yi ba, da yaƙi amincewa wai walima ya wadatar."
Tsaki ta yi cikin jin haushe ba ta ce komai ba ta koma ta zauna tana jin bikin babu wani armashi sosai, duba ga yadda take kallon a social media ana cashewa sosai.
"Allah ya kaimu nawa zai ga yadda za a yi hosting event differently, it will be a topic on social media."
"Allah ya kaimu. Ni ce amara ƙirjin biki.
Ganin an fara manna kuɗi suka tashi wanda dama jira suke su yi amfani da wannan damar.Rawa suka fara tiƙa suna musu manni, wanda ganin haka ya sa Huzaifah ya taso ya shiga zuba mata ruwan kuɗi tana tiƙar rawa.
Karab! Suka haɗa ido da Ajmal da ya tsaya cikin takaici da mamaki yana kallonsu yayin da baƙinci ya cika shi wai waɗanann ƙanninsa ne.
Ganin kallon da yake musu ya sa suka koma gurin zamansu.
"Kai Ya Ajmal bai yi ba, yanzu shikenan ya yi mana baƙin cikin tura shagalin bikinsa a social media. Gabaki ɗaya bikin nan babu daɗi. Ji yadda amaryar take motsa jikinta wai a dole rawa take yi."
A haka dai aka yi dinner aka tashi sam bata yi musu daɗi ba don haka suka ɗauki ƙudirin party da za su yi sai sun ƙayatar da shi.
Washegarin bikin sai shirye-shiryen paty suke yi. Sashin Hajiya Baaba cike yake da mutane haka Ammy don haka suka yanke shawarar su ƙayata gidan harabar gidan gonar Abby.
Duk wani hidima sa suka yi a aljihun mom ya fita wanda ta karɓa babu tausasa lafazi.
Ganin gidan a cike yake sai suka yanke shawarar yin party ɗinsu a bangaren gidan gonar Aby.
Gabaki ɗaya sun ƙure gidan da waƙar Umar m sharrif take tashi. Ba bu yadda Nahlin da Hajiya Baaba ba su yi ba kan su kashe, amma suka ƙi wanda ta yi fushinta ƙyale su.
Ajmal da ya shigo da abokansa su gaisa da Aby wanda suka zo masa daga waje. Hayaniyar mutane da kiɗan da suka sanya ya saukar masa da wani irin azababben ciwon kai.
"Yauwa Adamuu, gara da ka shigo waɗannan marasa jin maganar sun hana kunnuwana saƙat da kiɗa, don ko da na yi musu magana taƙadiriya Jannatu jawo ni ta yi cikin fage tana juya ni."
Tsaki ya yi ba tare da ya ce komai ba jin abin da ta faɗa. Matuƙar kunyar abokanansa suka kama shi.
"Albarkar auren nawa kuke son ku kwashe, saboda ga ku sheɗanu ko?!" Ya furta cikin ɓacin rai daidai lokacin da ya kashe kiɗan.
Jannah da ba ta lura da shigowarsa ba ta ibo shoki saura kaɗan ta faɗa jikinsa, Allah ya taimake ta ta ja ta tsaya tana mazurai tare da ɓata fuska.
"I just give you rest of two minutes, kowa ta ɓace daga nan kafin na yi ball da ku."
"Kai wallahi guy ɗin nan bai yi ba, ga shi dai a ido kamar wayayye." Cewar ƙawarsu Maryam tana ƙuta.
"You know what? Ku zo kawai muje mu kama waje, ai tun da muna da kuɗinmu bai isa ya hana mu wataya ba, dole na yi murnar aurensa za mu huta da takura." Cewar Jannah.
Haka kuwa aka suka kama guri suka sha rawa sai da su ka gaji don kansu sannan suka dawo gida, bayan sun ci sun sha.
Biki ya watse bayan an yi tarin shagulgula aka ɗauki amarya zuwa haɗaɗɗen gidanta tare da yin buɗar kai aka bar ta daga ita sai angonta.
Tana zaune akan doguwar kujera ta sha matuƙar kyai sai walwali take yayin da ɗakin yake ƙamshi mai daɗin shaƙa.
Sallama ya yi ya shigo fuskarsa ɗauke da annuri domin yana jin babu wanda ya kain shi farinciki.
Ya shigo shi kaɗai bai nemi rakiyar kowa daga abokanansa ba, domin tun daga get ya karɓi kayan da suka siyo ya nuna musu baya son rakiyar.
Tonan sa suka fara yi wanda ya ji ya shanye har suka gama suka ƙyale shi.
Da sauri cikin ladabi ta taso ta karɓi ledar bayan ta durƙusa a ƙasa.
