Showing 90001 words to 93000 words out of 137802 words

Chapter 31 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

"Aikin banza don ihu kike bayan hari aure sai dai ki ɗauki haƙuri da azaman yin biyayya don kin san kalar mijin ya jibge ki ba farau bane a garesa."



Ihu ta sa tana girgiza kanta." Kin ga Hajiya Baaba ba dake nake magana ba, domin tun da iyayena suka dawo babu ruwana dake."




"Au haka za ki ce, bayan na gama miki amfani ko?"




"Dad." Ta furta da ƙarfi tare da yin sashin da yake wanda har bacci ya fara kamasa.




"Muje ka gaya mata ba za ka amince da auren nan ba domin she is frustrating me da maganar."




Zare ido ya yi sai kuma ya kalli agogo."Please ki je ki kwanta za mu yi maganar sa safe.."






"No way." Ta katse shi tare da kama hannunsa tana ja.




"You must go and tell her, so that she will not be pestering me."




Jikinsa babu ƙwari ya bita har zuwa falon da murya Hajiya Baaba kawai ke ta shi.




Wani banzan kallo ta watsa mishi lokacin da ya shigo.




"Ai ni na ɗauka 'yan sanda za ki ɗauko mini sai kika tsaya anan, to sai ya ɗauko bulala ya zane ni."




"Ki yi haƙuri ba ta kai nan ba, amma don Allah ya kamata abi abun.."




"Ya kamata mene? Kai Jabiruu kake ko mene? Wallahi ka fita idona tun kafin na shuka maka rashin mutunci, domin ka san ina da cikinka na tsawon shekaru."
"Allah ya ba ki haƙuri."




"Oho, ko ma me za ka ce ka faɗi aure dai babu fashi, in kuma za ku nuna mini iyakata bismillah."






"Dad, ka na nufin kai ma ba ka isa da kanka ba sai abin da ta ce?" Ta yi mishi tambayar cikin tsananin mamaki.




"Ba ki san cewa ni dakali ba ne dole a zauna dani. Ai girman kenan tun da na haife su ai dole abi umurnina."




"Ina wallahi ba zan yadda ba ina ji ina gani ayi mini auren dole." Ta ce tare da kai wa tibin bangon falon duka, wanda nan take gilashin ya tarwatse hannunta ya fashe.




Sai kuma ta sanya kuka ta na jin yadda zafin raɗaɗin ciwon yake tasowa yana bin duk ilahirin jikinta.




"Wallahi ba na son shi. Ko a duniyar mafarkina ban taɓa tunanin auren mutum irin sa ba. I really hate him please dad do something if not I gonna die. How can I marry a such person like him?" Sosai take kuka ta faɗa kansa wanda hakan ya sa ya ji tausayinta ƙwarai to amma ya zai yi.




Kamota ya yi a hankali ya miƙar da ita ya zaunar da ita har zuwa lokacin ya rasa kalmar da zai rarrasheta da su, saboda sam baya ƙalubantar auren domin auren miji kamarsa ba ƙaramin tagomashi Allah ya yi mata ba.






"Hajiya Baaba, na san na saɓa miki arayuwarki kuma na yi butulci amma don Allah ki bari ta gama karatu kuma su fahimci juna, kin san suna da bambancin ra'ay.."




"Au wa'azi za ka fara ai ban sani ba, amma da ka je masallaci ka hau munbari domin an fi buƙatarka. Har kana da bakin da za ka yi wa wasu wa'azi?"




Sunkuyar da kanshi ya yi lokaci guda hawaye suka fara turereniya akan fuskarsa da take cike da haiba da kamala, yayin da yake nadamar abubuwan da suka faru a baya.




Cikin tsananin tashin hankali ta nufi inda Hajiya Baaba take tana girgiza da huci domin wani mugun haushinsa take yi kamar ta shaƙe shi in ta nuna irin abubuwanda ya aikata ya zama kura da fatar akuya..




"Ban san wane irin mutum ce ba kin takurawa kowa kin hana mu sukuni bayan kin ci lokacinki babu wanda ya takura miki, ba sai muna cikin rayuwarku za ku takura mana ba?"




Sai ta kama hannun dad ta riƙe cikin ɓacin rai ganin yadda yake zubar hawaye.






"Ka saki mom ka ƙara aure mu yi rayuwarmu cikin farinciki I hate them dad."




Gabkiɗayan su suk zaro ido har da su Aby da hayaniyar ya sanya suka shigo.






"What! Are you insane? Mahaifiyarki kike gaya wa mahaifinki ya sake ta? Cewar Nahlin kamar ta tsinka mata mari.




