Showing 15001 words to 18000 words out of 137802 words

Chapter 6 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

tagumi hannu biyu yana kallonta.
Tausayinsa ganin yadda ya damu da halin da take ciki ya kamata ta, duba ga iyayen ta da suka yi silar zuwan ta cikin duniyar ba su damu da halin da take ciki ba. Ba tare da ta sani ba sai ta ga ta salon mi shi murmushi mai kama da yaƙe ta yi masa tare da janyo jakarta ta fara sauka daga cikin jirgi, wanda ganin hakan ɗan saurayin ya rugo da gudu har yana bige ma'aikan jirgi, amma bai kula ba ya nufo in da take.
Ba tare da ya cimma ta ba har sai da ta sauƙa ƙasa tana waige waigen Abby domin shi zai ɗauke ta.
"Haba yake kyakykyawa mai kama da ɗawisu bai kamata ace kin gudu ba tare da ko gaisuwa, bayan irin damuwar da na shiga duk a dalilin halin ki.
Duk da cewar ta ji babu daɗi da ya yi mata magana, amma kuma ta saka wa ranta cewar aga yau zata cire komai ta manta koma kuma ta saka farinciki a cikin rayuwarta.
Kallonsa ta yi ba tare da tace komai ba ta fara tafiya. Ganin haka da sauri ya bi bayanta ba tare da ya damu da direba da ke jiran sa ba, amma ya ƙi tafiya sai dai ya miƙa wa direba trolley ɗinsa.
"I’m sorry idan na ɓata maka but don Allah ina buƙatar hutu please!" Ta furta cikin ɗan ɗaga murya.
Maimakon ta ga ya ɓata rai, amma sai ta ga saɓanin haka domin wani irin ihu ya yi tare da rungume wayarsa ya ce, "Wow! Wow!! Ka ji wata irin murya mai kama da sarewa. Gaskiya da zan iya gaya miki gaskiya sai na ce babu macen da na taɓa jin tana da murya irin na ki, amma don Allah ƴar indiya ce ke ko?"
Ba tare da shiri ba ta ji wata irin dariya ta kubce mata sosai. Haka kawai ta ji gayen ya yi mata zata iya ɗaukarsa a matsayin aboki domin shigarsa yanayinsa fuskarsa da kyawunsa ya yi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman gemunsa mai ɗaukar hankali.
Ganin irin dariyar da ta saki sai kawai ya ƙara sakin ihu da tsalle."Yes na jefa ƙwallon a raga."
Kallonsa ta yi sannan ta ce, "In ban da abin ka ka taba ganin indiya baƙa?"
"Haba sam ke ba baƙa bace cemin za ki yi chocolate beauty dai."
"Humh." Kawai tace ba tare da tace komai ba.
"Please don Allah in ba za ki damu ba ki ba ni numbarki, kin ga yanzu kin gaji haka ni ma. So nake na koma gida mom ɗina ta yi mini tausa, tare da b ni abinci a baki.
Wani irin tsau ta ji, jin ya ambaci abin da mom ɗin sa zata yi masa, har bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, wanda ya ɗaga hanklinsa matuƙa ya shiga tambayarta.
"Forgive me if I said something that upset you, eh!" Ya ƙarashe maganar cikin sigar damuwa.
"No, no at all. You didn't, buddy."
"Buddy?" Ya maimaita kalmar cikin razana da tsigar tambayar domin shi ba haka ya so ba, amma da ya tuna babban yarinya ce dole sai ya sha wahala sai ya kada kan sa ya ce, "All right, like you said. Wai Hausawa suka ce da babu ai gara ba daɗi kuma Ana yi da kai, ya fi ba a yi."
Sai ta yi dariya ganin kamar ya faye zolaya kuma like she enjoys it.
Dai-dai lokacin da ta hangi Abby a tsaye kusa da motarsa yana ɗaga masa hannu, tare da Nahlin da Hajiya Baaba.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093








Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K




*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 5-6*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM




Saboda tsananin farinciki bata san lokacin da ta saki troley ɗinta ta ruga cikin farinciki, domin rabon da ta ganta tun lokacin da ta zo hutu za su koma London shekara takwas kenan. Faɗawa jikinta ta yi tare da saka ihun murna yayin da take shafa bayanta.
"Ina kike jikalleta farincikin rayuwata jikalle ɗaya tamkar da dubu ina kike zo rungume ni ki kwashe albarkan shekarun da kika rasa."
Hajiya Babaa ta fito daga cikin mota tana taku da takalminta mai tsini sosai, wanda yake barazanar kayar da ita.
Wani irin ihu ta ƙara saki tare da sakin Nahlin ta rungume ta tana ihu tana sakin mata kiss ta ko ina.
"Na yi kewarki hajjjajuta na yi kewarki sosai, ina matuƙar sonki ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe." Ta furta cikin murna sai juyata take.
"Haba ai Halimatuu ni na haife ta, amma ban sa in da ta samo halinta ba, haka kawai ta nisanta ni dake akan wasu dalilanta mara ƙarfi, ina gaya miki yanzu kin dawo babu jirgawa ko ina, ko aure kika yi tare zamu je, don na san gidan ki ne kaɗai zani na huta." Ta ƙarashe maganar tana hararar Nahlin da take tsaya tana kyaɓe baki.
"Ai a ko sati ba za ki yi ba za'a koro ki sis, domin tsaf zata kashe miki aure, just imagined mijin ta na karyawa ki haɗa wannan kwacamalar ta ki, goro da lacasera. Oh my goodness. I will really pity him, how nausea and vomiting ɗin da zai yi. " Ta ƙarashe maganar tana yamutsa fuska kamar za ta yi amai.


"Wallahi yarinya ta zage ni. Uban baki mai haure zan ci. Kin sam ni ko uwarki ba ta ishe ni ba, balle ke da kike iƙirarin turancin ki da bai wuce rabin cokali ba. Kina zagina da turanci sai kin gaya wa aya sakin ta, don na ji kamar har da imanja kike fadi kome. Kin san ni da gidan ki har abada."
"Wo Hajiyata." Jannah ta ce, cikin rike baki duk da ta san hali, lokacin da ta zo za'a yi mata aiki a London an sha dirama, ga ba ido ga masifa.
"Wa ke gayyar ki a gidansa, ai never. " cewar Nahlin.
Babaa ta buga mata harara tana faɗin. "Allah ya kyauta wa rayuwa ni na je gidanki, domin na san yunwa sai ta kashe ni, an riga na gado baƙin hali.


Kama kumatunta tana dariya. "Mai hali baya fasa halinsa ko shekaru nawa za'a ɗauka. Kina nan dai da halin ki kamar yadda na sani. Tace cikin murmushi.
"Ya canza taɓ! Ai sai dai abin da ya ƙaru." Nahlin tace tana hararar ta. Nahlin ta kama hannunta tana faɗin. "Maza muje sis in dai Babaa ce sai ta kai mu dare a nan ba tare da mun je gida mun huta ba.
Babaa ta wafce hannunta da sauri. "Maza kar a ɓata mini jikalle da baƙin hali. Ma za muje kin ji ɗaya tamkar da dubu, ki huta kin shawo hanya." Ta ƙarashe maganar tare da jan hannunta suka fara tafiya.
Saboda dariyar yadda Hajiya Babaa take tafiya ya bawa Nahlin dariya, sosai har tana riƙe ciki. Rigima sosai ta yi kafin a sayo mata irin takalmar, domin Ammy sayo wa irin takalmar daga gani ta saka rigimar yana fifita matarsa, ganin irin takalmar ta kuma kafe akan dole sai ya siyo mata. Tun lokacin da aka siyo takalmar bata taɓa sawa ba, sai yau da zuwan Jannah domin takalmar hill ne, ko da za su shiga cikin motar a hannu ta riƙo su sai da suka ƙaraso filin jirgin ta saka.
Sai turguɗewa take yi amma ta nace dole sai ta yi tafiya da su, haka take tafiyar tana turguɗe, tana tafiya ta turguɗe sai gata tana shirin zubewa a ƙasa, ji ta yi wani saurayi ya riƙe ta yana faɗin,
"Kiyi a hankali Hajiya. Da sauri Hajiya Babaa ta juya tana kallon saurayin.
"Sannu ɗan saurayi Allah ya yi maka albarka." Ya amsa cikin natsuwa yana kallon Jannah da ta ƙaraso da sauri ta rungume ta. Nahlin ko me zata yi in ba dariya ba.
Tsabar haushin ta da Babaa take ji ko kallon ta ba ta yi, ta cire takalminta ta riƙe a hannun ta tare da jan hannunta suka fara tafiya zuwa motar su.
"Allah ya ƙara muki maganin ki da karambani kin ci lokacin ki kice sai kin ce na wani, in ban da rigima irin taki ina ke ina wani takalmi hill." Ta furta hakan a cikin ranta.
Buɗe ƙofar suka yi suka shiga yana tsaye yana kallonsa, duk da Jannah ta so ta yi masa magana, amma kunyar su Dad ya hana ta ko kallonsa.
Har sai da suka shiga cikin mota direba ya fara tafiya ta juyo ta kalle shi yana tsaye fuskarsa tamkar zai yi kuka duk sai ta ji bata ji daɗi ba, musammman da ta ga ya yi sororo yana nuna mata bata ba shi numbar wayarta ba.
Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi tare da ji gina kanta saman kujera ta lumshe idanunta.
A lokacin da suka isa gida wanka ta shige ta rinka kwararawa kanta ruwan sanyi tana jin sanyin ruwan yana sauka har cikin zuciyarta.


