Showing 132001 words to 135000 words out of 137802 words

Chapter 45 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Saboda tsabar kuka ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take wanda yake barazanar tafiya da numfashinta.




"Ina ga ya kamata mu kai ta asibiti she is convulsived."


"Eh haka ne na kuma siyo mata magani bari na kira Ajmal ya kaita." Ya ce yana ƙoƙarin kiran wayarsa, wanda bugu ɗaya ya ɗauka don a tunaninsa zai ce amfasa aurensa ne, amma sai ya ji saɓanin haka na kiransa, duk da hakan bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya zo yana addu'ar Allah ya sanya ayi masa albishir da fasa auren.


Da sauri ya ɗauki mota ya fice saboda Mushirat ta kira shi nan da awa biyu za ta iso Zariya ya je tasha ya ɗauko ta, wanda yake jin matsanancin tashin hankali saboda dole ya sanar mata don tana zuwa ɗakinsa, za ta nufa ga shi yanzu ya koma ɗakin Jannah an shaƙe shi da kayan da ya shiga sai da ya yi mamaki.


Yana isa ya same su a falo Jannah a kwance kan cinyar har lokacin ba ta daina hawaye ba tana ajiyar zuciya.


"Yauwa Ajmal, matarka za ka kai asibiti ba ta da lafiya." Cewar Aby fuskarsa a É—aure.




Ganin babu fuska ya ce."Ok, ta tashi mu tafi saboda zan je wani guri ne." Ya faÉ—a bayan ya gaida dad da ya masa cikin fara'a.




"Jannah, ma za tashi ki je ki sanya mayafi ku je asibiti." Cikin tsananin tsoro da rawar murya ya faÉ—a domin ya sam abu ne mai wuya ta amince.


Har ta buɗe naki za ta musa sai kuma ta ba su mamaki, ta miƙe bayan ta fakaici idanunsu ta galla masa harara wanda aka ci sa a ko kallon inda take, bai yi ba ballantana ya yi tunanin akwai wata halitta a gurin.


Da ta shiga É—aki a maimakon ta É—auki mayafi sai ta saka rigar sanyi kan doguwar rigarta ta saka hula tare da É—aukar wayarta ta saka a cikin aljihun.




'Dad, na shirya." Ta ce a sangarce tana jan majina, wanda gabakiɗaya suka bi ta da kallo har shi da ya ji kamar ya tashi, ya rinƙa kifa mata mari har sai ta je ta sanya hijabi.


"Haba Jannah, ke da kike jin sanyi ba sai ki saka hijabi ba." Cewar Aby yana nazarin fuskarta.


Kafin ta ce komai dad ya ce,"Go and wear hijab."


"Sun yi datti dama biyu ne duk gyale na ke da su."


"To ba sai ki ari na Nahlin ko Ummu ba."




"Ai ba na aron kaya." Ta ce ba tare da ta damu da tunzurar da suka yi ba, ganin duk inda suka ɓullo sai ta kauce.




Dad ya buɗe baki zai yi magana Aby ya ce,"Ƙyale ta je ki saka gyalen." Babu musu ta juya ta ɗako wani siririn gyale ta yafa iya kafaɗa, wanda shi dai bai ce komai ba ya miƙe yana mata wulaƙantaccen kallo.




"Sai kun dawo Allah ya yi muku albarka, ko Ummu ta raka ku?" Ransa ya ƙar ɓaci jin an ambaci ƙanwarsa ta raka su, wanda ya ƙara jin baƙincikin haɗa shi da ita da suka yi, fa yi nan an fara jawo masa raini wai Ummu ta raka su.


"A'a babu buƙatar haka, yanzu zamu dawo."


"To shikenan, sai kun dawo Allah ya yi muku albarka."


Shi kaÉ—ai ya amsa don ita ko kallon su ba ta yi ba ta fice.


Tana fita falon ta cire gyalen ta ƙudundune ta saka a aljihun rigar ya rage daga doguwar rigar sanyi.


Zuciyarsa ta kawo wuya ya ji tamkar zai yi hauka. Wani irin ƙululun baƙinciki ya taso masa ya zu wuyansa ya tokare shi bai wuce ba, kuma bai faɗa ciki ba.


"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ya ce yana kallonta ta madubi daidai lokacin da ta buɗe motar cikin isa da taƙama ta zauna a baya ta mai da shi direbanta kenan.


Tunanin yadda zai iya kallonta ya gaya wa mutane cewar wai ita matarsa to be ne duba ga shigarta ba ta da maraba da arniya.


"Anya iyayena sun san ni ɗin wane ne da matsayina aidanun duniya suke ƙoƙarin zubar mini da mutunci?" Ya tambayi kansa cikin ruɗani.


