Showing 24001 words to 27000 words out of 130520 words
Chapter 9 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
ita....
Abdul-Sabur ya cije lebe yayin da hawaye mai
zafi ya yi ta kwaranyowa masa. Ya kasa ci gaba
da magana saboda tsananin kunar da zuciyarsa
ke yi masa.
Faduwa ma ta matse hawaye ta girgiza kai ta ce,
Allah Sarki ka sake tuna min da uwata ita kadai
na
sani a duniya ta tafi ta bar ni.
Umaimah ta runtse ido sai hawaye ya bulbulo
daga idanuwanta masu radadin fita, tabbas itama
ta tuna da tata tsuhuwar.
Abdul-Sabur ya sa hannu a aljihu ya zaro hankici
ya sharbe ido da hanci ya ci gaba da cewa.
''Duk abin nan da ake wai sunan mahaifina yana
raye a duniya ya yi tafiyarsa ya bar mu. Abinci da
yake bari da kudin cefane bai fi na wata guda ba,
sai ya je ya yi watanni shida kuma sannan ya zo
ya yi wata daya ya koma. Sutura sai da sallah
zai yi mana guda daya-daya su ma ba na kirki ba
kafin shekara ta zagayo sun kece.
Mahaifiyata ta so ta dinga rike hannun Khausar
suna zuwa bara, na hana su, na ce su zauna a
gida ni zan fita nema.
Shekaruna goma sha daya na saba da dako a
kasuwar *yan rodi da ke kofar ruwa, nan cikin
jihar Kano.
Tokar itace ce muke daukowa aka mu ke kaiwa
masu karafe, su bamu naira biyu ko uku, a yini
dai baifi na sami naira biyar ba.
Ba zan manta ba akwai wata rana da na dauko
toka aka cikin wani katon daro ashe akwai
garwashi a ciki ban sani ba, tururin zafinne ya
cinye kwalin da na dora a kaina ya soma cinye
gashin kaina, sai da ya fara kona fatar kaina
sannan na ji zafi na yi wurgi da daron, sai ga
gashina kamar anyi gobara.
Ranar babu kudi saboda na zubar da toka ga
ciwo a kaina ba zan iya zuwa na nemo wata ba.
Da kafa na taho gida ga nisa, ga yunwa, ga ciwo.
Ina zuwa gida na iske taron jama,a aka
shaidamin daga Accra aka aiko da wasikar cewar,
mahaifina ya rasu.
Na gigice, na tambaya ina gawar aka ce an
binnne shi a can. Sai na yi mamaki me yasa ba a
kawo shi ba wajen mahaifinsa da *yan uwansa
ba an binne shi? Mun yi kuka sosai, musamman
mahaifiyata, ashe ita
tasan tashin hankalin da zata shiga nan gaba.
Muna nan dai a haka har ta gama takaba, ni
nake fita inayin dako na kawo muci garau-garau
mu kwanta.
Sai naga Malam Barau da abokan mahaifana su
uku suma *yan Ghana ne sun shigo bangarenmu
suka kira Mahaifiyata suka zazzauna. Sai aka
koremu waje ni da kanwata suka ce za su yi
magana. Na kama hannun kanwata muka fice, na
zaunar da ita a kofar gida, sai na dawo na labe
ina so na ji abin da yake faruwa. Kamar yadda
Umma Habibah ta girgiza ta razana da
jin bayanansu, haka nima na dimauce,
innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...
Abdul-Sabur ya yi shiru ya dafe kai ya kasa ci
gaba da magana.
''Me ya ke faruwa?'' Umaimah ta tambata a
gigice. Abdul-Sabur ya dago da jajayen
idanuwansa ya dube su.
Ya ce, ''Allah Ya yi mana maganin masifa, kada
Allah Ya maimaita mana bala,i.
Wato gaskiya ce aka fede ta daga wuya har bindi.
Malam Barau ya fadi duk kulla-kullar da aka
harhada wajen auren Umma Habibah aka ce shi
ne mahaifinsa alhali shi bai san shi ba, sai a
sanadiyyar kasuwanci.
