Showing 120001 words to 123000 words out of 137802 words

Chapter 41 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

don ya harzuƙa.


"Hello Ajmal, where are you?"
"At home dad, ai na zo gidan you were in ofis."


"Ok, can you come? We need to talk."


"Lafiya Aby?" Ya tambaya jin murya sa wani iri.
"Lafiya lau sai ka zo." Ya kashe wayarsa yana tausayinsa.


Ajmal ya juya yana kalon Mushiirat da ta fito daga ɗaki cikin riga da wando iya gwuiwa rigar kamar singeleti.


"Zauji, ya ka gani? I told you it would fit me sosai."


Tsayuwar da ta yi masa ya tafi da imaninsa domin cikin jan hankali ta yi da gantsarewa.


"Wow you look amazing and nice in that outfit, ashe na iya zaɓe."


Dariya ta yi tare da rungume shi tana faɗin,"I told you."


Juyo da ita ya yi yace,"Kin yi kyau sosai ɗin nan fa matar kirki, musamman hibs da waist ɗinki sun ɗauki kayan."


"Allah ko?" Ta ce tana canza tsayuwarta har sai da ya ɗauke ta hoto da yawa.


"Eh, Aby ya kira ni yanzu, I'm thinking is urgently lemme go, I will be back soon, na ɓata gayun nan don ya tsokale ni."


Dariya ta yi ta kashe masa ido."Ok, waiting don Allah ko na biyo ka."


"No, za a yawo ko?" Ya ce tare da ficewa don kar ta ƙara ce masa komai domin baya son ta san da maganar auren Jannah sai komai ya warware.


Tsayawa ta yi a bakin ƙofa tana kallon shi har ya fita ta ƙara sakin murmushi ta koma ta zauna tana begen sa.


Ajmal kuwa, a hanya yana ta tunanin kiran sai ya ji gabansa ya faɗi tunawa da bai gaishe da 'yar mulki ba, wanda zuciyarsa ta zargi akan shi ne.


Ko da ya shigo bai leƙa sashinta ba kai tsaye shashin iyayensa ya shige.


"Abby, ga ni ina ta tunanin lafiya." Ya ce tare da zama a gefen kujerar da yake.


"Lafiya lau, kuma ni da ɗana don ya yi auren ya yi nisa dani ba zan kira in na so na ga ganshi ba?"


Dariya ya yi yana shafa kansa jin tsokanar da ya yi masa."Ba haka bane Abby, I was thinking something differently."


"To zauna ka natsu na so na ganka kuma a kwai maganar da za mu yi."


"Ok."Ya ce tare da ije wayarsa da take hannunsa ya tattara dukkan hankalinsa, ya mai da ga mahaifinsa ganin yadda shi ma ya yi serious ya san dama dole akwai wani abu, sai yana addu'ar Allah ya sa alkhairi.


"Ya maganar da muka yi shekaranjiya akwai update?"


"No, Abby amma har yanzu ina addu'a ban cire rai ba." Ya ce tare da zaƙuwar ya je direct to streat point ba ya tsaya kwana-kwana ba.


"Ok, Allah ya sa mu ji alkhairi."


"Amin." Ya amsa zuciyarsa cike da zaƙuwar jin musambabin kiran.


"Da ma na kira ka akan maganar auren ka da Jannah, an saka rana wata uku." Ya yi ƙarfin faɗin hakan domin tsoro da rawar murya ya ji.


"What Aby! Ni Jannah aure na ga gaya muku ba na sonta kuma ba zan aure ta ba."


"Calm down, and be matual Ajmal." Cewar Ammy da ta daga shi ganin yadda ya miƙe a razane jijiyoyin jikinsa suka tashi.


"No Ammy! Na gaya mata bana sonta, lafiya nake zama da matata, ban ga dalilin da zai sanya na ƙara second wife ba. Besides that ,am not interested in her so there is no way." Ya ce cikin ɗaga murya wanda har ya sanya su Jannah da suke ɗakinsu suka ji.




