Showing 72001 words to 75000 words out of 137802 words

Chapter 25 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

"Na shiga uku." Ta faɗi tare da mayar da murfin tukunyar ta rufe. Leƙawa ta yi za ta kira Talatu daidai lokacin da su Ummu suka shigo kicin ɗin.




"By the looked on your face, I guessed you cooked delicious food." Cewar Ummu cikin tsokana tana ƙoƙarin ƙarasawa gurin tukunyar.




"I can't wait saboda tun ina waje nake perceiving the aroma ina ta salivating."


"Oh yes I do, ki bari I will serve you."



"Wai me kika dafa? Na ga ko Ummu da te girka taliya har yanzu ba ta gama ba, mun bar wa Jummala ta kula da shi?" Nahlin ta tambaya cikin mamaki.


"Fried rice na yi."


Tare suka haɗa baki gurin faɗin,"Fried me?"




Ummu ta ƙarasa cikin mamaki ta buɗe tukunyar.




"Kan uba, yau ke da Hajiya Baaba wannan abinci da kika tokare tukunya da s.."




Maganar ta tsaya mata a maƙoshi sakamakon ɗanɗana shinkafar da ta yi. Da gudu ta ruga sink ta buɗe famfo tana watsa ruwa a bakinta bayan ta furzar da abincin ta wanke bakinta.




"Haka ake girki? Aiko da tuni mun mutu. Jakar magi kika juye?"




Tsaki ta yi tana faɗin,"Ban sani ba." Ta tureta daga gurin tukunyar.




"Taɓ! Duk wanda ya ci abincin nan sai dai ya kwana a cikin bayi."


"Jannatu, wane irin girki kike yi? Gida ya cika da ƙarnin nama."




"Girki mai daɗi Hajiya Baaba, ma za shigo kar ayi babu ke yau mata sun yi girki, in dai kika ci wannan girkin sai kin suma." Nahlin ta ba ta amsa.


" Allah ya tsareni girki ko shiririta dai." Cewarta ta tana buɗe tukunyar.


"Innalillahi! Ni jikar maigishiri wannan tsunburen da kike yi fa? Ai wannan albazaranci ne. Ni dama na san babu abin da za ki tsinana shegen kafiya ce dake."
"Ni fa ba ni da laifi iya yawan da nake so na shinkafar na zuba, shinkafar ne ta kubburo."


Kwashewa da dariya suka yi." Wai yanzu sis kina nufin baki san in aka aka dafa shinkafa kubburowa take yi ba taɓ?!" Cewar Ummu.




"Oh ni kam na ga abin da girmi kakata an dai yi zuwan zomo kasuwa." Hajiya ta ce tana salati.




Wiƙi-wiƙi ta yi da idanu daga ganin ta kasan ba ta da gaskiya don ko ita ta san girkin bai yi ba duba ga yadda ya yi cikin shega ya tsunbure. Kuka ta saka sosai.




"You know what? Let me take pic and send it to him, so that he can give you mark."




Da sauri ta ɗauke tukunyar ta ɓoye a bayanta tana zare ido.




"Ni wallahi an tsane ni a gidan komai na yi kuce bai yi ba, kum ku ci ba da degrading ɗina, to ba zan ƙara yin girkin ba ya bar ni idan na yi aure aka koro ni ba shi da asara."




"Dallah ja can shashasha! Yanzu asara kika yi mini kenan?"


"To wa zai ci wannan abincin? Ai wallahi ko su Binbo karnukan gidan nan ba za su iya ci ba."


A kwana biyu babu abin da za ta iya rantsewa ta koya domin Hajiya ta rantse ta maya babu uban da zai ƙara shigar mata kicin, dama ita ba buƙatar koyon take yi ba don haka ta shiriritar da zancen.




Cikin sa'a kuma Ajmal ya yi tafiya don haka suka watsar da koyon girkin har suka gama hutun makarantar suka koma karatu.




Ranar Juma'a lecture na su ƙarfe sha biyu suke gamawa. Bayan sun gama Jannah ta kama hannun Ummu.


"Sis, kin san me? Ni kam Allah yau babu abin da zai hana ni yin kitson attach, don ina son na fito sosai bikin Maryam. Kin ga hoton kitson ya yi mini sosai musamman na ɗauko shi."



"Yanzu duk maganar da aka yi mana baki ji ba? Ni dai babu ruwana va zan sha dukar banza ba." Ta ce tana gwalalo ido.




Tsaki ta yi ta shige motar har ta kunna sai kuma ta kashe ta fito daga motar tana cillawa Ummu makullin da bayan ta zauna a kujerar me zaman banza.




