Showing 63001 words to 66000 words out of 137802 words

Chapter 22 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

ta wuce ɗakinta.Taɓe bakinta ta yi alamun ko a jikinta.


Ganin ta kwashi kaya sai ta fito ta saka kuka."Na shiga uku na banu! Adamuu ya raba ni da 'yar Halimatuu da nake ganinta tamkar uwarta. Allah ba zan yafe masa ba."


Ummu ta kama troley ɗinta."Please don't go anyway, you know I can do without you."


Balla mata harara ta yi tare da janye troley ɗin.


Sosai Hajiya Baaba ta riƙe jakar ta rantse babu inda za ta sai dai su tafi tare.


Ganin haka Aby ya ja ta suka shiga cikin ɗaki." Kiyi haƙuri ki kyaleta, inta huce za ta dawo. Kuma kin san zamanta a nan ba zai ɗore ba. Gidan Halima an gama komai, kawai dawowarsu ake jira. Kinga dole gidan iyayenta za ta koma.


"Ba bu yadda zan yi ne, amma wanann mara mutuncin ya cuce ni."


Kafin ma su fito ta fice wanda hankalin Ummu ya tashi ta saka a ranta ita ma dole ta koma zaman hostel don ba za ta iya rayuwa babu ita ba.


Tun da lamarin ya faru ta ƙi ɗaga wayar mom domin gani take duk ita ta ja mata shiga wannan halin. Ta yi kiran duniya amma ta ƙi ɗauka, haka ta tura mata tsako ko kallon numbarta ba ta yi.


Sai zaman hostel ɗin ya yi mata daɗi. In suka dawo daga lecture library take wucewa ta yi karatu sai yamma take dawowa. Abinci kuwa ba ta girkawa sai dai ta siya.


Ko sati ba ta yi ba Ummu ta haɗa kayanta ta biyo ta, wanda ta yi murnar hakan don ita ma ta san fushin da ta yi da ita na ɗan lokaci ne, amma she could not do without her.


Karatu suke yi sosai babu kama hannun yaro domin they have future accomplishment and they want to accomplish it."


Zaman hostel ɗin ya sa suka ɗauki wasu ɗabi'u suka ɗora ma kansu. Zuwa party da kitson attach. Hijabi kuwa sai dai in za su yi sallah, don wani lokacin hakanan za su sha gayu su ɗauki littafansu su tafi hostel babu mayafi, don cin kararsu suke babu babu babbaka.


Shirye-shiryen jarrabawa da ya tunkarosu suka mai da hankali babu dare babu rana, kullum cikin kratu suna library.

Cikin sa'a suka kammala jarrabawar. A tunanin Ummu Jannah za ta biyo ta su je hutu, amma sai ta ji saɓanin hakan. Ta kafe kan Zey za ta bi hutu zuwa gida.


Hankalinta ya tashi ƙwarai don haka ta ɗauki wayarta ta sanar da gida abin da ke faruwa.


Aby cikin ɓacin rai ya kira wayarta, wanda tana ɗauka ya fara magana cikin ɓacin rai,"Hello Jannah, in har ba kya son ranki ya ɓace, kafin na dawo aiki na ganku a gida ke da Ummu."


Ɗif ya kashe wayar ya barta sagale da ita. Kallon Ummu ta yi ta banka mata uwar harara.


"Munafuka na san ke kika faɗa masa." Ta ce mata tana jan troley ɗinta.


"Haba sis, ke ma kin san bai kamata ace ga gidammu ba kin tafi wata uwa duniya hutu."


"Kiyi mini shiru tun da kin haɗa ni da shi sai ki tashi mu tafi burinki ya cika."


Dariya ta yi tare da miƙewa ta ja troley ɗinta suka fito.


Ba ƙaramin frin ciki Hajiya Baaba ta ji da ta ganta ba. Har da kukan murna ta rungume ta.


"Ba ki da kirki kwata-kwata har ciwo na yi amma ba ki zo ba."


Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba don har yanzu hushi ta ke yi.


Tun tana bonewa har ta gaji ta saki ta kama harkanta.


Hutun ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba musamman yadda take nan nan da ita, kuma tun da ta sawo ba su yi faɗa ba.


