Showing 84001 words to 87000 words out of 137802 words
Chapter 29 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
mata ƙorafi akan rashin kula da cikinsa ko haƙƙinsa da tsafta ba. Sosai take dagewa gurin faranta masa rai, wanda yake ganin bai kamata ace mar'atussaliha kamarta za a yi mata kishiya ba.
A hankali ya fara karatun cikin muryarsa mai daɗin gaske. Mushiirat sai ta ji ta kasa cigaba da karatun domin muryarsa ta tafi da tunaninta da duk wata natsuwa ta shi. A kullum tana godewa Allah Ubangiji da ya ba ta shi a matsayin miji, domin shi ɗin mijine na nuna wa tsara wanda ya iya tattalin mace da ba ta duk wata kula da take buƙata. Babu abin da yafi burgeta a gareshi yadda yake da addini da kamun kai, komai na shi cikin tsari da natsuwa da koyi da Annabi. A kullum burinta Allah ya ba su 'ya'ya masu albarka wanda za su tashi cikin koyi da ɗabi'un mahaifinsu.
Ganin ta yi nisa cikin tunani ya sanya shi rufe ku'anin bayan ya yi addu'ar, gama karatun yayin da ya ji dama da sauƙi a zuciyarsa ya ƙarasa gabanta wanda ba ta san ya iso ba.
Saukar kiss ta ji a fuskarta wanda ya sa ta saki ajiyar zuciya tana kallon shi.
"Am sorry." Ya furta cikin jan hankalinta da wata irin murya.
Sai kawai ta tsinci kanta da fashe masa da kuka ta faɗa jikinsa."Please, na roƙe ka da karka rinƙa ɓoye mini abin da ke damunka zauji, in ba haka ba za ka yi sanadin rasa n.."
"Shiiiiit!"Ya ce tare da saka ɗan yatsarsa ya toshe mata baki.
"Waya gaya miki zan iya rayuwa in babu ke? Har yanzu ba ki yadda da ce miki da na yi kece mace ɗaya wacce na ke jin zan iya rayuwar aure dake ba? Kina girmama ni sam bakya mini rashin kunya sannan mace ce ke wacce ta ma sunanta ta kuma isa ta ɗauke hankalin ko wane ɗa namiji."
Murmushi ta yi tare da faɗawa jikinsa tana sunne kai. Kiss ta kai mishi a bakinsa ta ce,"Ina matuƙar son ka ya Sheshk!"Ta kira shi da sunan da in har ta kira za ta gaya mishi abu maimahimmanci ne.
Ƙara rungumeta ya yi yana faɗin,"Ni ma haka rayuwata." Sai ta ji wani matuƙar sanyi ya lulluɓeta lokaci guda ta manta komai suka shiga faranta ran junansu.
Bayan ya dawo daga sallar isha a masallacin gidansa tana falo cikin riga da siket da ya kamata sosai tana jera masa abinci a dining ya shigo.
Da sauri ya ƙarasa gurinta ya karɓi filet ɗin ya zuba abincin, tare da zaunar da ita kan kujera y gama gyara dining ɗin sannan ya zuba musu abincin ya fara ba ta a baki.
Sai kallonsa take yi lokacin da yake bata labarin abin fa ya faru a tafiyarsu da nasarar da suka samo. Tuni ya manta da komai domin zuciyarsa ta gaya masa wasa take yi, don haka bai yi ƙasa a gwuiwa gurin watsar da komai ya ci gaba da tarairayar matarsa da ya yi mising ɗinta mara misaltuwa.
Washegari da safe bayan Aby ya dawo daga masallaci ya shiga ɗakin Hajiya Baaba don ya gaishe sa. Tana zaune a cikin ɗakinta tana jan carbin da sai gyangyaɗi take yi.
Jin muryarsa ya sa ta daina gyangyaɗin tare da gyara zama tana kallonsa.
Har suka gama gaisawa zai miƙe ba ta ji ya yi maganar jiya ba, wanda ya sa har ya miƙe ta ce,
"Dawo ka zauna ina son magana da kai."
Gabansa ya faɗi a ransa yana addu'ar Allah ya sa ba zancan jiya za ta yi masa ba, amma sai addu'arsa ba ta karɓu ba domin tun kafin ya gama zama ta fara masa maganar.