Bayan ta ɗauki tsawon lokaci tana watsawa kanta ruwan sannnan ta fito daga cikin bayin ta sanya dogon riga kawai ba tare da ta shafa mai ba ta fito daga cikin ɗakin.
Kai tsaye kicin ta wuce in da take jin motsin Hajiya baaba tana kwarafniya da tukane.
"Yauwa shalelena kin fito? Yanzu nake son na shiga na yi miki magana jin kin daɗe a bayi. Ko ke ma kin ɗauki halin mahaifiyarki na watsa da ruwa lokacin wanka?"
Dariya ta yi mata Jin abin da ta fadi."Wai Hajiya har yanzu ba ki daina rigimar yi wa kanki girki ba?" Ta maida maganar tsigar tambaya.
"Ato ni hauka nake na rinƙa bari ina cin abincin da zai cutar da ni. Haka kawai ba za a ci abinci mai kwayu ba, sai kullum a rinka cin wata cimar da aka ɗauko daga wata Kabila can. Shi ya sa nake girki da kaina. Kin ga ma za je ki zauna yanzu zan kawo miki abinci, saboda ke na yi tuwon shinkafa miyar taushe, duk da na san ke ma ba'a iya miki."
Jannah ta yamutsa fuska jin abin tace mata."A haba Hajiya na yi duguwar tafiya sai ki rasa abin da za ki ba ni sai tuwon shinkafa. So kike cikina ya yi nauyi na kasa bacci?" Sai ta fice daga kicin din tana faɗin ni ba abinci zan ci ba tea kawai zan sha na kwanta bacci, sai bayan na tashi zan ci abinci, amma ba tuwo ba."
Hajiya ta biyo tana tana salati. " Haba Jannatuu so kike su yi mini dariya, tun da mahaifiyarki ta gaya mini za ki zo kwana na yi ban rintsa, don Allah kar ki watsa mini kasa a ido." Dariya kawai ta yi ta kwanta akan doguwar kujera daidai lokacin da Nahlin da mahaifiyarta suka shigo yayin da Nahlin take ɗauke da turen abinci, ganin haka Hajiya Baaba ta harari kwanon tare da ɗauke fuska bayan ta taɓe baki.
Murmushi kawai suka yi tare da shigowa. "Sannu da hutawa Hajiya." Mom ta furta da sauri ganin zata shige kicin.
"Ba aiki nake yi ba kamar yadda kike gani." Shiru ta yi ba tare da tace komai ba har ta shige kicin ɗin tana bambami.
Nahlin ta sauke tiren kwanon abincin tana bin bayanta da harara. Ba ta yi ninyar gaishe ta ba kamar kmar yadda tasan ba zata amsa ba.
Da sauri ta sauka daga kan kujera ta durƙusa." Mom barka da fatan na same ku lafiya?" Ta furta cikin jin kunya da girmamawa domin Allah ya sanya mata jin kunyar Ammy da ƙaunar ta.
Shafa kanta ta yi cikin so da ƙauna."Lafiya lau ya maihaifiyar ta ki."
"Daddy yana lafiya."Ta ce cikin basar da tambaya.
Murmushi ta yi kawai sannan ta miƙe tana faɗin."Bari na barki da Nahlin, in kika huta da fatan za ki shigo shashin nawa."
"Eh Amym ai a ɗakin Nahlin zan zauna." Ta furta domin ta ɗauki aniyar ba zata zauna a ɗakin Hajiya Baaba ba.
Akan me za za ki zauna a ɗakinta bayan tun kafin ki zo na sanya aka gyara mana ɗakinki." Ta ji muryar ta tana mata tambaya.
"Gaskiya ba zan zauna a ɗakin ki ba, kiyi ta damun mutane da surutu da labarin sa bai shafe ni ba, har da na matattu fisabilillahi ina wanda zai kwanta bacci za a bashi labarin mattatu salon na yi mafarkin fatalwa." Ta ƙarashe maganar cikin shagwaba.
"Jakar uban nan!" Ta furta ai kuwa in har ba za ki kwana a ɗakina kin ɗauko ruwan dafa kanki, domin magen da kike tsoro na ɗaura miki a jiki, jiya kasa bacci na yi ina murnar za ki zo, amma sai ki watsa mini kasa a ido, ai gara ki dawo hankalinki tun kafin ruwa ya kare wa ɗankada." Tana gama maganar ta wuce ɗakinta.


