Showing 51001 words to 54000 words out of 137802 words

Chapter 18 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

kurna. Wallahi na tsani abun nan."
Taɓe baki ta yi bayan ta buɗe kular."Taɓ, ni fa ban taɓa ci ba, ranar da Anty Nahlin ta yi sai dai na sha tea." Ta mayar da kular cikin ƙyanƙyani.
"Let's go to Hajiya's kitchen to see what she cooked. I'm starving to dead." Ta furta tare da jan hannunta suka kama tafiya sashin ta.
"Allah ya kyauta! I can't eat that concoction."
"Ok, then let's go and cook." Ta faɗa tana rufe ƙofar kicin ɗin.
"Allah ya sa ta yarda Hajiya is so abrasived."
Dariya Ummu ta yi ba ta ce komai ba suka nufi sashin, wanda kai tsaye kicin Ummu ta wuce yayin da Jannah ta zauna a kan kujera.
Harara Ummu ta sakin mata tana faɗin" What this sis, kamata ya yi ki biyo ni kicin ki gyara kayan miya kiyi blending, ko kuma mu jajjaga zai fi ko?" Ta ƙarashe maganar cikin sigar tambaya.
"Allah na tuba! Muje dai na taya ki hira, amma ni har yanzu ban gama sanin kalar kicin ɗin nan ba, ballantana na yi girki don ban iya ba."
"Wai da gaske kike?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki sosai. Jinjina mata kanta ta yi suka nufi kicin ɗin.
"Ban ga laifin ki ba sis, ai duk wanda ya samu rana ya yi shanya. Rayuwar hutu daɗi ne da ita. Ke ɗin babbar yarinyace, Allah ya tarfawa garinki nono."
Ta ɗauki tukunya ta ɗauraye sannan ta kunna gas tana kallonta."Lokacin da na ji mom na neman minister I was very happy. Allah ya yi miki tagomashi da ya ba ki uwa irin mom."
"No, please stop saying that. A kan mom kike cewa na ji daɗin samun ta a matsayin uwa, kin san wace ce ita? Ai ni mamaki na ji da take neman wannnn kujerar matar da ta kasa kula da gidanta za a ba wannan muƙamin! Initially, I was thinking my dad wasn't aware of this and he won't support her, amma kin san ta Mai da shi rakumi da akala."
"You don't support you mom in to politics, do you?" Ummu ta ce cikin tsananin mamaki abin da take fadi.
"Absolutely, I do not."
"A lallai na raina wayonki, kin san kuwa wace ce ita.."
"Oh, please. I don't wanna talk about her now, understand? Kawai na ije ta a matsayin bankina, in ina buƙatar kuɗi ta turo mini. That what she is to m.."
Jin abin da ta ce ta kuma canza fuska sai ba ta ce komai ba suka ci gaba da ɗor girkin bayan sun gama suka dawo falo suna kallo.
"Innalillahi na shiga uku! Dan ubanku gobara kuke son ku haɗa mini, kashe ni kuke son yi ko? Waton na mutu na bar muku duniyar ku ci ta da tsinke."Hajiya Baaba take faɗi tana fito .daga ɗakinta, wanda jin abin da ta ce suka kwasa da gudu zuwa kicin ɗin domin sun mnta sun ɗora girki.
"Mun shiga uku! Ya ƙone." Cewar Ummu da ta kashe gas ɗin ta buɗe murfin tukunyar tana kallon haɗaɗɗiyar tliyar da suka dafa ta ji bashshshen kifi sai ƙauri take yi.
"Taɓ! Ai wallahi ba zan yi asara ba haka kawai. Ban ci nanin ba nanin ta ci ne. Na rantse iyayen ku za su biya. Ma za Jannatu ɗauko mini wayata a ɗakina na kira uwarki ta siya mini tukunyata, ke kuwa Kursumu ubanki zai biya ni abincina."