"Na ɗauka yanzu za mu yi maganar auren da shirye-shirye, ka san lokaci fa ba ya jira. Ko so kake sai Halimatuu ta dawo sai ayi maganar? Ka ji na rantse maka tun da na faɗa auren babu fashi. Karka manta a lokacin da za ka yi aure ka mini alƙawarin daga wannan lokacin ba za ka taɓa saɓa mini ba."
"Eh Hajiya, don Allah ki daina tuna baya ai ba na ƙi auren bane, ina dai hangen abin da zai je ya dawo ne."
"Babu abin da zai dawo sai lkhairi. Ɗanka za ka ja ma kunne karya sake ya bugar mini ita, don ba zan lamunta ba."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 23-24*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Allah ya kyauta! Hakan ma ba zai faru ba, saboda yana da sani ba zai tasa matarsa da duka ba."
"Oho, jan kunne dai domin rigakafi yafi magani."
Zama ya ƙara yi cikin murya mai sanyi ya ce,"Don Allah Hajiya Na ji na amince ayi auren, amma ki bari matarsa ta ɗan ko haihu ɗaya ne, ita kuma Jannah ta yi zurfi a karatunta, kin ga kafin lokacin ma ta ƙara hankali tun da duka guda nawa take."
"A summa take ko ba a haife ta ba. Lokacin da na auri ubanka ko irgan dangi ban yi ba, kuma amma haka na rinƙa zaro ku sai da na yi takwas don dai ba su tsaya bane."
Ta ja numfashi tana kallonsa ko zai ce wani abu amma sai ta ji ya yi shiru cikin jimami don haka ta ci gaba da cewa,
"Kuma da kake cewa matarsa ta mutu in ta so, ai dama shi mijin mace huɗu ne ko alƙawarin ba zai yi mata kishiya ya yi ba. In an yi auren ta gungure ta faɗi ta mutu don kishi."
"To shikenan, za a yi duk bin da kike so Allah ya sa mu ƙulla alkhairi." Ya miƙe jiki a sanyaye tamkar kazar ƙwai ya fashe mata a ciki zai fice.
"Khairan zan ƙulla in sha Allahu duk wannan iskancin za su gaji su zauna dole, don rabuwarsu sai dai in bana raye." Ta ci gaba da jan carbinta tana gyangyaɗi.
"Wayyo Alllah na gode maka! Yau addu'ata ta karɓu Halimatuu za ta dawo gida. Allah na gode maka da ka bani tsawon lokaci na ga wannan lokacin. Ta furta daidai lokacin da ta kashe wayarta da suka gama magana wanda ta sanar mata.
"Dole na kira malamai su yi saukar Kur'ani da addu'oi akan Allah ya tsareta da mugun gani da ji." Ta ce tare da ɗaukar wayar tana neman numbar Aby.
Jannah da Ummu suka yi sallama suka shigo cikin yanayin na matuƙar gajiya, kasancewar da ga makaranta suke. Turus suka ja suka tsaya ganinta tana rawa a tare suka kalli juna sai suka ɗauke kai.
Wucewa ta yi ta zauna ba ta ce mata komai ba, domin tun da ta yi maganar auren ta da Ajmal ta ɗauke mata wuta suke zaman kurame wanda ko a tsummar gyalen Hajiya Baaba.
Ummu kuwa gabanta ya shiga dukan tara-tara tsoronta kar a kan maganar auren ne take rawa, domin ta san ba banza ba za ta rinƙa tiƙa rawa haka. Gabaki ɗaya sai ta ji ranta ya ɓace, yunwar da ta shigo da ita ta neme ta ta rasa, domin ta tsani maganar auren. Gani take tamkar takurawa rayuwar Jannah za ta yi, gara Ajmal yana da wata matar.
Kallon su ta yi ta watsar sai kuma ta fara magana bayan Aby ya ɗauki kiran da take masa.
"Kuna ina ne Muhammadu? Da gaske kake yanzu Halimatuu na gabanka a Nigeria? Oh Allah mahaƙurci mawadaci."
A tare suka kalli juna mamaki ya kamata ta jin har ta iso Nigeria, amma dad bai sanar mata da yau za su zo ba, duk da cewa ta san ta yi hakanne don su yi suprising ɗinta.
Ummu ta sa ihu da tsallen murna duk da cewar ba ta waye ta sosai ba, amma dole ta yi murna domin tsaƙonta yana tafe garesu ko da yaushe, don haka ya rungume ta cikin matuƙar farinciki.
"Wow, I can't wait to see mom." Ta ce cikin matuƙar ɗoki.
