Showing 93001 words to 96000 words out of 137802 words

Chapter 32 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

Ajmal tsaye a gaban madubi yana gyara gashin kansa da kuma.


Mushiirat ta yi sallama ta shigo ɗakin tare da takowa anhankali ta rungeme shi. Kis ta sakar masa a bayansa.




"Ina sonka mijina." Ta furta cikin wata irin murya wanda ya sanya shi sakin murmushi ba tare da shiri ba.






A hankali ya juyo da ita yana manna na shi kis ɗin a goshi.




"Ni ma ina sonki sosai Mushiirat fatana Allah ya barmu tare ki haifo mini kyawawan yara masu kama dake."




"Amin." Suka haɗa baki gurin faɗin hakan.




"Zan wuce work kuma daga yau zan fara duties na dare."




Ɗan ɓata fuska ya yi jin abin da ta ce."Ni fa wannan dutie ɗin yana shiga haƙƙina."




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093






KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 25-26*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Ɗan ɓata fuska ya yi jin abin da ta ce."Ni fa wannan duties yana matuƙar cutata, domin yana nisanta ni da jikinki mai sanyani bacci cikin jin daɗi."




Dariya ta yi jin abin da ya ce." Na fika shiga damuwa sosai, sai dai babu yadda zan yi, domin aikin taimakon al'umma ne."




"Haka ne, muje na saukenki. Ina matuƙar alfahari da matata da take taimakon al'umma."






Kama kumatunsa ta yi ta ja tana dariya sai kuma ta ɓata fuska." Amma ni wannan kwalliyar ta mini kyau, ko zan fasa zuwa aiki na zauna na ɓatata?" Ta tambaya cikin tsigar shagwaɓa tana kashe mishi ido.




"Da ko na ji daɗi in aka yi mini haka sai dai gida zanje, kin san na gaya miki mom ta dawo zan je na gaishe ta ne."






Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba domin 'yarta ta ja mata tsana a gurinta.






"Ok, ko zamu tafi tare na gaishe ta?" Ta yi tambayar ba wai don tana son hakan ba sai don ba ta so ya fahimci tsanar da ta yi mata.




"Da sauri ya girgiza mata kansa ya bar shafa turaren da yake yi ya juyo yana kallonta.




"Ba sai kin je ba ki bari zan kaiki har can Abuja ki gaisheta."








Sai ta ji daɗi jin abin da ya ce domin ba wai don tana son zuwa bane, sam ta tsani ganin Hajiya Baaba da kallon banza ba ta ishe ta ba.




A ransa sai ya ji daɗi jin ba ta ja da nisa ba domin ya san matuƙar taje gidan nan sai ta ji abin da ke faruwa, yayin da ya fi son har ayi maganar auren a fasa baya son ta ji.




Jakarta ya ɗauka tare da kamo hannunta suka fita.




A lokacin da ya yi sallama mom na zaune da waya a hannunta suna magana da Hajiya Baaba.




Ya shigo ya samu guri ya zauna cikin matuƙar jin kunyarta.
Kallon shi ta yi cikin fara'a tana amsa sallamar da ya yi, wanda Hajiya Baaba ta yi kicin-kicin ta ƙi kallonsa ballantana ta amsa.




"A sannu da zuwa malamai magada annabawa." Ta yi maganar cikin fara'a.




Duƙar da kansa ya yi yana shafawa bayan sun gaisa.




"Sannu isasshe shafaffe da mai da ya ji. Saboda na ce zan aura maka Jannah shine ka yi gudun hijira sai yau na ke ganin ka ko? Tunaninka ƙin zuwa gidannan zai sa na fasa aurenne? Ka ci gaba da ɓuya sai randa na kawo maka ita a lulluɓe sai kuma ka bar garin."




Shiru ya yi baice komai ba saboda mom amma ita ma ta san sai ya tanka. Gaishe ta ya yi cikin ladabi."