Zubbur ta miƙe kamar wacce aka tsikara."Rana ni da Ya Ajmal, aka sa? Ai dama wannan fitinanniyar tsohuwar ba ta bar maganar auren nan ba?" Ta ce tare da fara hawaye sai ta ruga sashin Hajiya Baaba tare da ta damu da kiran da su Ummu suke mata ba.




"Mene ne haka? Muna magana cikin sirri za ka ɗaga murya kowa ya ji.Tabbas yanzu aka sanya ranar da Jannah, kuma yadda ta nuna aure babu fashi, domin ko ƙwandala ba ta bari na biya ba."




"Ba zan amince ba, tun da bana so ai ba a aure dole, don haka sai ta janye sa ranar nan." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin ya yi sashinta ba tare da ya damu da kiran da suke masa, wanda suka rufa masa baya.




"Kin san Allah saimkin janye sa ranar nan, saboda na fita harkanki ko kallonko ba na yi don me kuma za ki dage sai an yi bikin."


"Don ubanki to za ki buge ni, ko ki tsare ni a fasa. A tunaninki shiru da banzan da na yi muku na ƙyale ku ne? Habawa yara sai ka ce ba ku san wace ce ni ba."


Ta ce tare da wafce rigarta da ta riƙe wanda ta sa kuka da faɗuwa ƙasa tana birgima.


"Ki fasa aurenan, na ce bana son shi in ba haka ba, saina sha guba na mutu."


"Kisha gubar bera in kin so, iyayenki kika yi wa asara ba ni ba." Ta ce daidai lokacin da Ajmal ya buga kofa da ƙarfi Yana huci ya shigo.


"Hajiya Baaba, tun ina miki mutunci ki janye maganar aurennan, domin ina da matata mai tarbiya babu yadda zan yi na auri jikarki fitsararriya."


"Au haba mai hurul ain, ai ba ka gaya mini matar taka daga sama aka sauko maka da ita ba saboda malinta, da ban damu kaina na aura maka wannan mara mutuncin ba, amma ka ga yanzu ka makaro sai dai a guji gaba. "


Ta ce cikin gatsali sai kuma ta ɗora da cewa, "Kana maganar ita mara tarbiya ce, kai kana da tarbiyarne kake tarar gabana ka gaya mini abin d ka ga dama. Idan iyayenka ne suke magana za ka musa musu? Kai Adamuu, inda zan fayyace wa duniya abin da kake yi wallahi in ka hau mumbari za yi wa'azi da dutsuna za a wartako ka. Shashashu kawai marasa mutunci a tunaninku tabon da kuka yinmini ƙyale ku zan yi? Ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha."


"Oho, koma me za ki ce ki faɗi amma ba zam auri wannann bagidajen ba, domin ina da saurayina ɗan gayu ba irinsa da ya tara gemu kamar na buntsu..."


Wani wawan mari ya zabga mata."Ke wallahi saina yi ajalinki yanzu nan, mara mutunci kawai ba duk abin da yake faruwa ke kika ja ba, saboda rashin tarbiyarki da fitsara." Ya ce cikin zafi tare da ƙoƙarin neman bulala domin wani irin haushinta yake ji yana dana-sanin dawowrta gidansu.


"Ka kasheta in ka so kaso ka ga sai kaima a kasheka, ka na huta da jarabarku amma aure babu fashi." Ta ce tana karkaɗa ƙafafunta ba tare da ta damu da dukan da ya ke mata ba, wanda ta canyara ƙara ta ci gaba da birgima, domin ta san ya yi haka ne don ta fasa auren.


"Kai Ajmal, in ka ƙara kai hannu gareta saina tsinka maka mari."Cewar Ammy da ta ke bayan Aby ta ƙarasa gurinta ta miƙar da ita tare da riƙe ta tana rarrashi.


Aby kuwa ƙarasa gurin shi ya yi ya ɗaga hannu zai tsinka masa mari sai ya ga rashin dacewar hakan ya fasa tare da sauke hannunsa.


"Ba ka da hankali ko? Dukanta za ka fara ka nuna mana abin da za ka yi in an kai ta ko, kana malami aana dukan matar da za ka aura?"




Sai ya juya gurin Hajiya Baaba da ke tsaye ko a kwalar rigarta."Hajiya, kin ga abin da za ki haɗa ko?"


