Showing 57001 words to 60000 words out of 130520 words
Chapter 20 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
ba ne a makaranta daya, makarantu biyar
ne za a rarraba mu ashirin-ashirin a kowacce
makaranta.
Ya danganta ashe da course din da ka zaba ka
cike. A makarantarmu FTMS mu ashirin ne mata
biyar maza goma sha biyar.
Sai Intii Nilai su ma garin Nilai za su zauna su
ashirin maza sha takwas mata biyu, sai su Hanif
da suke 'Legenda, sannan wasu aka kai su 'Help
Uneversity wasu kuwa 'Putra Jaya' aka kaisu, a
'Apiit University' kowa course mai kyau ya zaba
kamar ni da nake karantar Software Engineering
wasu medicine, wasu Computer Engineering da
dai sauransu.
Aka rarraba *yan rakiya kowannensu ya dauki
tasa tawagar ashirin-ashirin zuwa garin da
makarantar ta ke. A lokacin muka yi sallama da
Hanif har ya yi kamar zai yi kuka, ni kuwa sai da
na
yi kukan ma. Ya tafi 'Legenda' kauye ne mu
kuwa a cikin 'KL ne, na ci sa'a kuwa Alhaji Sani
shine jami'inmu.
Kai tsaye cikin makarantarmu FTMS mu muka
nufa ba mu tsaya wata-wata ba aka nuna mana
katon gidan haya a kusa da makaranta mata mu
biyar bangarenmu daban, amma mutum bibbiyu a
daki daya, daya dakin kuwa su uku ne.
Ni da Aisha bingyal aka hada mu ita ma mai ji da
kai ce kamata, don haka kowa ya juyawa kowa
baya, tunda kowa da gadonsa.
Washegari babu abin da muka yi sai cuku-cukun
registration da cike-ciken forms.
Da muka gama sai aka daddanka mana account
number mu da ATM aka nuna mana bankin da
zamu dinga zuwa daukar kudi. Bayan wannan sai
Alhaji Sani ya ja ni zuwa banki daban ya bude
min sabon account wanda Alhaji Rabi'u ya ce a
bude min na musamman zai sako min naira
miliyan daya.
Alhaji Sani ya yi waya da jami'in da yake
Lagenda ya umarce shi da ya budewa Hanif ma,
ya turo masa
da account number, haka kuwa aka yi aka
budewa Hanif shi ma. Sai na ga duk sun sayi
layuka ana ta musanya lamba, sai ni naki siya
fur. Alhaji Sani ya ba ni waya na yi magana da
Alhaji Rabi'u ya jajjada min zai sako wannan kudi
da ya yi
mana alkawari, na yi ta godiya.
Tun kafin Alhaji Sani ya bar Malaysia ya tabbatar
min an sako kudin nan muka je banki aka duba
min dallar dubu takwas tabbas nasan na yi
sallama da talauci a duniya.
Ban san da yaren da zan yiwa bawan Allah nan
godiya ba. Alhaji Sani ya sake kira min Alhaji
Rabi'u
a waya na fada masa da bakina na ga kudin
sannan na sake yin godiya, ya sake yi min
nasihohi da na yi karatu, kuma na kama kaina
ban da bin samari da lalatattun kawaye.
Wannan shine labarina.
Umaimah ta dube su tana murmushi.
Suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda,
Abdul-Sabur ya gyada kai.
Ya ce, ''Wannan labari ya kayatar da ni kamar
kada ya kare. To amma ya aka yi kika baro can
Hostel kika dawo nan gidajen?
Umaimah ta yi murmushi ta ce, ''Da na yi wata
guda na gane gari, ina ta hira da malamai ina
tambayarsu dokoki da tsarin karbar hayar
gidajensu, sai na ji da sauki babu tsada ai zan
iya kama gida ni kadai.
Suka tabbatar min akwai gidajen haya kusa da
makarantar nan wanda ba sai na hau mota ba
zan
iso. Ba ni da matsalar kudi, don haka na ba wa
wani malami dan kasa ne cigiya, ba tare da bata
lokaci ba ya samo min nan, na tarkato na dawo.
Daman ba dadi nake ji da dukka daliban ba
musamman Aisha Bingyal da muke daki daya, na
kasa sakin jikina da ita, na kasa yin ko hira da
ita balle mu saba. Dan Allah ta yi hakuri ta yafe
min,
wallahi ba halina ba ne tsoro nake ji saboda
abubuwan da aka yi min a baya.
Har yau haushina suke ji, na ware ni kadai, a ji
kawai nake shiga a gama lecture na fito na dawo
gida. Sai ta dauro dole a yi magana sannan nake
magana da su. Kamar misali idan an ba mu
group assignmen ko practical a lab. Ba ni da
waya balle na kira Hanif ya ji labarina, ba ni da
waya balle mu dinga gaisawa da Alhaji Rabi'u da
Alhaji Sani, ban kira kowa ba balle a san ina raye
ban ki ba dai ko Hanif yana da lambar wasu daga
cikin *yan makarantarmu ya tambaye ni ace
masa ina nan bana kula kowa. Ni kuwa bakin hali
da kyaliya ba halina ba ne, saka ni aka yi dole na
zama haka saboda duk wanda na amincewa sai
ya zalunce ni.
Ta sunkuyar da kai ta dafe ta yi shiru, tana mai
takaicin abubuwan da ta tuna a baya.
Abdul-Sabur da Faduwa kuwa suka zuba mata
ido kawai suna kallonta, suna masu tsananin
tausayinta. Can ya yi gyaran murya ya fara
magana cikin rarrashi da nasiha.
''Umaimah, na san MAKWABTAKA da kawaye
sunyi miki ba dai-dai ba, amma kada wannan
yasa ki zaci
duk wasu MAKWABTA da zaki yi nan gaba su ma
halinsu daya, ki dauka su daban mu daban. Ki
dauke ni a matsayin babban yayanki Faduwa
kuwa idan ba ki dauke ta uwa ba, to ki dauke ta
a matsayin kanwar uwa (Aunty) saboda ke
yarinya ce karama a cikinmu, babu zancen yi miki
gulma, kazafi, cin amana da dai sauran tarkace.
Rashin ilimi ne su ma can da kuruciya yasa suka
yi miki haka.
Umaimah, rayuwa ba zata yiwu a haka ba, babu
yadda za a yi ki ware ki ce kin daina gaisawa da
kowa a duniya musamman MAKWABTA. Ina kara
baki hakuri da ki cire duk wannan ra'ayi naki ki
kyautatawa MAKWABTA da duk wanda Allah Ya
hadaku zama tare....
Faduwa ta ci gaba da cewa, ''Da kika ba mu
tarihin rayuwarki sai na ji na fara sonki da na ji
dalilinki,
don a da haushinki nake ji, saboda nuna mana
tsana kiri-kiri da kike yi. Yanzu mun zama daya,
ke ma kanki idan kina shigowa cikinmu rayuwa a
Malaysia zata fi yi miki dadi akan rayuwar kuncin
da kike ciki ke kadai.
Ki shigo cikinmu mu zauna tare, mu yi hira, mu
zaga gari tare mu ba wa juna shawara. Allah Ya
hada mu
da babban Yaya Abdul-Sabur mai kaifin hankali,
hakuri da hangen nesa, shi yake ba ni shawara
koda yaushe. Ki dinga sauraron abubuwan da
yake fada miki idan kika bi ba zaki yi nadama ba.
Dadin kalaman Faduwa sai ya yi mata kama da
na Matawata koda yaushe tana ce mata.
''Umaimah mu hada kanmu, kada mu yi fada
kawaye su yi mana dariya, don haushin
kawancenmu ake ji a garin nan, an kasa kunne
ana so aji wata baraka a tsakaninmu.
Amma a karshe ita ta fara cin amanata a duniya.
Ta dago ta dubi Abdul-Sabur murmushi kadai ya
yi
mata yana yi mata kallo na tausayi da tsan-tsar
kulawa. Sai ta gan shi sak Ilah haka yake yi
mata, karshe ya ci amanarta. Sai ta ji da kyar
idan zata amincewa da wadannan mutane kamar
yadda suke tunanin zata yi.
Ta yi zumbur ta mike tsaye ta wawuri mukullin
gidanta babu abin da ta fi so irin ta ganta a
gidanta ita kadai.
Faduwa ta ce, ''Ki bari mu yi sallar azahar a
jam,i,
Abdul ya ja mu sai mu yi addu'a Allah Ya yayewa
kowa damuwarsa, Ya biya mana bukatunmu, Ya
kare mu daga sharrin makiya, Ya ba mu zaman
lafiya a tsakaninmu.
Umaimah har ta kai bakin kofa ta fara tafiya don
ta gaji da dadin bakin Faduwa, har ta fara ganin
kamar cutarta ta ke shirin yi.
Faduwa ta mike da sauri cikin wasa zata je ta
kamo hannunta ta dawo da ita, sai ta ga
Umaimah ta zabura ta ja da baya a firgice.
Abdul-Sabur ya dagawa Faduwa hannu alamar ta
dawo ta zauna ta rabu da ita ta tafi.
Umaimah ta juya da sauri ta fice daga cikin
gidan, sai ta ji ta tamkar wacce ta fito daga
kurkuku don ta takura da yawa zaman da ta yi a
cikinsu na tsawon awoyi.
Wai me me ya kai ta wannan katobarar a gurin
mutane?
Me yasa ta manta aminci ne duk ya jawo mata
matsala a rayuwa?
Ta shige lift ta haye sama ta isa gidanta,
hannunta na rawa ta bude gidanta ta shige ta
mayar da kofa
ta kulle ta je ta haye kan kujera ta takure tana
huci don an taso mata da dumbin takaici da
abubuwan
bakin cikin da aka guma mata a baya.
Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya ce, ''Kin ga abin
da nake fada miki ko?
Daman na ce ki yiwa yarinyar nan uziri tana da
dalilinta na yin haka, ashe an sha ta, ta warke shi
yasa ta shiga tsoronmu. Ki bari a hankali zata
gane mu su waye, kuma da wacce manufa muke
bin ta.
Ta sha wuya ne a rayuwa, ta rasa kowa, ta rasa
komai tana karamarta. Umaimah ta cancanci a
tausaya mata, a rarrashe ta, a daina damuwa da
duk wasu halaye mararsa dadi da zata nuna. Ita
a
ganinta idan ta yi haka shi ne zata sami sauki a
rayuwarta.
Faduwa ta ce, ''Ai dole ta tsorata da mutane, sun
ci amanarta, to Allah Ya sa mu dace.
Abdul-Sabur ya ce, ''Amin
Yayin da ya mike gami da yin mika da hamma.
Ya dubi Faduwa ya ce, ''Yau kin hana mu baccin
safe, daman ke baki iya ba. Da tuni sai yanzu
zan tashi na yi sallah sannan na karya kumallo,
amma yanzu cin abinci biyu kika sa mu. Daman
ke yini
kike kina dora tukunya, kullum bakinki yana ciye-
ciye.
Suka kwashe da dariya su dukka.
Faduwa ta ce, ''Au kana nufin ban sami ladanka
ba, na zaunar da yarinyar da ka dade kana so ta
amsa gaisuwarka ma balle ta zauna da kai ku ci
abinci a teburi guda ku yi hira. Ai na yi jihadi ba
don ni ba wallahi har abada ba zata amsa maka
ba.
MAKWABATAKA 25
Ya juya ya tafi yayin da Faduwa ta tura kofarta
ta rufe. Sallah ta yi ta kwanta, ta dade bacci bai
dauketa ba tana tuna labarin Umaimah shi ya fi
sosa mata zuciya.
Abdul-Sabur ma haka da ya yi sallah a masallaci
sai ya koma gida ya kwanta,
labarin Umaimah shi ne yake yi masa reto a
zuciya yana tausayinta yana tunanin hanyoyin da
zai bi ya
kawar mata da damuwar da ta addabe ta.
Yayin da Umaimah ma bayan ta yi sallah ta
kwanta bacci ya gagari idanuwanta,
labarin Faduwa da Abdul-Sabur ne ya ke yi mata
kewaye a zuciyarta.
Hakika ashe ba ita kadai ba ce ta fuskanci
matsalar rayuwa a duniya, a she su marayune, ba
su da aure
ba *ya*ya. Gara ita ma da ta taba auren har ta
haifi da, ko ba ta sake aure a duniya ba nan gaba
babu
damuwa, ko mutuwa ta yi ta bar wanda za a
kalla a tuna da ita a yi mata addu'a.
Ba kamar Faduwa ma ita mace ta fi ba ta tausayi
ta girma har ta manyanta babu aure, tabbas ta
cancanci a tausaya mata. Ta shiga jero addu'oi
Allah Ya fitowa da Faduwa miji na gari ta yi aure
ko sau daya ne ta samu ta haihu.
Asuba ta gari Abdul-fadu-maimah!!!
**********************
Faduwa da Abdul-Sabur ne suke zaune a gidan
cin abinci na Golden Folk da yake cikin KL.
Faduwa ta
kurbi lemo ta dubi abokinta Abdul-Sabur ta tabe
baki cikin harshen Hausa suke magana kamar
yadda suka yiwa juna alkawari sun daina yiwa
juna Turanci sai Hausa.
Ta ce, ''Mai hali baya fasa halinsa, da Umaimah
nake,
ka ga yau kwana hudu ke nan rabuwarmu ba mu
sake jin motsinta ba balle mu ganta.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ta daina ma fitowa baranda,
amma dazu ta fito da safe ta tsaya. Ta iske ni a
tsaye a baranda kallo daya ta yi min ta sunkuyar
da kai ba ta gaishe ni ba. Sai na ki yi mata
sallama don idan na yi mata zata ji na takura
mata, dole sai ta amsa tunda a musulunce ne.
Faduwa ta gyara zama ta kai lomar salad a
bakinta, ta ce, ''Yaya kuka yi daga karshe?
Abdul-Sabur ya ce, ''Tsayawa na yi ina kallonta
kawai, sai ta bata rai ta turo baki ta dube ni, ta
ce,
ina kwana? Irin na takura mata din nan. Sai na yi
murmushi na ce mata, assalamu alaikum. Ta juya
ta
shige gida ta rufe kofa. Suka kwashe da dariya su
dukka.
Faduwa ta ce, ''Har yanzu fa ba son zamanta ta
ke da mu ba, gani ta ke mun takure ta.
Abdul-Sabur ya ce, ''Za ta ware nan gaba mu
rage shisshige mata, idan ada bata san mu ko su
waye ba yanzu ta sani. *Yan uwanta musulmai,
Hausawa, duk inda ta je zata dawo ta neme mu.
Yarinyar tana burge ni ne haka kawai, ban san
dalili ba. Ba wai nace tana kyautatawa ba amma
sai ta kalle ka ta harare ka kuma sai ta ji kunyar
ka ta sunkuyar da kai, ta kasa hada ido da kai.
Faduwa ta ce, ''Ba ka karsa ba, ba ka ce ga ta da
kyau, fara mai gashi, ga dirin jiki dai-dai kauna
ba.
Abdul-Sabur ya harare ta, ya ce, ''Ni fa bana son
ki dinaga kawo maganar so idan ana maganar
zumunci.
Faduwa ta ce, ''Ni dai na yi maka kamu, zan
zauna da ita na isar da wannan sako naka. Kafin
ta dago da kai ta tsinkayo Abdul-Sabur ya kai
bakin kofa zai fice, ta wawuro jakarta ta biyo shi
da sauri. Daman ya biya kudin abincin ko rabi ba
su ci ba, ya tashi ya bar abincin. Wai shi nan
fushi ya yi.
Ta yi ta bin sa tana yi masa magana ya kyaleta
har sai da ta sauko, ta shiga ba shi hakuri. Ta
ce, ta fasa ba zata fadawa Umaimah ba, daman
wasa take yi masa, sannan ya fara amsa mata.
Su ka shiga jirgin kasa suka koma gida.
Ranar lahadi da sanyin safiya misalin karfe tara,
sai ga Faduwa a tsaye a kofar gidan Umaimah
tana ta danna kararrawa. Yayin da tsoro, fargaba,
gami da dimaucewa suka ruftowa Umaimah. Tayi
figigit ta fito daga cikin bargonta ta diro daga kan
gado ba shiri ta ruga da gudu zuwa bakin kofa, ta
leka ta jikin *yar huda dan taga me buga mata
kofa. Sai kuwa ta hango Faduwa dan haka
mamakin sai ya ragu. Ta bude mata da sauri
gami da yi mata murmushi da sannu da zuwa.
Faduwa ta ji dadi da taga ta karbe ta da farin
ciki, itama sai ta sake samun kwarin gwiwa ta
shigo da fara'ar ta. Umaimah na gaba Faduwa
tana biye da ita har kan kujerun falo suka zauna
suka sake gaisawa. Zata je ta dauko mata shayi
da lemo Faduwa ta tsayar da ita ta ce ta bar shi
a koshe take daman ta zo ne dan ta sanar mata
yau ranar haihuwar Abdul-Sabur ta zagayo
(birhday) suna gaiyatar walima da yamma.
Umaimah tayi dim! Kadan sannan tayi gyaran
murya ta gyara zama zata yi magana, Faduwa ta
daga mata hannu ta katse ta.
Ta ce ''Kada ki ba mu wani uziri ki ce ba za ki
sami damar zuwa ba dole ki je. Ki shirya da
yamma ki fito
ni da ke da Abdul ne kadai.
Sai Umaimah ta yi murmushi ta langwabe kai ta
ce ''to Allah Ya kaimu anjiman din zan je.
Faduwa ta yi dariya ta mike da sauri ta dafa
kafadarta ta ce,
''Yauwa Baby na zan biyo miki anjima sai mu
tafi.
Umaimah ta raka ta har bakin kofa suka yi
sallama kowannensu cike da fara'a. Ta tafi
sannan Umaimah ta dawo ta zauna tana ta
fargaba da sake-saken yadda zata bijire taki
zuwa dan bata son zuwan kwata-kwata.
Tana idar da sallar la'asar sai ta sake fesa
wanka ta tsala ado da wasu sababbin kayanta
wanda bata taba sakawa ba, riga fara me layi-
layi baki da bakin dogon wando
(jeans) sai ta sami dan yalolon gyale ta nade
kanta da shi kalar fari da baki ne, sannan ta saka
takalmi coge mai tsini sosai da bakar jaka mai
kyawun gaske. Ta dora da farin gilashi a fuskarta
mai
hasken gilashi.
Tana gama shiryawa tana tsaye a gaban madubi
tana sake saka hoda da jagira sai ta ji kararrawar
kofar gidanta tana kara ko kokonto bata yi ta san
Faduwa ce. Sai ta fito da sauri bata bata lokacin
ta ba na lekawa sai ta bude kofar ta fito gaba
daya.
Faduwar ce kuwa itama ta dandasa ado ku san
kwalli iri daya suka yi a tare.
''Kin yi kyau kanwata. ''Faduwa ta fada a lokacin
da take kallon Umamai sama da kasa. Kin fi ni
kyau Antina. Itama ta fada a lokacin da take
kokarin kulle kofar gidanta.
Sai suka yi dariya su dukka suka dinguma zuwa
cikin Lifter dan sauka kasa.
Suka nufi get din fita daga farfajiyar gidan kamar
Umaimah ta tambaye ta Abdul-Sabur sai ta fasa.
Su na fita sai taga Faduwa ta nufi wajen wata
tsaleliyar mota mai kyawun gaske, kalar baka mai
farin
gilashi tar! Har shekin kyau take dan sabunta, ko
ba'a fada ba ka san sabuwa ce fil! Daga ledarta.
Cikin sauri Faduwa ta budewa Umaimah gidan
baya, ta shiga tana sanda gami da yiwa mutumin
data iske a cikin motar sallama. Ya amsa mata
cike da fara'a gami da juyowa a tsanake ya dube
ta.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani sai ta cika da
mamaki tana tunanin inda ya samo aron mota
dan bata taba ganinsa da mota ba.
Faduwa ta bude gidan gaba ta zauna, ya tashi
mota suka hau kan titi suka fara tafiya.
Umaimah ta leka fuskarsa ta ce ''happy birhday''.
Ya yi murmushi ya ce Na gode. Yayin da Faduwa
ta hau magana ba kakkautawa dan ita bata
gajiya da
magana.
'Eh ko A,a ko ya ce rufemin baki kin fiye surutu'
Abdul ya fada mata, yayin da Umaimah ta kunshe
baki tana dariya dan ita dariya suke bata kamar
wasu *yan tagwaye. Ita Faduwa ta cika magana,
ta
fuskanci tana damun Abdul-Sabur bashi da
surutu.
Suka isa wajen da ake ajiye motoci suka sami
waje suka tsaya yayin da suka firfito zuwa cikin
KL plaza. Suka nufi babban wajen cin abinci,
babu abinda babu na ci abinci kasashe kala-kala
sai wanda
kake so zaka zaba. Suna zama aka kawo musu
takarda mai rubuce da duk launin abincin da suke
sayarwa a wajen. Sai kowa ya shiga cankar
abinda ya fi so ya ci, shinkafa da salad sai *yar
miyar gargajiya kaji kadai Umaimah ta zaba.
Sai Abdul-Sabur ya ce a'a yayi mata kadan sai ta
kara da wasu abinciccikan dan shi so yake a cika
kan teburin dankar da abinci da abin makulashe.
Ta yi murmushi ''ta ce to a kawo komai ma duk
sai a hadu a ci. Ma'aikata sun ga ciniki sai suka
hau rawar jiki suka garzaya a rude suka hau
harhadowa, ma'aikata a
layi suke ta zuwa suna ajiye farantai da kofuna a
cike da kayan alatu. Faduwa ta zabura ta mike
zata je kicin. Abdul-Sabur ya dakatar da ita da
sauri.
Ya ce, ''Kin fiye rawar kai, wa kika ga yana shiga
kicin, kowa ba'a zaune yake ba su suke zasu
kawo komai ba?
Faduwa ta mike gami da tabe baki ta ce, ''Ka ga
tafiyata, kai ma ka san babu yadda za'ayi in zo
waje
in zauna dam sai na motsa.
Umaimah ta tuntsire da dariya ta bi Faduwa da
kallo tana mamakin irin wannan hali nata.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya dubi Umaimah ya ce
''Kin fara ganin halin makwabciyarki ko? Haka
take
bata iya zama shiru.
Umaimah ta sake tuntsirewa da dariya ta gyara
zama ta dube shi ta ce ''Ina son halinta, tana
burge ni dan tana da kirki sosai. Dama ka aure
ta, da zan so haka wallahi.
Ya yi firgigit ta dago da sauri ya dube ta cike da
dinbun mamakin yadda aka yi wadannan kalamai
suka fito daga bakinta a daidai wannan lokaci.
Sai ya dan yatsune fuska ya tambaye ta me ta
ce, dan yana tunanin kunnuwansa basu jiyo masa
dai-dai ba. Data maimaita sai ya ji abun da ta
fada dazu shi ta maimata.
Ya gyara zama ya ce ''Me yasa kika yi wannan
tunanin?
Ta yi murmushi ta ce, ''Kamar yadda na fada
dazu tana da kirki kuma ina tausayinta har yanzu
bata
taba yin auren fari ba.
Sai ya sankare a zaune ya kasa amsa mata
wannan tambaya.
Faduwa ce ta taho dauke da babban