"Ba zan amsa ba! Na ce ba na buƙatar gaisuwarka. Ni daga yau ƙarka ƙara zuwa gurin.."




"Haba Hajiya Baaba! Don Allah k..."




"Ba ruwanki Halimatuu na ce ba ruwanki, ba ki san waye shi ba kina ganin shi kamar mutumin kirki kura ne da fatar akuya, domin in ya yi miki wani abun sai kin ɗauka daga bariki ya fito." Ta furta cikin faɗa.


Da sauri ya ɗaga kansa yana kallonta.




"Ƙarya na yi?" Ta ce mishi cikin gatsali.




Tsananin kunyar mom suka ƙara ka masa sai ya ji kamar ya duƙa ya roƙeta akan ta tursasa ta ta janye auren, amma ba zai iya ba don haka ya miƙe jiki babu ƙwari ya yi mata sallama zai fita.




Mom ta raka shi da idanu har ya kai bakin ƙofa sosai ya burge ta kuma take ma Jannah sha'awarsa, sai dai ko ita ta san auren na su ba ɗauko rigima ce babba domin rayuwarsu ba ɗaya ba.




"Na ɗauka za a kawo mini surikar tawa ta gaishe ni domin tunanina tare za mu tafi Abuja kuka guri?"




"Ya kawota ta ji zai ƙara aure ta yi masa duka. Ai wallahi an dai yi girmar kwabo, ayi ta wa ƙanni mazurai amma a gida a kasa kataɓus."




Shi da ita babu wanda ya tanka mata sai ya kalli mom ya ce,




"Za mu zo har gida zan kawota ina da aiki sosai."




"To shikenan, Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ta ce daidai lokacin da ya amsa da




"Amin." Ya fice da ga falon yana aika wa Hajiya Baaba mugun kallon da take aika masa daa irin sa.






"Munafuki macijin sari ka noƙe." Taace tare da miƙewa.




"Don Allah Hajiya Baaba, babu wanda yake daidai a rayuwarki ne? Ban taɓa jin kin yabi wani ba domin kowa a gurinki mai laifi ne da aikata ba daidai ba? Dubi yaronanna bawan Allah ko shigar da ya yi bai kamata ki rinƙa ci masa mutunci. Yaro mai hankali da addini." Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya.




"Ba ki san halin shi ba shin yasa kike faɗin haka."Ta ce tare da miƙewa ta fice daga falon.




Bayan sun dawo sun ci abinci dad yake gaya mata tafiyarsu wanda ya da cikin farinciki ta kalle shi ta ce,




"Yauwa dad, zan je kuma ga shi yau Alhamis gobe lecturer da muke da shi ba zai zo ba, ka ga zan yi weekend ɗina acan sai musha hirarmu.




Murmushi ya yi jin abin da ta ce yana ɗaga mata kansa.




"Bari na je na haɗa kayana." Ta ce tare da ficewa cikin tsananin kewarsa.




A lokacin da suka isa garin Abuja mai-gadi ya buɗe musu katafaren get ɗin gidan momi ba ƙaramin razana suka yi ba, domin ko ita mom gidan ya yi masifar burgeta duk da ta ga komai a waya sai dai ba kamar a zahiri ba.




Su Jannah iyayen hoto duk cikin damuwar da suke ciki bai hana su ɗaukar hoto ba, musammman garden da ya yi matuƙar burge su.




Da suka shiga cikin falon sai kansu ya kwance. Jannah ce kawai ba ta wani ruɗe sosai ba, saboda gidan da suke a London ya fi wannan.






Mom ta wuce ɗakinta don ta watsa ruwa. Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakinna ta kallo da aka danƙara dukiya.




Tsarin gidan ya yi mata da komai da komai ba




Bayi ta shiga bayan ta tuɓe kayan jikinta ta buɗe shower.




A hankalinta sauke ajiyan zuciya tana jin daɗinnruwan da yake rage mata gajiya.




Bayan ta yi wankan ɗa ɗaura alwala ta fito tare da sanya kaya ta fara sallah.