Wani irin matuƙar farinciki ya kama shi domin yana ɗaya daga cikin abin da ke ƙara masa sonta tsananin biyaryarta.
"Barka da shigowa ranka ya daɗe abin alfaharina, barka da wannan rana da ba zamu taɓa manta wa da ita ba." Ta faɗa cikin murya mai sanyi da son jan hankalinsa.
Ajiyar zuciya ya yi mai ƙarfi har tana jin hushin numfashinsa a fuskarta duk da ta mayar da gyalenta ta rufe fuskarta.
"Ina matuƙar sonki haskena, ina fatan mu yi rayuwarmu cikin farinciki."
"In sha Allahu, za ka same ni mai tsananin biyayya tamkar Sarki da bayinsa. Domin zan yi koyi da matan Annabi Muhammad (S.A.W.). Suka ƙarashe tare sannan suka shafa.
Miƙewa ya yi yana faɗin,"Bari na shiga kicin na ɗauko plate na ciyar da sahibata."
"Kaicona!" Ta faɗi tare da riƙe hannunsa da sauri.
"Ni kuwa mene ne amfanin numfashina matuƙar zan bar zauji da aiki? Kenan babu amfanin hannuwana."
Tsananin mamakin abin da ta furta ya kama shi duk da ya san cewa ta iya kalamai na sace zuciya, amma sai ya ji ya ƙara darajata da kimanta ta, domin shi mutum ne mai matuƙar son a nuna mishi girma, don haka ya kama hannunta duka ya riƙe yana faɗin,
"Kar ki damu kar kiji komai, ki yi mini alfarmar yau na yi hidima da rayuwarki sai ki ɗora da ga gobe."
"To shikenan zauji, yadda kake so haka za a yi sam babu jayayya a tsakaninmu." Ta ce tare da komawa ta zauna zuciyarta fal tamkar gonar addu'a ganin yau Allah y mallaka musu junansu.
Bayan ya ɗauko ya juye musu banƙararrun kaji da drinks masu sanyi. Kaɗan suka ci sannan suka je bayi suka yi brush tare da canza kaya.
A wannan daren Ajmal ya nuna mata irin sonta da yake yi da dakon jiran ranar da ya yi, domin ya shayar da ita ƙauna mai tsuma zuciya ya sa ka manta komai, wanda ya sa ta farinciki ta san ta wuce zarra.
Sosai take ganin wautan 'yan matan da suke faɗin ba sa son auren ustazu domin auren riba biyu ne. Ga soyayya kuma ga sa mace kan tafarkin tsira.
Washe gari da safe bayan sun tashi sun yi sallah duk yadda ya so Mushirat ta ƙi barin sa ya kunna wuta a ɗakin sabod wani irin kunyarsa da take ji.
Haka dai ya daure ya ja su sallah bayan sun idar sun yi azkar shine kawai ya yi karatun ƙur'ani, amma ita komawa ta yi ta kwanta sakamakon zazzaɓi da ya rufe ta.
Bayan ya idar ya yaye bargon da ta lulluɓa da shi yana kallon fuskarta da ta yi saurin rufewa da zanin gado.
Dariya ya tare da ƙara janye zanin gado."To kuma mene ne abin ɓoyewa kamar wacce ta yi laifi? Ai yanzu mun zama ɗaya babu kunyar wannan a tsakanimu."
Ƙara ɓoye fuskarta ta yi tana dariya ciki-ciki ta ce,
"Please ya Sheshk ka bari don Allah."
Sakin zanin ya yi tare da ƙarasa wa kan gadon ya haɗata da jikinsa ya rungume yana dariya cikin jin daɗi.
"Ina alfahari dake matar kirki Allah ya bamu tsawoncin rayuwa da zuriya ɗayyiba." Ba ta amsa ba saboda da salon tsokana ya yi maganar.
"Au kin ganni ko? Abinci na haɗa miki a maimakon na kira ki kici na tsaya ina tsokananki."
"Abinci ya Sheshk?" Ta tambaya cikin tsigar mamaki sai kuma ta ɗora da cewa bayan ya amsa mata da gira.
"Ai da ka bari na ɗan samu tsauƙi na yi tun da na sha magani saboda bana son ka wahala."
"Ai ko da bani da tausayi matar kirki. Kar ki damu watarana lafiyarki lau ma zan hutar dake in yi miki abinci ko na taya ki, domin koyi da rayuwar Annabi zan yi."
"Tabbas duk macen da ta samu namiji mai addini da aiki da shi ta dace sosai. Uwa uba ga kyau da hankali har ma da natsuwa." Ta ce tana ƙoƙarin miƙewa.
