Showing 129001 words to 132000 words out of 137802 words

Chapter 44 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

kuma ta ɗago ta kalle shi daidai lokacin da ya leƙa wayar yana kallon hoton Huzaifah.


"Shi kan dai murna za a yi masa da rabuwa da jaraba da ya yi, ni kuma a jajanta mini. Sai ya taɓe baki ganin ba ta ce komai ba, wayarsa ya ciro wayarsa tare da nuna mata hoton.


"Ki kalli wannan hoton."


Kallon banza ta yi kamar ba za ta kalla ba sai kuma ta kalla a wulaƙance.


"Na gani gidan kifi ne, ba ka da jari ne kake son na roƙi mom ta ba ka?" Ta ce mishi a gatsale.


"A'a." Ya ce tare da dariyar mugunta ya mayar da wayar a aljihunsa.


"Na zo na nuna miki na kuma yi miki albishirin da cewar matuƙar kika yadda aka yi auren nan, a daren amarcinki a nan za ki kwanta.


Juyowa ta yi da sauri tana kallonsa yayin da take son gasganta abin da ya faɗa.


Gira ya ɗaga mata sai kuma ya ɗora da ce,


"Matuƙar kika ba yi abin da za a fasa auren nan ba aka kawo ni ki gidana, sai kin gwammace dama guba kika sha kika mutu, domin ina da matar kirki kamila mai kame kanta da alfasha mai zan yi dake ballagaza."


Kuka ta saka da ƙarfi sai kuma ta ga babu amfanin haka ta juya ta kalle shi ta saka dariyar takaici.


"Ka kwantar da hankalinka domin in har ban sha guba na mutu ba, zan yi sanadin ranmu ni da kai domin ba zan taɓa yarda na jawa kaina abin kunya na auren bagidaje irinka ba."


"Ok, haka kika ce." Ya tambayeta cikin mamakin rashin kunyarta.


Ɗaga masa kai ta yi tare da balla masa harara za ta wuce sai kawai ransa ya ɓaci ganin kallon da take masa ya sa ƙafarsa a tsakaninta kafafunta wanda ta harɗe ta faɗi ƙasa wayarta ta fashe.




Tsabar baƙinciki da zafin faɗuwar ya sa ta canyara ƙara wanda sai ga mutanen gidan a gurin har da Hajiya Baaba.


"Lafiya Ajmal? Na lura ba za ku taɓa barinmu mu huta ba."


"Da ga na zo zancan shi ne ta yi mini rashin kunya shine na fara koya mata yadda ake yiwa miji magana domin matata, haka take mini ba, ka ga gara na koya mata don kar ta ɓata mini tarbiyar matata." Ya ƙarashe maganar tare da kallonta yana murmushin mugunta.


"Ba zan iya ba da kuɗin zance ba Hajiya Baaba, domin ko lokacin da nake zuwa zance gurin Mushirat, in har ta ɓata mini rai bana bada kuɗin zance."


Murmushin mugunta ya yi y fice tare da faɗin,"Sai da safe."


Hajiya Baaba, ta kalle ta da take kuka sosai ga baƙincikin sabuwar wayar da ta siya ya fasa har ta ƙi kawowa. Kuka ta ƙara rushewa da shi.


"Wallahi Allah sai ya saka mini akansa da wacce ta haɗa auren, ba zan taɓa yafe wa ba." Ta ruga da gudu tana kuka.


"Fitsararra! Kin dai ji haushi wallahi, saboda ko wace mace in aka zo zance kuɗi ake ba ta, amma ke tsabar rashin kunya ya jawo miki, duka kika samu, to wallahi ba zan takurawa kaina ba, iya abin da ya samu za mu kai miki." Ta wuce tana bambami ba tare da ta kalli su Aby ba.












Dad ɗin Huzaifah ya shiga cikin matsanancin tashin hankali, ganin ya ƙi ci ya ƙi sha sai kuka da kiran sunanta wanda ganin haka ya sanya shi yi wa Zariya dirar mikiya, ba tare da shawarar mom da take ta yi masa tsiya ganin zai kashe kansa a banza ba.


Bai sha wahalar ganin Aby ba wanda ya karɓe shi cikin mutunci ya yi mishi karɓa ta ban girma duk da ba a san da zuwan shi ba.


"Ni ne mahaifin yaronan Huzaifah, wanda yake son Jannah, na san kuna da labarin mun zo lokacin suna Abuja, yanzu ma na ƙara zuwa akaro na biyu, saboda yarona he is in critical condition. Na roƙe ku don Allah.." Ya ce hakan tare duƙawa a ƙasa yana hawaye.