Malam Barau ya kara da cewa shi ya ke basu
masauki idan sun kawo kaya daga Ghana. Ashe
zaman nan da muke yi agidan Malam Barau haya
ce muke yi, duk shekara mahaifina yana biya. Don
haka babu hadin mahaifina da Kano, danginsa
dukka suna Accra.
Wadannan da suke tare da Malam Barau sune
abokansa daga Accra su ma suke zuwa tare da
mahaifina, su ne ma suka kawowa Malam Barau
labarin rasuwarsa. Sun shaida cewar iyaye da
kakannin mahaifina *yan Accra ne. Mahaifinsa ya
rasu Mahaifiyarsa na nan a raye wato kakarmu.
Kuma yana da *yan uwa da yawa wadanda suke
uwa daya uba daya, da wadan da suke uba daya
kawai. Sannan yana da mata biyu a can da
*ya*ya takwas.
Bai fada musu ya yi aure a Kano ba har ya haifi
*ya*ya biyu ba, sai bayan rasuwarsa aka fada
musu sun ce babu ruwansu tunda bai fada musu
da bakinsa ba. Suka rabe gadonsu duk da
hotunanmu da aka nuna musu a cikin kayansa.
Kenan mu mun tashi a tutar babu, ba mu da gado
a can, a she a nan ma ba gidanmu ba ne.
''Allah Ya isa tsakanina da ku da shi da ya mutu,
kun ci amanata.'' Kalmar da Ummana Habibah ta
dinga fada ke nan, ta tashi da gudu ta shiga daki
tana kuka. Subhanallahi! Sai na sulale na tsuguna
na rike kai, har su Malam Barau suka fito suka
iske ni a inda na labe. Sai suka tausaya min.
Baba Mukhtar daya daga cikin abokan Babana ne
ya jawo hannuna ya rike ya ce, ''Yi hakuri Abdul-
Sabur ka zama jarumin namiji ka taimaki
mahaifiyarka da kanwarka. Gata daya zaka yiwa
kanka a duniya shi ne ka yi karatu, ka shiga
makaranta ka dage ka yo karatu duk runtsi,
sannan rayuwarka zata yi haske.
Ya damko kudi daga aljihunsa ya mika min,
sauran abokansa ma suka bani kudi mai auki
kuwa, suna tafiya ban shiga gida ba, sai na je na
kama hannun kanwata. Na ce da ita, ''Zo muje nu
shiga makarantar boko. Da rana tsaka head
master makarantar gwamnati ta unguwarmu ya
ganni a cikin ofishinsa. Na yi masa bayani ya
fahimce ni amma bai gamsu ba har sai ya ga
manya na, ya ce na je na taho da wani babba.
Na je na sami Malam Barau na shaida masa, sai
ya yi dariya ya ce, kada na bata lokacina wajen
yin boko,
na tafi kasuwa kawai. Na fito na je na sami
mahaifiyata na ce, ta zo ana nemanta a
makarantar boko. Sai ta yi mamaki da jin haka,
ta hau rawar jiki ta dafe kirji ta tambaye ni ko
lafiya. Na shaida mata lafiya kalau, Khausar ma
na can a ofishin shugaban makaranta shi ya ce
na kira babba.
Sai ta gigice ta dauka laifi ta yi, ta hau karkarwar
jiki muka dunguma muka je. Da muka isa sai ta
tambaye shi ko lafiya, me muka yi? Sai shugaban
makarantar ya yi mamaki da jin kalaman
mahaifiyata, amma sai ya yi mata bayanin abin
da na zo da shi.
Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni na turo su ba, ba ni
da kudin da zan iya saka su a makarantar boko.
Shugaban makarantar ya ce, ''Ah babu abinda za
ki biya makarantar gwamnati ce, sai kayan
makaranta da litattafai, wasu littattafan ma ana
basu a makarantar.