"Tsakanina dake Hajiya Baaba, Allah ya isa." Ya faɗa da ƙarfi tuna tashin hankalin da ke gaban shi.


"Dallah ni idan ba za ka yi driving É—in ba lemme know, ka sa ina ta sweating.." Maganarta cikin tsawa da son kuka suka doki kunninsa wanda bai san lokacin da ya juyo a sukwane yana mata mugun kallo.


Motar ya figa a fusace ya bar gidan wanda sai da suka yi nisa ya yi parking ya É—an jima ko mai ya tuna sai ya figeta a guje har suka shiga cikiin asibiti, wanda ko motsi ba ta yi ba ballantana ta hafimci me yake yi, saboda ta fishi iya gudu a mota.


Mushirat, cikin damuwa take kiran wayarsa wanda har ta yi ringing sau tari ba a É—aga ba, saboda ya manta da É—ayar wayarsa a falon Aby.


Adal da ke zaune da Ummita suna kallo a cikin falon hankalinsa ya kai gurin wayar da take ihu da neman agaji, wanda ya É—auka da sauri ya nufi gurin mom da take kicin ana haÉ—a abincin su mom da za su zo.


Yana gudu zai kai wayar ya haÉ—u fa Hajiya Baaba, da take sauri za ta shiga sashin Ammy don yin magana da Aby.




"Kai Adaluu, zo nan wayar waye a hannunka? Ka wo wayar maza kira mini Aby a waje.




Da sauri ya ƙarasa ya miƙa mata wayar."Ga shi ta Ya Ajmal ce, ina ga faɗuwa ta yi a aljihun shi kima ana ta kira."


Karɓar wayar ta yi wacce ta ƙara ɗaukar kuwa.




"Duba ka ga wane ne ke kiran maza ɗaga ka gaya masa baya nan." Ta ce tana miƙa masa wayar.




Ganin an rubuta matar kirki ya sanya jikinsa ya ba shi Mushiirat ce, amma bai ce mata komai ba ya É—aga wayar da sallama.




"Hello Anty Mushiirat, Ya Ajmal ba ya nan ya manta da wayar a gida sun fita da Anty Jannah."




Wani irin faɗuwar gaba ta ji har sai da kunnuwanta suka daina aiki na ɗan taƙin lokaci.




"Lafiya mai ya faru da Jannah? Kuma mene ne haÉ—insa da ita da zai su fita?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin ruÉ—ani wanda ba ta san ta fito waje ba.




Karaf sai a kunnin Hajiya Baaba, da har ta juya za ta wuce.


"Miƙo mini wayar nufinta ba ta san za a yi auren ba ko me? Oh tsoron da yake mata ya sanya shi kasa gaya mata kenan, ai shikenan bari na hutashshe shi." Ta ce tare da karɓe wayar.




"To isashshiya matar gwal! Waton tsoron ki da yake ji ya kasa gaya miki saura kwana biyu ya angwanje da yar'uwarsa Jannah."


"Aure, Jannah kuma?" Ta furta cikin tsananin mamaki da ƙarfi.


"Mamaki kike yi? Sai ki bari zuwa gobe ki tabbatar idan kin ga an kawo miki ita a gida..."


"Haba Hajiya Baaba, wannan ba girmanki bane ki bari ya gaya mata don Allah kar ki ɓata lamarin." Cewar Ammy cikin tsananin ɓacin rai wacce tazo wucewa ta ji tana faɗa mata hakan.


"Dallah, kauce ki ba ni guri in yana tsoronta kamar uwarsa ai shi ya sa na hutashshe sh..."


"No!" Ta ce da ƙarfi tare da sakin wayar ta toshe kunnuwanta da hannunta jin muryar Ammy tana magana wanda ya tambatar mata tatsuniyar da take gaya mata gaskiya ne.


"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Na ba ni na shiga uku Allah ka ɗauki raina na huta. Da gaske zauji zai yi aure ba tare da ya gaya mini ba, wannan ita ce maganar da yake sanar fa ni zai gaya mini. Ashe duk tsauri da jan ido da yake mata soyayya yake da ita a ɓoye? Yarinyar da na tsana fiye da mutuwata."


Ta ce tare da nufar titi tana suratai tamkar wata mahaukaciya.


"Wallahi haka ba zai taɓa yiwu ba, zan iya danne kishina ya auro ko wace mace amma ban da ita."


Kamar wata zautacciya sai ta kuma dawo gurin da ta watsar da wayarta ta É—auka wace har ta tsage tana neman numbar mahaifiyarta.