"Yarona zai mutu kuma shi kaɗai Allah ya ba ni ɗa namiji, ku taimaka ku bar yaran su yi aure."




Aby sai ya ji babu daɗi ganin mutum da girma kamar sa da muƙami yana roƙonsa. Sai dai, ko kuka ya yi baya tunanin za ta amince da idanunta ya rufe na ɗaukar fansa a kan dukanninsu.




"Ka yi haƙuri Hajiya Baaba, ba za ta amince ba, domin idanunta ya rufe fansa kawai take so ta ɗauka. Mu ɗin mun yi kuskure wanda ya shafi yaronmu. Ina fatan yaronka ya samu lafiya."




"A lokacin da muka je Abuja bamu ji da daɗi ba, amma don Allah ka ƙara kira mini ita na ƙara roƙonta ko za a dace."




Jiki a sanyaye ya miƙe bayan ya sanar masa da yana zuwa ya shige sashinta wanda ya same ta da uban tulin kaya a gabanta tana gyarawa ta a za saka a cikin mota a kai gidan
Ajmal saura ne wanda ba a kai ba.


"Hajiya Baaba, mahaifin yaron nan ne ya ƙara zuwa a karo na biy.."


"Kai dakata! Da hankalinka kake ƙoƙarin neman aure cikin aure? Ni ban ga wani abin damuwa don ya rasa Jannah ba, saboda ban taɓa ganin ubanka sai ranar da aka kai ni ɗakina, kuma muka yi zamanmu lafiya lau, har da ya mutu sai da na yi kwanaki ban dawo hayyacina ba, amma su da yake yaran ƙarshen zamani ne wai sun iya soyayya har yake shirin kashe kansa. To kace masa ya mutu kansa don ba ni za a turmuƙa a rami ba." Ta ce tare da cigaba da aikinta.


Ganin ba ta da ninyar zuwa ya shigo da shi har cikin sashin na ta wanda tana ganinsa ta ci magani ta ci gaba da aikinta ba tare da ta kalle shi ba.


"Barka Hajiya, m..."


"Kai dakata! Yi waje ka ba ni guri domin babu kalmar da za ka yi amfani da ita na sa a fasa auren nan, kuma kun san ai haramunne neman aure cikin auren, amma saboda mugun son zuciyarka kake son a fasa don a bawa ɗanka da yake gwal ne."


Jannah da take kwance tana kuka cikin bargo haƙoranta na karkarwa don ta bata da gaske auren za a yi mata. Tun ranar da aka yi danki ta kwanta ciwo take kuka da shuka rashin mutunci da ihu amma a banza don tana fanin ba duka ta rufe ta da shi ba babu yadda za a yi ta fasa auren


Jin an ambaci mahaifin Huzaifah ya sa ta diro daga gadon daga gadon da take kwance wanda Ummu ke gefenta har hawaye ta yi mata akan ta tashi tasha ko ruwan tea, amma ta ƙi.


Ganinta kawai suka yi a gabansu cikin kuka ta kalli mahaifinsa ta ce,"Dad, where is Huzaifah? I miss him. Don Allah ka gaya masa ya zo gare ni domin zuciyata ba za ta iya ɗaukar girman rashinsa ba."


"Munafuka dama lafiyarki lau, kike ma mutane iskanci ki kwanta kina numfarfashi, amma yanzu daga ambaton Huzaifah kin sheƙo da gudu kina gudu bamfaleƙe."Cewar Hajiya wanda ba ta bi ta kanta ba.




"Ta shi ki wuce ciki domin yanzu ke matar wani ne." Ta ce tare da kamata wanda ta fisge ta kama ƙafafun mahaifinsa da ya fara tafiya domin ya sare ba za ta amince ba ɓata bakinsa kawai yake.




"Don Allah karka tafi ka gayawa Huzaifah ya buɗe wayarsa zan kira shi mu gudu muje can mu yi aure." Ta ƙara faɗi cikin kuka.


"Au ki gudu ki ban ni da jin kunya ko kina ganin an fara zuwa bikin, to in kika ga kin leƙa waje sai kin gudun wawiya kawai." Ta ce tare da kamata ta riƙe tamau ta shigar da ita ciki wanda ta yi ƙoaƙrin ƙwacewa amma ta kasa.


"Haba 'yannan, to ko mahaifinki na riƙe ai bai isa ya ƙwace ba." Ta ce tara da kaita har cikin ɗakinta ta rufe ƙofa.


"Ummu!Ummu!! Shikenan, Hajiya Baaba, ta raba ni da masoyina Huzaifah na shiga uku!" Ta ce tare da ƙara rushewa da kuka ta faɗa jikinta.


Huzaifah kwance a tanƙamemen falon su yana riƙe da wayarsa da dad ɗinsa ya karma tun ranar da suka je gidan su Jannah.


