Showing 66001 words to 69000 words out of 137802 words

Chapter 23 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

Hajiya Baaba da ta fito da hura da nono a hannunta tana faɗin,"Ina kuke 'yan son jiki? Sai ku karɓi wannan hurar ku dama masa, ko banza ya samu yaci abincin da ya fito daga gidanku tun da ƙila kafin in gama abincin sun tafi."




Turus ta yi tana kallonsu don ba ta ji shigowarsu ba saboda bayan fitar Ummu rediyo ta kunna.



"A lale marhabin da zaratan maza." Ta ce tana washe baki ta ƙarasa gurinsa.


Sai suka yi tsuru-tsuru don a tunainsu sun ji abin da ta faɗa.


Duƙawa suka yi suna gaishe ta. Guri ta samu ta zauna taci gaba da cewa,"Haba ku tashi ai kamar Adamuu na ɗauke ku. Ma za ku tashi 'ya'yan albarka."


Miƙewa suka yi suka koma mazauninsu suna shafa ƙeya.


"Sai na ji kamar ka ce za ka ci girkin Jannah ko?"


Ɗaga mata kai ya yi cikin kunya yana sosa kai tare da mamakin tambayar.


"Taɓ! Aiko ka bugo don wallahi ko ru.."


"Hajiya Baaba kamar kin ɗora abu a wuta kamar yana ƙonewa." Cewar Ummu tama kama hannunta ta miƙe.


"Ke dallah kyale ni na faɗi gaskiya ai ita ɗaci ne da ita." Ta ƙarashe maganar tana wafce hannunta da ta tsaya kamar mutum mutumi.


"In kana jin sangartacciya na bugawa a jaridan ita ce, ka ga duk wannnan abincin da suka shirya maka, wallahi duk siyo shi suka yi. Ni saboda takaici kasa magana na yi, amma na ce sai na gaya maka kar na cuce ka saboda alkhairin da ka yi mini."




"Haba Hajiya Baaba, gaskiya abin da kike yi bai dace ba, kum.."


"Kin san Allah in kika ƙara magana sai na kwaɗe ki da maficin nan. So kike na cuce shi? Ai gara na gaya masa idan aka yi auren da ni za a taho don ni zan rinƙa masa girkina mai daɗi da rainon yara. Maganar aure fa ake yi, kuma ai dole sai an faɗi naƙasun kowa."


Sai ta gyara zama tana kallon Jannah da takaici ya hana ta cewa komai sai hawaye da kin bin ƙuncinta domin ta ji a jikinta dole sai ta kunyata ta.


Harara ta banka mata tare da kallonsa ta saki dariya."Ka na jina ko yaron kirki? Da Ummu takan yi abin kirki amma zuwanta gidan komai ta daina, ba su da aiki sai kallo da hira a waya. Shi ya sa na ce ba zan ɓoye maka komai ba gara na sanar dakai fare zamu taho in an yi bikin."




Saboda dariya Mufid har tuntsira ya yi. Shi kuwa Huzaifah dariyar yake ƙoƙarin ɓoyewa, amma har sai da ta ci ƙarfinsa ya dara.




"Oh my God! Gaskiya you Grandma is so dramatic, I love her." Ya ƙarashe maganar yana kallon Jannah ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye sai kuma ta share tana faɗin,




"Ai dama shi kansa ya san bai nemi aure inda matarsa za ta rinƙa masa kirki ba, in kin yi hakanne ki kunyata ni." Ta faɗa a tsiwace tana harararta.




"Au iyye a gabansa sai kin nuna halinki?" Ta ce tare da kama bakinta tana kallon ta. Sai ta juya kallonta garesa ta ci gaba da cewa,


"Ka gani ko? Allah na gode maka da ta nuna maka halinta. Yanzu da na ce maka fitsararriyace ba ta ganin kowa da gashi sai ka ji haushina, amma gara da ta nuna maka halinta ƙiri-ƙiri ka gani.Ita ɗin kura ce da fatar akuya. A waje kamar mutuniyar kirki."




"Oh common bab. Kin san ko wace irin mace kike ina sonki, saboda tsarinki da zubin ki duk sun yi mini." Ya ce mata bayan ya miƙa mata handkerchief ɗinsa, sannan ya juya yana kallon Hajiya Baaba da ta ɗaure fuska jin abin da ya ce don ita ba haka ta so ba, ta so ace ya nuna ba zai iya ba ko ta yi zuciya ta koyi aiki.


"Ba ki da matsala Hajiya Baaba, mu house is welcome to you at anytime you wish. Sosai kika burge ne Ina matuƙar son ki dawo gidana gabaki ɗaya da zama."


"Humh! Ka ji da gulman turancinka na bogi, ai ni ba na faɗa maka bane don na burge ka, na faɗa maka ne don na gaya maka gaskiya." Ta ce tare da juyawa za ta shiga kicin ganin haƙarta ba ta cimma ruwa ba.




