Showing 6001 words to 9000 words out of 137802 words

Chapter 3 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

yake dan samun kasancewar da ita. A haka sai suke rayuwarsu yau fari gobe tsumma.
Ranar kuma aka yi rashin sa'a bayan kwana biyar ciwon ta ya ƙara tashi. A lokacin duk ba sa nan, sai mai aikin su Kelen da take kicinn tana girki, kasancewar ranar ba duty ɗin Rose ba ne. Kelen yarinya ce domin da kaɗan ta girmi Jannah.
Tana bacci misalin shidda da yamma ta rinka jin sanyin na taso mata a hankali, tun tana controlling har ta ji this was more than she could take.
Wayarta ta ɗauka ta dialling number dad domin ta san shi ne kawai zai ba ta attention her more than mom. She might have been unlucky to call her phone and find it switched off; she could’ve been in a meeting.
Out of that temptation ta kira wayar dad, sai dai to her surprise, he wouldn't be coming due to a specific reason that he mentioned.
Jifa da wayar ta yi, tare da rufe fuskata da hannayenta, tana jin yadda sanyin ke ƙara tasowa.
Sai da aka kira mangariba ya shigo, cikin sauri ya nufi ɗakinta, duk da cewar ya kira doctor ya duba ta, amma sam hankalinsa na kanta.
Tana ganin shi ta samu kuka mai karfi. Hanunsa ta kama sosai. "Please do something about this coldness; if not, it will kill me. Look, my body is shaking. Don Allah, dad, i'm tired.”
Sosai ya ji tausayin ta lokaci guda kuma ya zargi kansa, domin shi ne sanadin komai. Don haka ya zama dole ya tilasta wa mata, komawa gida, saboda ko ita was like isolating kan ta ta yi, she wasn't enjoying the environment at all. Given her body language, she was pretending.
Da taimakonsa sanyin ya fara raguwa bayan ya haɗa mata tea mai zafi ta sha har yana kona mata Baki, sannan ta yi wanka da ruwan zafi sosai, ya kunna mata room heater, sai ta samu sauki duk da cewar har zuwa lokacin haƙoran ta na kaɗuwa.
Ganin ta samu bacci ya kashe mata wuya ya fito falo yana zaune har aka kira sallah, daidai lokacin da ta shigo tana rike da jakarta. Kasancewar ba ta san ciwon ya tashi ba, sai ta wuce ɗakin ta don gabatar da farali, sosai ta dawo da yunwa. Dad ya rufa mata baya.
A ɗaki bayan sun idar da sallah suka sakko kasa don cin lunch, sannan ya ke sanar da ita. Abincin ta bari na nufi dakinta, sai dai har zuwa lokacin bacci take yi, duk da alamu ya nuna ba ta enjoying ɗin sa, duba ga yadda ta tsakure kamar mage.
Kofa ta kama tare da juyowa ta da dawo wa falo ta zauna hannu biyu ta zuba tagumi.
"Mu koma gida Halee, don Allah. Our daughter needs that."
Kamar mai tunanin she couldn't say a word. She adjusted and hesitated for a moment. "In har muka koma gida ba zan taɓa manta wa ba duk da cewar na yi maka alƙawarin hakan, sai dai ya zama tabo mara guguwa wanda ya zama silar rashin nagartuwar raguwarmu." Ta karashe maganar cikin sautin kuka tare da juya bayanta.
A hankali ya taka har gabanta ya tsaya lokaci guda idanunsa suka canza. Gwiwowinsa a ƙasa ya kama hannunta a sauri ta janye, ba tare da ya damu ba ya fara magana. "Don Allah ki manta komai na roƙe ki a karo na ba adadi, ki taimake ni ba don halina ba. Kin san yadda abubuwa suka kasance, amma na yi miki alƙawarin hakan ba zai taɓa garuwa ba in sha Allahu kuma zan tsaya tsayin daka, domin na ga na kare ki da ƙarfina.”
Sosai take kuka ba tare da ta saurare shi ba, wanda dalilin kukan yake ƙoƙarin ɗauke numfashinta, ganin hakan ya sanya shi miƙe wa da sauri ya fice daga gidan domin ya san a wannan lokacin babu wanda zai iya rarrashinta. Shi kansa a zaman auren su ya san yana fama da wasu personlity ɗinta wanda suke unlike to his tunaninsa da hankalinsa. Kai tsaye harabar gidan ya fice yare da buɗe murfin motarsa ya shige tare da bata wuta ya fice daga harabar gidan zuciyarsa na tafasa tamkar garwashin wuta.
