Showing 102001 words to 105000 words out of 130520 words
Chapter 35 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
farko data taba yin karatu
mai zurfi kuma ma ba akasar nan ba a kasar
waje.
Rashin sani yafi dare duhu bata san kuncin da
Ilah yake ciki ba a yau har ya fi nata saboda yaga
alamar Abdul-Basi da gaske biko yake nema. Ya
kasa zaman gida ya kaura gaba daya bakin rafi
ya zauna yana lazimi.
Hehehehe..
Duk naku wasa ne kallon ku kawai nake naga iya
gudun ruwan ku.
Dan Umaimah ta dan Aunty ce..
MAKWABTAKA 44
A lokacin da Umaimah take fama da baki a cikin
gida, Abdul-Basi ya tara dattijai masu fada aji a
gari
cikin zauran gidan, yana yi musu bayanai da basu
hujjoji da zasu yarda dashi a tilastawa Umaimah
ta koma gidansa.
Daga duk alamu ba alfarma ya ke nema ba illa
shi ne zai yi musu alfarma saboda ya na ganin
su
kidahumai babu boko, ba wayewa, ga talauci, na
masara da dawa kawai suke nema.
Baffa da Sabitu suna gefe ba su ce komai ba
daga dukkan alamu ba su yi amanna da
bukatunsa ba.
Abdul-Basi ya kula da haka sai ya tuno wata
hanya wacce zai bi ba sai ya bi ta wajen Baffa ba
kuma ita
ce hanya mafi sauki da zai cimma burinsa,
daman ta inda a hau tanan ake sauka ba da
Baffa suka yi magana ba, da Dagaci suka yi
magana tun a lokacin auren Nasiba dan haka da
ya gama dandankawa dattijai na goro sai ya
dunkulo kudi mai dan yawa ya ajiye a gaban
Baffa da Sabitu ya mike tsaye ya ce
zai je ya gaida Dagaci.
Da kafa ya tafi ya bar bar motarsa a kofar gidan,
yana fita Baffa ya juya ya kalli *yan uwa da
abokansa na zaune a wannan zauren ya ce,
''Kada ku yi gaggawar amsawa Abdul-basi, yanzu
ba ra'ayinmu za'a bi ba ra'ayin yarinya za'a bi
tunda ita ce ta zauna da shi ita ya wulakanta
kuma ya wahalar, ita ce kuma nan gaba zata
zauna da shi dan haka sai abun da ta zaba za'a
yi.
Wasu daga cikinsu suka gasgata da maganarsa,
wasu kuwa suka ce ba zai yiwu ba, ba za'a bi
ra'ayin yarinya ba, dan ba ita ce ta haife su ba
su suka haifeta. Ko dan tayi ilimi tayi kudi shine
zata gagari manya?
To in shi ba zai iya tsawatar mata ba saboda ta
aiko masa da makudan kudi yayi jari su zasu iya
tsawatar mata.
Surutai dai barkatai suka dinyi suna fada harda
kumfar baki.
Sabitu ya kufula ya bude baki zai yi magana,
Baffa ya hana shi. Haka aka tashi daga taro
baram-baram
Baffa da Sabitu ne kawai suka rage a zaune a
zauren.
Baffa ya ce Sabitu ya shiga gida ya kira masa
Umaimah, shigar Sabitu gida ba dadewa sai ga
shi da Umaimah sun bayyana a gaban Baffa.
A gigice ta fito yayin da zuciyarta ta dinga dukan
uku-uku ta san maganar dai ta Abdul-Basi ce.
Fargabar da take yi ita ce wanne hukunci Baffa
ya yanke akan maganar, tafi kyautata zaton Baffa
yana goyon bayan Abdul-Basi yin hakan kuwa da
Baffa zai yi ba karamar matsala zai tayar mata
ba, dan ba zata bi ra'ayinsu ba. *Ya*yanta suna
makale da ita suka zazzauna.
''Baffa lafiya na ganku a cikin damuwa?
Umaimah ta tambaye shi cike da rikicewa.