Da ta idar da sallar ba ta ƙara waiwayar kowa ba ta ɗauki laptop ɗinta ta fara aiki, domin ta san yana nan birjik yana jiranta.




"Wai lallai Halimatuu, ta tara dukiya irin wannan gida sai ka ce a Ƙasar waje." Cewar Hajiya tana jinjina kanta.




Masu aikin gidan suka fara kawo musu kayan abinci wanda Hajiya ta ba da umurnin a sakko musu ƙasa, sakamakon gajiya da suka yi suna son miƙe ƙafa.




Jannah da ce da dad kawai suka cin abinci a dining a filet ɗaya wanda ta ci cikin tsananin murna.




Ba su yi wani hira mai tsayi ba suka kwanta saboda gajiya.




Washegari da safe misalin ƙarfe tara mutanen gidan suka hallara a falon don karyawa ko wannnen su ya yi wanka ya shirya cikin alfarma.




"Kai ina Halimatuu? Ita ce kawai ban ganta ba, ma za Jannatu ki kira ta." Hajiya Baaba ta furta tana kallon ta da ta tura baki alamun ba za ta je ba.




" Tun safe ta fita sakamakon aikin gaggawa da ya taso mata ta ce na sanar miki ba ta son ta tashe ku ne." Cewar dad da yake sakkowa daga upstairs




"Kai Halimatuu, ba za ta huta wa rayuwarta ba. Haba mutum ya baro wata uwa duniya, amma ba zai iya bawa kansa hutun kwana ɗaya ba."




Babu wanda ya ce komai sai Jannah da ta taɓe baki ta ci gaba da cin abinta.






"Kai ni fa ba zan iya cin waɗannan abincin ba salon basir ya kama mutum, domin in ban da dankalin turawa babu abin da na gane abincin nan, shi ma sai da aka ɓata shi da wannan abun mai kama da majina."




Gabaki ɗaya suka kwashe da dariya jin abin da ta ce.




"Yanzu Hajiya Baaba, nufin ki ba ki san ketch-up ba? Gaskiya wannan ai sai ki ba damu."




"Ai wallahi Anty Nahlin gabakiɗayanta ba ta waye ba domin Hajiya fa ko custard ba ta iya sha, sai dai ta sha koko. Ai tana ba da su mom."




"To haka kawai sai na cuci kaina na yi ta cusawa kaina abin da zai cutar dani ai lafiya uwar jiki, haka kawai na kashe kaina lokacina bai yi ba."




Ta ƙarasa faɗin hakan tana miƙewa sai ta ci gaba da cewa," Ni ba zan iya ci ba girki zan je na yi. Ke ungozi kike ko wa za a samu kullu a kicin ɗin nan na dama farau-faru."




Dariya suka ƙara kecewa da shi." Taɓ! Kullu a wannan gidan sannu Hajiya Baaba." Cewar Ummu tana gimtse dariya ganin kallon da take mata.




Shiga kicin ɗin ta yi tana 'yan dube-dube amma ta rasa gane gas ɗin sai ta fito tana faɗin,"Ke Hafsatuu, ma za zo ki nuna mini yadda ke kunna gas ɗin, wannan mai cinyeyen kan ko na yi magana ba ji na za ta yi ba."




Miƙewa ta yi ta nufi kicin ɗin ba tare da ta ce komai ba lokacin da Aby ya ce,"Ki duba ma ta ba za ki rasa na serchet ba."
"To." Ta amsa sannan ta shige kicin ɗin.




Mom zaune a bayan mota da waya a hannunta tana duba tsaƙonnin da aka turo mata ta twinter. Daina duba tsaƙon ta yi tana kallon tanƙamemen get ɗin da aka rubuta Alcharity Foundation Center da rubutu manya a saman get ɗin.




Idanunta suka kawo ruwa ta sanya hannunta ta share daidai lokacin da direba ya yi parking.




