Showing 126001 words to 129000 words out of 137802 words
Chapter 43 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
ba.
Tabbas ya san ta mace mai addini da aiki da shi, amma ya san tana da mugun zafin kishi wanda tun da suka haɗu ta sanar masa, kuma ko ba ta da zafin kishi dole abin ya taɓe ta, musamman da ta san halin wacce za a kawo mata a matsayin kishiya na kunya da fitsara.
Har bikin ya rage saura sati uku bai samu hanyar sa zai faɗa mata ba. Abin da ya ƙara tada hankalinsa kiran mom ta tambaye shi ranar da za a kawo kaya ya ba su key, wanda ya ji tamkar zai ɗora hannu aka ya yi ta zunduma ihu, domin ta tababata sai ta shigo cikin rayuwarsu da suka tsara daga su sai 'ya'yansu.
A ranar da ya rage saura sati biyu da kwana uku wanda ya zama kwan sha bakwai cip! Hankalinsa ya tashi ya sanya a ransa dole ya gaya mata yau, tun da gobe za su zo danki ga shi Hajiya Baaba, ta kafe kan dole sashin Ajmal take so ya tashi ya bawa Jannah, saboda uban kayan da mom ta yi mata.
Ya shigo cikin gidan cikin rashin karsashi don da ƙyar ya iya fitowa daga cikin motar, tulin kayan da ya siya mota ya ya ɗauko ya shiga ciki falon da sallama yana mamakin dalilin da ya saka har ya shigo gidan ba ta tare shi ba.
Yana buɗe ƙofar da sallama ya ji ta maƙalƙaleshi tana dariya da tsallle.
Tsayawa ya yi yana kallonta, ganin yadda ta cika da matsanancin farinciki, har ya rinƙa tunanin dalilin da zai sanya ta shiga cikin farincikin nan.
"Ka san me Zauji?" Ta ce tare da kai masa kis bayan ta karɓa ta ije abin da ya siyo.
"A'a sai kin faɗa sahibar raina, amma kamar wannan farincikin yana nufin mun kusa zama mu uku a gidan.?"
Ɗan canza fuska ta yi jin abin da ya ce." Ba kuma fa hakan ba ne, ai tun da na yi miscarriage, bab ban samu wani ba."
"Shikenan, is ok babu komai zai zo na yi tunanin wannan ne, in sha Allah next time in aka samu zan yi ƙoƙari na bi dokar likita kar na cutar da babymu."Ya faɗa ganin ta fara hawaye.
Miƙa masa takadda ta yi tana murmushi."Da ga gurin aikinmu aka ba mu zamu je kwas na sati biyu, wanda in sha Allah, in har na ci jararrabawar ina dawowa za a ƙara mini matsayi."
Gabansa ya yanke ya faɗi sosai ganin abin da take shirin yi wanda ya zama dole ya kwantar mata da hankali, saboda ba ta iya shiga damuwa ba, don ba ya manta lokacin ciwon mahaifinta da ya yi ciwo kamar za ta zauce haka ta yi.
Sai ya fara wasiwasin ya gaya mata ko ya ƙyaleta wanda zai zama in har sai ta dawo ana saura kwana biyu bikin ne, anya kuwa ya yi mata adalci kuwa? Amma kuma ba shi da zaɓin da ya wuce hakan.
"Masha Allah! Ina miki murna sosai yaushe ne tafiyarku?" Ya tambaya cikin zullumi da firgici wanda saboda tsabar murnar da take ciki ta kasa gane halin da yake ciki.
"Jibi fa bab, wallahi sun ba ni haushi da suka gaya mana a ƙure kuma duk salon munafunci da baƙincikin karmu ci ne, don ya fi son yarensu su ci, ka san halinsa da mugun nuna tribalism, don haka ga zama dole na jajirce na yi karatu tuƙuru."
"Allah ya shirye shi dole ki dage sosai, kuma in sha Allahu na san za ki ci domin ba ni da haufi a kanki dear Tabbas my you gonna rock it."
Kanta ne ya fasu jin abin da ya ce."Muje na haɗa maka ruwan wanka, ni ma yau zan fara shiri kar na manta da wani abun."Ta ce tare da aama hannunsa suka shiga cikin ɗaki.
Tsakar dare Ajmal ya kasa bacci sai tunani yake yi har ya buga filon da take kwance ya yi kundunbalar faɗa mata, wanda da ta miƙe sai ya kalle shi cikin mamagin bacci.
"Allah Sarki bab, ka tashe ni ko? Ka ga na manta da zan yi karatu ina ta bacci amma da yake kafi ni damuwa da shi ka kasa bacci." Ta ce tare da miƙewa ta shige bayi wanda ya bi bayanta da kallo.
