Showing 96001 words to 99000 words out of 137802 words
Chapter 33 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 26-27*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi?" Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsawa sai sharɓar kuka take.
"Don Allah Hajiya ki saketa karki shafa ma jikinki warin da take yi, idan ma kin san ta ne, to ki bari ta daina wannna warin."
"Ƙyale ni Hajiya Turai ba ki san wace ce ita a gareni ba, saboda ita ɗin ƙawace a gareni, wanda ƙawancenmu ya rikiɗa ya zama 'yan'uwanta tana daga cikin mutanen da suka ƙarfafa mini kafa wannan ƙungiyar ta kuma taimaka da hannunta har da gudummuwarta, daga baya bayan ta yi aure na neme ta na rasa. Don Allah ki bamu guri."
Jin abin da ta faÉ—i ya sa ta É—auki wayarta ta fita tana waiwayon matar cikin tsananin mamaki, domin farkon zuwanta sun yi tunanin mahaukaciya ce.
"Me ya faru kika dawo haka, ina Kham É—in ki? Ta ya ya akai ya barki cikin wannan halin duk da irin son da ya nuna miki, domin zan iya cewa soyyarku ita ce na farko da ya fara jawo hankalina na fara soyayya."
Kuka ta ƙara fashewa da shi."Me kike so na gaya miki akan Kham domin abubuwa da dama sun faru, wanda tuna su sawa yake na tsani kaina da ranar da na fara saninsa a duniya. Haƙiƙa ya cutar da rayuwata. Halee, labari ne mai tsayi wanda ba zan iya gaya miki a halin yanzu ba, domin yunwa na ke ji rabona da abinci kwana biyu kenan, ni kaina dauɗar jikina ji nake kamar zan amayar da 'yan hanjina."
Ƙara kallonta ta yi cikin mamaki tana ƙara mamakin wai Mujee 'yar ƙwalisa ta dawo haka! Lallai rayuwa ba abin taƙama bace, in ta tuna da turare in har bai kai 50k ba duk ƙamshinsa ba ta iya fesawa.
"Kai wai me wasu maza suka mai da mata ne? A kodayaushe sun mai da mu wulaƙantartu su yi duk rashin mutuncin da suka ga dama akanmu saboda sun san Allah ya haɗa rayuwarmu, ba za mu iya rayuwa sai da su ba?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ɓacin rai tana kallon yadda aminiyarta ta koma saboda tabon ɗa namiji wanda ita ma tana ɗauke da shi."
"Mu je gidana ki yi wanka ki canza kaya, sannan ki ci abinci sai mu tuna bayan rabuwa." Ta ce tana kama hannunta cikin rashin ƙyanƙyani.
A lokacin da suka fito mutane suka rinƙa kallon su cikin tsananin mamakin ganin tana riƙe da hannun matar da in ta matso su za su iya guduwa domin ba ta da marana da mahaukaciya.
A mota babu wanda ya iya magana a tsakaninsu sai Mujee, da take kallon unguwar da suka shigo mai tsananin kyau da gidaje masu kyau na fitar hankali.
A lokacin duka mutanen gidan suna zaune a falo suna kallo ban da Jannah da ta ke zaune gefen dad tana ta chatting da Huzaifah yayin da fuskarta ke saukar da wani irin tsadadden murmushi.
Da sallama ta shigo cikin falon Mujee na biye a bayanta, wanda ta tsinke da kyawun gidan sai kawai ta fara tasbihi ga Allah MaÉ—aukakin Sarki, domin wannan gida ya cancanci a kira shi aljannar duniya.
Da sauri Jannah ta miƙe cikin zabura ta ɓoye a bayan da wanda shi ma ya miƙe yana kallon matar cikin mamaki da tuna son inda ya taɓa ganin fuskarta.
"Mom, who is she? She looks like mad woman." Ta ƙarashe maganar tana toshe hanci don har ta ji amai zai zubo mata.
"Watch your mounth, she is friend of mine. We ran off today."
"No way! This is absolutely impossible this mad woman to be your friend, mom." Ta ce tare da rugawa cikin bayi ta fara kera amai.
