Showing 105001 words to 108000 words out of 137802 words
Chapter 36 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
su sha ba Huzaifah ya duƙa yana kuka a gaban dad.
"Dad Allah dad, kar ku raba ni da ita wallahi ina sonta ban taɓa jin son wata 'ya mace kamar ta ba, and we are compatible, zan barta ta yi duk a abin da take so, ba zan zamo azzalimi ba."
Sai ya yi matuƙar ba shi tausayi matuƙar gaske har yana jin ƙwallah na shirin zubo masa, yayin da momeries na tsawon shekaru suka dawo masa wanda ya fuskanci irin wannan ranar da ya sha tozarcin da ba a taɓa masa.
Sosai ya yi na'am da shi saboda duk da hutu da waye da gata, da aka ƙawata rayuwarsa bai hana shi zama cikakken namiji wanda kowa ne uba zai yi burin 'yarsa ta aura. Uwa uba ga kyau da tashen ƙuruciya da natsuwa, musamman yadda yake masa maganar yana hawaye, ya san idan ya aureta zai kula masa da ita saboda tsananin sonta da yake.
Hannunsa ya kama ya riƙe yana shafa bayansa wanda ganin hakan iyayensa suka fara murna suna ganin alamun nasara...
"Calm down, ɗan samari. Matsalar ba daga ni ba saboda da ace ni ne ayau zan aura maka Janah, don n yaba da hankalink..."
Mom ce ta katse maganar da yake yi wacce ta yi sallama ta shigo, saboda tun da ta sanar masa ya kira ta.
Sosai suka yi gaisuwar mutunci da girmamawa, bayan sun gama gaisuwa irin ta su ta 'yan boko masu ji da kansu da aljihu, sai mahaifin Huzaifah ya yi gyaran murya ya ce,
"Huzaifah ya sanar mana da soyayyar da yake yi wa 'yarku. Sai dai, ya gaya mana ita yarinyar tana son ta gama karatunta, kuma shima yanzu haka waje za shi ya yi phd ɗinsa, amma kwasam yau ta kira shi take sanar mishi da za a yi mata auren dole. Wanda ba mu yi ƙasa a gwuiwa ba muka zo neman iri tare da ba wa wancan haƙuri tun da tana son Huzaifah."
Shiru suka yi na 'yan sakwanni babu wanda ya ce uffan sai mom ta yi gyaran murya ta ce,
"Eh haka ne wallahi da yake ɗan yayana ne za a haɗa auren muna baku haƙuri yaje ya nemi wata."
"No mom, don Allah karki ce haka ina sonta ba zan iya auren wata in ba ita ba. Ki bani ita na yi miki alƙawarin zan riƙeta duk yadda kike so, amma don Allah don annabi kar ku raba ni da ita." Ya ƙarshe maganar cikin muryar kuka tare da ƙarasowa kusa da ita ya duƙa ya ɗaga hannunsa yana roƙonta.
Babu wansa bai ba shi tausayi ba shiru ta yi tana tuannanin yadda za ta ɓullo ma lamarin, saboda Huzaifah ya yi mata ita kanta za ta so ya aureta. A wancan lokacin da ta kawo wanda take so in har da ba shi aka aura mata shi ba Allah kaɗai ya san halin da za ta shiga.
"Yaran ba so suke ba mahaifiyata ta tilasta hakan, bari na kira muku ita in har kuka shawo kanta shikenan."
"Za ta amince Hajiya Baaba ba ta da matsala, alokacin da naje gidanta hannu biyu-biyu ta karɓe ni." Ya faɗa cikin murna domin shi tunaninsa har ya mallaki Jannah ya gama duba ga yadda ta yi ta nan nan da shi.
Mom kuwa miƙewa ta yi ta shige ciki a ranta tana fatan Allah ya sa ta amince, wataƙila don bai san halinta bane ya sa ya furta haka, amma Hajiya Baaba kura ce da fatar akuya."
Ta same ta a cikin ɗakinta tana ta haɗa kayanta tana gungunai. Ganin ta shigo ya sa ta haɗe rai ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da haɗa kayanta."Hajiya Baaba shirin tafiyar ake yi?"
"Eh to mene ne amfanin zamana a gidan da ba a da buƙata ta? Kullum ba ki da lokacina ai gara na koma gidan Muhammadu in ya so yanka ni matarsa za ta yi inna mutu baki da asara. Da ninyar zama na zo amma ba zai yi ba."
"Haba Hajiya, ina iyakan ƙoƙarina fa aiki ne suka sha mini gab.."
"Ki je ki kashe kanki akan al'umma ke kika sani."