"Yes I do. Auren su babu abin da yake ƙara mini sai baƙinciki don haka rabuwarsu ya fi, kin ga sai na ga uban da ya isa ya yi mini auren dole."




Mom wacce tun da jannah ta ji ciwo take kuka sosai damuwarta jinin da yake zuba a hannunta.




Kau ta wanka mata mari."Ki iya bakinki in kika yi mini rashin kunya na ɗauka ba zan lamunta gareta ba." Ta faɗa cikin kaukausar murya.




Rintse idanunta ta yi."Ni dai wataƙila ba zan taɓa samun farinciki ba, ga shi na gudu don na yi farinciki amma kuma na dawo an ɗora daga inda aka tsaya."




Sai ta ƙara sakin kuka ta nufe ta."Mu tafi asibiti jini kika zubarwa."




"Fisge hannunta ta yi cikin kuka."Go away, I hate you." Ta ce tara da riƙe hannun dad.






"Taɓɗijan! Lallai kin yi sake Halimatuu. Auren ta da shi shine kawai maganinta domin ya ci mini ƙaniyarta in ya so ya kakkarya mini ita akawo ba su Binbo ƙasusuwa."






Wani mugun kallo ta yi mata tare da jan majina daidai lokacin da dad ya kamata hannunta suka fita daga falon.




"Kai Jannah an yi fitsarrariya." Cewar Hajiya ta galla wa mom harara ta shige ɗakinta.




Faɗawa jikin Aby ta yi ta fashe da kuka."Haƙiƙa Allah ka jarabce ni! 'Yata ɗaya tilo take sanar da mahaifinta ya sake ni ya auri wata? Ni kam mai na yi wa duniya take gara rayuwata kamar ƙwallo."




"Ki yi haƙuri Halimatuu, ka da ki yi saɓo." Ya furta tare da kama hannunta suka yi sashinsa.




A sashin Ajmal dad ya zaunar da ita cikin ɓacin rai ya kalle ta sai kuma ta ƙara ba shi tausayi, amma da ya tuna kalamanta zucigarsa ta ƙara tafarfasa.




"Haba Jannah, I really hate the way you talk to your mom honestly I dislike it you are so insolent to her."




Ya juya mata baya yana jin kamar ya mareta daidai lokacin da ta ƙara sakin kuka.






" So now, you gonna tell me you wanna side her? Tana jin munanen kalamai da mahaifiyarta take gaya maka amma she sat and looking her becouse ba ta ɗauke ka da mahimmaanci ba."






Kama hannunta ya yi ya riƙe yana ya rasa yadda zai yi ta fahimce shi domin ya na ganin aminta da auren shi zai daƙile bankaɗar da Hajiya Baaba take son mishi, wanda in har ta ji ya san daga ranar ba za ta ƙara kallonsa da daraja ba.




"I really don understand cus the whole situation is akward." Kuka sosai take yi sai kuma ta faɗa jikin shi ta ci gaba da cewa,




"Na tsane shi wallahi ba na sonsa ban taɓa hasashen rayuwa da shi ba, a kwai wanda nake so and we are compatible dad, please do something."
Idanunsa ya zaro cikin tsananin mamaki." So you mean you are dating someone without my awareness, how could you?"




Cikin jin kunyar abin da ya faɗa ta rufe fuskarta."Am deeply sorry dad, initially he was my best friend, but later I found him very valuable to my life and we fall in love. Mun haɗu ne a faling jirgi a ranar da na dawo Nigeria."




Sai ya yi shiru yana saurarenta da mamakin ɓoye masa da ya yi domin bai taɓa tunanin hakan ba.






"I said am sorry for hiding it, but ina son shi kuma he is well off haka iyayensa they are prosperous. In har ta nace na yi aure ta aura mini shi."




Sai ta yi matuƙar ba shi tausayi matuƙar gaske saboda yadda take maganar ya fahimci tana matuƙar son shi.




"But please stop talking to your mom in that manner, you shouldn't talked to her in that tongue."




Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba ya fora da cewa,




"You have to go and sleep we will talk about it kin ji." Ya fada Yana shafa kanta.




Dukkan mutanen gidan ba su bacci cikin kwanciyar hankali ba sakamakon ko da abin da yake saƙawa a cikin ransu.




Washegari da safe ko da ta farka, babu wanda ta yi wa magana hatta dad domin shi kansa haushi yake bata don ko karyawa ba ta yi ba ta fice.




Mom da ta kwana kuka sai bayan kiran sallar asuba bayan ta yi sallah bacci ya ɗauke ta wanda ba ta tashi ba sai tara. Wanka ta yi ta sanya doguwar riga ta fito falo don ta karya.