Fuska ya ɓata yana faɗin,"Mene ne haka ina za ki?"
"Zan tashi muje dining."
"Haba sai kace ba ni da tausayi? Bari ki ga ɗaukarki zan yi don yau babu ke babu tafiya. Ko kin manta daren jiya ai kin cancanci a ɗauke ki."
Matsawa ta yi cikin kin kunya tana dariyar abin da ya faɗa." Don Allah karka ɗauke ni zan iya tafiya ka ji." Ta ce ganin ya nufo ta amma bai kula ba y sungume ta ba tare da ya ji nauyinta ba har sai da ya kai ta daining ya ije yana ɗan nishi.
Dariya suka kwashe tare ya manna mata kis tare da buɗe soyyayyen ƙwai da tea da ya haɗa sai ƙamshi yake ga bread sai kajinsu da ya yi warming.
"Laa! Ashe Zaujina ya iya girki ji wani suyan ƙwai yadda ya yi kyau?" Ta faɗa cikin sigar mamaki da zuba masa idanu.
"Au ba ki sani ba? Ai Ammy ba ruwanta da namiji ko mace gabakiɗaya yaranta tana koya musu girki I will give you suprised anjima ina yi mana jallop na rise."
"Really?" Ta tambaye shi tare da buɗe baki a hankali cikin jin kunya ganin ya gutsiri ƙwai ya nufo ta da shi wanda ya saka mata yana ɗaga mata kansa.Dariya suka kwashe da shi ya manna mata kis.
Amarcinsu suke dirza cikin so da ƙauna domin kunyar da amarya ta nuna duka bai wuce kwana biyu ba, ta fito masa da kalar zahirinta wanda dama abin da yake ƙauna kenan shi ya sa bai kai soyayyar ga ƙwaila ba. Yana son macen da za ta kula da shi ta mai da shi tamkar ƙwai ta nuna masa bajintar ta ta ko wane fanni kuma tsaƙar shi ta yanke a matsaƙa domin ya samu Mushirat ta cika ko wane fanni.
Ta fanni gayu da tsafta ba a magana uwa uba tunbinsa sannan fannin auratayya sai ya ce ita kaɗai ta ishe shi.
Jannah kuwa hankalinta ya kwanta sosai ganin ta yi kwana biyu babu wanda ya takurawa rayuwarta. In ta kwanta bacci sai Hajiya Baaba ta yi da gaske take tashinta.
A lokacin da Nahlin ta sanar da su ya ba ta umurnin ta rinƙa koya musu. Wani banzan kallo suka yi mata ba tare da sun furta kalami ba, sai Jannah da ta turo baki,
"Taɓ, amma wasa yake yi ko? Don ni da karatu sai na islamiya, ai yanzu ni ba jahila ba ce."
Bayan auren da sati biyu Nahlin ta sanar da su za su fara karatun asuba. Da asuba bagan ta yi sallah ta biya wa sauran yaran gidan amma babu ƙeyarsu, don babu tashin duniyar da Hajiya Baaba ba ta yi musu ba suƙa tashi, don tunda suka yi sallar asuba suka koma, amaimakon su tafi karatu.
A ƙalla sai Nahlin ta yi kwana uku tana fama da su, ganin sun fi ƙarfinta ya sa ta sanar da shi, wanda washegari da asuba bayan ya yi salla a masallaci ya wuto gidan.
Hajiya Baaba na zaune a falo da carbi a hannunta ya yi sallama ta buɗe masa ƙofa tana faɗin,
"Yauwa gara da ka shigo, waɗannan yaran sam ba na tunanin suna sallah cikakkiya. Su hana kansu bacci da daddare sai safiya ta yi suce lokacin za su yi bacci, ai dare shine mahutar bawa.
Ƙofar ta tura masa ya shiga tana faɗin,"Ita kanta Ummu da nake ganin ta fi ta hankali, ashe kura ce da fatar akuya. Gabaki ɗaya ta ɗauki ɗabi'unta ta sanya wa kanta."
Kai tsaye bayi ya wuce tare da ibo ruwa mai sanyin gaske ya watsa musu, Wanda ya sa ta mike a firgice tare da sakin ajiyar zuciya mai karfi.
"Uban wa ya zuba mini ru..?"
Maganar ta maƙalewa mata a maƙoshi lokacin da suka yi ido biyu da shi, wanda ya sanya ta tashi da sauri tana zare ido.
"Na shiga uku! Na mutu, wallahi na ɗauka Anty Nahlin ce ta turo Adal ya tashe mu, don na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login