"Ka bar shi ya kashe ta sai ya ƙara rayuwarsa a zaman kurkuku." Ta ce tare da shigewa ɗakinta ta barsu tsaye tamkar haƙora.




Aby ya kama hannunsa suka nufi sashinsa yayin da Ammy ta kama hannun Jannah da take kukan mari da saka rana suka tafi.


A ɗaki ya sashi ya nuna masa ɓacin ransa sai kum ya yi masa nasiha ya kuma koma rarrashi.


"Abby, wallahi bana sonta na tsaneta, ban taɓa tunanin ko mafarkin na yi rayuwar aure da ita ba, in kuma aka ƙulla auren nan akwai cutarwa, domin ƙyamarta nake saboda na tsani macen da za ta saka attach ko sau ɗaya ne, kuma ka san yadda nake nuna wa abu tsana in na tsane shi." Ya ce yana kallonsa ko zai ce wani abu sai ya numfasa ya ɗora da cewar ganin bai ce komai b.


"Ina matuƙar zaman lafiya da matata, an shiga haƙƙinta da tozartata na sanya ni na ƙara aure ko shekara bamu rufa ba. Tana matuƙar darajani amma ita zagina take a gaban kowa za ta sanya matata ta raina ni. Don Allah Aby, ka yi wani bu akan auren na, in ta nace sai na yi aure zan iya ƙarawa da mata masu mutunci da tarbiya, amma ba Jannah ba." Ya ƙarashe maganar hawaye suna zubowa a kan fuskarsa.


"To shikenan, zan ƙar mata magana da turo wasu mu gani ko za ta yarda ta janye ta shi ka tafi gida, amma kar ka ƙar kuskuren kai mata duka hakan ya saɓawa addininmu. Kuma duk wanda ya ji haka mutincinka zai zube."


"Ka yi haƙur zafin zuciya ne, ni kaina ban san lokacin da nake kai mata duka ba. Ina girmama mata bana son wani ya ci musu mutunci."


"Allah ya yi maka albarka maza tashi ka tafi gida."


"To." Ya miƙe kamar wani ƙaramin yaro ya fice zuciyarsa na suya.








Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093












KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 33-34*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


"To." Ya miƙe kamar wani ƙaramin yaro ya fice zuciyarsa na suya.


Jannah kuwa duk irin rarrashin da Ammy take mata ta ƙi yin shiru sai zunduma ihu take yi.

Da ƙyar da siɗin goshi Aby ya samu ya shawo kanta bayan ya yi mata ƙaryar ba za a yi bikin ba, wanda ta yadda ta sha paracetamol ta kwanta sai bacci.

"Auren nan na su babu fashi sai dai su yi haƙuri, yanzu dai bari ita Jannah ta gama jarabawa ka da maganar auren ya sa ta samu matsala, kuma kin san ta da kafiya tana iya cewa ba za ta yi jarabawar ba."

Bayan ta gama jarabawar mahaifinta za ka sa yazo shine kawai ƙila ya ci ƙarfinta, saboda ka san yanzu ko wayarsa ba ta ɗauka kuma duk akan maganar auren ne.

"Kai Hajiya Baaba, haƙiƙa ta ɓullo da inda za ta rama abin da muka yi mata cikin ruwan sanyi. Wallahi ba ki gani ba Ajmal hawaye yake mini akan a fasa auren nan, ya ba ni matuƙar tausayi, domin hakan ya nuna mini yan zaman lafiya da matarsa ba ya son ya kawo ruɗani."

"Aiko sai dai ya yi haƙuri, domin Hajiya Baaba ta yi nisa ba ta jin kira.Ɗaukar fansa ne a ranta."

"Allah dai ya kyau kawai." Cewar Aby da ya miƙe zai shige bayi jin kiran sallar magariba.

Ajmal da ya fita sai ya kifa kansa da sitiyarin motarsa, yana jin ransa na matuƙar ɓaci da dana sani akan bai canza mata kammannin ta ba, na cewa da ta yi gemun shi kamar na buntsuru ba.