Alwala ta yi sannan ta fito ta yi sallah raka'a biyu ta fara karatu, wanda ganin hakan ya miƙe ya ɗauro na sa alwalar ya fara sallah yana addu'ar Allah ya kawo abin da zai hana auren.
Washegari da safe Ajmal ya shirya zai wuce gurin aiki ya bi ta gidansu.
Yana ƙoƙarin shiga sashin su suka ci karo da Hajiya Baaba da ta fito daga sashin tana wa Adal bambami.
Kallon juna suka yi tamkar wasu abokan gaba sai suka ɗauke kai a tare, wanda hakan ya baƙanta mata rai domin ta so ya kulata ta ba shi na shi kason.
Fici-fici ta yi da idanunta tana kallon shi har ya shige sashi.
"Jarababbiyar tsohuwa kawai." Ya ce sannan ya ja tsaki saboda matuƙar haushinta yake ji.
Hajiya Baaba da ranta ya ɓace matuƙa domin duk tsiyar da take shuka musu ba ƙaramin son jikokin na ta take yi.
Haushin rashin kula ta da bai yi ba ya sa ta dage iya ƙarfinta, ta saka kuka wanda ya sanya shi daina ƙoƙarin buɗe ƙofar shiga falon Ammy da yake yi, yana mamakin halinta domin ya san sharri za ta kulla mishi.
"Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru?" Aby da Ammy suka furta a razane daidai lokacin da suka ƙaraso gurinta, wanda saboda tashin hankali ba su kula da Ajmal da yake tsaye ko kallon gurin sa take bai yi.
"A gidannan, na san an gama mai da ni bolar kowa. Ku yi mini rashin mutunci haka 'ya'yanku, in ban yi kuka ba zuciyata ba za ta taɓa samun sauƙi ba, domin Ajmal ya gama mugun raina ni a gidan nan, kamar ni zai kalla ya yi mini tsaki kamar ma harda zagina ya yi."
Zare idanu suka yi."Ajmal, shi da kansa awaya kenan, ko yaushe ya shiga cikin gidanan."
"Ai dama na san ƙaryata ni za ka yi ba a waya ba fatalwa ya yi ya zage ni. Ko yaushe ka makance da ba ka ganshi ba ya shigo yanzu don ya yi mini tijira ba."
Mamaki ya kama Aby don sai yanzu yaji ƙamshin turrensa wanda ya tabbatar masa yana gida.
"Ajmal!" Ya kira sunan shi da ƙarfi cikin tsananin fushi, wanda ya amsa tare da ƙarasowa gurinsu hankalinsa kwance tamkar ba akan shi take masifa.
"Na'am Aby ga ni." Ya ce yana nazarin fuskokinsu.
"Mahaifiyar tawa za ka zaga, wai mai ya sa ba ka da hankali ne?"
"Ni Aby da yaushe, matar da ko ganinta ban yi ba." Ya ce yana kallonta fuskarsa ɗaure don ya lura sai ya fito mata ta inda ba bata tunani.
"Au haka kace shikenan, abar maganar wataƙila fatalwarsa ce, ka san ba shi da mutunci a zahiri haka baɗini domin Allah kaɗai ya san irin mugun abin da fatalwarshi take aikatawa, ƙila yau rashin mutuncinta ta kaina ya ƙare, amma dai a bar maganar ba wannan ba." Ta ce tare da ɗan jinkirtawa tana kallon su sai kuma ta ɗora da cewa,
"Tun da aka saka rana bai taɓa zuwa ta zance ba, kuma na ga lokacin da yake neman aure, in har ya fita gidannan tun magariba, baya dawowa sai ƙarfe biyun dare yana can yana lalube musu yarinya. To yanzu ita Jannatun nufinsa haka za a kai masa ita a banza babu kuɗin zance?"
Mamakin abin da faɗa ya kama su, sai suka kasa magana suna kallonta wanda ya harzuƙata, ta buɗe baki ciki fushi sai Aby ya tari numfashinta da cewar,
"To yanzu me kike so ay.."
"Magana mai sauƙi ya fara zuwa zance, a yau kuma ba sai gobe ba."
"Aby zuciyata ta fara gaza ɗaukar abin da Hajiya Baaba, take mini da jawo mini raini.."
"To dukana za ka yi, eyee in za ka iya dukar bismillah, dama dukan ne ya rage fitsararre kawai." Ta tari numfashinsa tana faɗin hakan cikin gatsali.
"Mahaifiyar tawa kake gaya ma haka Ajmal? Ma za ka ba ta haƙuri, sannan anjima da daddare ka zo zance gurin Janna.."
