Showing 114001 words to 117000 words out of 137802 words

Chapter 39 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

wallahi ba ta da kunya ga kafiya da raina na gaba da ita, shi kuma zuciya da son girma."

"Humh, na ga yadda wannan aure da Hajiya Baaba ta haɗa zai yi wu kuma a zauna lafiya? Ita ma ta iya rigima."

"Ki barta sai sun kai ta lahira lokacinta bai yi ba, domin ta san ba alkhairi ta haɗa ba, dama ta ƙyale shi da matarshi mai hankali."

"To munafukai, duk na ji abin da kuka ce. Na ce kuna gulmata kun ƙaryata, yanzu mai za ku ce da na kama ku da kunnuwana."
Da sauri suka waiga suna mamakin ganinta a jingine da ƙarfen bene tana karkaɗa wayarta cikin isa da gadara.

"Ban sani ba, ai duk abin da muka faɗa haskiyane saboda mun zo gidanku kin gama raina mu har ki kalli idanun Anty Nahlin kice mata munafuka." Ummu ta ce.

"To malama kike so na kirata? Kuna ta wani gulma ba ku tausaya mini halin da nake ciki ba, ai duk na gane halinku kuma zan yi maganinku. Don kawai ina da wanda nake so ne da sai na yadda an yi auren kuga yadda zan wahalar da ɗan'uwanku na mai da shi tamkar almajirina na shishshuka masa rashin mutunci son raina sai na ga uban abin da za ku yi ku masu ɗan'uwa."

"Jannah, Anty Nahlin kike gaya ma haka?"

"Ki barta saman zan hauro na zane ta kuma ta san babu wanda zai ce mini komai."

"To mai ya hana ki ai gani a gabanki bismillah." Ta ce cikin tsiwa wanda ya tunzura ta ta fara hawa benen da sauri.

Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki!








Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093












KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 31-32*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki." A tunaninki bari zan yi ki duke ni? Muguwa kawai." Ta ce cikin tsoro.


"Matsoraciya ai da kin tsaya ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa dake." Cewar Nahlin cikin ɓacin rai.


"Ga rashin kunya sai shegen tsoron tsiya, ai ni addu'a zan yi Allah ya sa auren nan ya ƙullu, ko don ya koya mata hankali ta rinƙa girmama mom." Ummu ta ce suka ci gaba da kallo.


Tun da ta san tsiyar da ta shuka ba ta sakko ƙasa ba ko da ta ji yunwa frij ɗin dad ta buɗe ta yi ɓarnarta son ranta.


Tana kwance akan gadonsa gabakiɗaya ji take rayuwarta komai ya tsaya mata cak. Ko sallah ba ta tashi ta yi ba har sai da dad ya dawo sannan ta buɗe ƙofar ta faɗa jikinshi tana hawaye.


A tunaninsu wani ƙaryar za ta yi musu sai ta ba su mamaki don ba ta yi masa ƙorafin komai ba sai cewa da ta yi,
"Dad, I miss you." Ta furta tana riƙe da hannunta.


Ledar tsarabar da ya yi musu ya miƙawa kowa na ta sannan ya ije na Jannah yana ƙoƙarin buɗe mata robar ice cream.


Da kanshi ya fara ba ta sai kuma ya miƙa mata ya shige bayi don ya yi wanka.


Washegari da safe bai sakko ƙasa ba har sai sha ɗaya lokacin duk suna zaune a falo suna kallo.


Kwana biyu da tafiyar Hajiya Baaba, da mom duk sai gidan ya zama babu daɗi, domin tsoro yake ba su. Ko bacci za su yi sai tsoro ya kama su saboda girman gidan.


Zaman gidan sai ya yi musu babu daɗi domin shi kansa dad, sai dare yake dawowa, in bai fita da wuri bane ya fita takwas na safiya.


Ranar da ya cika sati ɗaya da tafiyar mom wanda ta gaya musu saura kwana tara ta dawo, suka cika da murna ganin an janye strike don haka suka fara shirin komawa Zariya cikin farinciki, ban da Jannah da take contemplating whether to stay or not, saboda ita kanta ba daɗin zaman gidan take yi ba.


