Showing 111001 words to 114000 words out of 137802 words
Chapter 38 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
domin ka san na yi maka soyayyar da ban taba yi wa wani ɗa namiji ba, son da nake maka dole ya sa na manta komai duk da cewar har yanzu akwai abin da ba zai taɓa goguwa a gare ni ba."
"Haka ne, na sani amma ki gafarce ni. In sha Allah ba za ki ƙara dana sanin zama da ni ba."
Rungumeta ya yi yana shafa bayanta cikin tsigar soyayya.
"Tabbas rayuwa da masoyi akwai daɗi! Ina matuƙar tausayin Jannah na raba ta da Huzaifah da Hajiya Baaba za ta yi. Kina ganin babu abin da za mu yi wanda zai hana hakan?" Ya tambayeta cikin murya mai sanyi.
"Ba na tunanin haka domin ka san in ta faɗa ya zauna ko lokacinmu, Allah ya kaddara zamu yi aure ne kuma da albarkacin kawu da yake raye, amma yanzu sai in ba ta numfashi. Mu yi wa Jannah fatan alkhairi a auren ta, domin zaɓin da ta yi mata ba tumin dare ba ne. Ajmal miji ne da ko wane iyaye zai yi fatan 'yarsu ta samu. Yaron yana burge ni karka manta shine malamin da ake ji da shi, wanda ya haɗa kyau da ƙuriciya uwa uba addinin boko da islamiya."
Ta yi shiru ko zai ce wani abu amma sai ba ta ji ya ce komai ba sai jinjina kansa da yake alamun abin da take faɗi yana shigarsa.
"Na sheda Huzaifah na matuƙar sonta, amma ka san ko sun yi auren matsaloli zai ta tasowa, saboda yanzu soyayya ke rufe musu ido, zama da Jannah sai mai tsauri."
"Haka ne, ni ma na kan yi m hakan, amma kin san..."
"Karka damu muyi mata addu'a domin jikina yana bani alkhairi zata haɗa, watarana sai mun yi alfahari da hakan. Tana jin maganarka ka samu ka shawo kanta."
"Kamar ba ki san Jannah ba, tana da kafiya ba ta da sausauci akan abin da take so."
"Duk da haka ka gwada nasararka za ka iya cin nasara wataƙila, tun da ni kallon banza ban ishe ta ba."
Fuskanta ya ciko da gawaye tausayin kanta da damuwar da take ɓoyewa suka bayyana.
Janyota jikinsa ya yi tare da haɗa hancinsu.
"Ina gaya miki watarana Jannah, sai ta nuna ba ta da wacce take so fiye da ke. Ki yarda ki jira lokaci domin ko yanzu tsananin kishinki na fifita aiki da rashin ba ta lokacinki yake damunta."
"Ina fatan hakan ina kuma jiran lokacin, ina addu'ar kar hakan ta faru a lokacin da ba shi da amfani." Ta ce tare da maida hankalinta kan aikinta tana jin hawaye na zubo mata.
Hannunta ya riƙe da take ƙoƙarin operating ɗin laptop ɗin.
"Hakan ba zai faru a lokacin da abu amfani ba domin da zarar ta yi aure hankali zai shige ta." Ya ce tare da sanya hannunshi yana ɗauke mata hawaye.
"Am hoping for that injiniya."
"Ni fa kwana nan ina fushi dake sam ɗan lokacin da kike bani, yanzu bana sanu, domin kwanan nan tamkar wani Zaki dake ɗauke da yunwar sati ɗaya nake." Dariya ta yi sosai tana kallon ƙwayar idanunsa domin yadda ya yi maganar ya sata cikin nishaɗi sosai, wanda hakan ya tuna mata da rayuwarsu na da wanda cike take da so da ƙauna.
"Please Injiniya ka bari bana so. Can't you see that am working and they need the details before tomorrow." Ta ce jin abin da yake mata.
Dariya ya yi sosai yana faɗin,"Haba, na ƙi wayon Allah kwana biyun nan, sai haƙƙina ya kama ki domin kina ƙwarata. Kullum aiki tamkar agogo."