Suna zaune ana hira Hajiya Baaba na gefenta da goro a hannunta. Ɓalla ta yi ta saka a bakinta, sannan ta ɗauki lakasera ta kurɓa ta ije tana kalloon Jannah da take ɓata fuska tamkar za ta yi amai.


"Kai Hajiya Baaba, wallahi na tsani kwacamalar nan da kike yi. Don Allah ki bari, ni kam ban taɓa ganin inda aka haɗa goro da lacasera ba."


Ummu ta kwashe da dariya tana faɗin,"Taɓ! Ai sai dai ki gaji ki daina, don dalilin da Ya Ajmal ya sa ya daina zama sashinta kenan."


"Eh, ina jin bakina ne, kuma cikina zan kai ba na wani ba? Na san lokacin tsufarku abin da za ku aikata."


"Allah ya kyauta na ci goro don ni ban ga amfanin cinsa ba."


"Gaya mata dai." Cewar Ummu tana kallon Hajiya da take harararta.


"Humh, kan ku ake ji. Kwayi kwa gam, domin wanda ya fi ku ƙyanƙyani haka ya gaji ya barni."


"To ku ya kamata ku fara maganar fara zance ko da ke Jannah kin fara. Kun dai san ba za mu tara ku ɗigi-ɗigi muna kallo ba."


"Haba Hajiya, wane irin magana kike yi, duka yaushe muka fara karatun da za ki fara maganar aure. By the way ni ba yanzu zan yi aure ba sai na gama karatuna ba ki ɗaya na samu aiki."


"Ashe laillai ba ki da hankali kuwa. Kai ni fa wannan bokon da kuke yi ba son shi nake ba, domin da za a biye tawa duk aure zan muku."


Harararta suka fara,"Aiko da kin cuce mu Hajiya. Allah ya kyauta don ke an cuce ki am miki aure da wuri sai ki rama akanmu. Ta Allah ba taki ba."


"Dallah rufe mini baki.Auren nawa ai shi ya yi muku gata a duniya, don ya yi mini rana ban yi karatun na haifi minister."


Dariya Ummu ta yi ganin yadda take doro da ji da kai.


"Tab! An ce miki zama minister wasan yarane. Ki tsaya ki gane tun kafin zaɓe za ta sha ƙasa.. Aure ne dai sai na yi degree da master har da phd if possible na fara aiki."


"Baƙinki ya sari ɗanyen kashi ta Allah ba ta ki ba." Ta bata amsa tana kai mata dunduni.


"Wayyo Allahna! Hannunki kamar icce don Allah ki daina." Ta ce tare da gamtsarewa.


"Ba dole ya zama icce ba ya ga jiya ya ji yau."


Ummu ce ta karɓi zance da cewa,"Wai da gaske kike har sai kin taka wannan matsayin sannan za ki yi aure? Ni dai if pssible I wanna marry before finish degree don bani da wannnan ra'ayin ina samu wanda nake so zan yi aure, ba zan yadda na tsufa a gida ba, kum kina tunanin Huzaifah zai yarda?"


"Mai zai hana shi ma ba yanzu zai yi aure ba, don yanzu haka Maleshiya zai je ƙaro karatu."


"Ashe ko wani zai yi wuf da ke don wallahi ana bikin Hafsatuu zan tasa ku agaba. Ko mahafiyarki da ta samu ɗaukaka duk tana gidan aurenta ta samu." Cewar Hajiya.


" God forbit over my dead body ayi mini auren wuri, don babu wanda ya isa ya yi mini aure da wuri saboda komai na rayuwata a tsare yake ba zan iya haɗa aure da karatu ba."


"Shikenan, lokaci zai nuna ai domin aure lokaci ne. Ni bari na yi walha na gaji da suratun banza." Ta miƙe tare da shigewa ɗakinta.


Ranar Juma'a suka shirya da Huzaifah zai zo. Tun ranar Alhamis suka je aka yi musu kitson attach sannnan suka lalli mai kyau.


Washegarin ranar Juma'ar bayan an sauko masallaci. Jannah na gaban mirrow da soson hoda a hannunta tana gyara hoton da ta shafa. Ummu na zaune kan gado tana kallon tiktok.