Sai kuma ya tsinci kanshi da kallon gemun a madubi yana shafawa cikin so da ƙaunar da yake masa, tare da tuna irin maƙudan kuɗi da gyaran da yake sha.

Mata nawa suke crushing ɗinsa tamkar za su mutu, na social mediya da 'yan mata masu ilmin addini da boko ba irinta mara tarbiya da kamun kai ba.

Ya daɗe a gurin yana jinjina abin da ta gaya masa da jin matsanancin baƙinci kamar ya mutu.

A hankali ya tayar da motar yana janta kamar mai jin bacci saboda gabakiɗaya babu karsashi a jikinsa.

A ransa yana tunanin abin da zai yi a fasa auren duba ga yadda ya kifa mata marin ko a kwalar rigarta.

A bakin gate ɗin gidansa ya yi ƙoƙarin manta komai domin baya son ta fahimci wani abu, a ransa yana addu'ar Allah ya sa Aby ya ɗauko wanda zai sanya ta fasa auren.

Da ya shiga gida yana ƙaƙalo murmushin da iya fuskarsa ya tsaya.

Faɗawa jikinsa ta yi tana murmushi."Bab, ka daɗe har na fara ƙoƙarin na kira ka."

"Eh, Aby ne muka je asibiti baya jin daɗi." Ya tsinci kansa da faɗin haka.

"Ayya! Allah ya ba shi lafiya, sai na je na duba sa ko? Ina ganin gobe ina dawo aik..."

"No karki je, ki bari zan kai ki da kaina kin san halin Hajiya Baaba, sam bana son ta faɗi abin da zai ɓata miki rai."

Ɗan jim ta yi sai kuma ta tuna da halinta wanda in har ta ganta sai ta ji gabanta ya faɗi.

"Tom, Allah ya kai mu, amma ya jikinsa."

"Yaji sauƙi." Ya ba ta amsa yana ƙoƙarin rage kayan jikin shi, saboda zufan dake keto masa tamkar wanda ya yi ƙarya.

"Bari na shiga wanka zafi na ke ji." Ya ce tare da riƙe ƙofar bayin yana kallonta.

"Na zo na taya ka, na ga sai gumi kake kamar wanda ya yi gudu."

"No karki damu shirya mini abincina." Ya ce tare da shigewa bayin saboda wani irin zafi yake ji sosai.


Bayan fitarsu Hajiya Baaba ta ja tsuka tare da garƙame falonta.


"Kuje can kuyi ta jarabarku, ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka jarabbbu kawai, da kun ɗauka rashin kunyar da kuke zuba mini iyayenku na gani saboda so basu iya kwaɓa muku, ni kuma na zama juji ku yi shuka mini rashin mutunci babu mai tsawata muku."

Kwana biyu da saka ranar sai yaran gidan suka ɗauke mata ɗip! Duk da cewar ba wani shiga harkarta suke yi ba, amma duk safiyar Allah za su shiga su gaisheta Jannah ce kawai ba ta zuwa, amma daga ranar da aka sanya ranar sai suka daina domin matuƙar haushinta suke ji.

Ba ta kula su ba kamar yadda suma ta kansu suke yi ba exam har suka gama suka shiga hutu sai zuwa islamiya.

Ranar talata da yamma sun fito za su je islamiya suka ga Hajiya Baaba zaune akan farar kujera na roba, tasha kunu da 'yar rediyonta tana ta canza tasha.

Babu wanda ya ce mata har suka kusa wuceta sai Nahlin da ta daure ta ce
"Sannu." Ta ɗauke kanta.

"Zo nan, na ce don ubanki da kika ce mini sannu ciwo nake?"


Tura baki ta yi ba ta ce komai ba. Miƙewa ta yi ta tsaya cikin masifa tana kallon Jannah, wacce ta yi kamar ba ta san da mutum ba, domin da za a tambayeta wace ce maƙiyarta da gudu za ta nuna ta, wanda hakan ba ƙaramin zafi yake mata ba, domin har ga Allah tana matuƙar jin sonta da ƙaunarta fiye da sauran jikokinata, Duba ga yadda iyayenta ba su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login