Haɗata da jikinsa ya yi tare da manna mata kis a leɓenta wanda ya sa suka yi shiru suna jin bugun numfashinsu yadda yake sauka a hankali kuma a tare.
"I adore you." Ya ce tare da janta suka faɗa gado.
Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ita kanta tasan tana kewar mijinta wansa ya iya ƙauna da tarairayar mace. Sai dai, abubuwan da suke sha mata kai su ke sanya ta manta ƙaunarsa mai kashe zuciya, amma ta san ta yi missing alot.
A hankali ya kai bakinsa kan nata wanda ta rufe idanu tana murmushin da ya ƙara ƙawata kyawun fuskarta.
"Ni ma ina sonka Injininiya." Sai suka runtse idanunsu suna jiran saukar laɓɓarsu akan na juna.
Wani irin ƙara suka ji Jannah ta ƙwala wanda ya sa ya janye jikinsa daga gareta.
"Tom lafiya mai ya kuma faru da wancan 'yar rigimar?" Mom ta ce cikin damuwa.
Dad da jikinsa ya mutu da ƙyar ya miƙe.
"Ba ya wuce rigimarta kin san yanzu kamar jaririyar goye take, in kika ga birgimar da ta yi sai kin yi mamaki." Ya ce tare da miƙa mata hannu da alamun ta zo, wanda ta noƙe.
"My dougher is crying I most go and check on her." Ta ce tare da gyara zaman rigarta.
Tsaki ya yi yana sakkowa daga kan gadon.
"A taƙaice ta hana mu samun lada?"
Gwalo mom ta yi masa ta fice tana dariya wanda ya biyo ta cikin kasala murmushi ɗauke a fuskarshi.
"Keeeeee! Ba na son iskanci, ina karatuna za ki sa uban ƙara sai ka ce wacce ka tsire, wallahi sai da na firgita. Uban mene ne?" Ba ta ko kalli Hajiya Baaba da take faɗin haka ba ta ci gaba da kukanta.
Dad da ya sauko ya kamata ya riƙe.
"What happen? Kin ci abinci wa ya taɓa mini ke?" Ya ce cikin tsigar rarrashi wanda ya sa Hajiya Baaba ta yi tsaye cikin baƙinciki ta na jin kamar ta kifa masa mari.
"No, I wanna go and take my food in the kicin, shi ne na zo wucewa Anty Nahlin ta mini dariya, kuma dama na ji suna mini dariyar za a aura mini tsoho."
Da sauri su Nahlin da Ummu suka zare idanunsu cikin tsananin mamakin jin sharrin da ta yi musu.
"To don ubanki da ta harare ki ciwo kika ji, ko ina hararar ta maƙale miki za ki haukata mutane da ƙarar ki kamar gyare?" Hajiya Baaba ta furta cikin ɓacin rai wanda ko kallon arziki ba ta samu ba ballantana ta yi tunanin za ta amsa mata.
Mom kuwa da dad kallon junansu suka yi suna baƙincikin ɓata musu yanayin da suke ciki.
"Tsoho, Ajmal ɗin ne tsoho? Ke Nahlin kika ce mata Ajmal tsoho?" Cewar mom cikin mamaki.
Nahlin da mamakin sharrin da ta yi mata ya cika ta sai tafa hannu take tana salati ta kasa cewa komai, domin ta daina shiga sabgarta tun jiya da ta kalleta ta zabga mata harara har da murguɗe ya sa ta kama kanta don ba ta son rashin kunya.
"Ƙarya ne ba tsohon bane? Mutumin da har ya yi aure da mata ai tsoho ne." Ta ce tana jan majina cikin zallar sanagarta.
"Ko da sanda yake tafiya da ita sai kin aure shi ja'irar banza kawai." Hajiya Baaba ta furta tare da tsakin tsaki ta koma kujera ta zauna.
