Showing 33001 words to 36000 words out of 137802 words
Chapter 12 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
canza ta ɗauki jakarta ta fice ta bar shi tsaye sororo.
Wayarta ta yi ƙara alamun ana kiranta ta whatsapp. Da sauri ta ɗauko wayar tana dubawa. Ganin Jannah ce ya sa ta ɗauka da sauri tare da kanga wayar a kunninta.
"Hello mom, Ina buƙatar kuɗi."
"Haba Jannah! What I have done to you to deserved this? Kar ki manta ni fa mahaifiyarki, you should respect me." Cikin muryar son kuka ta ƙarashe maganar.
Ƙin amsa mata ta yi sai ta ce a maimakon ta amsa tambayar. "I desperately need money. Ba kin ce saboda ni kika hana kanki hutu kike neman kuɗi ba? So do send me I wanna enjoyed."
"Amma ya kamata ki tambaye ni cikin girmamawa da sanin darajat.."
"To in har saboda ni ne, ina son ki siya mini braded car. Ki kuma tura mini kuɗi a account. Ki kuma yi wa mahaifiyarki magana, domin ta addabi rayuwata ta hana ni shan iska wai sai ta koya mini aiki. Ki sanar mata a haka kika tarbiyartar da ni, ban taso ina yin chores ba. I think is not bad, don kina gaya mini cewar nice wacce kika fi so, na tabbata ba za ki ɓata ni ba ko?" Ta furta cikin gatsali da rashin kunya.
Sai ta ji wani irin ƙululun abu ya toƙare mata ƙirji har sai da ta dafa mota. "Na yi kuskuren da na barki kika girma tamkar sakakken kashi, na kasa tsayawa na ba ki kulawa. In sha Allahu zan gara, zan zamo uwa wacce kowa yake fatan samu."
"Kina jina?" Ta tamabayeta jin ta yi shiru. "Eh, shikenan zan yi mata magana, kuma zan siya miki duk motar da kike so. Fatana ki damu da ni, ki so ni ko rabin son da kikewa mahaifinki. Ina matuƙar sonki, wallahi na fi kowa sonki. Sai ta yi ƙasa da wayar tare da fashe wa da kuka.
Ɗif! Ta kashe wayar da jan tsaki tana faɗin,"Kyaji da shi, haka kawai ki ɗora wa kanki wahala, sai kin tara kuɗi kin kula da al'umma, bayan gidanki kin kasa kula da shi wai ke joy giver ko."
Nahlin da ta yi mutuwar tsaye ta kasa ce mata komai na 'yan daƙiƙa si kaɗa kanta take tamkar ƙadagaren kutu.
"Are you high?" Ta yi nasarar tamabayarta cikin tsananin mamaki sannan ta ɗora da cewa,"Waɗannan mugayen kalamai kike jifar mahaifiyarki da shi? Kin kuwa son wace ce ita, kuma wane irin ɗubbin nasara kike da shi da kika zo a 'ya guda ɗaya da ta mallaka."
Wani banzan kallo ta yi mata mai kama da raini ta ce, "Na san dole sai kin yi maganar. Haba Anty Nahlin komai na yi sai kin ce ban yi daidai ba." Ta ƙarashe maganar a fusace tare da toshe kunninta ganin ta buɗe baki za ta yi magana.
Bin ta da kallo ta yi domin ta gama karamtar ta 'yar rainin wayo ce da rashin kunya. Sai ta sanya a ranta za ta daina mata magana akan duk abin da take yi, domin kamar yadda ta ce mom ce ta ba ta wannan tarbiyar haka ne, don su suka bata gurɓatacciyar tarbiya. Sai ta saka a ranta daga yau ba za ta ƙara mata magana ba don haka ta miƙe za ta fice daga ɗakin, wanda ganin hakan ya sanya ta miƙe da sauri ta riƙe ta.
"Am really sorry Antyna. Idan kika yi fushi da ni ya zanyi. Ba za ki gane wace ce mom ba. Sam ba ta girmama mahaifina agaban idanuna take daka mishi tsawa. Ta mai da shi kamar ɗan da ta haifa, sannan ba ta zauna a gida ta ba shi kulawar da aure ya sharanɗa ba."
"Yarinya ce ke ba za ki fahimci komai ba. Don't be dummy and think logically. Mahaifiyarki abin alfahari ce ga rayuwarki, ke har da ta al'umma domin ita ɗin jigo ce ga al'umma. Kin san gidan marayu nawa take da shi a Ƙasar nan da ma ƙetare? Don haka ki tausasa kalamanki, kar kiyi nadama a lokacin da ba shi da amfani."