Ya dago a hankali ya dube ta tabbas har yanzu
babu annuri a fuskarsa. Ya gyada kai ya ce,
"Umaimah na shiga matsanciyar damuwa akan
maganarki da Abdul-Basi, yana son ki koma
gidansa, dangina da abokaina suna son ki koma.
Yaya kike gani?
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Baffa, ka tuna a
sanda Abdul-Basi ya kore ni, kunya nake ji wani
ma ya ji abunda yayi min. Kai kanka ma kasa
fada maka nayi ina ta rufewa ina ganin kamar zai
zo ya
mayar dani. Ya juya min baya bai sake waiwayata
ba balle yasan wanne hali nake ciki. Alokacin
koda na fito da maganar wadannan mutanen nan
da kake kiransu *yan uwanka, abokanka babu
mutum daya da zai iya tashi ya je ya cewa
Abdul-Basi bai kyauta ba, ya zo ya mayar dani.
Daga masu murna da surutu, suna yada zance,
sai wadanda za suyi dariya suce Allah Ya kara,
babu wanda yasan wahalar da na sha, na dinga
garari a garin Gombe har hannun karuwai na
kusa fadawa, Allah ne Ya kiyaye ni ka tambayi
Sabitu duk na bashi labarin yadda aka yi.
Baffa zamani ya canja, kan mage ya waye, ka
rabu da ra'ayin mutane ka yi abunda ya dace da
kai. Maganar gaskiya ita ce Abdul-Basi yayi
sha'aninsa in yi nawa ba zan iya aurensa ba, dan
zamanmu a
yanzu ba zai yiwu ba.
Baffa ya nisa ya ce, "Bakya tausayin yaran nan
da suka shaku dake, ki duba kiga yadda suka
rirrikeki basa so ku rabu.
Umaimah ta dubesu ta sirnano da hawaye mai
radadi ta ce, ''Rayuwarsu, cinsu, shansu da kariya
duk yana hannun mahaliccinsu. Shi Ya rayasu a
lokacin da suna kanana basu ma kai haka ba na
tafi na bar su, ina kuka suna kuka Abdul-Basi ya
rabamu. Duk inda suke ina yi musu addu'a kuma
zata isa gare su, duk daren dadewa za su zo
inda nake.
Baffa ya girgiza kai ya ce, ''Bakya ganin zan
zama abin tsana a wajen Dagaci da sauran
jama'ar gari idan na bi bayanki?
Yanzu ma an yi min gori wai dan kin yi ilimi, kin
yi kudi, kin aiko min da jari shiyasa bana iya
tsawatar miki.
Umaimah ta ce, "Abun da na gama fada maka fa
kenan, ka bi ra'ayinka ka rabu da mutane dan
mutane ba'a iya musu. Su je suyi magana har su
gaji su daina babu abinda zai shafe mu.
Duhu ya gushe haske ya zo, kai yanzu ya waye,
talauci ya tafi. Babu abinda yanzu wani zai iya yi
maka wanda bazan iya yi maka shi ba, daga
Abdul-Basi har Dagaci balle
abokanka. Ka toshe kunnuwanka, ka rufe
idanuwanka, ka zamo baka ji baka gani su je su
ce duk abunda zasu ce.
Sabitu ya kyalkyale da dariya ya yi tafi ya ce,
''Yayi daidai Adda Umaiman, maganarki haka
take.
Baffa ya girgiza kai ya ce ''haka za ki ci gaba da
zama a cikin Rugar nan ba aure, ko birni zaki je
ki kama gida ba aure ki zauna?
Ai sai a zage mu.
Umaimah ta gyara zama yayin da ciwon da kanta
ke yi ya sake tsananta ta ce, "Ba'a kaina mace
take zama a gidansu ba idan aurenta ya mutu ba,
har zuwa ranar da Allah Zai aiko da wani mijin
ayi aure.
