Showing 27001 words to 30000 words out of 137802 words
Chapter 10 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
tura mata, amma ba ta duba wa ta ƙara turawa cikin sanyin jiki, tare da fatam Allah ya sa addu'arta ta karɓu ta duba.
Jannah ki dawo gare ni. Mahaifinki da kika fifita kura ne da fatar akuya, amma wallahi na fi shi sonki. Burina na taimaki al'umma, kuma dole saina tara kuɗi zan yi hakan.Tura mata ta yi ta online cikin karayar zuciya.
Zama ta yi a gurin tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tana jin wataƙila kukan da ƙarfi zai rage raɗaɗin da zuciyarta take ciki.
Wani irin tsawa aka saki mai razanarwa lokaci guda aka fara iska, mom ko motsi ba ta yi ba, ballantana ta nemi tsira da ruwan dake shirin gocewa.
Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
*KURA DA FATAR AKUYA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 8-9*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta, ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi, wanda hakan ya sa ta ƙi jirgawa ta ci gaba da kukanta mai amo da gunji, domin tana ganin saukar ruwan wani dama ne da Allah ya ba ta wanda za ta yi kukanta, ba tare da kowa ya ji ta ba, domin kuka rahma ce daga Ubangiji.
Haka Allah yake. Duk mulki da tarin dukiya da mutum yake da shi, ba ya rasa abin da Allah zai jarabce shi, domin cikin littafinsa mai tsarki ya na ce wa,
"Shin mun halicce ku, tunanin ku ba za mu jarabce ku ba."
"Ga misali da ni Hajiya Halimatu, uwa ba da mama, na shahara kuma Allah ya azurta ni da dukiyar da ko ni kaina ba na tunanin na san adadinsu, amma sai ya yi mini jarrabawar da na gwammace gara rashin dukiyar." Ta faɗa cikin ranta.
Tana wurin har aka gama ruwan, a lokacin har duhu ya fara yi sannan ta shigo gida, tana jin wani sashi daga cikin damuwarta ya ragu.
A falo ta fara ƙoƙarin cire doguwar rigarta har ta ƙarasa shiga cikin ɗakin. Kai tsaye bayi ta wuce ta yi wanka, sannan ta fito cikin rigar wanka. Busar da kanta ta yi tare da shiryawa cikin gajeruwar baƙar riga. Da sauri ta ƙarasa dining jin yadda 'yan hanjinta ke zillo suna neman agaji. Ba wani ci da yawa ba, ta miƙe tare da yin brush, ta canza kayanta zuwa kayan bacci. Ba ta yi bacci ba sai da ta tabbatar da ta samu visa, jirgin zai ɗaga karfe tara na safiyar gobe, sannan hankalinta ya kwanta.
Kwanciya ta yi, tare da jan ƙaton bargo ta kwanta idanunta a rufe kanta da shi lokaci guda bacci mai ƙarfi ya kwashe ta.
Washe gari kasancewar ta san tana da tafiya sai ba ta yi dogon bacci ba, ta shirya cikin gaggawa. Hankalinta a kwance ba tare da tunanin komai ba, ta isa filin jirgi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa Ukraine
A cikin jirgi ta zabga takumi hannu biyu-biyu, domin wannan tafiyar ya tuna mata da tafiyar da suka yi zuwa India da irin shirmen da ta rinƙa mata. Ciro wayarta ta yi tana kallon ta cikin tsananin shaukin soyayya.
Dad da yake zaune a katafaren falonsu yana ƙunar rai. Duk da cewar wannan karon ba shi ne karo na farko da ta ke yin tafiya ba tare da izininsa ba ko saninsa. Sai dai, wannan tafiyar ya fi masa ciwo. Ta ke ya yarda kuma ya amince cewar da 'yan'uwansa suke ba shi da kataɓus ya zama mijin-ta-ce, domin shi kansa ya aminta da hakan.
Lokaci guda tausayin Jannah ya kama shi na nisanta kanta da su, duk a dalilin su samu zaman lafiya, amma zai iya cewa komai ƙara rikicewa ya yi. Anyway ko ba bu komai, in har tana cikin farin ciki a inda take sai ya yi mata fatan alkhairi.