Har yau zuciyarsa ba ta daina tunanin wulaƙancin da Hajiya Baaba ta yi musu ba, wanda ya cika da mamaki ya gasganta kura ce da fatar akuya.


"My son, the you mean you will keep thinking about her? Ka na son na rasa ka ne? Ka san cewa ba zan iya rayuwa in har babu kai ba." Mom ɗinsa tace cikin muryar kuka tana share hawaye.




"I love her mom, I really love her like crazy. Tun ranar da muka haɗu a filin jirgi na ji a raina da ita kawai zan iya rayuwa. Ita ɗin tamkar maganaɗisu ce a cikin rayuwata, don Allah ku taimaka ku ba ni ita karku sanya zuciyata ta buga."


Sai ya riƙe hannun dad ɗinsa yana dannawa a kan ƙirjin shi da ke harbawa fat! Fat!! wanda har sai da mahaifinsa ya cire da sauri saboda irin ƙarfin harbawar da take yi.


"Ka ji ko dad, harbawar da zuciyata take yi ƙara mini sonta take a cikin zuciyata wanda in har ban same ta ba zan iya mutuwa. I have to give you my will cus I'm gonna die, I can't make it without her." Kamar ƙaramin yaro ya saka kuka tare da rungume mahaifinsa da yake kallonsa cikin tausaya.


"Ya kamata mu koma gidansu Jannah mu ƙara roƙonta saboda in har ɗana ya mutu na rantse sai na yi shari'a da ita." Cewar mom da take zubar hawaye domin ba ta taɓa ganin abin da ya ƙwallafa ransa akai har ya kaishi zubar da hawaye da kwanciya ciwo.


"Na nawa saboda, I went to Zariya jiya, amma in vein don ya rage one weeks aurenta da shi."


"What!" Ya ce tare da miƙewa tamkar zai zura.


"No, it can't be her. Jannah ba za ta bari ayi mata aure ba da ni ba." Ya ƙara faɗi cikin zautuwa sai kuma ya sa kuka ya koma ya kwanta yana suratai kamar ya zare.


"Innalillahi! Suma yake yi fa kar ya mutu." Cewar mom ganin idanunsa na ƙyafƙyaftawa.


Da sauri dad ya kama shi ya rungume yana kiran sunansa.


"Jannnahh." Ya ja sunan tare da yi masa wasali da gunna sai kuma ya yi shiru can ya buɗe idanu ya fara tari sai aman jini, wanda ya ɗaga hankalin iyayensa suka sa ihu tare da kiran direba.


Dad ya taitaye shi ya sanya a mota yana girgiza shi da kiran sunan shi amma ina sai aman jini yake yi.


A lokacin da suka isa asibitin da ƙyar likitoci suka yi nasarar dawo da shi cikin hayyacinsa ya daina aman jinin, amma bai daina kiran sunan Jannah ba.


Doctor ɗin ya fito yana share zufar goshinsa wanda yana buɗe ƙofa suka yi kansa.


"How is he likita? Ya farfaɗo ya jikinsa." Suka tambaya cikin tsananin tashin hankali.


"Please, do whatever you can to make him to have yarinyar da yake faɗi." Cewar likitan yana kallonsu.


"Ba zai iya samunta ba saboda kwana biyu ya rage a ɗaura mata aure doctor, da ace kuɗi na amfani da zan yi na samar mishi yarinyar, amma iyayenta ba sa buƙatar kuɗi, saboda suna da su." Ya ƙarashe maganar cikin rauni yana share zufar goshinsa.


"Mafitar ceton rayuwarsa shine a samar masa da abin da yake so."


"Hakan ba zai yiwu ba doc na gaya mata babu yadda za a yi na shawo kan iyayenta."


"Innalillahi! Yanzu rasa shi zan yi kenan? Don Allah likita ka yi wani abu wallahi shine kawai ɗa namiji da Allah ya ba ni."


"To ku yi masa viser ya bar Ƙasar nan, zan haɗa ku da wani doc a India yana da sani sosai akan zuciya in sha Allah zai samu sauƙi saboda ya kamu da ciwon zuciya gab take da ta buga."


"Innalilahi!"Suka furta a tare suna hawaye.


"Ok, I will give me the doctor's numba." Dad ya ce a firgice tare da ɗaukar wayarsa ya kira akan a fara nema masa viser na su duka ukun.


Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi viser suka nufin India ba tare da ɓata lokaci ba.


A lokacin da suka isa Ƙasar India hankalinsu ya tashi kwatankwacin tashin gwauron zabi! Don babu numfashi suka isa da shi, wanda jinin su ya yi sanyi tamkar ƙarƙarar dake cikin firij.