Me zai hana ni zama a gidan nan tunda anan
Allah Ya rubuto min, anan aka haife ni harna
girma, anan zan zauna inci gaba da rayuwata irin
ta da. Ba zan koma birni da zama ba duk da
cewa ya kamata in fara aiki sai in hakura da
aikin, nima nasan bai kamata a ce ina zaman
kaina ba a can. Ni dai zan
hakura da duk wani jin dadi da zan samu in dai
sai na koma gidan Abdul-Basi.
Baffa ya ce, ''A tsakanin Rugagen nan wanne
namiji kike gani zai iya tunkararki da maganar
aure?
Kowa gudunki zai yi saboda kinfi karfinsu babu
mai iya aurenki. Idan Ilah kike so har yanzu
shima yana sonki, amma kinsan halin Matawata,
kin kuma san irin tashin hankalin da aka yi a
baya.
Umaimah ta yi murmushin takaici ta dubin yaran
da suke kwance a jikinta ta yi magana cikin
harshe turanci ta ce su tashi su shiga gida zata
shigo itama yanzu.
Yara masu hankali da jin magana suka tashi
cimak suka shiga gida.
Ta dubi Baffa ta juya ta dubi Sabitu ta ce, ''A
yanzu ba ni da wanda nake so a duniya irin
Abdul-Sabur,
shine kadai namiji daya da halayyarsa suka yi
min, kuma wanda zan iya zama da shi in yi masa
biyayyar aure.
''Waye Abdul-Sabur?
Baffa da Sabitu suka hada baki suka tambaye ta.
Ta yi mumushi kuma hawaye ya cika mata ido ta
gyara zama ta fara basu labarin Abdul-Sabur. Ta
fara da fayyace musu asali, yare, da kuma kasar
da ya fito, ta fada musu a inda suka hadu da
yadda
akayi suka hadu, yadda aka yi suka saba da
dalilin da ya sa ta fara sonsa da yadda
kyawawan halayensa suka saka take marmarin
aurensa sannan ta fada musu yadda suka rabu.
Sai suka tausaya mata saboda suma sun san ta
rasa Abdul-Sabur din data ke so.
Baffa ya ce, "Zaki ki auren mutumin da kike da
shi a hannu saboda mutumin da baki da tabbacin
ko
zaki sake ganinsa a rayuwarki ba? Kuma har ya
fada miki da bakinsa ya tafi ya auri *yar uwarsa.
Dadin dadawa kuma bai ma san kina nan kina
sonsa ba, dan haka ko yana sonki ba zai yi
garajen nemanki ba.
Ta sharce hawaye ta gyada kai ta ce, "Wannan
haka yake, ko ban same shi ba na tabbata shi
nake so kuma zan sami wani makamancinsa
amma ba Abdul-Basi ba.
Kafin ta rufe bakinta suka ji sallama suka daga
kai gaba daya suka kalli me shigowa, Musa ne
daya daga cikin fadawan Dagaci, ya duka ya
gaishe da Baffa ya shaida masa ana kira a fada.
Baffa da Umaimah suka zurawa juna ido can
Umaimah ta juya ta dubi Musa Ta ce "Malam
Musa, ka je ka ce gashi nan zuwa Ya fice da
sauri da sauri, ta dubi Sabitu ta ce ''Ka raka shi
dan ka karfafa masa gwiwa ka da ya ga idon
Dagaci ya ji nauyinsa ya amsa musu abinda suke
so ni kuma in cutu.
Baffa ya dakatar da ita da hannu ya ce "Yi shiru
shiga gida ki bar ni da su ni na san amsar da zan
basu.
Ya tashi da sauri ya fice Sabitu ma ya bi shi a
baya, sai ta daskare a zaune tana kallon ikon
Allah,
mulkin mallaka kiri-kiri ake yi musu tuntuni ashe
rashin ilim ya hana su ganewa. Ta dade a zaune
sannan ta tashi ta shiga gida, ta iske *ya*yanta a
tsugune a tsakar gida sunki yarda su shiga daki.
Su Nene da sauran baki sun yi fillancin
duniyarnan akan su zo su zauna suka ki.
Umaimah tana shigowa suka taso da gudu suka
runguma ta, ta ja hannayensu suka shiga daki.