NIGERIA
Jannah zaune a cikin falon Hajiya Baaba tana kan doguwar kujera. Ta haɗe fuska sai kubbure-kubbure ta ke yi, sakamakon yau ko baccin kirki Hajiya Baaba ba ta kyale ta ta yi ba, ta bijiro mata da rigima. Yanzu ɗin ma kallon ta yi tare da zabga mata wata uwar harara ta ce,
"Kin san Allah ba zan zauna ƙazama ba, dube ki mace har mace amma ko ɗan kamfai ba kya iya wankewa, kuma wai abin takaici kike kiran kanki da mace."Ta ce tana kallon yadda take ta jijjiga tare da ƙara harararta. Sai ta ɗora da cewa,
"Ke fa gabakiɗaya rayuwarki matsala ce, domin in za'a sanya ni rubutu akan matsalarki wallahi saina cika littafi. Mace ba addini ba iya iya girki ba tsafta. Kullum sai shan kaɗe-kaɗe da raye-raye. Yarinya sai ka ce dangin dujal. Ke ni da tarihi ya zo cewar a mace dujal zai zo sai na ce ya bayyana a jikokina."
"Kin ga Hajiya ki daina ce mini Dujal."
"Rufe mini baki ina magana kina magana shashasha kawai!" Ta kai mata bugu da carbin da ke hannunta, wanda ta ji zafi sai ta saka kuka sosai." Kika duke ni? Wallahi saina gaya wa dad, kuma ba zan ƙara kwana a sashinki ba." Ta ce cikin tsigar shagwaɓa.
"Au iyye kashe ki na yi ba duka ba, ɗan wannan shauɗar da na kai miki? Taf ai ko kina da aiki, don wallahi gidan kowa ya sanni duka nake yi, ke hatta Ajmal ban raga mishi ba, kuma kifi ruwa gudu."
"Ashe ko wallahi za ki dukan ma kanki, domin na san right ɗin.."
"Au ramawa za ki yi?" Ta tambaye ta cikin sauri tare da ƙara kai mata bugu.
"Ni bance ba, amma kuma ni ban san mai zai faru ba."
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Hajiya ta ce tana salati tare da tafa hannayenta.
"Oh ni jikar mai gishiri. Ina ta murna jikallena za ta zo, zan huta da waɗancan marasa mutuncin ashe, lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi za'a kawo mini. Ko da yake ni dama tun da na ga idanunki ya soye na san cewar kura da fatar akuya ce ke."
Jannah ta buga kafafunta don ba ta gane karin maganar da ta yi mata ba, sai kawai ta ɗauki wayarta tare da tare sakin kuka.
"Dad zan kira na gaya mi shi kirana kike da sunayen sabbobi."
"Kira shi don ubanki. Daga shi har uwar ta ki ba su ishe ni na. Yo ni da ake jifana da tsafi amma na kasa taɓuwa, ballantana ke da iyayen na ki da kuke shashashu, ba ku riƙi komai ba sai aƙiddar banza ta yahudu da nasara. Ani na sha tabara na sha yasin tun ina ciki."
"Oh ko me kika ce dai ba zan saka atamfar nan mai kama da ruwan tumbuɗi ba. Mom na sanya atamfa amma ba irin wannnan marasa kyau ba, don haka dad zan kira ya turo mini kuɗi na siyo zaɓin raina"Ta ce cikin sangarta da shagwaba tare da dorawa.
A haka na taso, Kuma tarbiyar da 'yarki ta ba ni kenan, don haka masu aiki za'a ɗaukar mini.
"A'a bayi za'a siyo miki, ba masu aiki ba. kuma wallahi ba ki isa ki rinƙa zama mini a gida tsirarara ba. Ki gode wa Allah, da na ba ki atamfofina da ake siya mini duk sallah."
"Ba na so. Na lura "yar dirama ce kuma wallahi na fi ki iya tsiya." Ta ce cikin tsiwa.
