Showing 12001 words to 15000 words out of 137802 words

Chapter 5 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

koma ba kuma ba zan bi umurnin ka ba, don haka duk abin da zaka iya ka yi ba ni da haufi a kansa."
Girgiza kansa ya yi cikin takaici lokaci guda idanuna suka kaɗa tamkar garwashin wuta.
"Do you know that Jannah is dealing with a mental disorder, and she’s in therapy secretly That’s cause of your careleness."
Idanunta ta zare tare da Kallon shi cikin tsananin mamaki.
"What! Are you crazy? Ka San me kake faɗi Jannah ce in her age take shan waɗannan pills ɗin?" Sai kuma ta girgiza kanta tana faɗin, "Impossible! No way this could ever happen!"
"Saboda kin ba ta kulawar da ko wace uwa take ba wa 'ya'yanta? Sam ba ta yi miki komai ba, i dar har ba za ki iya yafe mini laifin da na yi miki ba, to ki hukunta iya ni din kawai."
Kuka sosai ta sa tana dukan shi tare da cin kwalarshi. "Anya zan iya yafe maka Injiniya? Ka cutar da rayuwata." Sai kuma ta sake sa da ko gezau bai yi ba ta kai mata mari. "Ashe dama mahaukaciya ce ke ban sani ba? Kin san me kike son jawo ma kan ki, kin san irin side effects din da suke da shi."
"Leave me, mom! Do you even care about ne?" Ta ce tare da fisge rigarta tana mata wani irin mugun kallo. "Yes, I know all the side effects.” Ta ja numfashi tana kallon dad cikin tsananin mamaki don ba ta taba tunanin ya san tana sha ba kuma Bai tana muna mata ba ko da wasa, lallai yana matuƙar sonta. "Amitriptyline’s for dealing with depression and anxiety, but it also works as a sleeping aid if you can’t crash. Olanzapine’s mostly for depression too, but it can help with eating disorder and can knock you out for some sleep too." Ta furta cikin rashin shakku sai duma ta ɗora da cewa, "Na sani, amma amfani nake don na samu sauki da bacci. Sam ba na iya bacci da karatu, Kuma kin takura mini da dole sai na yi karatu, bayan kin kasa zama da ni, ki bani farin cikin da zan iya mai da hankalina na yi karatu da shi." Sai ta karashe maganar cikin kuka sosai har tana sheshsheƙa.
Dad ne ya ɗora da cewa, "In har ba za ki bi umurnina ba dole na ɗauki mataki domin ba zan yarda na zamo mijin tace ba. Na kashe rayuwar 'yata daya da Allah ya ba ni Ina ji ina gani." Ya karashe cikin ɗaga murya.
Dariya ta yi mai sauti sosai har ta tafa hannu kamar ta kalle shi sheƙeƙe, duk da cewar ta yi matukar razana da jin abin da take yi, amma hakan bai sanya ta sauko daga dokin na ki da ta hau ba, sai dai ta dauko aniyar daukar likitar da za ta kula da ita har ta daina. Kallon shi ta yi cikin raini ta ce, "Yanzu ka san da wannan? Yanzu ne ka san akwai matakin da za ka ɗauka. Ai tun tuni kake jiran wannan lokacin, don haka gara ka ɗauki ko wane irin mataki, karka damu da ni na shirya tsaf wannan ranar nake jira."
Ransa ya ɓace hankalinsa ya tashi ya dafe kansa yana jin yana sara mishi tamkar zai rabu gida biyu, sau biyu yana ƙoƙarin magana, amma duk lokacin da ya buɗe baki sai ya ji wani irin baƙin ciki mai kama da ƙwallo ya taso ya tokare masa maƙogaro kuma ya ƙi wuce wa. Tabbas a yau ya gane ta gaji a zama da shi nemar hanya take yi. In kuwa hake ne bata yi masa adalci ba, musamman ƴarsa da yake ganin ta fi buƙatarta fiye a shi, sai dai ta yi nisa ba ta jin kira.
A hankali ya buɗe bakinsa domin ya furta abin da ya san daga bakinsa ne ko iya leɓensa, amma ba daga cikin zuciyarsa ba sai ya ji ya kasa, musamman da ya juya ya kalli Jannah da take ta kuka tun da suka fara muhawar kamar yadda ta saba kuka duk lokacin da suke sa'in sa, sai ya ji matuƙar tausayinsa.
"In har da gaske kike kin shirya karɓar duk matakin da na ɗauka to ki...."