Haka dai a ranar da aka yi call off ta wuni cikin tunanin ba tare da ta samu mafita ba, saboda hankalinta ya fi karkata da ta koma, amma in ta tuna auren sai ta ga gara zamanta a Abuja. In ta hanga a wata mahangar ta ga zaman kaɗaicin da take yi sai ta yanke shawarar gara ta koma Zariya duk abin da zai faru ya faru, saboda ko sun yi mata auren ita ce mai zaman ta ga yadda za a yi ta zauna.


Cikin wanann halin na tsaka mai wuya wanda take ganin rayuwarta yana gaba kura baya siyaki. Ta kwanta ba tare da ta samu mafita ba, tana ganin su Ummu suka haɗa kayansu cikin farinciki don har sun kira mom, sai dai rashin sa a wayarta ba ya shiga amma sun bar mata tsaƙon kar ta kwana na shirin tafiyarsu.


Cikin fargaba yake sakkowa da troley ɗinsa yana ja zuciyarsa cike da tsoron yadda zai tunkareta ya sanar masa da tafiyarsa.


Ilai kuwa ganinsa da jaka ya sa ta miƙe a zabure.
"Dad, traveling?" Ta ce tana kallon shi da idanunta har sun fara kawo ruwa.


Bai amsa mata ba har sai da ya sauko ƙasa ya riƙe hannunta suka zauna kan kujera.


"Eh Jannah, tafiya ta kama ni ban san da tafiyar ba, and I must go it is an important."


"No, you will no go anyway I know it is mom that send you."


"Haba Jannah, na gaya miki tafiya zan yi and I will stay a bit long." Ya ƙarashe maganar cikin tsawa domin ya san in ba haka ya yi mata ba zai sha fama da ita.


A maimakon ta saduda sai ta sanya kuka.
"Babu ind za ka dad, ita ba ta zauna ba kai ma ba ta barka ba, gabakiɗaya ta takurawa rayuwarka. Ga shi su Ummu za su koma Zariya sai a barni ni kaɗai a wannan ƙatoton gidan, ni wallahi ba zan iya zama ba, saboda yanzu I can't stay in loneliness, na saba za ma cikin mutane."


Dafe kansa ya yi cikin rashin dubara."So what do yo want Jannah? You know I must go cus na yi reserving flight ko so kike mom ta yi asara."


"Eh, Let her do. Ban damu ba in dai za ka kasance dani don ba zan iya zama daga ni sai masu aiki a wannan gidan ba."


"Am sorry but I have to go. nan da awaya ɗaya zai tashi I have to be hurry."


"I said you are not going anyway." Ta ce tare da riƙe rigarshi tana kuka.


Ransa ya ɓaci ya juyo ya kalli su Ummu da suka yi tsuru-tsuru suna kallonta.


"Nahlin, gobe za ku wuce ko? Mom told me that.I wished you safe trip and ku kula da karatu. Ga wannan mom ta ce a baku ku riƙe za ta yi booking flight na ku, sannan anjima direba zai kai ku shooping. Choose whatever you like it is on her."


"Ok, thanks dad, mun gode Allah ya ƙara buɗi."


Kallonta ya yi sai ya fisge rigarsa." Ba kya jin magana, karki manta ni mahaifinki ne, in na gaya miki magana you must obey haba you have to give me that respect I earned." Ya ƙarashe maganar cikin tsawar da ya firgita ta matsa gefe tana zare ido.


"Na gaya miki planning ɗina akan auren ki, amma you didn't agreed. Hajiya has power and authority that I can do anything than tha..."


"Leave me alone!" Ta ce tare da ƙara matsawa da fisge hannunta da ya yi.


"Na gane kai ma mom ta zuge ka da kuɗi, I understand that you were living in object puverty that's why mom manipulating you with money and make you like her errands boy. Your family are poor that is why you married mom to be rich. Saboda money sai ka kasa bani farinciki dad, ka na gani za a yi mini auren dole da wanda ba na so! Why did you marry mom becouse of money why dad?"


Sai ta fashe da kuka tare da durƙushewa.


"I love Huzaifah like crazy I want him to be my wedded husband, please do something."


"I'm sorry that I can't help, but you have to understand that my love to your mom is genuine."


"Isn't dad!"


"To shikenan, tun da ba kya jin magana you always do as you wish, sai ki je kiyi abin da za ki yi, kuma daga yau na cire hannuna akan maganar aurenki." Ya ce cikin fushi tare da ɗaukar jakarsa.


