Showing 36001 words to 39000 words out of 137802 words

Chapter 13 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K










KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 10-11*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ita kanta Hajiya Baaba ba'a barta a baya ba, gurin shirya masa tuwon shinkafa da miyar ganye har da dabbu masu rai da lafiya sanin cewar yana so. Jannah dake falonta tana kallon Arewa24 wani lokacin kuma tama danna wayarta. Juyo wa ta yi ta kalli Hajiya da take ta safa da marwa a kicin ɗin.
Miƙewa ta yi tabi bayanta ta shiga kicin ɗin tana hamma. "Hajiya ina Binta ta dafa mini indomie yunwa na ke ji." Hararta ta yi ta ci gaba da aikinta kamar ba ta ji me ta ce ba, don tun safe take cike da ita sakamakon ba ta tashi ta yi sallah ba sai bakwai da minti arba'in.
Jin ta yi shiru ya sa ta cika sai ta ɗaga murya cikin ɓacin rai. "Kina jina fa Hajiy.."
"Ke kin san Allah yanzu zan ƙwaƙƙwala miki ludayin miyar nan a kanki. Na ga mace kike da hannayenki? Don haka ki girka da kanki, ko ki ibi abincin da na yi wa Adamuu."
Dariya ta mai shewa jin abin da ta ce. "Ni kamata na yi girki, amma dai wasa kike mini ko? Da kika ce na ci wannan kwacamalar ta ki." Ta ƙarashe cikin tsigar mamaki.
Hannun rigarta ta fara naɗe wa kamar za ta yi dabbe. Ganin haka ya sa ta fara dariya tana matsawa.
"Na lura kamar 'yar dabbe kike wallahi, bari na kama kaina kafin ki sa mini wannan hannun na ki mai kama da icce. "
Hararta ta ƙara tare da ɗaukar muciya za ta tuƙa tuwon. "Da kin tsaya ki ga yadda zan yi miki fitsararriya kawai."
Wayarta ta ɗauka tana faɗin, "Wa ni? Ai kin fi ƙarfina 'yar dirama. Allah ya kyauta na ci abincin nan, na lura Ya Ajmal mugun bagidaje ne. Ya yi ta wani iyayi, amma ya je ƙasar waje sai ya ci local food taɓ!"
Hajiya Baaba ta ci gaba da tuƙin tuwanta aranta tana matuƙar jin haushinta domin da ba'a ce tana sonta ba, sai ruwa ya gagareta sha a gidannan domin halayarta sam babu wanda ya yi mata.
Sashin Ammy ta shige. Kai tsaye kicin ta nufa inda take jin kamshin cake da ake baking ya cika mata hanci har sai da ta shaƙa tare da lumshe ido.
"Wow! My Anty. The best cooker in the world. Please can I have a bite?" Ta ce tare da ƙarasawa kicin ɗin ta kai hannu ta ɗauki cake ɗin ta sanya a bakinta tana taunawa tare da lumshe ido.
Dariya ta yi cikin jin daɗin abin da ta ce. Tan ajuya kwaɓin cake ɗin ta juyo ta kalle ta.
"Kwaɗayayya, bayan wanda kika ci." Ƙara kai hannu ta yi sai ta ɗauke tana faɗin,
"A nan kika fi auki, ba ki iya komai ba sai kwaɗayi."
Ɓata fuska ta yi. " Haba duk yabon da na yi miki? Don Allah ki zuba mini yunwa na ke ji.
Yau kin ƙi yin girki da wuri. I beg you." Miƙa mata robar ta yi tana buɗe oven ɗin ganin alamun ya gasu.
" Na bari sai na gama aikina yau girkin dare kawai zan yi. "
Allah ya sa kiyi aure a kusa na rinƙa zuwa gidanki" Ta bata amsar tambayarta.
Ta ce tare da zama akan stool da yake kicin ɗin. "Huhm! You are indeed amazing cooker. I can give you award for that. Gaskiya ya yi daɗi ba kaɗan ba."