A hankali ya gangara motarsa zuwa gefen titi tare da kashe motar ya buga kansa da sitiyarin mota a hankali yace. "Prideful woman! Yes absolutely she is." Ya furta yana share fuskarsa da zufar da ta tsatsafo masa.
"Why, Halima, mai ya zuciyarki take kamar ta kafuran farko, Allah mun masa laifi ya yafe mana, amma sam ba kya yafiya."
Idanunsa suka kaɗa jajur har wani turiri kansa yake yi. Kifa kansa ya yi yana jin ina ma ana mai da hannun agogo baya, da ya gyara lamuran da suka faru a baya waɗanda suka zama mara guguwa suka canza alaƙar dake tsakaninsa da iyalinsa, amma sai sai kash! Bakin alƙalami ya bushe kaddara ta riga fata.
Tsawon lokaci ta ɗauka tana durƙushe a gurin zuciyarta tana tafasa ji take tamkar ta mutu ta bar duniya duk da cewar Allah ya wadata da komai na jin daɗin duniya, domin tana cikin matan da suka amsa sunansu kuma suke fantamawa da kuɗaɗensu. Kasacewa mace ce jaruma mai kamar maza a tsaye take. Shahararriyar yar kasuwa wacce ta aje aikin gwannnati domin zagaya ƙasashe don kasuwancinta, don zata iya shiga cikin jerin matan da za'a iya irga kuɗinsu a matan Nigeria. Sai dai duk da irin arzikin da Allah ya yi mata amma akwai tabon da ya raunana zuciyarta wanda take jin tamkar gara ta yi bankwana da rayuwar a take ciki, amma sai dai mutum bai da ikon canza kaddarar rayuwarsa.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093










*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*




*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*Page 3-4*












BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM






Kimanin awa ɗaya tana gurin ba tare da ta motsa ba, duk da irin kiran wayar da ake damunta da shi, amma ko motsi bata yi ba, gyara zama da ta yi tare da lumshe idanunta tana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarta wanda yake santa kanta sarawa tamkar zai fashe gida biyu. Nannauyar ajitar zuciya ta saki tare a sharce hawayenta ta miƙe daidai lokacin da Jannah ta fito daga cikin ɗakinta tana kallonta, tare da sun yi wa juna magana ba, ta shige cikin ɗakinta.
Duk da cewar Daddy ya kan kwana ba'a gida ba, sai dai wannan karon hankalin Mom ya tashi ƙwarai, domin a tunaninta fushi ya yi, don haka ta shiga kiran layinsa, amma bata shiga.
Misalin ƙarfe biyu na dare tana zaune a tangamemen falonta idanunta akan fuskar wayarta har yanzu layin shi take kira amma ta ƙi shiga. Jifa ta yi da wayar kan kujera tare da dafe kanta lokaci guda ta shiga sintiri a falon.
Motsi ta ji a bayanta da sauri ta wai ga, daidai lokacin da Jannah ta fito daga kicin hannunta riƙe da kofin madara.
Murmushi ta sakar mata amma sai Jannah ta kauda kanta, ba tare da ta ƙara kallonta ba ta shige cikin ɗakinta. Saboda ba tana jin abin da ya faru tsakanin su har fitar dad, sakamakon fitsarin da ya fashe ta ta ji suna hayaniyar. Mom ta saki ajiyar zuciya. Zubbur ta miƙe tare da bin bayanta.
Zaune ta same ta da kofin madaran a hannnunta, tana kurɓa idanunta na kafe akan wayarta da take kallon korian film.
"Jannah na hana ki kallon dare, amma ba kya ji saboda ban isa na gaya miki magana ba ko?" cikin tsigar tambaya da kashedi.
Nauyayyan idanunta ta zuba mata wanda bacci ne a cikinsu sun kaɗa sun yi jajir saboda kukan da ta sha
"Oh! Please, Mom, ki bar ni na yi kallo saboda ba na jin bacci."Momi ta buɗe baki zata yi magana Jannah ta katse ta cikin muryar kuka, yayin da wasu zafafen hawaye suka gangaro kan kyakyawar fuskanta. "Please, Mom!"