"Amma Aby ai..."
"Umurnin nake ba ka ba shawara ba." Ya ce cikin fushin da yake ji na Hajiya Baaba, amma babu damar sauke mata sai dai shi.
Juyowa ya yi ya wuce yana tausayinsa wanda Ammy, ta rufa masa baya tana kallon ɗan na ta da ya yi sororo yana kallonsu ya kasa ko motsi.
"Ka yi haƙuri Ajmal, duk laifina ne da soyayya ya sa na biyewa mahaifinku na aure shi a tunanina in muka haifi Hajiya Baaba, za ta so ni da 'ya'yana, ashe ban sani ba tun da ta tsani ni don ina ƙabila ba za ta taɓa ƙaunata ba." Ta ce tare da share hawayen da suka gangaro mata.
"Yauwa, ka ji abin da ya ce sai kuma ka taho da toshi, don na lura sai an gaya maka, domin daga ganinka mugun maƙo ne da kai, saboda duk zamana da kai a gidan nan, kyautar ka ta girma ba ta wuce dubu ashirin sai aukin siyo ma mutane littafan addini kamar kai kafi kowa sanin Allah." Ta ce tare da ballama masa harara.
"Ba da ni kake yi ba a gidanan, har za ka gani ka yi mini kallon banza ka nemi bangaje ni bayan zagin da na ji kana mini a zuciyarka, za ka sani muje zuwa, ka san kowa ya ci tuwo da ni miya yasha." Ta ƙarashe maganar a gadare tana tafiya tamkar wata sarauniya.
Idanunsa suka yi raurau hawaye za su zo saboda takaici, amma sai ya yi bamijin ƙoƙari ya mayar da su yana jin zuciyarsa na ƙara ɓaci.
Ya jima a tsaye yana kallon inda ta wuce yayin da ya rasa wane irin tunani zai yi. Juyawa ya yi ya fita gidan gabakiɗaya tare da dana-sanin shigowa.
Misalin ƙarfe bakwai bayan an idar da sallah Hajiya Baaba, dake jiran Ajmal ya zo taɗi ta ji shiru har aka yi isha, wanda ranta ya ɓaci sosai, take ta ɗauki waya ta kira Aby da ke zaune a masallaci yana lazimi, wanda ganin kiran sai da gabansa ya buga da ƙarfi, amma ya daure ya ɗaga domin ya san rashin ɗagawar matsala ce.
"Na ji shiru bai zo ba, ko ba ka isa da shi bane?"
"Ban sani dalilin da ya sanya bai zo ba Hajiya, ƙila wani abun ya riƙe shi."
"Muhammadu, in har na isa da kai ma za ka ɗaga waya ka gaya masa ya zo zance. Ai na gaya maka ka yi sakaci da baka ɗauki irin tarbiyar da na ba wanda baka isa na ije kara ka tsallaka ba, amma ka bari wata shashasha can ta ɓata maka tarbiyar 'ya'ya." Ɗif! Ta kashe wayar ta ci gaba da bambami.
Ran Aby ya ƙara ɓaci domin har da damunsa da ya san za ta yi, ya sa ya tsaya a matsallacin da nufin sai dare ya yi.
Wayarsa ya ɗauka yana neman Ajmal wanda zuwa yanzu ya fara ba shi haushi.
"Ajmal, kana son mu saka ƙafar wando ɗaya da kai ko? Na ɗauka idan na yi maka umurni za ka bi, domin a tunanin 'yar Halima ko musaka ce aka ba ka za ka yi mini biyayya ka aura. Ma za ka je zance kamar yadda Hajiya tace."
"Ɗip ya kashe wayarsa don kar ya yi masa ƙorafi wanda jira yake ya dasa ya.
Tsaki ya yi ganin ya kashe wayar yana jin yadd zuciyarsa ke zafi.
Miƙewa ya yi ya ɗauki key ɗin motarsa zuciyarsa cike da mamakin wai za shi zance gurin 'yar fifigiyar yarinyar da baya tunanin ta fara irgar dangi.
"To na ce mata me?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki, wanda tsabar haushi da rashin amsa ya sa ya ije key ɗin tare da komawa ya zauna ya dafe kansa, amma da ya tuna abin da Aby ya ce sai ya miƙe da sauri ya fice gidan cikin tsananin ɓacin rai.
A ƙofar gida ya tsaya sai bai shiga ba saboda kowa haushinsa yake ji.
Har zai kira wayar Ummu ta kira masa ita sai ya fasa ya kira numbar Nahlin, domin gani yake girmansa zai zube don wataƙila ta ce su fito tare.