Ta ce, ''Ba ni da kudin siyen kayan makarantar
ma,
idan ma ya fara zuwa makarantar waye zai je ya
yi dako ya samo mana abin da zamu ci?
Ai shi ne mai fita nema dan haka ba ma son
karatun.
Na fito da kudi daga aljihuna na ce, ''Ina da kudi,
Baba Mukhtar ne ya ba ni suka ce na shiga
makarantar boko shi ne kadai zan yi wa kaina
gata.
Shugaban makarantar ya yi farin ciki dajin haka.
Ya ce, ''Wannan haka yake yaro, ka daure ka yi
karatu. Hajiya ki barshi ya yi karatu don inganta
rayuwarku gaba daya''.
Ba ta da ta cewa, sai ta yi min addu'ar Allah Ya
sa albarka a karatun da zanyi, sai dai Khausar ce
ake ta shawara a kanta, na ce a saka mu a aji
daya.
Daga makarantar kasuwa muka wuce da
Ummanmu Habibah ta yankar mana yadin
makaranta, aka kawo wajen tela ta dinka mana,
muka fara zuwa makaranta. A aji daya aka
sakamu,
*yan ajin namu duk yara ne dai-dai Khausar, na fi
duk *yan ajin girma a haka dai nake zuwa duk da
tsokanar da nake sha a wajen yara wai gardi a
cikin yara da dai shauransu.
Ban damu ba haka nake zuwa makaranta idan na
dawo na tafi kasuwa neman kudi, sana,a kala-
kala babu irin wacce bana yi ta karfi. In samo
kudi na zo muyi tuwon masara miyar kuka,
kullum shine abincin mu.
Malam Barau ya yi mana mutunci bama biyan
haya a kyauta muke zaune, ya ga babu yadda
zamu yi. Nine monita a ajinmu na fi kowa
kokari daga ni sai kanwata Khausar ta iya karatu
radau a baki, nan da nan ta fara iya rubutu itama
kai ka ce daman an taba koya mana a gida.
Muna aji uku na firamare Malam Barau ya rasu,
ko wata daya bai yi ba iyalansa suka ba mu
lokaci mu tashi daga gidansu.
Tashin hankali ya same mu, ba mu da mafita sai
dai mu koma Gwarzo wajen danginta, duk da bata
da uwa da uba tana da *yan uwanta da dakinta
na gado duk da na kasa ne. Can muka kaura
muka zauna, sai na samu aka yimin cuku-cuku
na shiga sakandiren maza ta kwana, na bar
Khausar a gida suna ta sana'ar cura fura ita da
Ummarmu.
Ba laifi talauci ya ragu saboda rayuwar kauye ta
fi ta birni sauki, duk inda kaa samu rogo da gyada
ka ci na naira biyar sai ka yini kana shan ruwa.
Mahaifiyata ta yi wani auren a cikin Gwarzo ta
tafi da Khausar ni aka bari a cikin gida wajen
dangi yau na kwana a nan gidan, idan an min gori
na koma wani gidan. Har na fi so na koma
makaranta idan mun yi hutu dan na fi jin dadin
makarantar, saboda ina tare da abokaina *ya*yan
masu hali dakikai, ni nake ba su amsa su kuma
su bani kudi ko biskit da madara.
Allah ba Ya hadawa mutum daya komai, ni ya
bani kokari Ya hanani dukiya, su Ya yaye musu
talauci, Ya dauke kwakwalwar.
Mahaifiyata ta haifi *yan biyu a gidan sabon
mijinta mace da namiji, Hassan da hussaina. Da
ta sami ciki na biyu kuma a garin haihuwa ta
sami matsala har ta rasu a garin haihuwa, ta
mutu ba ta haifi cikin ba.
Muka zamo babu uwa babu uba....
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Faduwa da Umaimah suka hada baki suka fada.
''Allah Sarki, Allah Ya jikanta. Inji Umaimah.
Faduwa ta rushe da kuka, daga dukkan alamu ta
tuna ranar da ta rasa ta ta mahaifiyar ta rasu.