"Ki yi shiru muje ki zauna zan yi mata faɗa." Mom ta ce tare da kama hannunta wanda ta wafce ta riƙe dad tana faɗin,
"Dad, am sterving." Kama hannunta ya yi yana faɗin,
"Ok, lets go and eat." Abincin ya zuba mata da kan shi ya ɗauko tana biye da shi a bayansa tamkar jela. Ya ije abincin akan dining tare da fara ba ta a baki tana ci tana danna wayarta duk wanda ya yi nasarar kallonta sai ta balla masa harara.
"Kai innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ni kam ina ganin taɓara da sangarta. Wai shin arziki hauka ne da kuka mai da yarinyar nan kamar wata 'yar goye? Irin tarbiyar da na ba ki kenan Halimatuu? Wallahi da irin ta ne tuni Jabiru ya sake ki. Kun ɓata yarinya kun sagartata kun mayar da ita taɓararriya. Kun san Allah ku kiyaye ni domin in kuka ci gaba da haka, tsaf zan sheme ku har da Jannah."
Ta ja tsaki za ta shige ɗaki tana faɗin,"Adamuu, ka yafe mini domin na haɗaka da masifa da bala'i."
Mom da dad babu wanda ya yi magana sun san gaskiya ta faɗa, amma ba za ta gane ba ne, domin ita ce 'ya ɗaya tal wanda Allah ya mallaka musu in ba su kula da ita ba wa za su kula da shi.
Ɓata rai ta yi tana kallon ƙofar da Hajiya ta wuce bayan ta rakata da harara.
"Dad,"
"Do eat your food don't nagging." Ya ce da sauri tare da kai saka mata loma yana tunanin mood ɗin da ta ɓata mishi, sai ta ci gabada tauna abincin kamar an mata dole.
Washegari da safe mom ta shirya ta sauko ƙasa za ta wuce aiki ta tsaya turus tana kallon Hajiya Baaba da ta tsaye da jaka riƙe da kwankwaso.
"Lafiya Hajiya Baaba, na ɗauka tafiyar jibi ce?"
"Ban sani ba, yau na ga damar komawa gida." Ta ɓata masa cikin ɗaure fuskar da babu hanyar da za ta gani ta yi musu.
"Amma Hajiya Baaba, da kin bari sai gobe saboda jirginku na jibi na yi reserving."
"Kin san Allah? Yau in kika ga na ƙara kwana a gidan nan sai dai ba ni iya tafiya, amma ko a ƙafa sai na koma gida."
"Hakan ba zai taɓa fauruwa ba dole na san yadda zan yi." Ta ce tana ƙoƙarin kira a wayarta daidai lokacin da ta ce,
"Haka kawai, sai na zauna baƙinciki ya kashe ni. Ba ki da lokacin da za ki yi hira da mutane, sai dai wuni mutum ya yi ta kallon tibi, salon idanun su makance da wuri. Ga yar banzar yarinyarku da ku ka sangartata ba ta kallon kowa da gashi ta hana mutum saƙat da koke-koke. Gara na koma gidana zaman can yafi mini, in lokacin bikin ya yi kwazo ayi akai masa tsiyarsa."
Mom dai ba ta ce komai ba har aka ɗaga wayar da take kira ta yi magana sannan ta kashe.
"Ki ɗan jira zuwa rana sai ku wuce bari na sa a haɗa muku tsarabarki. Su Nahlin su bari sai an janye strike sai su dawo har da su Janna..."
"Jann me? Kin san Allah ko aljannah take karki sake ta dawo mini gida, domin ni da ita mun yi hannun riga mara mutunci kawai. Ai na yi muku tsawon shekarun da na yi tana gaza mini gyaɗa a hannu ya isa. Ku da kuka ɓatata can muku na gaji a sakin mini mara na yi fitsari."
"Ni ma ba dawowa zan yi ba, ni da gidan ki ko a ƙiyama in ana ziyara ba zan zo ba."
Jannah da ta fito da waya a hannunta ta ce ba tare da ta kalle ta ba ta wanda ita ba ba ta tanka mata ba domin ba ta da lokacinta.