Ta yi sallama ta shigo cikin falon tana kallon dad da yake zaune a gefen Aby suna suna hira.




Ido ya raka ta da shi har ta ƙaraso kusa da shi ta zauna a gefen kujear da yake zaune cikin murya mai sanyi ta gaishe shi, ba tare da ta jira ya amsa ba ta fara gaida Aby.




"Ina ga yau zan wuce Abuja fa saboda gobe akwai taro da zan halatta."




"Aiko ba ki isa ba daga zuwanki ina murna." Cewar Hajiya Baaba da ta fito daga ɗakinta.




"Dole na tafi Abuja akwai abubuwan da zan yi, ki yi haƙuri da na kammala zan zo."




"To kiyi mini wayon Halimatuu, yau aka fara kefa a koda yaushe ba ki da lokacin kanki ballanatana na ahalinki, in kika na ce za ki tafi sai dai na biki domin dama ba wani daɗi na ke ji a gidan ba." Ta yi ƙuta tana faɗin haka.




Dukkanninsu ba su ji daɗin abin da ta ce ba musamman Aby da ya san matarsa na iyakan ƙoƙarinta, kawai tsana ce da ƙiyayyar da ta ke mata.
"Amma Hajiy Baaba, in kika..."




"Rufe mini baki shanyayye kawai! Da ma kai ai bayanta za ka bi tun da ta wanke ta ba ka ka shanye."




Shiru kawai ya yi yana girgiza kansa cikin ɓacin rai idanunsa sun kaɗa sun yi jajir.




"To shikenan, zuwa anjima za mu tafi har da kai ko Ya Muhammadu za ka bimu akan maganar nan?"




"Eh ya ba ta amsa yana ɗaga masa kansa.




"Ina ga a shirya tafiyar duk gida sai suje su ga gida ko?"




"Ai kuwa hakan ya yi sosai zan so hakan." Mom ta ba Aby suka faɗa cikin fara'a.




"Jannah da Ummu suna school sai a jira su." Cewar Aby.




Ɗaga masa kai ta yi ta ci gaba da duba tsaƙonnin wayarta, har ta zo kan tsakon da aka turo anonymous kamar haka




"Ina miki murnar dawowa ƙasarki da kika gujeta na tsawon lokaci, sannan ina miki murnar tsayawa takarar minister, amma ki sani burinki ba zai taɓa yiyuwa ba matuƙar ina numfashi domin nine ajalinki."






"Innalillahi wa inna ilahir raju'un." Ta furta cikin kiɗima tare da zazzaro ido.




"Subuhanallahi mai ya faru?" Gabaki ɗayansuka haɗa baki gurin faɗin haka tare da miƙewa a razane.




Fiffita ta fara yi da hannunta take zufa suka fara karyo mata. Ji ta yi yawun bakinta ya ƙafe.




"Halee, lafiya?" Cewar dad da ya kama hannunta cikin kiɗima.




Cikin dubara ta fita daga mesages ɗin don kar su gane abin da ya sanya ta razana.




"Im ok, rasuwar wata mar lafiyarmu na ga ni ya kiɗani." Ta samu kanta da gindira musu ƙaryar saboda ba ta san me za ta ce musu ba musammman dad da baya supporting ɗinta.






"Allah ya jikanta ya gafarta mata ai mutuwa is inevitable price, kowa sai ya ɗanɗani ɗacinta." Cewar Aby.






Tun daga lokacin sai ta nemi natsuwarta ta rasa duk bayanin da suka mata ta kasa fahimta ƙarshe miƙewa ta yi ta shige cikin ɗaki ta kulle kanta.






"Waye wannan, mai na yi masa kuɓa mai na tsare masa?" Ta furta cikin tashin hankali tana safa da marwa a ɗakin.






Ƙara duba text ɗin ta yi tana ƙoƙarin goge komai ta da son mata tsakon kiran Hajiya Turai ya shigo wanda ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba.




"Hello, uwa ba da mama." Ta furta bayan ta yi sallama.




Amsa sallamar ta yi ba tare da ta ce komai ba ta yi shiru.


"Wannan matar ce wanda na gaya miki ta zo neman taimako, amma ta ce dole ke take son gani, yau ma ta ƙara zuwa bayan tsawon lokacin da ta ɗauka ba ta zo ba."




"Ok, ki gaya mat gobe ta dawo kamar wannan lokacin za ta same ni." Tana faɗin haka ta kashe wayar yayin da zuciyarta ta karkata tunanin wacce mata ce.




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login