"Halima yanzu taimakon ya wuce ki taimaka a waje sai ƙin kawo su gida, ai wannan gidan mahaukata ya kamata ki kaita." Cewar Hajiya Baaba cikin zare ido.
Ta kalli dad da fuskarsa take cike da alamun tambagar wace ce, tare da mata kallon sani ta ce,
"Na san ba lallai ba ne ku iya gane ta ba, domin duk kusancin da ke tsakaninmu na kasa gane Mujee, 'yar Kaduna wacce muka yi Jami'a har tana zama a gidammu." Ta ƙarashe maganar cikin kuka tana rungume ta.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'in!Duniya ina za ki damu? Ke Mujidatuu, mai ya same ki ina mahifiyarki Hajiya Maryama da mahaifinki Alhaji Sani."
Kuka ta fashe da shi ta nufi Hajiya Baaba za ta rungume amma sai ta matsa tana toshe hanci saboda wani irin ƙarni da ya dumfaro ta.
"A'a ki dai bari kiyi wanka wannan wari sai ka ce kin yi kashin kwance." Cewar Hajiya Baaba.
Zubewa a ƙasa ta yi tare da sakin wani irin zananen kuka tana faɗin,"Sun mutu ba ni da kowa kowa ya guje ni Hajiya Baaba."
Zare idanunsa suka yi cikin jimamin jin mutuwar su da suka zamo kamar 'yan'uwa a baya.
"Oh rai baƙon duniya Allah ya jiƙansu da rahma, hatsarin mota suka yi?." Cewar Hajiya Baaba cikin hawaye, wanda ta kasa ba ta amsa sai girgiza kanta da ta yi tana share hawaye.
Mom kuwa kuka ta fashe da shi tare da janta cikin ɗakinta, domin ta kasa cewa komai irin ƙauna da kular da suka yi mata yake dawo mata ƙwaƙwalwarta, wanda ba za ta taɓa manta hakan ba.
"Ki shiga ki yi wanka ga kaya ki shirya, ba ri na sanya a haÉ—a miki abinci."
A falo sun yi jugum-jugum dad kuwa tsananin mamakin yadda ta koma yake yi, tunawa da lokacin da suna Jami'a ita ce take ke amshe gasar wanka da É—aukar gayu, amma dubi yadda duniya ta yi mata É—aurin goro ta wuntsilar da ita cikin duniyar da ta yanke zumunta da su.
"Please mom, I can believe that, you brought that mad woman into our house. Haba you should have think, saboda ba zan iya cin abinci ba idan ina ganinta." Ta ƙarashe maganar tana yamutsa fuska.
"Jannah, ki iya bakinki ba zan lamunta rashin kunya a gareta ba, wanda in kika ƙi ji zan mummunar saɓa miki."
Wani irin kallo ta yi mata sai kuma ta kalli dad da ya kasa mata magana tun da ta fara maganar.
"Ki taimaka mata can kamar yadda kika saɓa, amma ba zan lamunta wata ta shigo mana cikin rayuwarmu ba. Don Allah dad ka ce ta bar mana gidammmu."
Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Mom ta juya za ta shiga kicin don ba da umurnin a shirya mata babinci, sai ganinta ta yi tsaye da brush a hannunta.
Turus ta tsaya tana kallonta cikin jin kunya wanda ta tabbatar wa kanta da ta ji duk abin da Jannah take cewa.
"Na kasa buÉ—e shower ne kuma na duba ban ga makilin ba." Ta faÉ—a cikin sanyin murya yayin da idanunta suka kawo ruwa tana jin babu daÉ—i akan abin da ta ce.
"Ok, mu je na nuna miki." Ta bi bayan ta ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Bayan ta gama wankan ta fito falo cikin rashin sakin jiki ganin kallon da Jannah da Jannah take mata wanda daga ƙarshe tsaki ta saki ta shige cikin ɗakinta.
Zama ta yi a takure tana cin abincin wanda ganin hakan ya sanya mom ta sa aka kai mata kayan abincin É—aki daban wanda ta ware mata akan ta zauna acan.
Abinci sosai ta ci sannan ta yi sallah ko da ta buƙaci ta sanar da mom labarinta, amma sai ta kalle ta tare da riƙe hannunta ta ce,"Kar ki damu ki kwanta ki huta da safe za mu yi maganar."