"Gaskiya ina son ga na iya all intercontinental dishes sosai. Kiyi dedicating time na koya miki."
"Humh!" Ta ce tare da kauda zan can ta hanyar cewa, "Wai Anty, duk wannan girkin is for Ya Ajmal? Hajiya ma fa na ga har kusan kala biyu ta yi mishi. Shi kam wane irin ci ne da shi." Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ke dai kin sama Yaya ido."
"A,a ba zan zancen haka ba ne, am just jealous don na ga ko lokacin da na zo ba ki tarbe ni haka ba."
Dariya sosai ta yi jin abin da ta ce. "Kar dai ki juya zancen don na yi miki maganar koyon girki. Ya Ajmal mutum ne mai son abinci kala-kala, wannan dalilin ya sanya budurwarsa da zai aura sai da ya sanya ta koyon girki. Tana cikin matan da sunan su ya shahara a yanar gizo suke koya girki, don ya hana saka hotonta da kin santa."
"A lailai good for him. Na kosa a yi auren mun rinƙa zuwa kwasar girki ko da na lura sam ba shi da kirki, kullum fuska a ɗaure yana mazurai." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar cinyar kaza ta nufi falo da sauri don kar ta yi mata tsiya. Dariya ta yi ta girgiza kanta ta ci gaba da aikinta.
Misalin shidda na yamma jirginsu ya sauka a Nigeria. Ayaan ya ɗauko shi daga filin jirgi sai da ya yi baccin gajiya bayan sallar magariba ya shiga sashin Hajiya wacce ta idar da sallah jin sallamarsa yasa ta shafa addu'ar da take yi. Cikin jin daɗi ta juya tana kallonsa.
"A maraba da baƙon turai." Zama ya yi kusa da ita yana gaishe ta.
Fura kawai ya sha ya miƙe. "Hajiya Baaba, bari na shiga na gaida su Ammy, aka wo mini tuwon sai anjima zan ci." Fuska ta canza jin abin da ya ce.
" Kar ka damu zan ɗumama na ci abincina, Allah ya ƙara mini na dage na yi girki, bayan na san da wuya a barka ka ci."
Bai ce mata komai ba ya kam hanyar ficewa. "Sai da safe." Ita ma miƙewa ta yi sannan ta kalle shi rai a ɓace.
"Ina tsarabar Jannatuu? Na ga nawa ne kawai." Shi kam har ga Allh ya manta da wata aba wai jannah domin tun da ya tafi kansa ya yi zafi.
"Wace kenan?" Tsaki ta yi jin abin da ya ce don ta ɗauka rainin wayonsa ne ya tashi.
"Ban sani ba, 'yar babin roba ce da na siyo na ke wasa da ita bayan tafiyarka. In har za ka manta da ita, ai za ka manta da kanka tun da a gidan nan kowa da bazar uwarta yake taka rawa."
Ransa ne ya ɓace take jin abin da ta ce amma sai danne don baya son ya saka ma kansa damuwa daga dawowarsa. "Oh! Na gane.
Mantawa na yi. Da safe sai na haɗa su duka na ba su."
" Da dai yafi." Ta ce tare da shigewa ɗakinta ta bar shi tsaye yana mamakin rayuwarta.
Falon Ammy ya nufa ya same su dukan su a falon har da Jannah da tafi zama acan sai dai jn tsiyar Hajiya ya tashi sai ta zo ta wartake ta, amma ba shi zai hana ta dawowa ba.
Zama ya yi yana kallon Ammy da farin cikin ya bayyana a fuskarta sosai.
" How was the journey?" Abby ya ce bayan ya amsa gaisuwar da ya yi masa.
"Great!" Ya ba shi amsa. "
Sannu da dawowa ya Ajmal." Suka haɗa baki gurin faɗi har da Janaah da ta bi ayarin gurin yin motsi da bakinta.
Ɗaga kansa kawai ya yi yana murmushi. "Ke Nahlin suko masa da abincin ya ci a ƙasa, zai fi masa sauƙi." Cewar Ammy wanda ya sa ta miƙe da zamarta don ta ɗauko. A maimakon ta taimaka mata sai ta yi zamanta tana ta kallonta a wayarta wanda yansa ya yi mata mugun kallo bai ce komai ba.