"Ok, from now on I will take note." Ta ce sannan ta fice ba tare da ko kalami ɗaya ya yi tasiri a gareta ba ta koma ta zauna.
Murmushi ta saki ganin maƙudan da suka shigo akawunta. Sai ta mirgina tana ƙoƙarin kiran dad, daidai lokacin da kiransa ya shigo. Jikinta har rawa yake ta amsa.
"Jannah, ke ce kika buƙaci mahaifiyarki ta siya mota? Kin san fa Nigeria ba kamar London bane."
"Eh, ina son na tuƙa, kuma siyen shine kwanciyar hankalinta wacce take trending." "Ho yarinyata rigima. To shikenan, in sha Allahu cikin satinnan motarki za ta iso branded kuwa." Wani irin ihu ta sanya tare da kashe wayar ta fice don ta yi wa Nahlin albishir.
A hankali shaƙuwa mai tsananin gaske ta shiga tsakainta da Huzaifah wanda take matuƙar daɗin hakan. Domin kaso cikin tamanin na damuwarta ya rage sosai. Maganin da take sha sai ta manta kwana biyu ba ta sha ba, kuma ba tare da ta ji canji ko wani alamu ba.
Da fari abota suka fara duk da cewar shi ba haka ya so ba, don ya so kai tsaye ya bayyana mata soyayyarsa. Sai dai, zana masa tarin burikan da take da shi da yadda take son tsarin rayuwarta ya sa ya fasa hakan, saboda burinkanta sun girmi tunanin sa da ƙwaƙwalwarsa. Rashin sanin abin yi ya sa ya haƙura, amma kullum cikin bayyana mata yake a zahirince wanda take pretending akan ba ta fahimta ba.
Huzaifah mutum ne wanda ya taso cikin 'yanci da kulawa da kuma gata. Mahaifinsa Janar ne daga baya ya koma shahararen ɗan kasuwa. Sai tsarin rayuwarta bai wani dame shi ba, domin yana son rayuwar yanci da hutu.
A haka suka yi ta soyayya da sunan abota kullum suna maƙale da juna. Yana matuƙar tsarinta, zubinta da surarta musamman kalar fatarta da ke tafiyar da hankalinsa. Burinsa kullum Allah ya mallaka masa ita sai ya ce ya fi ko wane ɗa namiji sa'a a duniyar. Kasancewarsa yana matuƙar son mace mara ƙiba, shi ya sa ta dace da tsarinsa.
Kasa jurewa ya yi don kar wani ya yi masa ƙafa ko late comer ya yi wuf da ita. Sai ya sanar mata da irin tarin ƙaunarta dake faman ɗawainiya da rayuwarsa, wanda hakan sai da ya sa suka yi faɗa har na tsawon sati ɗaya ta ƙi ɗaukar wayarsa. Sakamakon hakan, hankalinsa ya tashi har rama ya yi. Ita kanta ta wahala, amma tsabar girman kai da son cika burikanta ya sanya ta ƙi nemansa.
Ranar da ta ɗauki wayar ya cika da murna sosai ya bata haƙuri suka shirya. Ba bu yadda zan yi don tafi ƙarfinsa, amma she kansa ya san she was interested on him. Sam! Bai yadda akwai wata soyayya tsakanin mace da namiji in dai ba ta aure ba. Sai ya ɗauki hakan a matsayin yarinta becouse she was so young. Sam ba ta da wata magana sai ta maganarsa. Kullum cikin posting ɗin hotunansa take a shafinta. Da ga chatting, video call, and voice, babu wanda ba sa yi. Short video na sa da hotonsa jibge a wayarta. Wanda haka the same with him. Ita kanta ta san ya shallake mizanin buddy ya koma wani bangare mai girma na daban.
Jannah ta fara zuwa makarantar boko mai tsadar haske, da islamiyar da su Nahlin suke zuwa har da hadda, amma ba ta mai da hankali. Ko islammiyar ta je hankalinta na kan wayarta tana chatting. Ko ta sanya earpiece ta yi kamar tana jin karatun. Da ta dawo gida ba ta ƙara waiwayan karatun da aka yi mata sai in za ta koma islamiyar. Hajiya Baaba ta yi ta ƙorafi tana magana, amma sam ba ta kula ta domin ta yi mata wani irin raini. Wani lokacin ita ce take shakkarta.