"Ki kwanatar da hankalinki daɗin abun mu ɗin ba matsiyata bane da sai kin kira iyayenmu kiyi kuɗin tsiya na biya ki."
"To ƙaramar mara kunya fitsararra. Ai dama na san ke za ki fara magana. Fita a kicin ɗin tunkafin na yi ball dake, tund ba ubanki ya saya mini gidan ba. Kin ji da kan ki kamar tsandar rake."
"Aby da mom uwa ɗaya uba ɗaya suke, don haka nima ina da iko da gidan."
"Ok haka kika ce ko? To ba ri na zo kusa dake zan fi gane maganarki, don kamar ba da yaran da na sani kike magana ba." Ta ƙarasa maganar tare da ɗauko muciya ta yi kanta, wanda gain haka ta kwarma ihu ta yi waje.
Kan Ummu ta yi da take tsaye tana mamakin tsaurin idanunt do ko Ya Ajmal ba y gaya mata magana ya kwana lafiya.
"Fita daga kicin ɗin nan, kema wallahi na ƙara ganinki sai na canza miki kamanni."
"Taɓ! Ai in dai Jannah tana sashin nan, sai dai kiyi haƙuri ko ki barta mu koma sashinmu za mu fi sakewa." ta ƙarashe maganar tare da zurawa da gudu, Jannah ta rufa mata baya tana faɗin,
"Muje kin ji ni ma ba zan ƙara dawowa ba, na huta da tashina da asuba da take yi kamar me kashin kwance."
"Oh Allah na ga ta kaina! Ni kam an haifa mini jikoki sun zamar mini ƙadangarun bakin tulu. Da na yi magana ɗaya sai sun mayar mini da goma."
Jarrabawar makarantarsu yake ta matsowa na fita daga sakandiri. Hnakalinsu gabaki ɗaya yana kai ba kamar jannah da ko abinci ba ta iya ci sosai kullum karatu duk ta bi ta rame. Inda suka ɗan samu natsuwa da ana saura kwana goma su fara za a yi bikin Ajmal sai kuma aka ɗaga sakamakon mahaifin Mushiirat da ba shi da lafiya an fita da shi waje.
Cikin nasara suka gama zana jarrabawar wanda har sai da ta kwanta ciwo bayan exam ɗin sai hankalinsu ya koma kan bikin Ajmal da za a yi wanda aka ƙara wata biyar.
Tun kafin ya matso suke shiri da murna da tsare-tsaren shagalin da za su yi ranar auren.
"Na ɗauki nauyin haɗa paty da ƙawayenmu ranar auren don murnar zai bar mana gida muci karenmu babu babbaka. Wayyo Allah har na ga irin rayuwar da zan yi, ga shi lokacin mun shiga higher institution, kai akwai bidiri."
Jannah ta ce wa Ummu da take kwance a kan kujerar da Jannah take zaune.
"Habawa ke dai bari. Allah dai ya kai dare ga hawara, ko bai ci ba ya yi birgima.Kin san Allah in yaya ya bar gidan nan, akwai kankaro mutunci. Wani irin shiga zan rinƙa yi na mata masu class ina zuwa makaranta."
"Ki dai bari kawai! Duk na ƙosa Jamb ɗinmu ya fito. Dole mu hau mota masu kyau, kuɗin mom zai yi kuka."
Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa sannan suka fice daga falon zuw ɗakinsu.
Suna zaune suna kallo Hajiya Baaba ta shigo da kwanon fura a hannunta ta ce,
"Ke Jannatu, maza ki kaiwa yayanki Adamuu hurar nan, yau isasshen ya tuna da hurata mai daɗi."
"Ni fa Hajiya kin san ban cika son aike ba, haka kawai ga 'yan aiki sai kin wahalar da ni, kuma kin san halin jarabben mutun nan so kike na je ya ce n yi masa wani abu..."
"Ta shi ma za kije, sai kin kai mishi banga damar aiken wani ba sai malalaciya kawai, ke Ummu ta ki rakata." Miƙewa ta yi tana zumɓura baki kamar za ta zubar ta fice.