"Daddiiiiiii." Ya ji muryar Jannah ta kira sa tare da janye bargon da ke jikinta ta sauko daga gadon ta ƙaraa gurin shi tare da rufe masa baki.
"No daddy.” Tace cikin matsananciyar kuka tana yi wa mom wani irin kallo.
Sai ta juya ta kalle sa tare da girgiza masa kai, duk da cewar ita kanta a wannan lokacin ta fara tunanin rabuwar iyayenta shine kawai matsalar rikicin da sike samu, domin tana gani auren da babu zaman lafiya rabuwa yafi, tun da har ba zata iya yafe masa ba, amma ba akan dalilin ta ba. Sam bata son iyayenta su rabu saboda ita gara ace akan matsalar da suke samu ne, don haka ta girgiza masa kai a karo na biyu cikin kuka tace.
"Idan har a kaina zaka rabu da mom don Allah dad ka haƙura na koma Nigeria ni kaɗai karku damu kuyi zaman ku, amma ina roƙon ka don Allah ka kai ni gidan Abby zan fi samun natsuwa a can tun da akwai sa'oina don Allah." Ta ƙarashe maganar tare da ƙara rushe da kuka.
Dukkkannin su jikinsu ya yi sanyi dad ya kama hannunta cikin tausayi tare da shafa kanta. Hannnunsa ta kamata haɗe tare da riƙe su duka. "Please! Dad."
Sosai ya ji tausayinta duk da cewar ya so ta zauna a gurin mahaifiyarsa, amma babu yadda zai yi wataƙila amincewar zai iya bata farincikin da suka kasa bata a matsayinsu na iyayenta. Sai ya juya ya kalle ta da ta yi halin ko in kula da su, sai cika take tana batsewa tare da kada kafarta, matukar bacin rai ya kara kama sa. Cikin raunanniyar murya ya ce mata, "Na amince, idan hakan zai ba ki farinciki fatana a ce ki yafe mini don Allah." Ya faɗa cikin muryar da ta ƙara bayyanar d tsananin ɓacin ran da y ke ciki. Murmushi mai kama da yaƙe ta yi.
"Thanks." Iya abin da tace kenan ta juya ta koma ba tare da ta kalli in da take ba, yayin da wasu irin zafafafan hawaye suke sauka da ga kuncinta. Tsananin tsanar mahaifiyarta yake kara samun gurbi a zuciyarta.
Mom ta yi shiru tamkar gunki ta tsaya tana jin ta zuciyarta kamar zata fashe. Zuciyarta ta gama haƙiƙancewa Dad ya zama azzalimi mai son kansa, domin duk abin da yake faruwa a sanadinsa ne shine ya zamo silar komai kuma ya shafa mata kashin kanji yarta take ganin laifinta. Idan har Jannah zata din ga ganin laifinta akan duk abin da yake faruwa sai ta ce rayuwarta da abin da take nema ba shi da amfani a gurinta, sai dai kuma babu yadda zata yi, ammm akwai Allah shine zai hisabi ya bayyana mai laifi tsakaninsu, don bi yi wa rayuwarta adalci ba.
Maganarta ta katse mata duniyar tunanin da ta shiga daidai lokacin da ta ji muryarta tana faɗin,
"Dad don Allah ina son na bar gidan nan yau in da hali na samu jirgin da zai tashi yau ko ƙarfe na wa ne!” Ta furta maganar cikin rawar murya da karayar zuciya. Dukkannin su zuciyarsu ta karye idanuwansu suka kawo ruwa gabakiɗaya zargin kansu ya kama su.
"Kina ji ko Jannah kiyi..."
"Don Allah na ce fa!" Ta katse shi cikin muryar da ba ta san ta yi masa ba, sannan ta ci gaba da cewa.
"Ina son na yi nesa da ku sosai yadda zan baku damar zama ku kaɗai kuyi tunanin cewa akwai wata halitta wacce ta damu daku take zubar da hawaye a duk lokacin da, in har ba ku daina faɗa ba na roƙe ku don Allah kar kuzo gare ni ku, zan yi ƙoƙari sake wasu ahalin na san iyalan Abby za su bani ko da kwatankwacin farincikin da na rasa agare k..."
"Haba Jannah ya kamata ki natsu don Allah ki fahimce ni." Mom tace tare da kamo hannunta.
Da sauri ta fisge hannunta tare da cewa, "Don Allah ki bar ni mom, domin babu abin da za ki gaya mini ya tausasa zuciyata. In har akwai bai wuce ki yafe ma mahaifina ba, sannan ki damu da ni and take your responsibility, na ga kuna farin ciki kamar yadda ko wane ma'aurata suke yi."