Ganin haka ba ta ce komai ba ta fito daga motar don ta san me take nufi.




"It is my life, and I will do whatever I like." Ta ƙarashe maganar tana jingina kanta akan jikin motar.




"Ok." Ta ce kamar ba za ta ƙara magana ba sai kuma ta buɗe baki za ta yi magana.




"Please drive the car, or the you want me to start my madness?" Ta ce tare da kunna waƙa ta ƙure tana rawa da kanta.




Ganin haka ta figi motar suka bar harabar makarantar.




Cikin Samaru suka ta je aka yi mata kitson mai shegen kyau sai ɗaukar ido yake yi wanda ana gamawa ta biya suka dawo gida.










Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093

















KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 20-21*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Tun da aka gama kitson take ta ihun raki da faɗin zafi. Ummu sai dariya take mata ganin yadda ta take ta jin zafin kitson. Tun akan hanya take haɗa gumi duk da AC motar.


"Kai wannan matar hannunta akwai zafi kamar zata cire mini ƙwanyar kai."




"Allah ya ƙara ai wanda bai ji bari ba ya ji hoho." Cewar Ummu wanda ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da danna saman kanta da take jin kamar zai ɗaɗɗake.




Suna isa gida maigadi ya buɗe get da sauri ta buɗe mofar ta ito ko jira ta gana parking ba ta yi ba.




Kai tsaye sashin Hajiya Baaba ta yi ta shige ɗakinta ba tare da ta damu da dariyar da take mata ba.




Wanka ta yi ta jiƙe kan da ruwan sanyi sannan ta ji dama-dama ta saka doguwar riga ta dawo falo ta ƙure fankar sama da ƙasa tana jin yadda iskar ke shiga cikin kanta yana rage raɗaɗi.




"Ke don ubanki ba kya jin magana ko?"


Kamar daga sama ta ji muryarsa wanda ya sanya ta miƙe tana zare ido don ko kaɗan ba ta yi tunanin shigowar sa ba asalima ta san ya yi tafiya.




Mari ya kai mata cikin zafin nama yana faɗin," Dole na ɗauki mataki don ba zan bari ku jawo mana abin magana ba."




"Wayyo Hajiya Baaba, don Allah kizo kashe ni zai yi." Ta furta cikin ƙara tana sosa fuskarta don ta ji shigar marin.




Da sauri ta fito tana gyara zani."Na shiga uku da wannan mai zuciyar kafuran wai kashe ta za ka yi?" Ta ce lokacin da take ƙarasowa gurin.




"Don Allah karki barshi ya ƙara dukana kashe ni zai yi."




Kallonta ta yi ba tare da ta tambayi ba a sin dukan ba ganin uban kimin atach a kanta don ko lokacin da suka shigo tana sallah bata ganta ba.




"Ba kya jin magana Jannah, kin fi son ya yi ta dukanki kamar ya samu jaka. Kina 'yar gidan malamai kina jawo mana zagi?"


"Ki yi mini tsakani da shi don wallahi ba zan fasa yadda nake so da rayuwata ba. Ko iyayena ba su isa su hana ni ba balle shi ya fita daga rayuwata na tsane shi. Mugu kawai azzalimi kuma sai Allah ya saka mini wa.."




Wani irin mari da ya ƙara kai mata ya sa ta yi shiru tare da ƙara sakin wani ƙaran ta yi bayan Hajiya, amma idanunsa sun rufe zaginsa da maganganun da ta gaya mishi suka tunzura shi yake jin in har bai cire mata haƙoran rashin kunya ba ba sunan shi Adamu ba.




"Kai ni jikar mai gishiri! Jikoki sun zame mini fitina. Kai Adamuu kashe ta za ka yi? Ka bar dukan nan, anya za ku yi zumunci bayan bamu da rai." Ta ce cikin ɓacin rai tare da kai hannu za ta ƙwace wayar wutar da ya fisgo.




"Karka ƙara dukana ba ka da wayewa. I have right na yi abon da na ga dama."




Bige bakinta ta yi."Ke kam Jannah ba ki da kunya. Shegen bakinki yake ja miki duka, kamar Adamu za ki rinƙa zagi."




"Ok, bayansa kike goya ko? Wallahi saina shigar da ƙara inhar ya illantani."






Dukanta yake bakinta yaƙi rufuwa yayin da idanunsa ya rufe. Tun yana dukanta da bulala har ya fara haɗawa da hannu.