Ajmal da ya yi sallama ya shigo don kawo mata maganin da tun safe ta addabe shi da kira ba ta da lafiya, amma ga mamakinsa tun daga ƙofar ɗakin ya fara jiyo muryarta tana zuba.


Idanu ya zuba musu bayan ya yi sallama ya shigo. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita musu magana ba duk da ganin yadda suka yi razana don sun ɗauka har su tafi ba zai shigo ba.


Da sauri Huzaifah miƙe zai bi bayansa amma sai Jannah ta hana shi,


"Lemme go and great Babban Yaya."


"No you don't have to do that."Ta ce tare da riƙe gefen rigarsa tana girgiza masa kai cikin rashin karsashi domin gabakiɗaya Hajiya Baaba ta ɓata mood ɗinta.


Sun daɗe suna hira har sai da suka gaji don kansu suka yi wa Hajiya Baaba sallama suk tafi bayan sun cika lalitarta da bugun Abuja wanda ta rinƙa shi masa albarka kamar a ta goya su.




"Wayyo Allah! Tun shigowa Ya Ajmal na rasa sukuni. Ni kam mun bani Allah ya sa karya gayawa Aby." Cewar Jannah tana dafe ƙirjinta ganin motar su ta ɓace daga gurin.


"Amin, ni wallahi har sai da cikina ya murɗa. I was thinking that he would embarrassing us in front of him, but thankfully he didn't."


"He never try that, cus i won't stay an watch it." Cewar Jannah cikin ɗaure fuska, sai kuma ta juya tana kallon hanyar da suka bi.


"Kin san Allah yau ni da Hajiya Baaba a gidan nan about what she did to me I was very devastated."


Dariya ta yi ta ce," To me za ki yi mata kamar ba ki santa ba, ki ƙyaleta kawai kar ki ja ma kanki. Allah I was expecting that, infact more than that from her. Kawai dai we don't have any options ne shi ya sa."




Ƙuta ta yi ba ta ce komai ba ta buɗe get ɗin suka shiga.


Washegari da safe ko breakfast ba su yi ba kiran dad ya riske su. Gwalalo idanu suka a tare.


"Kai anya kiran nan ba lafiya ba fa. Ni fa kallon da Ya Ajmal ya yi mana na san dole sai ya kai ƙararmu gurin Aby, don ya cika gulma kamar ba malami ba." Cewar Jannh da ta miƙe cikin tsoro.


Ita dai Ummu ba ta ce komai ba ta miƙe har ta murɗa ƙofa sai ta dawo ta kalleta,"Don Allah ki yi sauri kin tsaya sai kuma mun ƙara wani laifin."




Ta faɗa ranta a ɓace ganin ƙoƙarin zama take wanda ya sa ta miƙe suka fice da sauri.


Ganin Hajiya Baaba zaune a kan kujera tana ta girgiza da kaɗa ƙafa jikinsu ya ba su ba lafiya ba.


Da sauri suka durƙusa a tare."Ina kwana Aby."


"Rufe mini baki shashashun banza! Ina kallon ku masu hankali har na barku kuke zaman hostel ashe wawaye ne ku ban sani ba?"


Aby ya furta murya a zafafe," A'a Muhammadu ka san ba zan ɗauki hakan, wanda na san duk zugin wannan munafukin ne. Ai tun da na ga ya shigo ya ije maganin ba tare da ya ce komai ba na san sai ya haɗa munafunci. In ban da gulma tun yaushe na rinƙa kiransa ya siyo mini, amma da yake isashshe ne bai zo ba sai da gulmarsa ta kawo shi."




"Haba Hajiya Baaba, ya muna ƙoƙarin gyara za ki ɓata kuma." Sai ya juya gun su.


"Ke Jannah da gaske kun kawo saurayi gidanan?"Ya ƙarsa maganar cikin tsawa.


"To laifi ne hakan Muhammadu? Na ga shi mace ya aje a gidansa yana hutawarsa. Ko so yake mu rinƙa ado da su a ƙofar gida? In ban da gulma da sa ido waɗannan tiƙa-tiƙan da 'yan matan da ba bu abin da suke yi, sai warin balaga za a tsaya ana tambyarsu don sun kawo maza gida zance."


Zare ido suka yi suna kallonta,"Warin balaga?Kai amma Hajiya ta cuce mu duk irin ƙanshin da muke yi." Jannah ta ce tana hararar ta tare da shinshina jikinta.


"Ni fa ba aure zan yi ba kuma abokina ne. Bayan wannan babu abin da ke tsakaninmu." Ta furta cikin rashin shakku da tsoro.




"Gabakiɗaya ke kike ɓata yarannan Hajiya. Idan aure za su yi ai babu wanda zai hana su, amma sa bari su yi zurfi a karatunsu. Duka fa yanzu suka zana jarraba na first semester, ko Nahlin sai da ta kai 3 hundrent level za ta yi aure."