"Nahlin, ku gida gida zan kira in ji kun sauka lafiya." Ya kama hanya zai fita yana jin yadda kukanta ke ƙona masa zuciya.


"Ni ma zan bi su do the viser with me I can't stay alone." Ta ce cikin muryar kuka.


Jiyowa ya yi ya kalleta sai kuma ta ba shi tausayi ya kasa ce mata komai domin ya sani suna cutarta da yawa, ya yi tunanin dawowarsu zai ba ta farinciki, sai ga shi maganar aurenta ya taso wanda shi ne sanadin dagula komai, ba shi da zaɓi wanda ya fi ta koma gidan Aby ta amince da auren, domin zaman ta da rayuwarta acan sai ya fi mata fiye da nan da ba su da lokacinta.


"Shikenan, I will do the viser." Ya ce tare da ficewa ransa na ƙuna.


Nahlin da Ummu sai ta ba su tausayi sun sani duk wani abin da take yi da ɗaurin gindin iyayenta da suka yi sakaci da rayuwarta.


Kuka take sosai kamar ranta zai shiɗe tana ganin sam iyayenta ba su da buƙatar haihuwarta, wannan dalilin ya sanya da suka haifeta suka tsaida haihuwar gabakiɗaya, domin rashin lokacin da za su kula da yayan, duba ga ita kaɗai da suka haifa sun yi wa rayuwarta riƙon sakainar kashi tana watangaririya cikin duniyar rayuwarta, saboda da sun tsaya sun kula da ita har yaushe za a laƙa mata wannan ƙaddarerrren auren


Ganin kukan ya ƙi ƙarewa ya sa Ummu ta ƙarasa gurin ta kama tana matuƙar jin haushin Hajiya Baaba da ta kafe sai anyi auren domin duk ita ta jagula komai, suna rayuwarsu cikin farinciki da annashuwa.


"Please sis, stop crying. Kina sa na ji kamar na yi. Kyakkyawar fahimta ya kamata ku yi tsakaninki da iyayenki." Faɗawa jikinta ta yi.


"Me zan fahimta ba sa sona kawai, dad ne kuma shi ma gashi za ta yi nasarar raba mu, honestly dad, is after money ba ya son ya bi zaɓina mom ta rabu da shi ya yi rayuwar talauci."


"No, don't say dad." Cewar Nahlin ta riƙe hannunta.


"Anty Nahlin mu bar gidannn yanzu zuciyata tana mini zafi, na tsane su ba na son zama a gidansu."


"Ki yi haƙuri mu bari zuwa goben." Ta ce tare da kama hannunta suka zauna.


Lallaɓata suka yi ta ci abinci Ummu ta shirya mata kayanta wanda dama duk iskancin da take yi da ya ji ba za ta koma Zariya ba sai da ta ci babu daɗi tana tunanin yadda za ta saba da tashinta.


Duk kiran da mom take mata ta ƙi ɗagawa sai dai suka yi waya da Nahlin da Ummu. Ta tura musu maƙudai suka je shoping, wanda ko tsinke ba ta ɗauka ba sai Ummu da in ta ɗauki abu, ta ke siya biyu tun da dama komai iri ɗaya suke sanyawa.


Washegari suka koma Zariya wanda Jannah tun da suka hau jirgin ba ta ce ƙala ba, tana ganin kiran dad da ya dame ta da text har da hotonsa ya turo masa da ya isa amma ba ta kalla ba.


Adal da Ummita suka rugo da suka rungume su suna faɗin,"Oyoyo Anty Nahlin, Ummu da Jannah."


Wani irin zabura Hajiya Baaba ta yi domin duk da ta san cewar su Nahlin za su dawo ba ta san da ita za a dawo va, sai Aby da Ammy kawai suka sani.


"Kamar su nan Jannah na ji an ambata a gidannan?" Ta ce tana kallon su Adal da suka ruga da gudu suna rungume su da suke fitowa daga cikin mota.


"Ke! Uban me ya dawo sake daga gidan?" Ta ce mta cikin tsawa.


Jannah da ta fito daga motar fuska kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa kallonta ta yi ba ta ce komai da troley ɗinta za ta nufi sashinta.


"Tsaya na ce, ina za ki ai ba dai sashina ba?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai tana girgiza.