"Sis Huzaifah zai zo amma bamu yi mishi komai ba don ni kam sai yanzu na tuna duk ni ma na shiririce. Ko iya drinks da snack za mu ba shi."


"Don't worry about that I have ordered food for him. They will bring the food before his arrival."


"Ok" Ta ce tare da ci gaba da kallonta, sai kuma ta juyo tana kallonta ta ce,


"Na so na ce miki mu yi wa matar ustazu magana ta yi mana girki mai rai da lafiya, amma sai na tuna muna zuwa za ta fara mana wa'azin mu koyi girki."


Dariya ta yi jin abin da ta ce,"I was thinking the same, but na so na yi mata maganar, amma na san ɓata mini mood ɗina za ta yi. So, it should be better na yi oder."


"Eh hakan yafi ai. Rashin kuɗi su ke janyo maka wulaƙanci. Akwai maƙociyarmu da take snacks ba ri na sanya ta turo mana da samosa ta ita sosai."


"Thanks." Ta ce ta zauna gefenta tana murmurshi.


Bayan an kawo abinci da samosa. Suka jera a dining ɗin Hajiya Baaba sannan suka sha gayu tare da turare gidan da turare .




Ta fito za ta shiga kicin ganin su a falo tamkar waɗanda za su fita. Ta kalli dining ɗinta da yasha kayan daɗi, sai ta juyo ta kalle su da suka ɗaure fuska, babu alamun son amsa tambayar da suka san dole sai ta yi.


Ga mamakin su sai suka ta basar tare da taɓe baki, ta shige kicin wanda 'yan mintina kaɗan ta fito za ta shige ɗakinta, sai kuma ta dawo da zauna tana faɗin,


"Ban gane ba, an yi yamma da kare. Munafunci da ƙus-ƙus da na ji kuna yi, na san da walaki goro a miya. Uban me kuke shiryawa.Ni da gidana mallakina ba za ku gaya mini Kon baƙi mata za ku yi? Don na lura yamzu kun iya kwashe-kwashe."


Kallon junansu suka yi tare da kwashewa da dariya."Gidan Abby dai." Cewar Jannah.


"Ai kai da kaya duk mallakar wuya ne." Ta bata amsa.


"Daɗina dake akwai son jin ƙwaƙwaf, wato tun ɗazu kin yi kamar ba ki san me muke faɗi ba, ashe kin baza kunne kina jinmu."


"Ah to za a hana ni ne da kunnina." Ta katse Jannah da faɗin haka..


"Abokin Jannah ne zai zo yau." Ummu ta ba ta amsa tana kallon Jannah da ta tsinci kanta da jin kunya ta rufe ido.


"Aboki ko? Munafukan banza. Kwa fito fili ku gayi gaskiya."


Dariya sunne kai da Jannah take yi ya bata mamaki.


"Eh, abokinta ne mana. Huzaifah ne, kuma ai kin san shi. Saurayin da ya ya riƙe ki a filin jirgi da za ki faɗi, wanda Ya Ajmal ya ce yazo bikinsa."


Sai ta faɗaɗa fara'arta tana kallon abincin da suka shirya a dining.


"Allah Sarki! Ce mini za ki yaron kirki, na gane shi. Kuma shi ne don son jiki da sangarta kuka kasa yi masa girki sai dai ku siyo masa? Ai da kun gaya mini da na yi masa girkina mai matuƙar daɗi na tsofaffinnda suka ga jiya suka ga yau akan girki."


"Dabbu, fate, tuwo, shishshika, ko caccaka ne sunan abicin ko me oh. Shi ne abinci da kika iya masu daɗi? Allah ya kyauta ya ci. Huzaifah namiji ne wayyayye ba irin Ya Ajmal ba. Sam ba ya cin abincin gargajiy..."


"Ai ko dai da yaji haushi kuma basir sai sun yi ajalinsa. Ai duk wanda ya bar gida, gida y barshi. Na fi gwara gurbin buduwar da yake so, wacce ko murhu ba ta iya haɗawa."