"Ni ba wannan ya kawo ni ba muna da baki a guest room."
"Mene ne haka?"Ta tambayeta a ƙubule tana mata mugun kallo.
Dafe kanta ta yi sam ta manta ta yi turancin."Ɗakin baƙi nake nufi"
"To shine sai an nuna mini iyaka na rashin turanci?" Tsaki ta yi ta ci gaba da haɗa kayanta ba tare da ta kalle ta ba.
"Hajiya jiranki fa suke yi." Ta faɗa cikin ƙosawa wanda ta taso mata a harzuƙe.
"Su waye ne? Wa na sani a garin Abuja da za su zo mini? Ki fita idanuna ki barni na haɗa kayana, na koma Zariya tun kafin na taɓa miki halina."
"Ni dai don Allah ki zo ki gannin ma idanunki." Ta ce tana ƙoƙarin ficewa.
Tsaki ta ƙara saki kamar ba za ta je ba komai ta tuna sai ta ije jakar da take shiryawa ta fice.
Jannah dake laɓe a bayan labule don tun da suka shigo ta zo gurin ta laɓe, tana addu'ar Allah ya sanya kunnuwanta su ji mata Hajiya Baaba ta amince, wanda za ta sa a sanya rana a gurin don kar ta canza shawara.
Hajiya Baaba da ta so za ta shige ɗakin sai ta hangi ƙafafunta a basu shige ba. Yaye labulen ta yi tana kallonta wanda ta fara mazurai.
"Uban me kike yi a gurinan? Yaushe kika zama munafuka kike laɓe?"
"Ban sani ba kuma ba ruwanki da ni." Ta ce a hankali kuma cikin tsiwa.
Jikinta ya bata bakin na ta ne ko iyayen Huzaifah. Wani rashin mutunci ta saka a ranta don ko maka fa madina za su ba ta ba za ta fasa auren nan ba.
"Iyayen Huzaifah kika ɗauko mini ko? To ko shugaban Ƙasa kika kawo bai isa yasa na janye ƙudirna ba. Shashasha kawai."
Ta saki labulen tana mata mugun kallo wanda ba ta ce komai ba saboda da ƙarfi take maganar, kuma ta san tana yi ne don mutane suji.
Da sallama ta shiga falon yayin da ta yi fiƙi-fiƙi da ido sannan ta haɗe rai tamkar an aiko mata da mala'ikan mutuwa.
Zama ta yi a hamshaƙe tana masa gaisiwar da iyayen Huzaifah suka yi mata a gajarce do ko na Huzaifah da lafiya kawai ta masa ta sha kunu.
Jikinsu ne ya yi sanyi ganin yadda ta karɓe su.
"Hajiya Baaba don Allah ki taimaka kar ki raba ni da Jannah wallahi ina sonta zan iya mutuwa in ban sa.."
"Kai ko Huzaifah kake ko wa? Wane irin rashin kunya kake da shi? A gaban manya kake maganar son da kake ma mace? To ai ni ban ga amfanin zuwan iyayenka ba matuƙar kai za ka yi magana." Ta faɗa tana salati da tafa hannu sai ka ce wanda ya aikata mugun zunubi
Huzaifah sai ya cika da matuƙar mamaki, take ya gane ita ɗin kura ce da fara kauya, domin lokacin da ya je gidanta ba haka ta karɓe shi ba. Jikinsa a sanyaye ya koma ya zauna lokaci guda hawayen da yake ƙoƙarin mayarwa suka wanke masa fuska.
Ganin hakan, sai jikinsu ya ƙara matuƙar sanyi jin abin da ta ce, don ba su ga abin aibu ba mahaifinsa ne ya yi gyaran murya.
"Ki yi haƙuri kin san sha'anin yara da abin da suke so. Ki taimaka mana ki bamu auren Jannah za ki yi alfahari da hakan."
"Haka ne, ai dama ban ce ba zan yi ba, amma gida bai ƙoshi ba ina za a bawa dawa? Adamun da zan haɗa shi aure da ita shine kawai zai iya zama da ita domin kura ce da fatar akuya. Kuma tunani juya Adamun ya aura in har ba aure na yi masa ba, yadda matarsa ta mallake shi ba zai iya ƙara aure ba ni kuma ina son kafin na mutu na aurar da yarsa."
"Hajiya magamar da ya kawo shi daban da wanda kike masa. Yaran suna son junansu don Allah karki raba so.."
"Sannu Laila da Majnun! Na gaya maka Jabiruu in ima magana kana saka mini baki wallahi sai na yi maka tonon silili, saboda ba ka da ta ido har baki kake da shi."