Ta furta yayin da ta rushe da kuka sosai. Jim Mom ta yi yayin da take jin kukanta har cikin ƙahon zuciyarta, sai dai bata da kallmar da zata iya rarrashinta a shi, domin in da zata samu damar kukan da tafi buƙatar hakan, don haka ta jawo mata ƙofar tare da jingina jikinta da ƙofar daidai lokacin da wani guntun hawaye ya siraro mata a ƙuncinta waɗanda suka fi garwashin wuta zafi.
"Wayyo Allah na!" Jannah ta furta cikin kuka tare da jifa da kofin dake hannunta ya tarwatse ƙarar fasa ƙofin ya ɗaga hankalin Mom ta rintse idanunta tana jin karar yana kuwwa a kanta.
"Wace irin uwa nake da ita, wacce ta ruguza duk farincikin rayuwata? Mom sam ba ki yi adalci a rayuwarmu ba, domin kin mai da rayuwarmu tamkar makabarta. Ko mene ne Dad ya yi miki ta cancanki ki yafe masa." Kuka take sosai tana sumbatu.
Lumshe idanunta ta yi take zuciyarta ta ƙara ɓaci. "Ke nan Jannah haushina take ji? Sam bata ganin na mahaifinta." Cikin mamaki ta furta hakan a ranta. Da gudu ta ruga cikin ɗakinta ta kulle.
A ranar Dad bai dawo ba, sai washegari da misalin shidda da rabi na safe daidai lokacin da Mom ta fito daga cikin ɗakinta, tana sanye da doguwar rigar bacci fara ƙal.
A tare suka kalli junansu na ɗan daƙiƙa sai suk ɗauke kai ba tare da sun furta magana ba.
Dad ya mai a kallonsa gareta lokacin da ta zauna akan dining table tana ƙoƙarin kiran waya.
A hankali ya ƙaraso gabanta ya yi kamar zai zauna a kujerar gefenta sai kum ya fasa ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata ido.
Ba tare da ta kalle shi ba duk da cewar ta san ita yake kallo, amma ta yi biris da shi har sai da ta kammala kiran wayar duk da ba dogon magana ta yi ba, domin umurni ta bada a wayar ta kashe.
Idanunta ta ɗaga ta yi ɓasa wani irin kallo sai ta miƙe da sauri ya kama hannunta ganin zata bar gurin. "Ina fatan sarauniyar mata ta tashi lafiya." Yace da ita tamkar bata ji abin da yace ba ta fisge hannunta zata wuce.
Dad ya yi sororo duk da cewar ya saba da hakan amma ya ji babu daɗi kamar duk lokacin da ta yi masa hakan.
Tana ƙoƙarin hayewa sama mai aikinta, Rose, ta fito daga kicin tare da durƙushewa ƙasa tana kwasar gaisuwa. Cikin sakin fuska ta amsa mata tare da yi mata, umurnin abin da take so saɓanin wanda yake a rubuce akan timetable, sannan ta haye sama tare da bugo ƙofa garam! Ya daɗe a gurin tamkar gunki zuciyarsa na suya, sannan ya shige ɗakinsa.
Ƙarfe goma daidai mutanen gidan suka hallara akan dining domin karyawa. Sam babu mai magana a tsakaninsu. Ga abinci kala-kala amma sai juya cokulansu suke yi, domin gara Mom da Daddy sun sha titi Jannah kuwa babu abinda ta kurɓa. Dad ya yi gyaran murya ya ce,
"Jannah, eat up. I don't want you to starve youself. You know that not eating is dangerous for a person, and you’re going for a check-up today. Remember?”
Murmushi ta sakar masa ta ce, "I do. Zan ci, dad. Kai ma ka ci abinci. please Dad."
Ya mayar mata da murmushin tare da kai lomar soyayyen ƙwai a bakinsa, ganin haka ya sa ta gutsira bread ta saka a bakinta, suka kalli juna tare da ƙara sakin murmushi a karo na biyu.