Abdul-Sabur ya goge hawaye ya ci gaba da
cewa.
''Dangin Baban Hassan da Usaina suka dauke su,
ni da kanwata ce abun tausayi. Ina makaranta ina
tunanin Khausar saboda na san babu mai kula da
ita. Sannan idan na dawo ba jin dadin halin da
nake
zuwa na iske ba nake ji, abinci a wulakance ake
ba ta, haka babu mai kulawa da lafiyarta da
tarbiyarta.
Ba zan manta ba, muka yi fada da wani dan
yayar Ummarmu mai suna Gali, ya yi min gori
wai shegu wadanda ba'a san asalin Babansu ba.
Tun daga lokacin na kuduri aniyar sai na nemo
dangin Mahaifina.
Ina aji hudu a sakandire na daina zuwa
makaranta na shiga aikin gona sosai, muka sami
amfanin gona a gonar Mahaifiyata data bar mana
gado, na siyar da abinci buhu-buhu na kunshe
kudina na boye. Na dawo Kano na sami Yaya
Bala babban dan Malam Barau na ce ya kai ni
wajen da su Baba Mukhtar suke sauka, abokan
Babana.
Na ci sa'a kuwa sun zo gari a lokacin, ya kai ni
har masaukinsu. Sai suka yi mamaki da ganina,
bayan mun gaisa sannan na shaida musu
Ummana Habibah ta rasu, sun girgiza da jin haka
sun tausayamin gami da yi mata addu'a Allah Ya
jikanta da rahama. Na ce musu so nake su kaini
wajen
dangin Mahaifina a Accra. Sai suka hau kame-
kame da alama basa so su kai ni, na ce ni dai ina
so na je na gansu. Yadda na fuskanta gudun
wahala suke,
sun dauki ba ni da kudin mota. Da na nuna musu
kudina sai nan da nan suka yarda zan bi Baba
Mukhtar dan shine zai tafi kwanakin.
Muka ci gaba da hira na shaida masa cewar zan
tafi da kanwata Khausar. Ya ce, a,a na ja dai ni
kadai tukunna, na ce a'a nafi so naje da kanwata
tunda Kakarmu na nan mu zauna tare da ita
saboda bamu da kowa a nan. Muka shirya ranar
tafiya ya ce na je mu shiryo mu zo mu tafi wani
satin.
Na ke na sanarwa Khausar, ya amince, sannan
muka je muka yi wa dangin Mahaifiyata sallama
na ce zan bi wani dan uwan Babana Accra za mu
ga dangin Mahaifinmu. Wasu sun amince, wasu
basu amince ba, daman ba amincewar su muke
nema ba,
don babu wanda ya ke tsninana mana komai.
Zumuncin yanzu ya zama kamar shuka gyada a
bakin kurege.
Kawu mai kudi ne Yaya ne ga Umma Habibah
Babansu daya ya dage ba zamu ta fi ba saboda
ba'a san wanda zamu bi ba yadda duniyar nan ta
zama abar tsoro. Sai na je na kirawo Baba
Mukhtar ya je har Gwarzo ya yi musu bayani.
Sun
gamsu ya san Mahaifinmu amma dole aka ce sai
an hada mu da wani Babba ya raka mu. Da aka
yi shawara sai aka ce Shehune zai raka mu shine
mai bin Ummana Habibah a dakinsu, muka
dungumo
muka taho tare zuwa Kano tashar Unguwa uku,
muka wuce kai tsaye, muka hau doguwar motar
nan zuwa Lagos da magruba. Ba mu isa Lagos
ba sai da sassafe, sallah kadai muka yi muka
sayi gayan biredi da ruwa muka ci
muka sake shiga wata mota wacce zata kaimu
har Accra. Tafiya yankin azaba, mun gaji likis ga
yunwa, saboda wahala ta yi ta amai saboda
rashin sabon shiga mota da ba ta yi. Ledoji aka
yi ta bata tana cikawa ana jefawa ta wundo.