"Ashe ko za'a kwashi 'yan kallo, ba ki san wace ce Hajiya Baaba. Lokacin ƙuruciyata saɓa ƙato nake na nuna ma Allah na buga da ƙasa, sai da na gagari hatta mai-gari ballatana ke karan kaɗa miya kina ji da kwakwankaso kamar an ɗaurawa tabarya zani"
"Ki dai ce komai, islamiyar ma ina dama ba zan je ba."
Da sauri ta dawo tana jifan ta da kallo ta ce,'Inda kika yi kaɗan kenan, daƙiƙiyar banza kawai."
Haƙura ta yi da neman dad sakamakon layinsa da ya ƙi shiga, sai ta miƙe tana harararta har da su muguɗa baki, wanda hakan ya ƙara ƙular da Hajiya ta bita a guje har zuwa bakin falo. Tuntuɓen da Hajiya ta yi da ƙofa ya sa ta daina gudun tana nishi.
"Wayyo Allahna! Wanann sheɗaniyar yarinyar ta ja na fasa ƙafa! Allah ya isa tsakanina da ke."
Jannah da har ta shige sasan su Aby ba ta ji me ta ke cewa ba.
"Hello dad ka na ji na? Please I need to upgrade my drower." Ta furta cikin shagwaɓa tare da fatar Allah ya sa ya ba ta kuɗi da yawa tana son ta yi sub na data don kuɗinta yawanci a data da chaculate yake ƙarewa.
"Ok, I will send you 200k, but please do answer your mom's calls."
Jan numfashi ta yi jin abin da ya ce."But dad.."
"No kar mu yi haka dake, ki bi umurina. Mahaifiyarki na buƙatar ki. She is in depressed and she needs your acompany. Trust me she really adore you."
Wannan karon shiru ta yi na ɗan lokaci domin tunaninta ya ba ta kawai yana faɗin haka ne don ya shirya su, ko kuma ta hura masa wuta da rashin mutuncinta kullum.
"Ni gask.."
"I said please! For the sake of me."
"Shikenan ta ci albarkacinka I will give her a call."
"Good girl. I know you will.
Sure, why not dad?" Sai ya yi dariya yana jin daɗin abin da ta ce.
"But seriously dad, don't put the blame on me. Don har yau ina jin babu daɗi yadda take yi maka. Ka duba yadda ta ɗora ma kanta wahala kula da duniya, amma a gidanta ta kasa bamu farin ciki. Shugabanci a gida ake fara yin sa. I knew tafiyar da ta yi, shi didn't seek your permission. Arrogant woman kawai."
"Well, my girl I see you poin, but please na ga ya miki your mom has good intention and she is doing the right things."
"Oh please dad! She isn't, you are just depending her as you do always." Dariya ya yi sosai jin me ta ce.
"Ni dai ƙara roƙon ki na ke da ki kira ta, support her and encourage her for havean sake, will you?"
"Sure I will, za ta ci albarkacin son da na ke maka." Ta ba shi amsa.
"Promise?" Ya ce cikin muryar roƙo hakan sai ya ba ta tausayi matuƙa, ta san cewa mahaifinta na matuƙar son ta wanda dalilin da sanya take garasa kamar ƙwallo.
"Saboda hakan zan tura miki da 300k sai ki saya harda abayoyin da mom ɗinki take sawa, yauwa ba ri na zaɓa miki colour."
Sai ya ɗan numfashi yana tunanin can ya ce,"Uuummmm! Pink, pich, and purple. It will fit you, like it does to your mom. Ba ki ga kalar da ta sanya ba da za ta yi tafiya ash colour, sosai ta yi kyau. Tamkar na sace ta na gudu. Yauwa ki haɗa har da ash."
Dariya suka yi sosai yana faɗin." Your mom is really beutiful and she has Charming charisma.."
"Dad, kai ma fa wani lokaci ba ka iya controlling kanka a kan soyayyar da kake mata shi ya sa ta yi ta gara ka kamar ƙwallo. Please do pretend you don't, don ita ma pretending kawai take yi, amma ai tana sonka, don babu macen da za ta kalle ka ba ta kware ma ka ba."
Sosai ya ji daɗin abin da ta ce."Ya zan yi Jannah? Ba ki san soyayya ba shi ya sa., kuma ke yarinya ce har yanzu..."