"Allah ya ba ki haƙuri." Ya ce tare da kama bakinsa bai ƙara cewa komai ba yana kallon mom, da ta dafe kai tana dana-sanin kiranta, yayin da kunya ta kamata kamar za ta nitse, jin ta ɗauko magana daban.
"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ka bani?" Bai tanka mata ba ya yi shiru.
Juyawa ta yi ta kalli iyayen Huzaifah aure da na ƙulla babu uban da ya isa ya sa a fasa ko da iyayensu.
"Ɗanku ya je ya nema a waje ga matanan birjik sai wanda ya zaɓa, don ma bai san halinta bane har yake asarar hawayensa da kun san ita ɗin kura ce da fatar akuya ba za ku nema wa ɗanku ba. Ai Jannah sai Adamuu shine daidai da ita."
Jin abin da ta furta Jannah dake kuka abayan labule ba ta san lokacin da ta banko cikin falon da ƙarfi ba.
"Ina sonsa kuma shine wanda nake jin zan iya rayuwa da shi. Na rantse babu wanda ya isa ya raba ni da shi, in ba haka ba zan kashe kaina
"Shashasha! Wa ya damu don kon mutu. Kafin ke mutane nawa suka mutu akan soyayya kuma har yau ba a daina raba masoya. Ni da kaina iya siyo miki gubar kici ki mutu kuma ba zan fasa aura miki shi ba sai ku yi rayuwar auren a kiyama." Ta ce tare da juya ta kallo iyayensa ta ci gaba da cewa,
Kun ga ku tashi ku fice mini daga gidan 'ya kuka wani zauna ɗika-ɗika daku kun cika kujera."
Wani irin gigicecen ƙara ya saki ta nufi Huzaifah ta faɗa jikinsa.
"Ina son shi don Allah karku bari ta raba ni da shi don Allah dad, do something I love him." Ta ƙarashe maganar tana gurmusheshen kuka.
"A lallai fitsararki ta kai intiha a gaban iyayenki kike rungume ƙato? Ai ko ba ki ji kunyar ta da kika raina ba ka ji kunyar iyayenki. Mara kunyar banza kawai."
Huzaifah ya kama ta ya riƙe sosai shima kukan yake yi.
"Don Allah dad, ka yi wani abu ka sanya kuɗi ka aura mini ita I really love her and I can't do without her."
"Au ya sanya kuɗi an gaya muku mu ɗin matsiyata ne? Ko tirelal kuɗi za ku kawo ba zan aminta da auran na ba."
Dad ne ya ɓanɓare Jannah daga jikin shinya riƙe tana kuka sosai yayin da hawaye ya cik masa zuciya.
Wani irin haushin Hajiya Baaba ya ke ji kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ya huta. Sai yake ji a ransa kamar yabi maganarta kan ya rabu da mom ya ƙara aure in har hakan zai sa ta auri wanda take so, amma da ya tuna halin da mom take ciki da siyasar da ta faɗa, wanda dole tana buƙatar wanda zai ba ta kariya, don ko ita ba ta san ta sa kanta cikin tashin hankali ba. Sai ya ji ba zai iya ƙyale ta ba domin yana sonta yana jin ransa fansa ne a kanta. Yana son ta manta baƙincikin da ya sanyata na wasu tsawon shekaru.
"Ku ɗauki ɗanku kubar mini gida kar ya ƙara kiran sunan Jannah domin ina komawa gida za a sanya ranar aurenta." Ta faɗa a zafafe tananmusu kallon banza.
"Na shiga uku shikenan ta raba ni da shi Jannah ina sonki! Rabamu tamkar raba rai da gangar jiki ne ba zan iya rayuwa in babu ke ba." Sai kawai ya yanke jiki y faɗi a sume.
Ganin haka Jannah ta ruga ta faɗa jikinshi tana kiran sunan shi amma babu numfashi.
"Huzaifaaah!" Ta ja sunan tare da zubewa a kansa ta sume wanda ganin haka suka yo kansu da ruwa aka watsa musu.
"Kai amma 'ya'yannan sun iya shirin film ku gama shirin film ɗin aure babu fashi." Ta ce tana dariyar takaici, ta fice ba tare da ta damu da halin da suke ciki ba.
Tsananin mamaki ya kama su na rashin imaninta. Take dad ya fara tunanin anya ta san zafi da raɗaɗin soyayya? Ruwa suka wasa musu wanda sika farfaɗo kusan a tare.
"Dad, ta amince kuwa?" Cewar Huzaifah. Jannah kuwa kuka ta saka tare da faɗawa jikin dad.