Da muka zo bodar Abijan, Immigration suka
tsayar da mu suka sa kowa ya firfito suka ce
kowa ya fito da passport dinsa. Masu shi suka
fito da su, irin su
Baba Mukhtar. Mu da ba mu da shi sai
hankalinmu ya tashi. Baba Mukhtar ya ce, na
kwantar da hankalina dan kudi kawai zamu rike a
hannu maimakon Passport
sai mu sunna musu cin hanci, sai zance ya wuce.
Haka kuwa aka yi, na rike naira hamsin na bawa
Khausar da Kawu Shehu suma suka rike, da aka
zo kanmu sai muka mika musu kudi, suka karbe
aka ce mu koma cikin mota mu zauna, aka ci
gaba da tafiya (cin hanci ruwan dare).
Haka da muka zo bodar Togo ma immigration
suka tsayar da nu irin na bodar Abijan aka yi,
naira hamsin ta raba mu da su muka wuce daga
nan har cikin Accra babu matsala kuma. GHANA,
ACCRA
Mun isa Accra daf da magruba muka sauka a
tashar Aflawu, daga nan muka dauki tasi muka
nufi
'Lagon New town' a in da gidan Kakarmu ya ke.
Sunanta Husaina suna kiranta da Ummana Fuse.
Da yake ta san labarinmu daga wajen Baba
Mukhtar, tana ganin Baba Mukhtar da yara biyi
jikinta ya bata mu ne, sai ta fashe da kuka ta
rungume mu.
Mahaifina kamarsu daya sak da mahaifiyarsa,
haka Khausar tayi kama da su sak, bakake ne
sannan ba su da tsayi sosai masu dogon hanci.
Ni kuwa da mahaifiyata nayi kama, don ita farar
bafillatana ce, doguwa ga ido da hanci.
Ghana kasa ce da take dauke da kabilu daban-
daban, arna sunfi yawa duk inda kaga musulmi
Bahaushe, to zuwa ya yi kamar daga Niger ko
Nigeria.
Manyan yaren kasar guda biyu ne, Ankara da
Asanti. *Yan yaren Asanti su ne asalin *yan
Ghana sun fitone daga Kumasi, akasarinsu gajeru
ne bakake. Ankarawa kuwa farare ne masu bille
sunfi *yan kabilar Asanti kyau. Su ma ana tunanin
zuwa suka yi shekaru aru-aru da suka wauce.
Sunan kudinsu CEDIS wanda ko rabin darajar
Naira bai kai ba, idan ka ji ance Cedis 1000
tabbata bai wuce naira 10 ba.
Washegari kakarmu Ummana Fuse ta aika aka
hado mata *ya*ya da jikokinta ta gabatar damu.
Babu
tantama kowa ya shaida mu ma *ya*yansa ne,
daman can suna da labarinmu. Da bakinsa ya
shaida musu cewar ya yi aure a Nigeria har yana
da *ya*ya biyu, amma fa sai daf da zai mutu ya
fada.
Mu ne dai bai fada mana ba yana da wasu matan
da yara a can.
Gado dai an rabe, daman ba wani abin kirki ya
bari ba. Sai suka yi ta zukewa kowa yana gudun
wahala aka rasa mai rike mu. Ummana Fuse itace
dolenmu don haka wajenta muka zauna. Gida ne
a gine ginin sumunti daki biyu da tsakar gida,
*ya*yanta suka gina mata a unguwa mai kyau.
Bayan
wannan kuwa babu wani abu da suke ajiye mata,
komai ita ta ke nema ta yiwa kanta. Sana'ar kera
tukwane na kasa take yi kuma ba wani kudin kirki
ta ke samu a yini.
Ta shaida mana cewa a garin nan babu mai
zaman banza, kowa fita yake ya nemi abinda zai
ci,tun daga
safe zuwa dare. Idan ka zauna a gida babu mai
baka, haka mata da maza, yara da manya suke
yi. Ga su da nuna kabilanci, Hausawa koma na ce
Musulmi ba su da karfi a kasar wajen yin mulki
ko samun aikin gwamnati.