Mom ta tsaya sagale tana kallonta cikin rashin dibara, sam bata yi tunanin ta yi nisa haka ba.
Miƙewa ta yi zumbur tare da isa wadrop ɗinta ta fara haɗa kayanta, bayan ta kammala ta ta janyo trolley ɗinta ba tare da ta kale ta da take tsaye ba cikin rashin dubara.
Riƙe trolley ɗin ya yi tare da buɗe baki zai yi magana sai dai kallon da ta yi masa ya tabbatar masa da in har ya ƙi aminta da ƙudirinta to tabbas za ta iya ɗaukar mataki wanda zai iya zamar musu nadama har ƙarshen rayuwarsu, don haka ta bawa zuciyarsa shawara tun kafin tusa ta karewa bodari.
"A halin da kike ciki bai kamata ki bar gidan ba, duk da cewar ba zan hana ki tafiya ba tun da hakan kike so, amma kiyi haƙuri ki samu lafiya Jannah."
Murmushi mai ciwo ta yi jin abin da tace ta janye troley ɗinta da ta riƙe. "Rayuwa a cikin gidan zai zami tamkar maƙabarta ina jin gara na rayu a cikin a wata duniyar sabanin wacce nake ciki da na rayu a duniyar da ba'a maraba da zuwana."
"Wa ya gaya miki wallahi ina matuƙar son ki kamar yada yake matuƙar son ki amma kin ƙi fahimta ta." Mom tace yayin da ta nemi sauran maganar ta rasa domin ita kanta bata da abin da zata ce ta kare kanta.
"Idan har kina sona ki yafe masa sannan ki bini mu koma gida cikin iyalanmu." Jim ta yi jin abin da tace can kuma ta furta. "Ba ki san irin girman laifin da ya yi mini ban.."
"To ki sanar da ni sai na yanke masa hukuncin idan ya cancanci ki yafe masa idan kuma bai cancanta ni da kaina zan ba ki shawara." Ta ce da ita tare da kafe ta da ido.
Wuri-wuri ta yi tana zare ido cikin rashin mafita. Ganin hakan yasa ta girgiza kanta tare da kama hannunsa suka nufi hanyar fita. Har sun kusa fita, ta dawo a baya ta tsa gab da ita da take tsaye ruwan hawaye na shatata tana jin ƙara tsanarsa matuƙa tare da tambayar kansa anya za ta iya yafe masa! Muryarta ta ji tana faɗin, "Don Allah kar ki zo gare ni na roƙe ki, idan kuma ya zama dole sai kin zo ki sanar da ni na bar gidan domin bana buƙatar ganin ki." Da sauri ta fice ta bar mom da take kuka tamkar numfashinta zai fita, sai ta durƙushe a gurin tare da sakin kuka mai ƙarfi.
"Haƙiƙa ka cuce ni ka raba ni da 'yata wacce na fi so a duniya kuma na ke neman duk wata dukiyata domin ta.”
A lokacin da suka fita Jannnah ta faɗa kan jikin shi tana wani irin kuka kukan da take jin tamkar zai tafi da numfashinta. Tana amatuƙar son mom sosai. Mahaifiyarta mace ce wacce ko wace ƴa zata yi alfaharin samun ta, amma sai dai wasu dalilai zai saka ta nisanta kanta da ita. Ƙunshe kanta ta yi cikin rigar sanyin ta, wani irin raɗaɗin zafi take ji a zuciyar tare da kewar mahaifiyarta tun kafin ta bar ƙasar amma ya zama dole ta rabu da ita wataƙila nesanta da ita da ta yi zai zamo maslaha ya saisaita tsakaninsu.
Duk irin rarrashin da yake yi mata amma ta kafe kan dole sai ta bar London a yau. Babu yadda zai yi hakan nan ya ɗauki asara ya nema mata visa na jirgin da zai tashi ƙarfe ukun dare sannan ta daina kuka. Tsura mata ido ya yi yayin da tausayinta ya cika masa zuciya. Yana jin da ace zai iya da ya sanar da ita laifin da ya yi mata su taru su bata haƙuri sai dai sam baya son tuna abin da ya faru ballantana ya ta da zance.
Dad ya rako ta filing jirgin. Duk da cewa ba bu mai magana a tsakanin su, amma duk bayan mintina sai ya juyo ya kalleta, hankalinsa a tashe, ganin yadda hawaye yake bin fuskarta ba tare da ta yi kokarin sharewa ba.