"Ke Nahlin kira mini wannan mara kunyar yarinyar, tsaƙo zan bata." Ya ce a gajarce yana mamakin kansa da jin haushin kansa da ƙarfa-ƙarfar da ake masa.
"To yaya." Ta ce tare da miƙewa tana kallon Ummu dake kallo a wayarta.
"Where is Jannah?" Ta ce mata da sauri.
"I don't know, but ɗa zu tana nan." Ta ce tana ƙoƙarin miƙewa.
"Kamar tana waje na ga ta sayi sabuwar waya da sim, ina ga numbar Huzaifah take nema. Lemme call her."
"A'a ƙyaleta bari na dubo ta." Ta ce tare fa miƙewa wanda ya sa Ummu ta zauna ta ci gab ada kallonta.
Ɗan tafiya kaɗan ta yi ta hangeta zaune akan kujera a tsakar gida. Gabakiɗaya hankalinta nakan wayar tana ta kira numbar da baturiya ke sanar mata da akashe take amma ta ƙi daina kiran sai hawaye take yi.
Cikin tausayi ta ƙarasa gurinta wanda har sai da ta ɗan tsorata ganinta ya sa ta saki ajiyar zuciya tare da ci gaba da kiran ba tare da ta ce mata komai ba.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 35-36*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Ya is calling ya ce yana gurin aje motoci." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba za ta tanka ba sai kuma ta ji ta ce,
"Wa kenan?"
Haushin tambayar ya sa ta ji tamkar ta tsinka mata mari duk da tana tausayin halin da take ciki. Sai dai, kuma ba ta son rashin zuwanta ya shafeta don haka ta daure ta cije ta ce,
"Ya Ajmal, tun ɗazu ya aiko ni ban ganki ba ina ta neman.."
"Ya makance ne da ba zai iya shigowa gidan ba yake nema na na yi masa jagora?" Ta ce a gatsale bayan ta miƙe.
"Jannah, ki kama kanki tsaƙo ya bani kuma na isar in kin.."
"To kije kice masa na ce ba zan zo ba, Allah ya sa makantar ta tabbata ya dauwama anan har ƙarshen rayuwarsa. In kuma ba makanta ya kama sa ba, to in ya isa ya zo ya jani."
"Jannah, ki fita.." Nahlin ta fara magana cikin fushi dai kuma ta kasa ƙarasawa ta juya ta koma domin ta san ko kasheta zai yi ba za ta zo ba, kuma in ta daɗe duk laifin zai iya ko awa kanta, wanda tuna hakan ya sanya ta wuce kamar kububuwa.
Tsaki ta yi ta ci gaba da neman layinsa tana hawaye.
"Ta ce ba za ta zo ba."
"Ok." Ya ce domin ya yi tunanin hakan wanda har zai ɗaga waya ya kira Aby sai ya fasa tare da yanke shawarar ya je da kansa ya yi mata warning wataƙila ta iya sawa a fasa aure.
Har Nahlin ta juya ta fara tafiya bayan ta yi masa sai da safe a ranta tana tausayinsa na jawo masa raini da aka yi, amma sai ta ji ya ƙwala mata kira wanda ta juyo ta ƙaraso, tana addu'ar Allah ya sa ba ƙara aikenta zai yi ba, domin ita kanta haushin rainin da baƙaƙen maganganun da take faɗi take ji.
"Tana ina ne?" Ya tambayeta ba tare da ya daina danna wayarsa ba.
"Tana gurin bishiyar lemo zaune."
"Shikenan, je ki sai sa safe." Ya ce tare da zaman shi a mota har sai da ta ɓule sannan ya fito, domin kunya yake ji wai shi zai ta ka ya je gurinta.
A lokacin da ta ji alamun tafiya hawaye take yi amma jin ƙamshin da ta tabbata ba na Nahlin ba ne, ya sa ta fara kuka da ƙarfi.
"Wayyo Huzaifah masoyina don Allah ka ɗauki wayata, domin kai kaɗai nake so kuma nake ƙauna, saboda bayan kai kaɗai sauran mazan duk losaraye ne."
Ta ƙaraso tana faɗin hakan kuma ya ji ta bai tanka mata ba.
Hotonsa ta yi zumming tana shafa fuskarsa."Ina matuƙar son gemunka domin na ka baya ka a da irin na bagidajen mazan da suke ajewa kamar na buntsu.."
"Ke!" Ya ce cikin tsananin fushi wanda ko gezau ba ta yi.
"Saboda iskanci na aika a kira ki kika ki zuwa, na zo shine za ki fara gaya mini magana don kin raina ni ko?"
Banza ta yi da shi sai