Da misalin ƙarfe huɗu jirgin Hajiya Baaba ya ɗaga wanda Jannah tafi kowa murna a gidan domin gani take kamar babu wanda ya isa ya biyo ta har gida ya yi mata auren dole. Karatun ta ne kawai ta ke jin babu daɗi na transfer da za a yi mata saboda ƙawayenta da sabon da ta yi da su. Ummu kuwa dama ba wani harkanta take shiga sosai ba, tun da ta yi mafarkin ta yi mata dariya wai za ta riga ta aure ta ɗauke mata wuta.
Zaman na su sai ya yi babu daɗi ko kaɗan domin kowa harkar gaban shi yake yi. Su kansu su Ummun ba wani daɗin hutun suke yi ba duk da cewar ga komai nan sai dai cuci su sha su yi kallo, amma fa mom ba ta da lokacin su har gara dad ya kan yi ƙoƙari ya gansu kafin ya tafi aiki, da in ya dawo, amma mom sai ta yi kwanaki ba su sanya ta a idanunsu ba, domin da wuri take fita har gara Nahlin da take ɗan tashin wuri.
Su Bala da Mudi tuni suka kama kansu cikin murna suka tafi ganin yadda mom ta cika su fa abin arziki da jari mai nauyi, wanda suka yi matuƙar jin daɗi da alƙawarin wa kansu dawowa bayan wani lokacin, domin sun ga gurin zuwa.
Washegari da safe suna zaune a falo kowa na harkar gabanshi. Dukanninsu waya ce a hannunsu wani ni lokacin su duba wayarsu wani lokacin su yi kallo, amma babu mai ko tari a tsakaninsu.
Mom ce ta fito tana janye da troley cikin maroon ɗon abaya ta yi kyau sosai tamkar ka saceta ka gudu.
Murmushi ta yi lokacin da suka ji ƙarar saukkowarta suka kalli saman benen
"Nahlin, Ummu, Jannah, tafiya ta kamani zuwa cameroon kuma I think I will stay long, akwai komai da kuke buƙata duk abin da kuke so babu ku kira ni ko ku yi wa masu aiki magana. Da fatan za ku kula da kanku?" Ta yi musu tambayar yana nazarin fuskokinsu.
Ummu da Nahlin suka ɗaga kansu amma Jannah ko alamun da ita take magana ba ta yi ba ta ci gaba da danna wayarta.
"Jannah, I w.."
"Oh please mom! I heard you. If you like go to heaven I don't bloody care, since my dad is around." Ta ce cikin ɗaga murya ta ci gaba da abin da take yi.
Shiru ta yi tana kallonta sai kuma ta miƙe tana hamdala da ta riga shi tafiya domin ba ta san wainar da za a su toya ba, matuƙar ta ji zai yi tafiya kuma sai ya daɗe sosai donnsai gabda zaɓe zai dawo.
"To na tafi, Allah ya yi muku albarka."
"Amin." Ummu da Nahlin suka amsa ita kuwa miƙewa ta yi tana faɗin,
"This house is so boring." Ta haye sama kallon mamaki suka bi ta da shi.
"Wannan yarinyar fa ba ta da mutunci lokaci guda ta canza mini fuska, saboda mun zo gidansu. Na lura kallon banza take mana ba, wallahi zan mata mata ni ma ɗin ba kanwar lasa bane, kuma ta san gidan ubana ba abin rainawa bane." Cewar Ummu cikin ƙubula domin haushin shareta da ta yi take ji, tana ganin she didn't deserved that duba ga how very closely they are.
"Wallahi kuwa, ni kallon mamakin sharrin da ta yi mini nake kuma tai mursisi duk da na san kurace da fatar akuya ban yi tunanin ta kai haka ba.'
"Ƙyale mara mutuncin kawai! Ki barta maganinta zan yi. Ni Yaya nake tausayi yana zaman lafiya da matarsa za a kai masa fitina."
"Yayan za ki tausayawa ko ita? Ke ma kin san halin shi daidai yake da ita ba zai ƙyale ta ba, ƙaniyarta zai ci shi ma ba ƙyaleta zai yi ba. Kin san halin shi."
"Duka za ta ci kamar jaka