Babu karatu babu aikin gwamnati don haka
sana'ar karfice ta wajaba akansu. Ummana Fuse
ta sa aka
samo min aikin jiran shago a wani kantin dan
uwanta da yake kasuwar Art Traditional Tourism
inda suke siyar da kayan gargajiya, kamar
takalman fata, abin wuya na dutsuna, gangam
hula dara, kayan kinta (yadi) da dai sauransu.
A nanne zaka ga Turawa daga kasashe daban-
daban suna zuwa suna kallo, kuma suna siya.
Abinka da Nasara asarar duniya, sun fi sha'awar
irin wadannan abubuwan na gargajiya. Ciniki ake
yi sosaikullum nake zuwa tun daga safe har
zuwa magruba.
Cedis dubu biyar yake ba ni kwatankwacin naira
dari kudin Nigeria, kasancewar kudin Ghana ba
shi da daraja kamar yadda na fada a baya.
Cedis dubu biyar din nan abinci kadai nake iya ci
na rana da dare, shi ma kuma ba don na koshi
ba,
kuma babu nama. Dukunu da Tankwa nake ci
kullum, shi zai fi kosar da ni, don ya fi arha.
Umaimah ta dubo shi, ya ce, ''Meye dukunu da
tankwa kuma?
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya ce, ''Abincin *yan
Ghana ke nan. Dukunu shi ne kamar tuwo,
tankwa
kuwa ita ce miyar da ake ci da shi.
Idan aka jika masara ta kwama sai aje a markado
sai a dan dafa ya yi kauri shi ke nan sai a ci da
tankwa.
Tankwa kuwa kayan miya ne da attaruhu, albasa
da tumatir ake murjewa a asanka.
Kanwata Khausar kuwa a kasuwar Agulgoshi aka
kai ta nan ce kasuwar da ake siyar da danyen
kaya buhu-buhu, ana saukewa daga mota-mota.
Shagon wata mata mai suna Hajiya Momi tana
sayr da bainci, Khausar ta ke taya ta dafawa da
siyarwa.
Suna siyar da shinkafa da miya, Dukunu, muri da
Algilma, su yi miyar gyada ko miyar kwakwa.
Idan kuna neman muguwar mata aka samu Hajiya
Momi to aja layi a tsaya, saboda bata da tausayi
ta
wahalar da kanwata Khausar, ba kudi ta ke ba ta
ba, abincin rana da na dare ne kawai ta ke ci ta
koshi. Sai shegen fada da duka kullun ta ke yi
mata bayan aikin da ya fi karfinta, da ta ke jifga
mata.
Idan ku kaga daron da ta ke dauka a kanta ta kai
markadem kayan miya da markaden masarar yin
Dukunu sai kun tausaya mata duk da dai ba wani
nisa ne ke da akwai ba tsakanin inda suke
kasuwancin da gurin kai markaden.
Gashin tsakiyar kanta har saisayewa ya ke yi
saboda daukar kaya. Idan abinci ya yi kwantai
akai
zata dora mata ta yi zagayawa gari sai ta siyar.
MAKWABTAKA 15
Khausar kullum tana kuka da zarar gari ya waye
saboda fargabar wahalar da zata je ta tarar a
kasuwa. Ni da kakata abin nan ya fara isarmu ita
ba kudi ta ke kawo mana ba, don ba ta biyanta
komai. Da kakata ta yiwa Hajiya Momi magana
akan ta rangwanta mata wahala, ta kuma dinga
biynata
kudi, sai ta ce sai dai idan ta daina aikin saboda
abincin da ta ke ci ma ai na kudi ne, mai yawa.
Dole muka bar Khausar ta ci gaba da yi don idan
ba ta yi ba wa zai ba ta abinci ta ci, kowa yana
ta kansa? Ana cikin wannan hali ne sai Allah Ya
kawo wani kawunmu Hamza