"Ban san girman laifin da na yi mata ba take son aura mini shi."
"Ku yi haƙuri don Allah! Domin bamu da zaɓi wanda ya wuce mu bi umurninta. Ku kanku shedane akan rarrashinta da muke yi."
"Zo muje son na ga jikar na ta ba gwal ba ce da in ba ka aureta ba za ka mutu. Ka zaɓi wata macen ko 'yar gidan uban wane ne zan aura maka." Mahaifiyarsa ta furta cikin tsananin zafi tana hucin ganin ƙasƙancin da Hajiya ta yi musu.
"Duk abin bai kai haka ba kuyi haƙuri zan yi iyakan ƙoƙarina kan abin." Cewar dad cikin tausaya.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 29-30*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Mom kuwa ta kasa cewa komai tsananin tausayinsu ya cika zuciyarta. A ranta dana-sani take yi akan bijirewa umurninta na ƙin auren zaɓinta, wanda ba ta taɓa tunanin ko a duniyar mafarki za ta ɗauki fansa a kan 'yarta ba. Ga shi wanda ya isa ya yi mata dole babu shi ƙasa ta rufe idanunshi.
Ta ɗago idanunta tana kallon Huzaifah da ya kama ƙafafunta yana kuka ya ce,
Please help me, ina sonta ba zan iya rayuwa babu ita ba." Sai ta kasa ce masa komai idanunta suka kawo ruwa. Tana ganin mahaifiyarsa, ta ja hannunsa za su fice, wanda ganin haka Jannah ta bi bayanshi da gudu tana kiran sunan shi.
Da sauri dad ya kamata ya riƙe sosai yana rarrashi har sai da ya ji fitar motarsu. Kuka ta ƙara saki ta duƙa ƙasa.
"Yanzu shikenan, ta raba ni da shi? Kai ina ba zai yiwu ba!" Ta tambayi kanta tare da bawa kanta, amsa sai kuma ta ruga fa gudu zuwa ɗakin Hajiya.
Tibin dake bangonta sauke ta danƙarashi da ƙasa tare da watsi, da kwalaben turare da na kwalliyar show glass da suke ciki.
"Na ce bana son shi ko an aure dole? I dan laifi iyayena suka yi miki, ki yi musu hukunci, amma ba wai ki raba ni da wanda nake so ba!"
"Aikin banza in kin so ki fashe kayan gidan nan ko ki rushe gidan, ko a kwalar rigata don iyayenki kika yi wa hasara."
"Hajiya Baaba, ba kya sona kin tsane, kuma wallahi kin ji na gaya miki ko mutuwa za ki yi, ba zan aure shi ba." Ta ce cikin fusata jin abin da ta faɗa.
"Aikin banza kike don banga abin da za ki faɗa ya sani baƙiciki ba, saboda kin faɗi wanda ya fi wannan, kaffara dai ki shirya bayan bikin na rantsuwar da kika yi, ko da yake ina kika damu da addinin ballantana ki rama."
"To shikenan, tun da haka kika ce."
"Jannah ki iya bakinki mahaifi.."
"Please ki ƙyale ni don tana mahaifiyarki sai ta shiga rayuwata, ai duk ke kika ja mini inda kin tsaya kin kula da ni, da ban je gidanta ba har ta maƙala mini wannan auren." Sai ta sa kuka tare da zaman 'yan bori tana faɗin,
"Saboda ina gurin ki ne shi ya sa za ki yi mini auren dole. Na rantse ba zan dawo Zariya ba, domin na tsani zaman Zariya gara dad ya yi mini transfer na dawo Abuja da karatu."
"Au Allah ko? To ki sani ko London kika koma wallahi sai an ɗaura auren nan."
Tamkar wata ƙaramar yarinya ta ci gaba da ihu tana birgima a ƙasa. Sai suka rasa yadda za su yi da ita, suka zuba mata idanu domin hatta shi kansa dad, da ya matsota kuka ta ƙara saki tana matsawa ta ce,
"No! I said don't come closer to me, in har ba za ka iya hana auren nan."
Kamar umurni ta ba shi ya juya ya fita kanshi na sarawa domin shi kansa lamarin ya ishe shi.
Yana ƙoƙarin shiga cikin motarsa ya ji muryar maigadi yana magana da ƙarfi, wanda ya sa ya juya da sauri yana kallon gurin.
"Na ce maka ka ƙyale ni na shiga cikin gidannan, saboda ɗan'uwana Mudi yana cikin gidannan."
"Waye wani Mudi? Ma za ka ɓace domin bamu san wani Mudi ba."