"Barka da dawowa shugaba." Ma'aikatan gurin suka rinƙa faɗin haka cikin girmamawa.




Hannunta take ɗaga musu cikin murmushi har ta ƙarasa cikin ofis ɗin.




"Barka da dawowa uwar marayu haƙiƙa ƙungiyarmu ta yi kewarki ƙwarai."




Rungume juna suka yi cikin farin sake ganin juna.




"Na yi kewarku gabakiɗayanku musamman ke aminiyata." Ta ce tana murmushi.




Kujera ta isa gareta ta zauna tana kallon Hajiya Turai da ta ƙaraso ta nemi kujera kusa da ita.




"Ba ni da lokaci sosai ina files ɗin da na ce ki aje mini, sannnan kin tura ma wannan matar da za a yi mata aikin ƙoda?"




Wayarta ta ciro tare da shiga cikin hotuna tana faɗin,"Tun daren jiya na tura musu domin har anyi aiki, jiran farfaɗowar matar kawai muke jira."




"Good! Aikin ki na kyau, Ubangiji ya bamu ladar hakan."




"Amin." Ta amsa sai kuma ta mai da hankalin akanta bayan ta karɓi wayarta da ta gama kallon hotunan ta miƙa mata ta mayar cikin al'jihunta.




"Wannan matar da ta damu kan tana son ganinki, yanzu haka mun yi waya da ita tana kan hanya ina fatan za ki jira ta, saboda yanayin matar tana cikin tsananin buƙata, amma ta ƙi yadda mu taimaka mata dole ke take son gani."




"Eh, zan iya jiranta, amma in har ta ƙara minti biyar ba ta ƙaraso ba sai dai gobe, domin ina da meeting." Ta ƙarashe maganar tana duba agogon hannunta.




"In sha Allahu za ta ƙaraso."






"Allah ya sa hakan." Ta ci gaba da duba files ɗin da take yi.



Wayar Hajiya Turai ta yi ƙara da sauri ta miƙe tana faɗin,"Yauwa ga ta nan ma ta iso."





"Ok, ki shigo da ita ciki."




Fita ta yi tare da ɗaga mata kanta wanda ba ta cika minti goma ba, sai ga ta sun shigo da wata mata cikin wani yagalelen hijabi da doguwar rigar da ta mutsutsutsuke.



Duk yadda mom ta so karta toshe hanci sai da abin ya faskara, domin wani irin wari take jin yana tashi, wanda ba ta san lokacin da ta kai hannu ta toshe hancinta, tana jin yadda kayan cikinta ke hautsinawa ba, inda Allah ya taimaketa ba ta karya ba don babu abin da zai hana ta amayar da kummmalon.



"A uwa ba da mama ko dai na fita da ita ne? Na ga yadda kike ɓata fuska kar dai kiyi amai? Sai da na gaya mata ta nemi duk irin taimakon da take so za mu ba ta, amma ta n ce dole sai ta ganki"Hajiya Turai ta furta cikin ɗaga murya tana mamakin matar.



"A'a, kar ki damu ƙyaleta." Ta furta tana ƙoƙarin daure warin amma ta kasa.



"Wayyo Allah na shiga uku! Yanzu Halee, nufinki ba ki gane ni ba? Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Khamis ka cuce ni kai mai da duniyata mara amfani in har zan yi canzawar da Halee, za ta kasa gane ni. Ni kam mene ne amfanina a rayuwata"



"Mujee!" Ta furta cikin tsananin mamaki da tare da sakin wayarta ta ƙaraso gareta ta kama ta, ba tare da ta damu da warin ba."





"Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi? Ta riƙe ta tana girgiza ta tare da kallon mamaki ganin yadda ta joma tmkar mahaukaciyar da ta shekara tana hauka.







" Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsa ko ɗaya, sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta.







"Zuciyata ta kasa yarda kece wannan Mujee, ina iyayenki suka bar ki cikin wannan halin?"








Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093








KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login