Abincin kaɗan ya ci ya miƙe."Ammy bari na je, ina son zan fita zuwa ten zan dawo."
Dariya ta yi." Surukar tawa ta yi kira kenan?" Shafa saman kanshi ya yi cikin jin kunya.
"A'a, ni ne na yanke shawarar na je yau, don gobe Abuja zan wuce kuma sai na yi kwana biyu." Ta kalle shi daidai lokacin da ya murɗa ƙofar fita.
"To shikenan, a dawo lafiya. My regards to her." Kaɗa kansa ya yi ya fice yana taya Abby dariyar abin da Ammy ta ce da yake tsokanarta ba ta da kunya.
Jannah duk sai ta ji wani irin babu daɗi ganin yadda ahalin suke farinciki, da yadda suka ɗauke shi kamar wani waliyinsu. Ga shegen girman kai da nuna isa ko ita da mahaifiyarta take damawa ba ta nuna hakan.
Fafffaɗan ƙirjin shi ke ba ta haushi sosai domin sam ba ta ƙaunar namiji mai wannan surar, wannnan na ɗaya daga cikin abin da ya sa take son Huzaifah domin komai na sa daidai ya yi mata. Gemun shi irin na gayu ya aje ba kamar shi ba da ya tara da babu laifi, wai shi sunnah.
Ɗakinsa ya wuce ya sheƙa wanka tare da saka shadda ash colour ya fashe jikinsa da turare ya shiga cikin mota ya fice.
A lokacin da ya isa ƙofar gidansu Mushiirat ya ɗauki wayarsa ya kirata wanda bugu ɗaya ta ɗauka.
"Hello, I'm outside you house?" Ya kashe wayar daidai lokacin da take faɗin,
"Oh bab stop teasing me." Dariya ya yi yan kaɗa kafarsa da ma suprised ya so yi mata don tun ana gobe zai dawo take roƙon sa akan ya zo gidansu a ranar da dawo.
Ko minti biyu cikakke ba'a yi ba sai gashi ta fito da dogon hijabinta har ƙasa da carbi a hannunta. Ganin motarsa ya sa ta saki murmushi cikin tsigar jan hankali.
"Oh my God! Bab, you surprised me." Sai ta koma cikin gidan tare da buɗe masa get ba tare da ta jira direba ba.
Da sauri ta isa gare shi daidai lokacin da yake ƙoƙarin buɗe ƙofar motar. Hannunta ta kai ta riga shi buɗewa.
"You are welcome Sadaukina. Allah na yi mamakin zuwanka har na fara shirin bacci da na idar da hadda." Sai ya haɗe hannunsa ya ɗora a kirjinsa.
"Good girl, ina fatan kin gama wanda na ba ki ko." Ta kashe masa idanu tare da kara matsawa kusa da shi.
"Na gaya maka umurni ne kawai naka, cikawa kuma nawa. Har na gama na ƙara ma kaina."
Hannunsa ya tafa jin abin da ta ce."Wow! You did great my angel. Ma za muje ki na karɓa duk da dare ya yi, ba daɗewa zan yi ba."
A hankali ta raɗa masa."Don Allah ka tafi a hankali, ka san ka dawo duk ka gaji bana son ka wahalar mini da kanka."
Murushin jin daɗi ya yi sosai, wannan dalilin yasa yake matuƙar sonta. Mace ce wacce ta iya san duk wani techniques and procedures na iya jan hankalinsa. Da ma tuni tsarin rayuwarsa baya son ƙaramar yarinya, yafi son mace mai shekaru wacce sai dai ta kula da shi, ba ya yi rainonta. Mushiirat nurse ce a asibitin Shika.
Ƙofar falon mahaifinta ta buɗe masa tare yane labulen falon ya shiga.
"Ka ga yadda Ƙasar ta karɓe ka? Ka yi kyau da fresh."
Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar ƙamshin turarensa da yake tafiya da imaninta a dul lokacin da ta shaƙe sa.
Zama ya yi yana kallonta daidai lokacin da ta ce masa."Ina zuwa." Ta shige sashinsu. Jim kaɗan ta dawo.
"Yaya, ban san za ka zo ba ai da na yi maka snaks kala-kala. Wannan na bikin 'yar Alhaji Bello da na yi ne."
"Good shi ya sa nake ƙara sonki sosai, you re not liability." Murmushin jin daɗi ta yi har sai da haƙuronta suka bayyana.
Ya ɗauki samosa ya kai bakinsa tare da taunawa yana mata wani irin kallo."Is testy. Da gaske ya yi daɗi sosai fa! Anya in na aure ki zan iya cin abinci a waje. Gaskiya I salute you interms of cooking."
"Relly.?" Ta ce masa sai ya ɗaga kansa tare da kashe mata ido, wanda hakan ya ba ta kunya ta yi dariya ta yi tare da sanya hijabinta ta rufe fuskarta.
Sun sha hira duk da cewar ba ta yi tsawo ba ya karɓi haddar sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bayan ya isa gida ya kira ta ya sanar mata da ya isa sannan ya kashe wayar bayan sun yi sallama.


LONDON
Mom zaune a gaban dressing mirrow tana gyara hodar fuskarta. Wayarta ta ɗauka da ke neman agaji ta kanga a kunninta.
"Hello James, have you done with the article?"
"Almost ma'am." Ya ba ta amsa.


Kashe wayar ta yi ta ci gaba da gyara fuskarta da soson hodar. Bayan ta gama ta ɗauki jakarta tana ƙoƙarin fita dad ya shigo fuskarsa a ɗaure da wayarsa a hannunsa.
"Is that real about the rumors Halee?" Ya faɗa cikin tsananin fushi yana nuna mata labaren da yake karantawa ɗauke da hotont ɓaro-ɓaro.
Ba tare da tsoro ko fargaba ba ta kalle shi cikin ɗaurewar fuska za ta fice ta ce,
"Yes it is." Tare da kama hanyar fita cikin takun isa.
Da sauri ya juyo da ita yana zare mata ido."Look Halima, what do you take me for? A ce ina matsayin mijinki za ka shiga politics without my awareness?"
Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya ba tare da ya bari ta furta komai ba ya ɗora da cewa,
"Babu yadda ban yi ba dake akan mu koma Nigeria saboda 'yarmu and you didn't, now you wanna go back because of politics?"
"By the look on your face you are surprised ko?" Ta ce masa cikin gadara.
"Na gaji da wulaƙancin da kike mini, kin maida ni kamar yaron gidanki, kullum ba ni wannan ƙasa duk a dalilin hidimarki, kuma ban isa na juya ki ba. Gabaki ɗaya na zama mijin-ta-ce."
"Eh, haka ya kamata na yi kuma nake son rayuwa. Mene ne ba ka sani ba game da ni? Har kana da bakin da za ka iya mini magana akan tsarin rayuwa?"
Ta ɗaga murya fiye da ta sa sannan ta ci gaba da cewa,"Ba ni da ra'ayin shiga politics, amma suka ɗora ni saboda ganin na cancanta, don haka I don't have any options than to be Minister."
Ganin yadda lokaci guda ta canza sai ya sausauta murya domin shi kansa ya yarda mijin-ta-ce ne a gareta.
"You wouldn't understand Halee, ke mace ce. Mutanen nan, they are user they will only use you and dumb you. You shouldn't have accepted it. You better think logically and make the right decision."
Wani banzan kallo ta yi mishi na rainin wayo." Na yi addu'a kuma na yi istihara kan lamarin Allah na ke roko, na san zai kare ni. Amfani da ni na nawa? Mutane nawa na aminta da su suka ha'ince ni, sai wannan dalilin ya sanya na ƙi yiwa Ƙasata hidama. Allah shi zai kare ni, domin yanzu zamanin nan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login