"Ke kin san Allah ba zan raka ki ba, yau ikin da muka yi masa daban ne, ka wo wayarki ki same ni a sashinmu."Ta wuce ba tare da ta tsaya ta ni ƙorafin da take mata.
Da siririyar sallama ta shiga cikin falon amma ganin ya juya baya yana waya bai ji ta ba sai ta ja ta tsaya tare da maƙala kunninta sosai yadda za ta jiyo shi jin ya rage murya.
Cikin salo da jan hankali duk wata 'ya mace yake waya. Dariya ya saki mai sauti yan lumshe idanu, wnda ya ba ta matuƙar mamakin jin yana da irin muryar.
Hankalinsa gabaki ɗaya ya tattara akan wayar don har wani takun ƙasaita yake yi a hankali a tsakiyar falon.
Cikin wata irin murya ta ji ya ce,"Buɗe bakinki na yi miki kiss, kuma ki rufe ido."
Jin hakan ta hangame baki tana mamaki ta zare ido tare da haɗiyar miyau da ƙyar.
Wani irin zazzafar kis ya sakin mata har uku sannan ya ce,"Bye, ki kular mini da kanki."
Cikin tsananin razana ta saki kwanon furar domin saboda tsabar gulma kayansa ta ji ya ce ta kula da shi.
Ƙarar faɗuwar kwanon ya sanya ya juyo da sauri yana kallonta wacce ta zura a guje ganin aika-aikar da ta yi.
Sashin su Ummu ta same ta a falo tana waya da Huzaifah. Da sauri ta ja hannunta zuwa ɗakin Nahlin tana faɗin,"Humh zo na shafa miki labari, yau na ji abin da ya girmi kakata Hajiya Baaba.
"Mai ya faru sis, give me the gist."
"Sai da na gaya wa Anty Nahlin Ya Ajmal kura ne da fatar akuya, fakewa yake da addini yana cin karensa babu babbaka, wi shi a dole uztasu Ahlulu sunnah, amma ta shafawa idanunta toƙa ta ƙi yarda. Ga shi yanzu na gani da idanuna. Kun san me na ji yana faɗi wa budurwarsa?"
Anty Nahlin ta kasa magana sai kaɗa kanta take tana mata nuni da shi da yake tsaye a bayanta, amma gulma na cinta ba ta lura ba.
Ummu da ba ta ganshi ba ta ce," Do tell me now." Ta faɗa cikin zaƙuwa da son jin gulma.
"Kiss guda uku ya yi mata, kum har yana faɗin ta kula mishi da kayanshi. Oh ni Jannah ko wane kaya yake da shi a gurinta oho? Ashe ya Ajmal gogaggen ɗan duniy..."
Maganar ta maƙale mata a maƙoshi sakamon Ummu da ta yi mata alamun yana jin ta.
Wani irin tsalle ta yi sai ga ta a tsakiyar gado, domin ko kaɗan ba ta taɓa tunanin zai biyo ta ba.
Nahlin ta buɗe baki za ta yi magana ya daka mata tsawa,"Rufe mini baki shashashar banza kawai! Kin tsaya kina jin shirmenta."
"Yi haƙuri." Ta ce tare da bin bayan shi ta wuce wanda Ummu ta bita a guje domin tsuntsun da ya ja ruwa. A ranta addu'a take Allah ya taimake ta ganin yadda ransa ya ɓace.
"Yau zan yi maganinki, ba ke baki da tarbiya ba. A gidan uban wa kika ji na ce ta kular mini da kayana? Saboda kallon finafinai ya ɓata ki."
"Am very sorry. Wallahi ba haka na ce ba, please understand me."
Mari ya kai mata yana faɗin," I should understand what? Kin ɓata tarbiyarki kina son ki ɓata na ki, sannan ki sanya suna ganin mutuncina su raina ni. Wato dama you been spying on me?"
"No, wallahi I don't, I really respect you. It was mistake please forgive me."
Marin da ya ƙara kai mata ya sa ta canyara ƙara daidai lokacin da Ammy ta shigo.
"Kai Ajmal, so kake ka ƙara janyo wata rigimar? Ma za yarda bulalar nan." Ta faɗa cikin ɓacin rai. What has she done to you?"