"Ka cuce ni ka ci amanata Allah ya isa tsakanina da kai tun da har za ka iya haÉ—a baki da 'yan gidanku ka uri 'yar'uwarka ba tare da na sani ba, saboda mahaifiyarta tana fa kuÉ—i ko?" Ta yi tambayar kamar yana gabanta.


Sai kuma ta dawo inda ta yar da wayar ta ɗauka kamar wata taɓaɓɓiya ta nemi numbar mahaifiyarta wacce ta ɗauki wayar ba tare da mata lokaci ba.




"Mama, kin ji Ajmal zai yi aure kuma yar uwarsa wannan fitsararar?" Ta ce cikin tashin hankali tana kuka wanda hakan ya tada hankalin mahaifiyarta ta fara kiran sunanta.




"Shi Ajmal ɗin? Yuashe kuma wace ƙanwarsa?"Ta jera mata tambayoyin cikin tsananin ruɗani.


"Ba zan iya gaya miki ba domin ban san halin da nake ciki ba, sai dai ina jin rayuwata ta ƙare domin ba ta da amfani sam ban ga amfani samun girman da na yi ba, duba ga cin mutuncin da ya yi mini aure fa zai ƙara aurenmu ko shekara bai rufa ba."


"Kina ina ne Mushirat, kin sauka don Allah ko natsu ki kaantar da hankali."


"Ajmal ka cuce ni saninka bai yi maka amfani ba rayuwatavta ƙare mama, ki turo Ya Najib ya zo ya ɗauke ni ina tasha ba zan iya tarar abin hawa ba, dama mun yi da shi zai zo ya ɗauke ni amma ya tafi kai ta asibiti." Ta ce ba tare da ta lura titi take nufa tana maganar ba sai kawai ta ji ana faɗin "Ke!Ke!!." Wanda ya sa ta yi sauri ta waigawa tare da ɗora hannu a sama ganin ƙatuwar mota ta tunkarota gadan-gadan.




Mom tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa ƙauyen. Ɗaukar matar da jarirai suka yi wanda kai tsaye asibiti suka wuce ganin yadda suke cikin mawuyacin hali.




Bayan an duba matar da ɗaura mata jini sannan ta biya tare da bada maƙudan kuɗi da za su kula da kansu.


Saboda tafiyar da za su yi ba ta wani jima ba suka kama hanyar Zariya.


Sun É—an yi tafiya mai nisa suna tafe suna hira da Mujee.


"Inyaa!Inyaa!! Inyaaa." Suka ji kikan jarirai a cikin bayan motarsu wanda ya sanya suka saki salati tare da waigawa.


"Innalillahi! Mun shiga uku. Jariran 'ya'yan aljanu muka É—auko a bayar motar?" Mom ta tambaya cikin tsananin tsoro da tashin hankali.


Da sauri direba ya gangara ya yi parking zuciyarsa cike da tsananin tsoro da mamakin yadda aka yi jarirai a cjkin motar, wanda ya tabbatar da 'ya'yan jarirai ne.


Cirko-cirko suka yi sun kasa isa gurin boot ɗin motar ballantana su yi ƙoƙarin buɗewa sai zare ido suke yi.


Direba ne ya yi namijin ƙoƙari ya ƙarasa jikinsa na kyarma ya buɗe boot ɗin tare da rintse idanunsa kar ya ga aljanu, wanda tun yana yaro ya san cewar duk wanda ya ga aljani kwanan shi ya ƙare.


"What!" Mom ta furta cikin tsananin mamaki tana kallon yaran da suke cikin kwali suna canyara kuka.


"Mujee, this is absolutely impossible! WaÉ—annan ba yaran da muka kai wa mahaifiyarsu taimako ba ne."


"Mun shiga uku, wallahi sune garin ya akai suka shigo cikin motar nan."


Mom da gumi ya jiƙata sharkaf ta share zufar zuciyarta saboda bugawa tamkar za ta sinke, domin ta gane sharri za a ƙulla mata.


"Someone is behind this Mujee, sharrin maƙiya ne, kuma da makusancina a ciki. Shikenan, rayuwata ta ƙare na shiga uku."


"Tabbas sharrin abokan takara ne Hale.."


"A'a duk wanda ga aikata wannan ya san da duk motsina na jikina n..."




Ajmal kuwa, suna isa cikin asibitin ya fahimci ya manta da wayarsa wanda ya tabbata a falon Aby ya ciro ta domin ya yi chatt da Mushiirat.






Da sauri ta ɓalle motar ta fito da sauri ganin ya fita burinsa ya rigata shiga karsu jera tare, wanda ta gane lagonshi ta haɗa da sauri ta isa gare shi tana kallonsa suna tafiya.