Ta yi shiru ko za ta ce komai amma sai ba ta ce komai ba sai dai harararta da ta yi domin hankalinta na kan wayarta da take tsammannin jiransa cikin sakannni don ya sanar mata sun iso 'yan mintina ya rage.


"Allah Sarki har na fara tausayinsa. Ga shi yaron kirki amma ya yi zaɓen tumun dare. Lallai ya haɗu da jarrabawa." Ta canza fuska zuwan kalar tausayi kamar za ta yi kuka.


Wani kallo ta watsa mata dai dai lokacin da ta juya zuwa kicin tan faɗin,


"Bari na je na yi masa tuwon shinkafa miyar kuka mai daɗin sai kunnensa ya kusa tsinkewa, na rama alkhairin da ya yi mini dama shi danƙo ne."


Da sauri ta kalli Ummu da ta yi zuru tana kallon Hajiya Baaba cikin takaici.


"Sis ya iso yana ƙofar gida." Ta ce tana kallon fuskar wayarta da ke ɗauke da numbarsa ɓaro-ɓaro.


"To sai ki bar girkin babu buƙata don sun ƙaraso suna ƙofar gida, kuma ko kin yi sai dai ya yi kwantai, kuma wallahi in kika kunyata ni kin san halina" Ta bata amsa da faɗin haka da ƙarfi don ta shige kicin sai ɓarin tukwane take yi.


Tabe baki ta yi ba ta ce komai ba ta karasa shigewa kamar ba da ita ta yi maganar ba.


Ummu ce ta bita kicin ɗin daidai lokacin da jannah ta buɗe ƙofa ta nufi harabar gidan.


"Hajiya Baaba don Allah in suka shigo kar kiyi wani abu da bai dace ba kin ga su ɗin baƙi.."


Kamar za ta cinyeta ɗanye ta taso mata."Dallah can shashasha rufe mini baki! Saboda gani ƙaramar yarinya, in suka zo zan je na sa hannu a abincinsu ko na yi rashin kunya ko?"


"Allah ya ba ki haƙuri ni ba haka nake nufi ba, kin san me nake nufi."


Harararta ta yi ta ɗora tukunya a kan gas ta ce,

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093












KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 18-19*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM














Harararta ta yi ta ɗora tukunya a kan gas ta ce,


"Kun san kuna da abin faɗin ne ni dai ina gani ba zan yarda a cuci yaro ba don ba zan yarda na mayar masa da sharri akan alkhairin da ya yi mini."


Ba ta ce mata komai ba ta juya ta fita daga kicin ɗin amma zuciyarta sai faɗi take tana addu'ar Allah ya sa kar taba da su don sanin hali ya fi sanin kama.




Da murmushi mai tsada ta ƙarasa gurinsu wanda ya kashe mata ido tun da ta taho. Hure masa idon ta yi da ta isa gare shi. A jiyar zuciya ya saki mai ƙarfi.


"A koda yaushe muka haɗu gani nake kina ƙara kyau bab, kin kuwa ganki tamkar wata a cikin taurari.


Murmushi ta yi jin abin da ya faɗi."Ku shigo ciki Mufid ka ga abokinka sai zuba yake."


Dariya ya yi."Ai dole ya yi zuba kamar fanfo samun mace irin ki ai baiwa ne. Tabbas abokina ɗan baiwa ne."


Ƙara murmushi ta yi tare da nufar hanyar shiga cikin gidan wanda ganin haka suka bita.


"Ƙawarmu, aminiya, kuma 'yar uwarmu."Ya faɗa daidai lokacin da ya buɗe labulen falon bayan ya yi sallama.


"Barka da zuwa ku shigo. Huzaifah duk wannan matsayin ni kaɗai?"




"Ai kin wuce haka ko bab?" Ya yi maganar yana tambayar Jannah dake gefensa.


Ɗaga masa kai ta yi tana murmushi.


Bayan sun gaisa da tsokanar juna sai Ummu ta miƙe tana murmushin ta ce,
"Bari mu shiga ciki mu barku ku ci abinci."




"A don Allah ku tsaya na fi son ina kai loma ina cin abinci mai daɗi da my future wife ta girka. I know it will be very testing"



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login