Kullum malamai cikin ƙorfi suke yi. Abby da kansa ya yi mata magana, amma ta ƙi ji. Gabakiɗaya ta mai da hankalinta kan boko babu dare babu rana. Wani lokacin ko baccin kirki ba ta iya wa, domin horan da mom ta yi mata na cultivating reading culture ya yi matuƙar tasiri a rayuwarta. Burinta kullum shi ne ta zana jarrabawa ta fito da distinction.
Ganin suna barazanar dukarta sai ta dena zuwa wanda kan dole Aby ya je da jansa ya ba da haƙuri. Ita gani take takura mata islamiyar take yi, don a lokacin da ta dawo daga school za ta huta ta yi waya da Buddy, sai kuma a dame ta da maganar islamiya. Sati da lahadin ma ba hutu hadda. Ga Hajiya Baaba da ta addabi rayuwarta kan sai ta yi karatun da aka yi mata a gida.
Ranar da ta je islamiyar tana zaune a ciki ajin ana yin karatun hadisi, amma hankalita na kan waya suna chatting.
"Ba ni wayar." Ta ji mutum a tsaye akanta ya furta cikin tsananin fushi. Da sauri ta miƙe tana zare ido.
"Ni babu abin da nake yi da ita, kawai na riƙe ne." Ta ce cikin shagwaɓa da sangarta wanda hakan ya ƙara baƙanta ran Malam Aliyu sabon malamin da aka ka wo musu, sai kawai ya zula mata bulala da ƙarfi.
Wani irin ihu ta yi sai ga ta a ƙasa warwar! Babu numfashi, amma ko kaɗan hankalinsa bai tashi ba, domin ya tsani rashin kunya a rayuwarsa.
Gabaki ɗaya 'yan ajin suka dare a tunanin su aljanunta ne suka tashi. Kimanin minti ɗaya ba ta motsa ba, wanda ganin hakan hankalinsa ya tashi. Ruwa aka samo tare da watsa mata. Firgigif ta yi ta miƙe sai ta zura da gudu waje tana zunduma ihu.
Tun kafin ta shigo ciki Hajiya Baaba ta jiyo ihunta. Barin tuƙa tuwon shinkafar da take yi ta fito har zaninta na faɗi, amma ba ta kula ba.
"Uban wa ya taɓa mini jikalle? Waye shi ya san waye mahaifiyarki?" Ta jera mata tambayoyin tare da kamata tana rarrashin.
"Wayyo na shiga uku! Inna ƙara zuwa makarantar nan ba dad ya haife ni ba. Dukana ya rinƙa yi, sai da ya yi mini bulala ɗari."
Wani irin razana ta yi tare da dafe ƙirji."Na shiga uku ni jikar mai gishiri! Bulala ɗari? Aiko ya ibo ruwan dafa kansa. Ma za muje na ga uban da ya tsaya masa a duniyar nan. Motar 'yan sanda zan sa Halimatuu ta ɗauko masa makarantar gabaki ɗaya ya shafe su."
Daɗi sosai ta ji ganin ƙaryarta ta ƙarbu. Sai ta share majina tare da miƙa mata hannu. "Ina jin ma ya karya ni. Ni kawai a cire ni a makarantar sai a ɗaukar mini malami a gida." Ta fakaici Hajiya ta yi murmushi sai ta ƙasa sakin kuka ta ce,
"Mugu azzalumi kawai! Ya san irin kuɗin da nake kashe wa jikina da man da nake shafawa, salon ya ɓata mini jiki. Yana ji da fuskarsa kamar ta biri."
"Mu je ki ga abin da zan yi masa, don sai ya yi dana-sanin dukanki. Shalelen jikata zai duka..
Kama hannunta ta yi suka nufi makarantar daga shiga ajin ba ta yi wata-wata ba ta kwaɗa masa mari har biyu.
"Uban wa ya tsaya maka za ka duki jikalle ta, ka san waye uwarta da abin da take shirin za ma?"
"Faɗa mishi Hajiya. Ƙila ya ɗauka yar gidan talakawa ce, wato ga matsiyaciya ya dake ni ya daki banza, mom zan kira sai ta wulaƙanta kaf zuriyarku."
Malam Aliyu da zuciya ta turniƙe shi sai ya tsaya yana kallonta ganin yadda take zuba uban masifa bakinta har kumfa yake yi.
Malam Kamal ne ya shigo da sauri jin hayaniyar dake tashi a cikin ajin, wanda ya cika da mamakin ganinta tana faɗa.
"Haba Hajiya! in rai ya ɓace bai kamata hankali ya gushe ba. Kiyi haƙuri abi komai a sannu-sannu. Ke Jannah wuce ki shiga aji."