"Da ma na san kashi da tusa duk nice a gidannan, saboda n bi ta bayan gida an shanye ka. Ni dai auren ƙabila babu abin da ya ja mini sai shata layi a tsakanina da ɗana. Ƙiri-Ƙiri ina ji ina gani an yi mini faƙara'u an raba ni da ɗana. Wallahi sai Allah ya saka mini." Ta ce tare da ƙara saka kuka tana share hawaye sai kuma ta kalle su Jannah da idanunta da kamar ba kuka take yi ba dai dai lokacin da Aby fara cewa,






"To yanzu don Allah mene na kawo wannan maganar a gaban yara? Na ɗauka mun riga mun zama ɗaya." Ya ƙarasa cikin jin zafin abin da ta furta yana kallon Amy lokacin da ta miƙe za ta shige ɗakinta hawaye na bin fuskarta.




"Dallah kyale ni! Sai a dake ni a hana ni kuka." Ta ƙarashe maganar tana kallon Ajmal da ya yi dana-sanin maganar.


Zuciya ta ciyo shi kawai ya ɗaga ƙafarsa ya kai musu ita da nufin ya haure su.




"Shikenan, ba ni da damar tsawata musu sai ta shige ta hana hakan? Kalli kansu Aby gabakiɗa atach ne a kansu, saboda iskanci sun tare a hostel babu mai tsawata musu sai sheƙe yarsu suke yi. Malaman islamiya sai magana suke ba sa zuwa islamiya da hadda."




Ya fara ƙoƙarin nemo bulala ya co gaba da faɗin,"Saboda iskanci a maimakon Ummu ta yi ƙoƙarin a ƙwato ta daga halaka, amma sai ta biye mata suna iskancin su babu mai kwaɓa musu."




Ƙara suka saki tare da ɓoyewa a bayanta.


Hajiya Baaba ta juya ta kalle su tare da wafce ɗankwalin Ummu ta girgiza kainta.


"Kuma fa in anbi ta ɓarawo, abi ta maji sawu. Ni kaina wannan uban gammo da suka ɗaura a kansu yana damuna, in dai akan wannan ne ba zan haka ba ka yi mini ƙasa-ƙasa da su."




"Ma za suje da direba ya kwaso kayansu babu wacce za ta ƙara kwana a hostel, in ba za ku yi karatun a gida ba ku bar shi, tun da aure kuke so sai ku kawo miji."


Jin abin da ya ce hankalinsu ya tashi ba kamar jannah da har ta fara kuka.




"Kuma awa ɗaya na baku ku kwance wannan gashin in ba haka aski zan yi muku." Ajmal ya ce tare da yarda bulalar ya fice, sai kuma ya dawo lokacin da suke hararar Nahlin da take musu dariya ciki-ciki.




"Ke Nahlin da ga yau ƙarki ƙara aiki komai su za su yi, kafin su tafi makaranta ki tabbatar da sun yi aiki gudan nan, sannan a wata uku nake su iya girki." Ya fice daidai lokacin da ta amsa masa.




"Ai wallahi gara ya yi musu haka dama ni zaman makarantar nan sam bana son shi domin Jannah ƙara lalacewa za ta yi." Ta fice ba tare da ta damu da yadda take kallonta ba, yayin da zuciyarta fari ƙal tamkar farin takadda, don Allah kawai ya san halin da ta shiga da ta koma makarantar.




Suna shiga ɗaki tasa ihu tana didddira har sai da ta faɗi ƙasa.


"Duk ke kika ja mini wannan bala'in da yanzu na bi Sham duk wannan tashin hankalin bai same ni ba." Ta gallah mata harara tana faɗin hakan.




"Na tsane shi wallahi. He just like thread in my life, threatening me all the time for what reasons?"




Tsayawa jikin mirrow ta yi tana kallon yadd kitson ya ƙawata fuskarta, ta yi ƙuta tare da faɗawa kan gado tana girgiza gashin dokin.


"Yanzu duk kyan da na yi haka zai sanya na tsefe shi saboda rashin mutunci da shegen sanya ido? Wallahi sai Allah ya saka mini."


Sallama Nahlin ta yi ta shigo cikin fuskar dariya ta zauna gefen gado.




"Please Anty Nahlin, we are not in the mood and you have to respect yourself. You know respect is reciprocal."




"And what?" Ta ce Ummu jin abin da ta fada tare da daure fuska, amma cikin zuciyarta dariya kunshe ganin yadda Jannah ta yi da fuska.


"I came to pass a message. Ya ce na gaya mu haddar shafi goma za ku bayar gobe, don haka sai ku fara karatu, sannan gobe zan fara koya muku girki tun da muna hutu sai kuyi amfani da damar ku."




Wani uban tsuka suka ja."Ya ce mu sauke kur'anin a gobe mana, in yana ƙaryar malinta. Ni wallahi haushi yake bani, in ya ga damar zai zama ustazu dole sai koya ya zama irinsa. Ai tsoron Allah a zuciya yake." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta kunna data ba tare da ta ƙara kallonta ba.




"Na rantse ko shafi biyu ba zan kawo ba don ban iya ba." Cewar Ummu.




"Ki gaya masa gobe menstruation ɗina zai fara kuma kin san wahalar da nake sha don haka ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login