Cikin lungu ta shige ta dinga shirgar kuka amma
a wayence bata son yaran su gane. Allah Yayi
dare gari ya waye ta dawo kasarta har matsaloli
sun sake dawo mata.
Idan ta dubi yaran sai su bata tausayi su ne
kadai suka saka take ragawa Abdul-Basi tana
gudun kada ayi baram-baram ya hana ta ganin
yaran ma gaba daya, dan kadan daga cikin
aikinsa.
A haka ta daure take dan cin abincin nan dakyar
take hadiyewa, saboda babu kamshin curry, bana
spies, sai karni take ji a hancinta yayin da
harshenta ya gauraye da zakin kafi zabuwa babu
magi, nan da nan ta ji zuciyarta ta fara tashi
kamar zata yi amai.
Su kuwa su Babangida da yake yara ne sai suka
ji dadin abinci miya mai zaki cakwai.
Duk da gajiya, barci da ciwon kan da yake
damunta bata so ta fara bude akwatinan tsaraba
yanzu ba amma ya zama dole ta bude taci biskit
da butter tunda ta kasa cin abinci kuma ta dauko
tsarabar da
ta siyowa yaranta su tafi da ita taga alama yau
ita da Abdul-Basi zasu rabu baram-baram, idan
aka yi
haka kuwa ba zai sake kawo mata su ba.
Jaka guda ta cika musu da kayan sakawa,
takalma da alewowi da a wata shida ma ba baza
su iya shanyewa ba duk shan da zasu yi, bayan
wacce suka sha suka gaji a gidan. Duk wanda
zata tafi sai
Umaimah ta zabo abin da ya dace da ita ta bata.
Tabbas haka ne duk abinda ta siyo, anan suna
ganin darajarsa, tunda ba su taba ganin irinsa ba
sai taga sun barke da murna da zarar ta mika
musu.
Godiya da shi albarka abun baya kirguwa suke
tayi mata.
Baffa kuwa ana can ana ta fafatawa a fadar
Dagaci shi da Abdul-Basi. Yayin da Abdul-Basi ya
cika da mamaki a lokacin da yaga Baffa ya fara yi
masa musu, alhali a da duk abin daya fada sai ya
zauna yayi daidai.
Baffa ya murje ido bai ji nauyin Dagaci ba haka
bai ji shakkar Abdul-Basi ba ya ce ba shi da
magana da Abdul-Basi sai dai da manyansa.
Nan fa gizo yake saka dan mahaifin Abdul-Basi
ba zai zo Dugge ba da niyyar biko saboda sun
boye masa a lokacin da suka kori Umaimah san
sun san idan yaji zai ce a dawo da ita ko ya hana
auran Zulayha. Sai da ta sami fiye da shekara
sannan ya ji a gari cewar Umaimah basa tare da
Abdul-Basi.
Dan haka har yau ya ki maganar zuwa bikonta,
yayi fushi ainun, don sun zubar masa da mutunci.
Abdul-Basi ya san ba zai iya tarar Alhaji yayi
masa maganar bikon Umaimah ba dan haka sai
ya nemi su sulhunta a tsakaninsu shi da Baffa,
amma Baffa ya kekasa kasa ya ce sai Alhaji ya
zo, ko bayan ya zo din ma sai an kira Umaimahh
ta fadi ra'ayinta.
Tabbas Baffa shi zai kawowa Abdul-Basi cikas,
dan haka sai hankalinsa yayi matukar tashi ya
fuskanci ba tunanin Baffa ba ne wannan mai ilimi
ce ta karanta masa abunda xai ce.
Dagaci yayi amanna da bayanan Baffa cewar ya
turo magabatansa. A haka aka tashi daga taron.
Cikin fushi Abdul-Basi ya shiga mota ya zauna ya
aika cikin gidan ya ce Babangida da Bilal su fito
su tafi. Sai suka ki fitowa wai su sai tare da
Umaimah.