"Kin ga Hajiya Baaba, ki matsa mini na shiga babu ruwanki da ni."


"Akan me saboda ina jin tsoronki ko? Ko gidan iyayenki ne da kika raina kowa ba kya ganin kowa da gashi?" Ba ta ce mata komai ba ta matsa ta gefenta za ta wuce.


"Kin san Allah in kika ga kin shiga cikin ɗakin nan, sai dai in bani a gurin nan. Daga zuwa gidanku kika rinƙa suka mini rashin mutunci kala-kala ke mai iyaye. Shi ne yanzu kun ɓata kin sassaɓo jiki kin dawo gani tsohuwar banza na karɓe ki ko? To ba za ki zauna a ɗakina ba, sai in ki nemi wani gurin ko ki zauna da su Bimbo, ai dama idanu na zuba miki saboda iyayen na ki har wasu iyaye ne da za a yi togiya da su. Mutanen da basu da buri sai kuɗi. Ki ji da kyau auren da zan yi miki da Adamuu wallahi gata na yi miki, domin ba ki da kowa sai shi don haka ki yi masa biyayya."


Tsaki ta yi ta ƙara matsawa za ta shige.


"Au kin ɗauka wasa nake miki, bari ki gani."Ta ce tare da janyo ƙofarta ta rufe.


"Ƙyale ta Jannah, kin ji zo mu koma shashinmu da zama."


"Eh, can gasu gada, zomo ya ji kiɗan farauta. Ba dai ɗakina ba fitsararriya kawai." Ta ce jin abin da Ummu ta ce.


Tafiya suka yi ba tare da ta ce mata uffan ba domin a mood ɗin da take ba za ta ji kalmomi ma su daɗi ba in ta ce za ta kula ta.


Suna shiga sashin Ammmy ta rushe da kuka wanda Ammy ita ta zauna ta rinƙa rarrashi har ta yi shiru ta ci abinci.


Hutun kwana biyu suka yi na gajiyar dadowa suka koma makaranta da ake karatu babu kama hannu yaro don exam suke shirin farawa har ana ƙara fito musu da sabon time table.


Tun da suka dawo ba ta nufi shashin Hajiya ba kamar yadda ita ma babu ruwanta da ita domin da gaske fashin take da ita, amma ko muryarta ta ji sai ta leƙa ta ganta.


Bayan sun dawo da sati ɗaya suka fara exam wanda hankalinsu ya koma kan jarrabawar gabakiɗaya ba su da lokacin kansu.


Zaman su ya yi daɗi sosai duk wani rashin kunya da iskanci da ta ke musu ba ta yi wanda kuma ba su nuna mata komai ba suka cigaba da zamansu lafiya. Nahlin ce wani lokacin ba ta shiga sabgarta don kar ta ƙara raina na.


Ranar laraba dukanninsu suna zaune a falo suna hira bayan sun kulle kansu a ɗaki sun sha karatu na exam ɗin gobe.


Ajmal ne ya yi sallama ya shigo fuskarsa a sake ganin Ammy zaune a tsakiyarsu ana hira da ita.


Jannah dake zaune kusa da Ammy kamar za ta shige jikinta ta ɗago daga kallon wayarta da take daddananwa ta kalle shi ta watsar.


Shigowarsa ya sa suka daina hirar da suke yi suna gaishe shi ban da ita da ta yi kamar ba ta san wata halitta ya shigo ba kuma yana lura da ita.


Zama ya yi gefen Ammy." Kwana biyu shiru har zan fara cigiyarka." Ta ce tana murmushi ganinsa.


"Eh wallahi Ammy, am on the go. Abubuwa sun cuɗemini ba ofis ba karatutttukan da nake da shi."


"Allah Sarki Ubangiji ya dafa ya yi albarka."


"Amin." Ya amsa cikin farinciki yana kallon 'yan ƙanninnasa da suka rame saboda exam.


"Ya exam kun ga yadda kuka rame kuwa?" Ya ce daidai lokacin da idanunsa suka sauka akan Jannah, wanda sai da ya ɗan saki dariya ganin yadda ta rame sai idanu zuru-zuru, domin abu abubuwa da dama suka ramar da ita, wanda rashin magana da dad shi yafi komai ƙara ramar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login