"Kai Adamuu kar fa ka yi kisa tun da bakinta ya ƙi rufuwa ka yi haƙuri ka ƙyale ta ai babba juji ne." Ta ce tare da ƙoƙarin shiga tsakaninsu.




"Ki barshi ya kashe ni wallahi sai ya yi dana sanin haka don dad ba zai taɓa ƙyale shi."




"Hajiya Baaba, ƙyale ni yau saina sauke mata duk wani iskancin kanta sai ta yi dana-sanin zagina."




Hajiya Baaba ta rasa yadda za ta yi dasu shi yana dukanta bakinta ya ƙi rufuwa. Kukan kura ta yi ta shiga tsakaninsu tare ƙoƙarin karɓe bulalar hannunsa.




Ajmal da zuciya ta tiƙo shi jin yadda take zaginsa tana yin fitsarincinta son rai. Ya sanya hannu ya ture Hajiya Baaba da ta kawo hannu da nufin ya damƙo Jannah.




Cikin rashin sa'a ta bugi center table na glas ɗin falon y fashe ta faɗi kansa wanda ta yi taga-taga za ta faɗi kansa amma sai ta yi ƙoƙarin dojewa sai dai duk ƙoƙarinta sai da ta faɗa wanda ya sanya ta ƙwala ƙara tare da zubewa ƙasa luu ta sume.


Ƙarar da ta saki ya sa ya bar dukan ya yi kanta yana girgizata tare da kiran sunanta ganin aika-aikar da ya yi.




Jannah da ta sha wuya wani irin jiri ya ibe ta ganin goshin Hajiya Baaba na zubda jini sai kawai ita ma ta bi bayanta ƙasa babu numfashi.




Ummu da ta shigo cikin falon domin sashinsu ta wuce don yunwa take ji. Ganin abin da ya faru ta sanya ihu tare da girgiza su sai kuma ta ruga da gudu zuwa ɗakin Ammy da ta fito daga wanka ɗaure da tawul.


Saboda tsabar kiɗimewa ta kasa magana sai dai nuna sashin Hajiya take tana ihu.




"Na shiga ku don Allah ki gaya mini mutuwa aka yi, mai ya faru da Ajmal ɗin ko hatsari ya yi da zai dawo daga tafiyar?" Ta shiga jero mata tarin tambayoyin amma ta gaza furta komai.




Ganin haka sai ta ruga har za ta fice sai ta tuna babu kaya a jikinta ta zura hijabi ta fice zuwa sashin Hajiya Baaba.




"Kai Ajmal, mai ya faru mutuwa Hajiyar ta yi?" Ta ce tan kallonsa cikin kiɗima ganin ya ɗauko ta jini na zuba goshinsu.




"Ammy Jannah, ita ma ta mutu." Cewar Ummu ganin hankalinsa ba shi gareta don har ya fice da Hajiya ya tada mota.




"Innalilahi! Ajmal, ya janyo mini musifa daga dawowarsa." Ta ce cikin muryar kuka don ta fra fahimtar komai.




"Ma za ɗauko mota mu kai ta asibiti." Cewar ta tana girgiza ta.




"Ba zan iya tuƙi ba sai dai direba Musa ya kaimu." Ummu tace tana kallon 'yar'uwarta cikin tashin hankali.




Har Ammy ta shiga mota tunawa daga ita sai tawul ya sa ta ruga da gudu sashinta ta ɗauki doguwar riga ta zura suka wuce asibiti bayan ta kira Aby ta sanar mishi.






"Wash Allah, a ina nake nan, duniya ko kiyama? Shikenan, sun kashe ni sun huta dama na san watarana sune ajalina." Ta ce tana kallon doctor Irfan da yake dressing ɗin kanta."


"Ki kwantar da hankali ki a asibiti ne kin samu minor injury ne."




"Kai dallah ni sake ni sai ku yi ta saka fararen kaya a asibiti, saboda ku tsorata mutane su ɗauka mala'iku ne." Ta ce tana ture hannunsa daga goshinta.




Murmushi ya yi jin abin da ta ce." Saura kaɗa a gama miki dressing ki tsaya na gama na ɗaure." Ya ce yana kallon Ajmal da yake ɓoyewa a bayansa.




Karab! Idanunta suka hango mata shi."Za ka ci ubanka wallahi kai da jannah sai na muku rashin mutuncin da ba za ku taɓa mantawa da ni ba, don saina sanya muku irin tabon da kuka yi mini gashi nan sai dai na tafi lahira da shi. Zan ga ƙarshen ƙiyayya." Ta ƙarasa maganar tana nuna shi da yatsa.




Buɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login