"Zuciyata tana zargin mu da gazawa a rayuwar ki Jannah. Komawar ki Nigeria kamar mun kasa cike gurbin da ya kamata mu cika ne." Ya dan tsagaita ko za ta ce wani abu, amma sai ya ji ta yi shiru ko tari ba ta yi ba, don haka ya dora da cewa, "Going back to Nigeria don't meanyou will outrun your destiney. No, not at all. Rayuwa cike take da jarrabawa. Domin Allah Madaukakin Sarki ya fada a littafin sa mai tsarki, dole ya jarrabe mu ta ko wane hanya. Life has its inevitable challenges, which means you must face them one way or another. Kin ga dole ki ko yi adapting in any situations you find youself in."
Shiru ba magana har yanzu, domin zuciyarta cike take da tunani iri-iri. Ga shi tun kafin ta bar London ta fara jin kewar su, amma babu halin zama da su by all means.
Kallon ta ya kara yi, sai bai ce komai ba ya ci gaba da tuka motarsa.
Yana faka motar ta fito da sauri ko direba ba ta bari ya dauki trolley dinta ba.
Dad ya zura mata idanu lokacin da take hawa matakalen upstairs din jirgin tana hawaye tare da daga masa hannu. Ba tare da ya sani ba, sai ya ji zubar hawayen a fuskarsa. Lokaci guda ya kara tabbatarwa kansa da ya zama mai son zuciyarsa da ya ruguza farin cikin rayuwar ahalinsa.
A hankali ta karasa kujerar da aka nuna mata mallakin ta ta zauna. Sai ta rintse idanunta ta ce, "I missed just you, dad, and I will keep you posted on everything."
Sai kawai ta fashe da kuka sosai tana jin kamar ta yanke shawara cikin fushi ne, saboda tun ba'a yi ni sa ba, fara kewar iyayensu na ta.
“Hi, young and cute lady.”
Ta ji muryar namiji ya furta daga gefenta, wanda ya sa ta juya da sauri cikin tsoron.
Ya dan sakar mata murmushi tare da lumshe ido. "Wow! You look dashing beautiful and adorable! I must say it. Wallahi ke kyakykyawa ce." Ya furta cikin tautausar murya da salon jan hankalin duk wata 'ya mace.
Wani irin kallon uku tara ta yi mishi. Kamar za ta yi mishi rashin kunya akan shiga rayuwarta da ya yi, sai kuma ta ga rashin amfanin hakan. Ta taɓe tare da kara kallon shi ƙasa-ƙasa ta mayar da kanta gefe, ba tare da ta ce masa kala ba.
Jim ya yi a tsaye don ya ji ba dadi yadda ta yarfa shi, saboda zai iya cewa this is the first time he got disappointed and humiliated in public. Sai dai kuma the way she looks, he would not let someone to downgrade or humiliate her. Don haka jiki a sanyaye tamkar kazar da kwai ya fashe masa ya koma kujerarsa ya zauna yana kallon ta, dai-dai lokacin da ta sake earpiece a kunninta.
"She is such a woman with arrogance! But, anyway, she is my type." Ya furta yana kallon yanayin shigarta, kyawunta, har da haiba.
Jannah duk ta bi ta takura domin ta tsani kallo a rayuwarta. Matukar mutum ya ci gaba da kallonmu ta tsam take tashi daga gurin, don haka ganin ya kafeta da idanunsa da ta kira mugaye, don har sai da ta faki idanun sa ta tofa addu'ar. A cewar ta kar ya zo maye ne.
Har zuwaa kacin hawaye ba su bar shatata da ga fuskar ta ba, wanda hakan ya daga hankalin sa kwarai.
"Life’s full of twists and contradictions." Ya furta ganin wannan zukekiyar budurwar da take kuka wanda zai iya kiran ta da hurul ain.


NIGERIYA ƘASARMU TA GADO.
Misalin ƙarfe goma na safiya agogon Nigeria jirgin su ya sauka, tun da suka iso garin Kaduna ta rintse idanunta a suka kumbura suka yi girma luhu-luhu, sakamakon kukan da ta sha.
A hankali ta yi miƙa da salati tana shaƙar iskar garin Kaduna sai ta ji kaso ishirin a cikin kashi ɗari na damuwarta ya ragu.
Karab! Suka haɗa idanu da ƙyaƙyawar suarayin da ya zabga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login