Jannah a ɗakinta tana zaune da laptop ɗinta tana buga game gefenta Ummu riƙe da wayarta assignment da aka basu take yi wanda ita ma ba ta daɗe da gama wa ba.
Bayan ta gama ta gama ta ije a drower sannan ta koma inda take zaune tare da buÉ—e data.
"Subuhanallahi! Yanzu maganar strike ɗin nan ya tabbata!" Ta ce cikin jimami tana nuna wa Jannah abin da aka rubuta a wayarta cikin ɓacin rai.
"Kai! WaÉ—annan mutanen fa ba su damu da future na mu ba, domin they are after money. Yanzu in suna yin strike how many years they want us to obtain degree, they should consider us as their youngers."
"Kin san Allah ba haushin da na ji muna gab da fara exam fa, ya kamata su bari mu gama exam bayan mun sha karatu."
"I'm hoping that they should call off the strike if not, zan gaya wa dad kawai na koma outside Country na ci gaba da karatuna."
Tsaki Ummu ta yi ta kashe datar ta ije wayar domin ganin strike ɗin ya ɓata mata mood ɗinta gabaki ɗaya.
Wayar Jannah ya yi ƙara wanda ta ɗauka da sauri ta kanga a kunninta tana sakin wani irin murmushi bayan ta kashe mata ido.
"Umh, bari kika na tashi kar ku ƙone ya shafe ni." Ta ce tana kai mata dukan wasa a bayanta.
Ba ta ce mata komai ba sai murmushi da ta yi.
"Hello, my angel kina lafiya?" Ya furta da salon muryarsa na jan hankali lokacin da ya ƙaraso kan gadonsa ya faɗa yana shafa kansa.
"Am good bab and you?" Ta ce murya a hankali.
"Ina lafiya lau in dai babbar mace tana lafiya."
Murmushi ya yi har sai da sautin murmushin ya bayyana."Ina lafiya sosai, musamman yanzu da na ji muryarka sai na ji wani irin annashuwa bab."
Dariya sosai ya yi."Ina sonki Jannah, amma yau na yi mafarkin da bai yi mini daɗi ba, domin wani na gani ya riƙe hannunki zai ƙwace ki daga gare..."
"Bab, me ka yi mishi, ina fata ka sare kanshi da takobi?" Ta ce da muryarta da ya bayyana razana da firgici.
"A'a, ban samu na yi hakan ba a mafarki, amma na É—auki ninyar haka a zahirce ga duk wanda ya É—auki É—amarar yin hakan."
"Hakan ma ba zai faru ba bab." Ta ce mishi cikin taushin murya.
"Ki ba ni dama na bayyana kaina a gurin magabatanki Jannah, ina sonki wanda in ban aureki ba zan iya rasa rayuwata. Kin ga tafiya waje zan yi in ya so ayi maganar auren, da na dawo sai aure, kuma auren za a ɗaura muje can muyi karatunmu is ok Jannah, duk abin da iyayenki suka ce daidai ne matuƙar ba za su raba ni da ke ba."
"I will bab, in dai hakan zai faranta maka ko da ace gobe za a É—aura mana aure."
Wani irin ihu ya saka tare da rungume wayarsa." Da gaske kike Aljannata, da gaske kin sauko da burinki mu yi aure da da wuri ba sai kin kai matakin da kika da kike so ba."
Dariyar jin ce mata da ya yi aljannarsa domin wani lokacin haka yake ce mata wanda yake sanya ta nishiÉ—ani.
"Eh, na amince in har hakan zai saka nishaÉ—i." Ta furta a bayyane a ranta kuwa cewa ta yi,
"Ba ka san tashin hankalin da nake ciki ba wanda ya sa na sauke duk wani burina, domin wancan kinibabbiyar tsohuwar na neman kashe ni da raina.
"Yaushe za ki ba ni dama na yi intruducing ki gurin iyayena? ba su da matsala kuma duk sun sanki na nuna musu hotonki."
"Ni ma zan so haka, amma kafin nan ka shirya haÉ—uwa da dad É—ina sun dawo Nigeria."
"Wow, masha Allah. Na yi miki murna sosai I would like to come to see my dad and mom."