Suna kallon shi ta gilashin ɗakin an sanya masa oxygen yana kwance shememe kamar gawa sai cikinsa da yake ɗan motsi alamun akwai numfashi a jikinshi.


"Ke kam wannan tsohuwa sam ba ki yi man adalci ba sai Allah ya sakawa waɗannan yara saboda son zuciyarki ki nemi ki kashe mini ɗana ɗaya tal da na mallaka." Ta ce cikin matsanancin kuka tana jin kamar ta ɗauki bindiga ta harbe ta har lahira.


A ranar da mom ta shirya za ta taho sai aka kira ta kan wata mata ta haihu 'ya'ya biyu babu jini babu abincin da za ta ci ballantana kayan da za a sanya wa jariran ga shi mijin ya mutu."


"Innalillahi! Kai maza anya wasu suna tausawa mata kuwa? Dole na zo na taimaka mata ina ganin ke Hajiya Turai, ki je garin nan da za ku je ni da Mujee, sai muje cikin shiri daga nan mu wuce Zariya, kin ce sai jibi za ku zo ko?"


"Eh, kon san dole na jira baƙinan mu taho."


"Ok tom shikenan, don Allah ki karɓo mini kayan mata na SURAIYA D kin san ba kowa ne maganin mata nake iya siye ba, amma sai nata saboda yana da inganci kuma akwai aiki sosai."


"Haka ne km SURAIYA D kayan matan ta ingantattu ne, ko ni bana iya amfani da ko wanne sai na ta. Ki ce wannan ango babu ragi tsakaninsu domin Uwa ba da mama kusan na dubu ɗari biyu kika siya."


"Eh, so nake ta kama mini shi a hannu kamar yadda na riƙe mijina, sannan surukin nawa tsadadde ne mai aji da ilmin addini, wanda ya san haƙƙin aure da sanin darajar mace, kin ga dole na yi mata gyara."


"Allah Sarki! Aiko na tausaya masa domin ya zo hannu don kayan mata na SIRAYYA D ka yi amfani da kaɗan ya ka ƙare ina ga kuma an sha da yawa."


Mai buƙar kayan matan SURAYYA D *Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*




"Eh, haka nake so 'yata ta zamo zinariya a gidan aurenta kamar yadda na zamo, don Allah ki dafa duk sauyoyin nan in za ki zo."


"Yauwa na manta na ce zan gaya miki waɗannan magungunan ki fara mata kamar haka:

Kyaran jiki
Ki samu kokumba ki yi blending a tace a sai ki shafa a jikinki. Sau biyu ya kamata a yi, kin ga ko bayan auren sai ta ci gaba.


Maganin warin jiki:
Kanumfari lalli a haɗa a jiƙa a shafa a gaba.


Siddir
A ije mata siddir a gidanta ya fi ƙarfin aljanu.




Haɗin ayaba:
Ki sayi ayaba ki ɓare ayi blending 7-or 10 ya niƙu sai ki zuba milk the quantity you want then sai ki sugar ki aje a frij in ya yi aanyi kisha.


Sannan ki sanya ta kullum bayan asubahi ta rinƙa karanta YA WADUDU ƙafa ɗari hudu yana saka soyayya tsakanin masoya da kawo buɗi. Bari dai na barki da waɗannna in sha Allahu in zan taho zan dubo masu yawa harda addu'oin sace zuciyar miji da zaman lafiya."




Ajiyar zuciya mom ta yi mai ƙarfi a ranta tana tunanin yadda za ta iya tunkararta da magungunan.


"Na gode sosai Allah ya bar zumunci."


"Ba ki da matsala, sai mun zo ki gaishe mini da Hajiya Baaba uwar biki."


"In sha Allahu." Ta ce tare da kashe wayarta sannan suka shirya suka kama hanyar ƙauyen.


Jannah ta ci kuka har ta bawa uku lada tamkar za ta shiɗe duk ta rame ta fita hayyacinta.


Sosai Aby ya tausaya mata sai dai ba shi da abin da zai yi mata sai addu'a.


Dad kan dole ya shiryo ana saura kwana biyu biki ya kamo hanya don rarrashi jin taƙi ci ta ƙi sha.
Hankalinsa ya tashi ganin yadda ta koma wanda har sai da ya zargi kansa.


Ganinsa ta faɗa jikinsa ta yi kuka ta yi kuka tamkar za ta shiɗe wanda ya tausaya mata har sai da ya yi ƙwalla, domin tsananin tsanarsa da take yi ya bayyana a idanunsa.


Saboda tsabar kuka ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take wanda yake barazanar tafiya da numfashi








Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093














KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)



















Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 36-37*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login