Tamkar ya shaƙeta haka ya ji ga kunyar yadda mutane suke kallon shi duk da sun san 'yar'uwarsa.




"A'a Ya sheshk, kai ne haka da yammar nan?" Cewar doctor Irfan yana kallon Jannah da ta shigo a bayansa.




Ba bu wanda ta kalla a cikinsu ta samu guri ta zauna tare da fito da wayarta tana kallon tiktok duk matsanancin zazzaɓin dake damunta amma burinta ta ƙuntata masa.




"Madam ce ba lafiya?" Ya tambaye sa ganin tun da ya ba shi hannu ya kasa ce masa komai domin zuciya ta tuƙo shi.




Bai tanka masa ba haka Jannah ba ko kalli inda Irfan yake ba.




Ganin haka ya ɗauko abin gwajinsa ya fara duba ta yana kallon yadda take kallonsu a wulaƙance.




"Zazzaɓi ne mai zafi ya kamata kuma ta saka damuwa a ranta. Zan ba ta magani sannan za a yi mata allura guda biyu har na tsawon kwana uku."




Wani irin zabura ta yi ta miƙe tare da ja baya domin idon akwai abin da ta tsana be wuce allura ba, don ba ta yi tunanin zai ce zai yi mata allura ba da ba ta zo ba.




Murmushin mugunta ya kubce masa ganin ya gano lagwanta daidai lokacin da ta ce,"Kai mugu don't inject me, just give me meds." Ta ce tare da bayyana tsoronta a fili.


"Ba ki da kunya ko? Irfan ka haɗa mata duka allurar, saboda ka san jibi ne bikinmu cin amarci ba zai bari muzo ba." Ya ce fuskarsa a murtuke wanda ya sanya ta daka tsalle ta miƙe tana mazurai.


"Haba, sai ka ce ba ka san yadda ake allura, dole biyun É—in za a yi mata inyaso na zo gida na arasa mata sauran."


"Na rantse babu wanda ya isa ya yi mini allura sainka ce wacce ta zo a sume da ƙafafuna na zo ni na ma daina jin ciwon na warke." Dariya ta so ta kubce wa Irfan ganin yadda ta tsorace tana mazurai.










Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
























KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)



















Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 37-38*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"Ba ke iskanci da taɓara ba, kin ciwon ƙarya kina ta zuba iskanci sun biye miki, zan yi maganinki."


"Ma za Irfan haÉ—a ruwan allurar." Ya ce yana nannaÉ—e hannun rigarsa.


"Wayyo na shiga uku! Dad zan kira na sanar masa don ba zan yarda a yi mini allurar ba." Ta ce tana ƙoƙarin kiran dad wanda ya wafce wayar ya aje kan kujera, ya sanya hannunsa ya damƙota da take ƙoƙarin ficewa da gudu.


Wani irin ƙara ta canyawa wanda ya sanya har ya sake ta ya ƙara damƙota da hannunsa ɗaya yana toshe kunninsa tare da ɗaga hannunsa zai mareta.


"Ba ki da hankali ne za ki ƙwala kamar mahaukaciya?"Ya ce cikin zafi da tsawa.


"No, please karka duƙeta ka ka yi haƙuri, ka san akwai waɗanda suke tsoron allura.


"Ƙyale ni Irfan in har ban duketa ba, ba zan ji daɗi ba. Za ayi mata allura kamar za a kasheta. Mushiirat da kanta take yi wa kanta allura, sai ita za ta zauna tana buɗe baki."


"Mushiirat, babba ce ita kuwa wannan da ƙuruciya."


Tsaki ya yi ya ƙara damƙota da ƙarfi sosai." Caka mata allurar sauri nake yi, in ta ƙi bari ka karya allurar a ciki."


Wani irin ihu ta ƙara saki sosai take kuka duk ta cika ofis ɗin da ihu da ƙara.


Lokacin da ya tsira mata allurar sai da ta yi wani irin ƙarar da ya fi wancan, wanda haushi ya sa ture ta ta faɗi ƙasa.


"Abin da nake gudu kenan, a haÉ—a ka da yara suyi ta maka hauka. Jibi abin da take yi wannan haukar."


"Walllahi Allah ya isa kuma saina gaya wa dad mugaye kawai." Ta ce cikin muryar kuka tana taɓa inda aka yi mata allurar.


Da sauri ya ƙarasa guri ta zai ɗauke ta da mari." Haba, don Allah karka biye mata."


"Ka na ji fa zaginmu take."


"Ka kyaleta ku dubi yadda ta yi har cikin zuciyarta ba ta son allurar."


"Allah ya sa ya zama ajalinta."Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login