Mom ta ije wayarta da tun da ta zauna take amsa waya, wanda hakan yana matuƙar ɓatawa Jannah rai, domin kusan kodayushe bata da aiki sai waya. Ita kam bata taɓa ganin uwa wacce bata damu da ƴarta ba, domin in suna labari da ƴan ajinsu suna gaya mata irin yadda iyayensu suke wasa da su tare da basu lokacinsu, amma ban da Mom da bata da lokaci saina tare kuɗi da business ɗinta, wanda a irin kuɗin da take da shi ya kamata ace ta bar komai ta ba su farinciki, duk da cewar ta fahimci mom tana tara kuɗi ne don ta wulaƙanta mahaifinta son ranta duba ga tafi sni kuɗi nesa ba kusa ba.
Tuni ta gama fahimtar kuɗin da ta fi shi ya sanya take wulaƙanta sa, domin in dai ba don kuɗin ba, ya kamata ace ta yafe masa akan lifin da take iƙirarin ya yi mata.
Tun da suka zauna mom bata ce ƙala ba har suka kammala karyawa ta miƙe cikin sauri tare da sumbatar Jannah a fuska. "Ki kula da kanki na wuce amma ba zan daɗe ba." Ba tare da ta jira amsa ba ta fice.
Jannah ta taɓe bakinta tare da rakata da idanu har ta isa gurin escouts ɗinta da suke jiranta ta fice daga falon. Taɓe bakinta kara yi tare da mayar da hankalinta kan Dad ta sakar mishi murmushi sannan ta ci gaba da cin abincinta.
Kimanin minti biyu da fitar Mom har zuwa lokacin babu wanda ya yi ko tari, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. Mom ta buɗe ƙofa ta shigo. "Jannah ki zo mu fara kaiki asibiti daga nan mu wuce."
Jannah ta juya jin abin da ta faɗa, ta gyara jibgegiyar rigar sanyin dake jikinta tace. "No, kar ki samu Dad zai kai ni in ba shi time zan yi driving ko Nups ya kaini."
Iya abin da tace mata kenan ta juya tare da ci gaba da cin abinta ba tare da ta kara kallonta ba. Shiru ta yi tare da tsayawa sai kuma ta juya ta fice daga falon.
"Dad mu koma gida Najeriya ko da Mom ba zata bika ba, in ta zabi kasuwancinta." Ta furta cikin muryar tausayi tare da kallonsa.
"Kiyi haƙuri Jannah in sha Allahu zamu koma gida gabakiɗaya, amma kiyi haƙuri yanzu dole zan tura ki gida ko da Mom ba zata so ba."
"Ka bar damuwa da damuwarta, domin ban taɓa ganin mace mai son kanta ba Dad. Laifi ne ka yi ma ta kuma ka nemi yafiyarta, ya kamata a ce ta yafe ma ka." Murmushi ya yi ji abin da ta ce. "Wataƙila da a ce ke ce minjinki ya yi miki hakan, ƙila ba za ki iya masa afuwa."
Dariya ta yi jin ya ambaci mijinta. Kunya ta kamata sai ta sunkuyar da kanta tace." Allah ya kyauta, zuciyata ba irin tana bane tuni zan yafe masa." Shima dariyar ya yi jin abin da ta ce.
Kama hannunta ya yi. "Har yanzu ina ƙara gargaɗinki da ki daina shiga faɗanmu, ko me ta yi mini na cancanci hakan, kuma ina ƙara gaya miki ita ɗin mutuniyar kirki ce. Fatana watarana zata haƙura mu ci gaba da zamanmu lafiya."
Shiru kawai ta yi ba tare da tace masa komai ba, lokaci guda idanunta suka fara zubar hawaye.
Tausayinsa take ji sosai domin a tunaninta tsanannin son da yake mata ne ya sanya shi rashin ganin laifinta, amma ita ta auna mom a mizanin hankalinta ta fahimci mace ce mai son zuciya da son kanta wacce ta fifita kuɗi akan komai take yin abin da ta ga dama, wannan dalilin ya sa ta ɗauki alƙawarin ba zata taɓa yarda ta nemi kuɗi fiye da mijinta ba, domin gani take a dalilin hakan ne mom ta raina mahaifinta.
Ture plate ɗin gabanta ta yi tare da miƙe wa zuwa ɗakinta don ta ɗauke mayafi su tafi asibiti. Dad ya bi ta da kallo cikin so da ƙaunar ƴa guda ɗaya tal wacce Allah ya ba shi.
Bayan ta gama ganin likita direba ya dawo da ita. Kai tsaye ɗakinta ta nufa tare da kwantawa a kan makeken gadonta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta saka tana jin babu daɗi a ranta. Rose ta shigo cikin girmama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login