"I really disappointed, having you as a sister." Ya ce tare da yarda bulalar ya fice ba tare da ya amsa tambayar Ammy ba.
"Ba kya jin maganar Jannah, kina ganin kowa a gidan nan, kaffa-kaffa yake kar ya shiga gonarsa amma ke kullum cikin takalarsa, bayan kin san abin da zai je ya dawo."
Wuri-wuri ta yi alamun rashin gaskiya sai jan majina take yi.
Ammy ta juya za ta fita daidai lokacin da Ummu ta shigo."Sory sis, I was signalling you, amma ba ki gani ba. Dukanki ya yi?"
Ture ta ta yi tana harararta." A, a albarka ya shi mini, tare da ba ni kyautar kuɗi. Ai wallahi na san matsayina da inda na aje ki, you left me in, wato ya kashe ni ba ki da asara." Ta faɗa tana harararta.
"Am deeply sorry. Kin san halinsa, ya zan yi? Amma ke ɗin tawa ce."
"In ban da neman rigima irin na ki, ina ruwanki da wayarsa ba matarsa ba to be ba ce? Kar ki manta it remains 26 days for their weeding."
Zuɓɓura baki ta yi ba ta ce komai ba sai ta kama hannu Ummu."Kin ji muje sashin Hajiya Baaba."
Shirye-shiryen biki ya kankama Ajmal babu zama duk da bikin gata ake masa amma shi kansa nuna bajinta yake yi. Kmar yadda mom ta yi alƙawari ita ta haɗa lefe na gani na faɗa wanda samun sa sai 'yar gata mai ƙashin arziki.
Events kala-kala aka shirya duk da angon yana nuna ustazu ne amma hakan bai hana tsara bikin yadda zai ƙayatar.
Amaryar ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta kawo kanta gidanta ganin irin kayan alatun da ka shirya a ɗakin. Duk da iyyen amaryar sun yi bajinta, amma Ajmal sai da ya sanya kayan furnitures a bangarensa masu kyau.
A gefe ba a bar su Jannah ba da suke jin kamar an biya musu kujerar makka, ba ma kamar Jannah za ta huta da tashin asuba karatu. Don haka suka gayyaci 'yan makarantarsu da shirya shagali na musammman. Sun ɗinka kaya masu tsada da kyau.
Kowa ya yi tunanin mom za ta dawo kafin bikin amma sai dai ga mamakin su, ƙiri-ƙiri ta ƙi zuwa wanda hakan ba ƙaramin haushi ya bawa Hajiya Baaba. Ita ko Jannah ko a tsummar rigarta don ta san abu ne mai wuya tazo sai dai ra'yin kanta.
"Anya ba kurciya aka yi wa Halima ba? Lamarin nan akwai ruɗarwa. Tun yaushe take waƙar za ta dawo, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa. Ƙila sai na tashi tsaye."




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093



KURA DA FATAR AKUYA



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)

*SADAUKARWA GA:-*

*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)






Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.





*PAGE 15-16*



BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM







"A'a Hajiya, karki saka kanki ga bibiyan malamai da babu Allah a zuƙakansu. Halima za ta dawo, wani aiki ne ya taso mata. Kuma kin ga dole ta dawo ko dan takarar da ta tsaya. Lokaci ne kawai bai yi ba." Cewar Aby jin abin da ta faɗa.
Dinner da aka shirya suke shiri. Sun shirya cikin wani haɗaɗɗen less kalar milk kallo wanda ya karɓi jikinsu matuƙa don anko mom ta yi musu.
Ummu ta shigo da turare a hannunta tan fesawa sai kuma ta fara fesawa Jannah,
"Kiyi sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login