Ta ji hankalinta ya tashi ta shiga lallashinsu tana
yi musu dubara iri-iri tace itama gobe zata hado
kayanta ta biyo su. Suka ki amincewa, sai da
karfin tsiya ta ce Sabitu ya dauke su saboda sai
danna horn din mota Abdul-Basi yake yi a fusace.
Suna kuka kamar ransu zai fita aka banbare su
daga jikinta suna kiranta suna cewa "Mu a wajen
Aunty Umaimah zamu zauna. ''Su da jakar
tsarabarsu a ka jifge a baya.
Yayin da Abdul-Basi ya daka musu tsawa guda
daya ta wadatar suka yi kulas a lungu, amma
basu fasa kukan zuci ba. Ya ja mota ya tafi a
fusace ko sallama bai yiwa Baffa ba.
Umaimah tana zaune a cikin dakinta ko rakiya
kasa yi musu tayi, ta rike kai ta rushe da kuka na
takaicin rabuwa da yaranta, lallai tana cikin wani
hali idan ta kwallafa son yaran nan saboda ita ta
yankewa kanta ba zata sake zama da Abdul-Basi
ba shi ma kuma ba zai bata yaranta ba.
Magruba ta yi, da ta kewaya bandaki zata kama
ruwa sai ta kasa tsugunawa saboda cakwalin
kasa mrtik da bawali babu siminti, *yar zana ce
aka kewaye. To wannan idan ta tashi yin wanka
ya za ayi kenan?
''mishkila" inji Larabawa
Haka da daddare ta ji sauro yana gantsara mata
cizo sai hankalinta ya tashi. Ta kuduri niyyar
tafiya Dukku da sassafe ta siyo shaltos da gidan
sauro, ruwan swan, kayan shayi, risho food flask
da duk kayan abinci. Sai dai jama'ar Ruga su
zage ta amma ba zata zauna yunwa da wahala
su kashe ta ba alhali tana dashi.
Haka kuwa akayi washe gari da safe ita da
Sabitu suka tafi birni suka yi siyayya, kaya cikin
bayan mota 'a kori-kura aka zo aka jifge himilin
kaya a dakin Umaimah. Ai kuwa tasha zimde da
yafice a
wajen su Nene kan ka ce kwabo magana ta yadu
a gari Umaimah ta siyo kayan abinci irin na
turawa ba
zata iya cin tuwo ba.
Haka tasa aka yi mata siminti a bandaki daidai
inda zata dinga hawa tana yin wanka. Tabbas
gayunta ya tabbata, dan ma tana daurewa tana
hakura da wasu abubuwan da kada maganar ta
yi yawa. Da generator zata siyo ta dauko me
alsawa ya hada mata ta dinga yini tana kwana a
cikin fanka, dole ta hakura da wutar lantarki.
A daddafe ta shafe wata guda cur sai ta ce da
Baffa zata je Gombe ta ji yadda ake ciki da
zancen tafiyarsu bautar kasa. Sabitu ne ya rakata
da kayansu kala biyu suka zuba a cikin jaka.
Tana shiga birni Gombe ta sayi layi ta kunna
wayarta, Hanif ta fara kira, ya ji dadi dajin
wayarta dan har ada ya fara tunanin muddin bata
zo a cikin satin nan ba sai ya je Dugge da kansa
ya sanar mata maganar tafiyarsu bautar har sun
yi taro sau biyu a gidan gwamnati, saura sati
biyu su tafi Abuja.
akwai Post anjima in kuna so.?
MAKWABTAKA 45
Da kansa ya sanar mata maganar tafiyarsu
bautar har ma sun yi taro sau biyu a gidan
gwamnati,
saura sati biyu su tafi Abuja
Tana gama waya da Hanif sai ta kira kawarta
Aisha Bingyal, da farko Aisha bata gane mai
magana ba kasancewar sabon layi ne yanzun nan
Umaimah ta saya sai daga baya ta shaida
muryar, Umaimah Bello ce aminiyarta.
"Gani a garinku, kwatanta min gidanku" Umaimah
ta fada cike da fara'a. Farin ciki ya rufe Aisha ta
ce "Fada min inda kike bari na zo kawai in dauke
ki. Ko da mota kika zo?