"Common dad am not under age, am 18years. So am full grow woman."
"That is why I keep calling you baby." Ya furta tare da kashe wayarsa yana faɗin,"Bye do take care of youself."
Ya faɗa jin abin da ta ce ya yin da zuciyarsa take cike da farin ciki don ya san in har ta kira zai samu sausauci daga gurinta.
Rungume wayar ta yi cikin farin ciki matuƙa domin tana matuƙar son mahaifinta.
Suna gama wayar sai ga alert ya shigo daga gurinsa. Murmushi ta yi mai sauti. Wayarta ta ciro ta tura mata da tsaƙo hi, wanda ko sakan biyu bai ya ba sai ka kiranta. A gadare ta ɗauki wayar.
"Wane ne?"
Zuciyar mom ta karye sai ta ji babu daɗi duk da ta san ta yi hakanme don kawai ta ɓata rai, amma ta san cewa ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta numbarta ba.
"Yanzu kina nufin ba ki da numbata Jannah?" Shiru kawai ta yi ba ta ce mata komai ba sai zuwa can ta ce,
"Ina son kuɗi zan je shoping." Ta furta ba cikin rashin ladabi da girmamawa.
"Na wa kike so? Faɗa mini na yi miki alƙawari ko nawa Jannah, domin komai da nike nema na ki ne. Ki faɗa mini zan ba ki."
"200k." Ta sanar mata.
"Ok, iya hakan kwai kike so? Ba ri na tura miko dubu ɗari biyar. In ba su isa ba sai na ƙara, ni dai burina ki damu da ni, ki ƙaunace ni ko da kwatankwacin rabin na mahaifinki ba ne."
"Yauwa mom, ki gaya ma wancan rigimammiyar mahaifiyar ta ki, ta kiyaye ni, kuma ki ɗaukar mini aiki don ba zan iya aikin da take saka ni ba. Na ga haka kika koyar da ni, idan da ce babu kyau ba za ki tarbiyartar da ni a haka ba, saboda iƙirarin son da kike cewa kina mini."
Sai ta ji kalamanta tamkar saukar aradu a ƙwanyarta. Rintse idanunta ta yi cikin ƙunar rai. Wasu zafafen hawaye suka wanke mata fuska.
"Na yi kuskuren da ba zai gyaru ba. Ki yi haƙuri zan yi mata magana."
"Humh"
Ta ce tare da kashe wayar da sauri tana hararar wayar don duk wayar da suke yi daurewa kawai take yi, amma wani zafin ta take ciki.
Mom ta ije wayar cikin tsananin damuwa domin a maimakon ta ji sausaucin kirar sai baƙinciki da ya cika zuciyarta, domin ba haka ta so ba, don ta so ta gaya mata kalamai masu daɗi na tsakanin 'ya da uwa sannan ta tambayeta cikin girmama, amma kiran wani nasara ce.
"Watarana za ki fahimci gaskiya ki soni fiye da yadda kike so mahaifinki. Sai dai, ina miki fatan ka da ki yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada. Wataƙila ba ni a raye ko kuma ba ki da halin gyara kuskurenki. Allah ya yi miki albarka." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.
Ƙarar shigowar kuɗin ya sa ta zuba wani irin ihu.
"Da ma na san za ta tura mini, ai mom is open handed. Ko da yake kuɗin ta ke samu ba ta san darajar kuɗin ba.
Miƙewa ta yi tana mazurai ganin Hajiya Baaba a kanta.
"Da ga gani ba ki da gaskiya. fitsararriya kawai."
"Tun da ba sata na yi miki ba sai a sha fa mini lafiya."
Hajiya ta yi ƙuta tare da kai mata bugu amma sai ta dakata jin wani uban ihu da ta ƙwala har sai da gidan ya amsa.
"Na ba ni! Ki ji mini 'ya za ki tara mini mutane. Wallahi in kina cin ƙasa ki kiyayyi ta shuri, ki yi mini biyayya mu zauna lafiya babu mai jin kammu. Ungo maza ki je direba ya kai ki a gwada ki ɗinki, da kayan