Dirama sosai aka yi akan inda za ta zauna ganin ta ki cinyewa da kanta ta zaɓi ta zauna a sashin Hajiya Babaa.
"Da dai kin hutar da kan ki. Haka kawai an mallake mini ɗana, kuma wanann 'yar gudaliyar za'a haɗa da ita. Ina wallahi uban kuturu ya yi kaɗan. "
Ita dai Ammy ba ta ce komai ba. Ajiyar zuciya ta saki, sannan ta fice daga ɗakin. Nahlin ta yi ƙunƙunai wanda ba za ka gane me take cewa ba zata fice daga ɗakin, wanda hakan ya kubular da Hajiya Baaba ta wawuri mafici ta jefa ta da shi. Nahlin ta ruga da gudu tana dariya.
Jannah ta yi shiru duk irin surutun da take ba ta da labarin yadda ta mallake mata ɗanta. Sam ba saurara take yi ba domin hankalinta ya yi nisan kiwon dan saurayin da ta ji ba ta kyauta masa ba, ya kamata ace sun yi exchanging contact if possible su rinƙa gaisawa.


"Magana na ke, kike kunnen uwar shegu da ni. Wato ga mahaukaciya ko? Kin ga wallahi zamu saka kafar wando daya dake, ba zan lamunci wannan isgilancin na ku da kuka gado ko a ina ba. " Sai kuma ta sausauta murya ganin halin ko-in-kula da ta yi mata.
"Kina ji na shalelensa jikata. Kin san ke kaɗai na fi so, duk cikin jikokina ko? Ya kamata ki tausaya mini, matar nan ta riƙe makogaron ɗana sam ba shi da wani kataɓus. Abynku ya zama mijin-ta-ce."
Wani irin takaici ne ya kamata sai ta ki ganin ba'a rabu da bakar bane aka haifi habu. Ita da take ganin za ta zo ta huta da damuwa, sai ga shi ko hutawa ba ta gama yi ba, an dauki mata wani damuwar, wannan dalilin ya sa ta so ta zauna a sashin Ammy, amma ta hana to ga shi ba'a je ko ina ba ta fara dana-sa-ni.
"To ni mai zan ce miki Hajiya Baaba? Kin san ni ban san komai ba game da rayuwar da kuke yi. Ki yi hakuri don Allah"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login