Umaimah ta ce "Da motar haya muka zo ni da
kanina Sabitu gamu nan a bakin tashar Dukku, ki
zo ki dauke mu.
"Gani nan zuwa yanzu, daman a shirye nake tsaf.
Inji Aisha.
Su Umaimah suna ta tsayuwar jiran Aisha a bakin
titi, sun dade suna jira kasancewar akwai tafiya
daga unguwarsu pantami zuwa tashar Dukku.
Mota kirar discoussion continious ce baka me
bakin gilashi ta zo ta tsaya a gaban su
Umaimah. Sai suka tsurawa motar ido dan basa
ganin cikin motar saboda duhun gilashin bata
zaci Aisha ce a cikin
motar ba har sai da ta sauke gilashin motar ta
leko da kai.
Ta ce "Umaimah Bello, ku shigo mu tafi Umaimah
ta yi mamaki da ganin Aisha cikin wannan daula,
bata zaci *yar gidan masu kudi ba ce haka.
Umaimah ta shiga gaba Sabitu ya zauna a baya
suka tafi, bayan sun gama gaggaisawa sannan
hira ta rincabe.
Aisha ta gyara farin gilashin da yake fuskarta ta
dubi Umaimah tayi murmushi. Ta ce "Kin gudu
garinku ba waya kin bar ni a nan jama'arki sun
hana ni sakat wai sai na kai su gidanku.
Cike da rashin fahimta Umaimah ta tambaya "Su
waye kuma jama'ata?
Aisha ta ce "Na san baki san su ba amma dai
idan nayi miki bayani zaki gane su, wallahi
jama'a da yawa da suka je graduation dinmu
Malaysia suka gan ki suka ce suna sonki. Yanzu
dai su biyu ne suka zo suka same ni daban-
daban kowanne yana son in bashi adireshi da
lambar wayarki. Na ce
musu ban sani ba amma su zo ranar da zamu
tafi Abuja karbo 'call up letter' mu ta bautar kasa
za su ganki.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya jikinta a sanyaye ta
juya ta dubi kaninta ta ce "Malam Sabitu ka ji
wata sabuwa kuma.
Yayi dariya ya ce "Alhamdulillah, haka ake so
Allah Ya zabar miki duk wanda ya fi alkhairi a
cikinsu.
Umaimah ta dafe kai ta ce "Ai zai yi wuya in so
ko dayan ne ma daga cikinsu saboda ni tuni na
dankawa Abdul-Sabur zuciyata.
Sabitu da Aisha suka dau salati a lokaci daya dan
mamaki kasancewar su dukka suna da labarin
Abdul-Sabur, da yadda suka rabu.
Aisha ta fada cike da gatsali ta ce "Au anga
Abdul-Sabur din ne daga in da ya bace din?
Umaimah ta harare ta ta ce "Daman bata yayi?
Aisha ta yi dariya ta ce "Kin cika abun haushi ana
miki maganar mutanen da suke sonki a zahiri
kina maganar mutumin da ya tafi zai auri wacce
yake so.
Umaimah, wadannan mutane manyan mutane ne,
kusoshin gwamnati ne wadanda ake damawa da
su a kasa, masu kudi, masu fada aji, kuma ba
yara ba ne.
Idan kika gansu za ki shaida su
daya ma kawun Khadija Jauro ne wannan yarinya
fara doguwa wacce suke tare da Zainab *yan
Legenda makarantar su Hanif tai graduation dinta
kuma kasashen waje yake zuwa yana shigowa da
kaya.
Ita ta rako shi ma gidan nan nemanki. Sunan sa
Alh. Bilyaminu, da naga motar da ya zo da ita sai
da na tsorata saboda kyan motar, matarsa daya
*ya*yansa hudu, gashi matashi ga kyau ga kudi.
Daya mutumin ban san yadda aka yi ya sami
lambata ba, kwatsam na ji ya kira ni ya kwatanta
min kansa sannan na gane shi. Kin tuna wani
mutumin da ya dinga magana da masu awon
kayanmu a