Tureta ta yi da ga jikinta fuskarta sake tamkar gonar adduga.
"Hello dad, is it true that you have came back to Nigeria?"Ta yi masa tambayar cikin zaƙuwa.
"Oh yes my baby, I wanna suprised you. Did I?" Ya ƙarasa maganar cikin tsigar tambaya.
"Yes you did, I can't wait to see you. Ko muzo mu ɗauko ku?"
"A,a kar ki damu yanzu haka muna Jaji mun kusa dawowa Aby ya ɗauko mu."
Wani irin ihu ta saki ba tare da ta kashe wayar ba tana juyi da Ummu.
"Wallahi am not longer hungry my dad on his way. Allah na gode maka zan huta da fitina." Ta ƙara rungume ta sai kuma ta sake ta tana faɗin," Bari na yi wanka ki raka ni na sayo masa suprised.
Saboda tsabar ɓacin rai Hajiya Baaba ta kasa magana sai kallonta take cikin tsananin damuwa.
"Anya kina son ki gama da duniya lafiya kuwa, kin san haƙƙin uwa a kanki kuwa? A ce mahaifiyarki ta yi tafiya zuwa wata uwa bangon duniya, amma ba kya murnar dawowarta sai mahaifinki, bayan sai da Allah ya ambaci uwa sau uku. Kai gaskiya dole Halima ta tashi tsaye domin Jabiru ya gama da 'yarta."
Tsaki ta yi jin abin da ta ce har ta kama hannu Ummu za su shiga ciki sai kuma ta dawo ta fara magana.
"Eh shi kawai na damu da shi saboda na san saboda ni ya dawo, ita kuwa 'yarki siyasa ya dawo da ita ba don ni ba, domin a lokacin da nake tsananin buƙatar mu taho tare ba ta dawo ba, don haka babu ruwana da ita."
"Dallah can tafi wawiya kawai! Ni na ga wanda take son mahaifinta ta ƙyale uwa. Ina ga duk yadda aka yi akwai tanbotsai akan ki, amma ba haka kike banza ba."
"Zo muje kin ji na siyo mishi kar su dawo." Ta ja hannun Ummu suka fice daga falon ba tare da ta ba ta amsa ba.
"Ki fi ruwa gudu ai ni ina murnar dawowarta ɗiyar albarka jinin arziki." Ta ce cikin jin haushinta sai kuma ta ɗora da ce wa,
"Kai godiya ga Ubangiji Sarki mai yawa. Ba ri na tashi na je na yi musu girki kafin su dawo, Allah ya so jiya naje kasuwa." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa.
Sannu a hankali take takowa daga matakalen benen, cikin wani irin yanayin da ba za ka iya tantance farin ciki ko akasin haka take ba. Idanunta suka kawo ruwa daidai lokacin da ta sauko daga matakalen benen, tana shaƙar ƙamshin Ƙasarta wanda ta yi kewarta matuƙa.
"Please Halee, don Allah ki manta komai.Na yi miki alƙawarin zama miji adali da kawo farinciki har ƙarshen rayuwarki." Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya tare da kama hannunta na hagu ya riƙe.
A hankali ta sanya gefen hannunta ta share hawayen da ke gangarowa bisa ƙuncinta, ba tare da ta ce masa ko ba ta ƙarasa gurin motar Aby tana sakar mishi murmushi, sai kawai ta faɗa jikinshi ta saki kuka.
"Na yi kewar Ƙasata na san cewa ban yi wa dangina adalci ba, ina fatan su yafe mini na dawo gare su ba zan ƙara nesa da su ba."
"Is ok Halima, duk abin da ya faru yana cikin kundin littafin kaddararki."
Share hawayenta ta yi tana kallon dad daidai lokacin da ya ƙaraso gurin.
"Ina son na ga mahaifiyata don Allah mu wuce Zariya, ka san matuƙar na shiga garin Abuja ba zan samu damar kasancewa da su ba."
"Ok ba matsala hakan zai fi domin kowa ya yi kewarki matuƙa."
Dariya ta yi mai ciwo ba tace komai ba ta shiga cikin mota escouts na ta suna biye da ita.
A lokacin da suka ƙaraso get ɗin gidan sai ta fashe da matsanancin kuka yayin da farinciki ganin Jannah da mahaifiyarta ya cika ta.
Babu wanda ya ce mata komai domin sun san kukan murna take yi.
Jannah na ji