"Ta je ina? Allah ya kyauta, sai ka ce ba ta da gata. Ai tabar islamiyar nan kenan."
"Faɗa musu." Cewarta tana gyara zama hijabinta tare da kaɗa kanta.
Nahlin jin muryarta da ga cikin ajinsu ya sa ta sheƙo a guje cikin ɓacin rai." "Hajiya Baaba, wannan wane irin zubar da ka.."
"Rufe mini baki shashashar banza! Saboda ba ki da hali maimakon ki taso ki ceci 'yar'uwarki, amma kina ji an kamata an yi mata bulala har ɗari saboda rashin mutunci."
"Ɗari?" Suka haɗa baki gurin tambaya. Majina ta ja tare da sakin kuka
"Ƙarya na yi? Haka fa ya rinƙa dukana kamar ya samu jaka." Kama hannunta tayi suka fice ya yin da take yi wa malamin gwalo. "
A hanya jawo mishi tsinuwa d jafa'i ta rinƙa yi har suka shig cikin gida.
"Hajiya Sanyi na ke ji ba ni da lafiya." Tsaki ta buga tare da kama ta tana faɗin,
"Ma za hau gado ki kwanta. Bari na ɗauko ruwan zafi na daddana miki jikinki, haka kawai saboda mugunta ya tashi kashe mini jikata ɗaya tal da na samu."
Murmushin jin daɗi ta yi. "Yauwa Alhamdulillahi na huta da fita zuwa islamiya." Sai ta ɗauki wayarta don ta sanar da daddy.
Hajiya Baaba kuwa hnakalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin tana matuƙar sonta sosai. Gani take kamar Halimatu ce a gabanta. Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi tare da ƙara janyo mata bargon ta rufe ta, don a tunaninta bacci za ta yi.
"Ina sonki fiye da yadda nake yi wa mahaifiyarki, don ma wani lokacin ba ki da mutunci da ko tsinke ba zan bari ya taɓa ki ba." Ta furta a ranta ta ɗauki robar ruwan zafin ta fita bayan ta ja mata ƙofa.
Tana fita ta saki dariya tana rawa. Wayarta ta ɗauko ta kunna data. Numbar Hazaifah ta kira suka fara hira, yayin da zuciyarta ke cike fall da farin ciki, domin ita a ganinta karatun takur ne a gareta, don ko lokacin da take London so huɗu a wata ake mata karatu, kuma duk lokacin da malamin yazo sai dai ta ce ba ta iya ba ya biya mata, don haka take jin kamar an cire mata ƙaya.
Aby na dawowa ko parking bai gama ba Hajiya ta fito tana bambami tare da rantsuwar ba za ta ƙara komawa makarantar ba.
Saboda tsabar takaici kasa ce mata komai ya yi, sai da ya ɗauki tsawon lokaci yana sauraren ta, sannan ya fara ba ta haƙuri cikin ladabi. Girgiza kansa ya yi kawai ya wuce sashinsa.
Haka kuwa aka yi. Hajiya ta shafa ma idanunta toka akan ba za ta ƙara zuwa islamiya ba, duk da irin haƙurin da Aby ya ba ta ya kuma sanar mata da ya gargaɗe su akan ba za su ƙara dukanta ba, amma ƙememe ta nuna ba shi da iko da it ta hana zuwa.
"Ni ma naga ba jahila ba ce, sai da na sauke kur'ani, kuma ɗan haddar nan da hadisai na sani, don haka zan fara koya mata kafin a samu wata makarantar."
Jin abin da ta ce babu yadd zai yi kan dole ya haƙura domin ita ce mai faɗa a ji a gidan. Fatan shi Ubangiji ya ba shi damar yi mata biyayya har ranar da mai rabuwa za ta raba su.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ajmal ba ya nan, domin ya tafi Ƙasar Cairo zai yi tsawaon watanni uku.
A ranar da ake sa ran dawowarsa. Gidan ya kacame da aiki ba matsaƙa tsinke sa toye-toye ake yi, yayin da ƙamshi ya cika gidan.
It kanta Hajiya Baaba ba'a barta a baya ba, gurin zama ta shirya masa tuwon shinkafa da miyar ganye har da dabbu masu rai da lafiya sanin cewar yana so.
Jannah dake falonta tana kallon Arewa24 wani lokacin kuma tama danna wayarta. Juyo wa ta yi ta kalli Hajiya da take ta safa da marwa a kicin ɗin.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo