Showing 117001 words to 120000 words out of 130520 words

Chapter 40 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8039

fi
sau uku akan zai tafi ta rufo masa kofar mota,
bata ji ba ta rike murfin kofar tsam a hannunta.
Sai shima ya yi tagumi ya zuba mata ido yana
kallo har lokacin mai tsawo, can data dawo
hankalinta ta kalle shi ta
ga ashe ita yake kallo sai ta yi firgigit ta tambaye
shi. "Me kake cewa?
Ya yi murmushi ya ce "Bance komai ba amma
idan kin bani izini zan tafi.
Shima ya gane ba'a son ranta zai tafi ya bar ta
ba.
Sai ta matsa daga jikin motar a hankali, ta masa
fatan Allah Ya kiyaye hanya cikin sanyayyiyar
murya.
Ya ji hawaye ya cika masa ido dan
tausayinta lallai ba dan dole ba da ba zai tafi ya
bar ta a cikin wannan hali ba, amma babu yadda
zai yi.
Kalmar karshe da ya fada mata ita ce "Idan sati
biyun nan ya cika kije Gombe wajen aikin dan ki
sa hannu ki kunna wayarki ki kira ni. Ya ja mota
ya tafi dan yaga wani sabon hawaye ne yake
shirin rikito mata a lokacin da ya kunna mota zai
tafi.
Ta jikin madubi ya dinga lekenta, ta dade a tsaye
tana daga masa hannu har sai da ya karya
kwana.
Gidan Dagaci ya nufa, bayan sun gaisa ya shaida
masa matsalar dake faruwa tsakanin Matawata
da Umaimah.
Ya ce "Ya kamata manya su shiga maganar ayi
musu tsakani tunda ga abunda aka ji ta fada zata
aikata kuma idan ta samu waje zata iya shigowa
gidan su Umaimah ta ce zata dake ta da hannu
koda makami, ko ma ta saka mata gobara a daki
a cikin dare ta hallaka ta ma gaba daya tunda
kiyayyar ta kai ga har haka.
Dagaci ya ce wannan maganar gaskiya ce kuma
zai sa a kira iyayen Matawata, da ita kanta, da
iyayen Umaimah a yi musu tsakani, kada ta sake
lekowa ta jikin zana ta zage ta ko ta yi mata
habaici. Kuma wannan boka da take zuwa
wajensa zai kore shi ma daga garin gaba daya.
Kuma a tsorata Matawata ace za'a saka mutanen
gari su saka mata ido duk sanda aka ga zata fita
daga garin, zata je wani kauyen wajen wani
bokan sai an kamata an daure ta a kurkuku.
Abdul-Sabur ya ce "Haka yayi kyau kuma ko me
zata je ta kulla na sihiri a boye ko a bayyane
Allah Zai kare Umaimah dan tana addu'a sosai
idan kuwa har wani abu ya same ta daman da
izinin Ubangiji.
Ya rubuto zai same ta daman.
Amma zagi da habaici shine za'a hana ta.
Kudi mai yawa Abdul-Sabur ya bawa Dagaci da
*yan fadarsa, sai suka rude dan dadi. A take
Dagaci ya tashi mutum ya ce aje a taho masa da
Matawata da iyayenta da kuma Baffa da Nene
za'ayi musu
tsakani. Har da an ce a taho da Umaimah, sai
abdul- Sabur ya ga ba ajinta ba ne ta taho rabe-
rabe ana yawon zuwan shari'a a fada da ita.
Sai ya hana a kira Umaimah ya ce "Baffa ya
wakilci Umaimah saboda idan suka hadu da
Matawata akwai matsala.
Da yake Abdul-Sabur mai kudi ne sai suka yarda
da shawararsa nan da nan.
Abdul-Sabur ya kwashi takalmansa yayi musu
sallama ya shiga motarsa ya kunna ya fara
tafiya.
Kwatsam!!! Sai ya ga wata bakar mota CRB ta
shararo da gudu ta tunkaroshi gaba da gaba,
kamar yadda raguna suke fada kaho da kaho.
Nan da nan Abdul-Sabur ya taka burki a gigice
da sauri,
yayin da numfashinsa ya fara daukewa. Ya zaci
ma mafarki yake yi dan bai zaci zai hadu da wata
mota ba a cikin Rugar nan balle a yi karo. Amma
dai koma waye wannan da biyu yayi masa haka
dan filin ya isa motocin dukka biyu su wuce a
lokaci guda.
Abdul-Sabur bai fito daga motarsa ba gashi an
tare gabansa ba zai iya wucewa ba sai dai idan
baya zai yi. Bakar motar ce ta taho da sauri daf
da kofar da Abdul-Sabur yake zaune.
Bakinkirin gilashin motar yasa baya hango wanda
ke cikin motar. Kallon motar kawai Abdul-Sabur
ke yi yana mamaki marar misaltuwa, dan shi
bashi da abokin gaba a duniya. Amma da wancan
ya sauke gilashin motar kuma ya zare bakin
gilashin dake fuskarsa,
sai Abdul-Sabur ya gane ko wanene, kuma ya
daina mamaki, dariya ce ma kadai ta kubce
masa.
Abdul-Basi ne ya bayyana a gaban Abdul-Sabur
fuskarsa babu sauran annuri, tabbas yau daga
dukkan alamu Abdul-Basi bazai raga masa ba ko
kadan dan ya gama bincike yana da labarin
komai.
Abdul-Sabur ya sauke gilashin motarsa shima sai
ya yi masa sallama gami da tambayarsa me yai
zafi haka?
A matsayinsa na mai ilimi bai kamata ya yi masa
haka ba.
Abdul-Basi cikin fushi mai tsanani yana duban
Abdul-Sabur duba irin na tsana.
Ya ce "Dalla malam ka rufe min baki, na daina
yarda da bayaninka yanzu na munafinci.
Abdul-Sabur ya sake kyalkyalewa da dariya, ya
girgiza kai ya ce "Ka yi hakuri idan nayi maka
laifi dan uwana a musulunci, a tunanina ban yi
maka laifi ba dan ina son matar da ka daina so
kuma ka sake ta, ai abun bana yaki ba ne, zabin
Umaimah muke bi. Me na fada maka a baya?
Na zauna dakai na baka shawara duk hanyar da
zaka bi ka sami Umaimah ta dawo gare ka, ka
kasa bi amma daman ban boye maka ba na
tabbatar maka ina son Umaimah amma nafi so ta
koma ta zauna da kai saboda *ya*yanku.
Nan da nan ja'amar gari suka taru ana kallon
wannan karo da aka so ayi da motoci, kura da
karar burkin da Abdul-Sabur ya yi sai da kowa ya
razana ya fito da gudu.
Kan ka ce kwabo labari ya kai kunnen Umaimah
cewar ga Abdul-Basi can ya tare Abdul-Sabur har
ya dauko bindiga ya ce zai harbe shi.
Mummunar faduwar gaba ta karu akan ta da a
cikin zuciyar Umaimah. Dan da aka ce Baffa da
Nene suzo fada Dagaci na nemansu a gigice.
Wannan karon ko gyale babu a jikinta ta daka
tsalle ta fito kofar gida, Sabitu da Baffa na rike ta,
ta fisge a guje ta taka da gudu bata tsaya a
ko'ina ba sai a gaban gidan Dagaci. Ta iske
suma a wajen ga motoci biyu a manne da juna,
dukka kofofin biyun ba zasu iya buduwa ba, ba
karamin tashin hankali ta ji a lokacin da taga
gaba dayansu suna haurawa ta daya kofar suna
kokarin fitowa a gaggauce.
Suna firfitowa sai suka tsaya gaba da gaba kowa
yana magana cikin daga murya musamman ma
Abdul-Basi. Sai tayi matukar mamaki da ta ji
Abdul-Sabur yana fada yana sake maimatawa.
Ya ce "Ban fito na nunawa Umaimah ina sonta ba
har sai dana tabbatar kun kasa daidaita kanku.
Shin tunda Umaimah ta ki yarda ta koma gidanka
sai a kyaleta a haka ta zauna ba aure?
Abdul-Basi dai sai huci yake tamkar kumurcin
maciji. Ya ce "Daman can munafunci ne, kun
gama shirya maganarku sannan ka zo ka tsara
min makirci.
A fusace Umaimah ta fado fili ta tutture jama'ar
da suka zagaye su, sai gata a gabansu ta saka
hannayenta biyu da karfi ta wara kirjinsu ta shiga
tsakiyarsu ta fada cikin tsawa.
"Wai me yake faruwa ne haka?
Me kunnuwana suke jiyo min kuna fada?
Daman kun san junanku, bakin ku daya ku ke
munafunta ta?
Hawaye mai radadi ya zubo daga idanuwanta, ta
juya ta dubi Abdul-Sabur.
Ta ce "Ban zaci kana daya daga cikin irin
mutanen da zasu rufe ni ba, ka ha ince ni, na zaci
kai ne makwabcina na farko da ya taba yi min
abin arziki,
wanda bai ci amanata ba. Sai gashi dubi irin
abubuwan da suke fitowa, shiyasa daman na rasa
kanka.
A Malaysia ka tafi ka bar mu, sai gashi da
bakinka ka ce min bayan tafiyarka muna tare duk
abunda nake kana ganina, a Gombe ma ka ce
kana biye da ni, dana tambaye ka ka ki fada min
dalilinka na yin haka, sannan yanzu da kunnena
na ji kana fadawa Abdul-Basi ka bashi shawara
akan yadda zai same
ni wato kai baka sona kenan. Ba komai na gode
amma ina mai tabbatar muku babu me aurena sai
dai idan gawata za'a dauko muku ku aura.
Abdul-Sabur ya ji tamkar an sauke aradu a
kirjinsa nan da nan ya ji ya gigice kansa ya sara
da ciwo.
Sai ya lalubo kamar 'Innalillahi wa inna ilaihi raji
un'
Yana fada yana sake maimaitawa.
Ta juya ta kalli Baffa ta ce "Baffa, ka yafe min
amma ba zan iya ci gaba da zama a cikin
wannan kangi ba, kowa ya tsane ni, kowa na
zauna dashi sai ya ci amanata. Dan haka daga
wannan rana, kuma daga wannan lokaci zamana
a garin Dugge ya kare kuma na daina shakka ko
gudun abunda mutane zasu ce.
Jama'a ku fada ku sake fada Umaimah ta shiga
duniya, ta yi karatu kanta ya waye tana zuwa
birni yawon ta zubar, kuyi ta yadawa na daina
damuwa. Ina Matawata kin sami abun fada ki je
kiyi ta fada, cewar Umaimah *yar iska ce dan
bata da miji, kuma na fada na sake maimaitawa
ba zan yi
aure ba hakan zan zauna na daina yarda da
kowa,
na daina zaman amana da kowa musamman ma
Makwabtana. Haka daga yau na daina takurawa
kaina ina biyewa abunda mutane suke so, abunda
yayi min daidai da rayuwata shi zan yi tunda ina
da hankali da ilimin da ba zan yi abunda zan
sabawa Allah ba.
Baffa ya dafe kai sai kuka yayin da Sabitu ma ya
fara kuka, Umaimah ta rushe da kuka ta juya
baya a fusace zata fita daga da'irar da mutane
suka yi musu suna kallo har da su Dagaci. Sai ta
ji an fusgota da karfi tana waiwayowa sai ta ga
Abdul-Sabur ne, bata taba ganin ya yi irin
wannan fushi mai tsanani ba irin na yau, hawaye
zazzafa ne yake ta kwaranya daga idanuwansa.
Magana yake cikin kakkausar murya daga dukkan
alamu ya shiga tashin hankalin da bai taba shiga
ba.
Ya ce "Umaimah, a rayuwata na tsani wannan
kalmar mai suna 'cin amana' ban taba cin
amanar kowa ba shiyasa ma ban taba yin
soyayya da kowacce mace ba balle in ki aurenta
ta ce na ci amanarta. Kada Allah Ya kawo ranar
da zan ci amanar wani ma ballantana ke yarinya
da nake so fiye da komai da kowa a rayuwata.
Ki duba ki gani na zo garin Gombe alhali ban taba
zuwa ba kuma bani da dangi ko daya a Gombe, a
Gomben ma a karamar hukumar Dukku sannan a
cikin Rugar Dugge babu wanda na sani sai ke dan
ke na taho daga wata kasa ma ba daga kasar
nan ba. Kin bani mamaki Umaimah da kika saka
ni a sawun Makwabtanki masu cin amanarki. Har
kika fara tunanin tafiya ki bar ni, ki bar iyayenki
bayan shekarun da nayi ina yaki da halayenki har
sai da zuciyarki ta sassake wannan mummunan
tunanin da kika saka mata, kika dawo kika ci
gaba da mu'amularki da *yan uwanki.
Ta gyada kai ta sharce hawaye ta ce "Haka na
dauke ka ada kafin gaskiya ta bayyana. Abdul-
Sabur, kana cin amanata a boye, akwai abubuwa
da yawa da kake boye min dan haka na daina
yarda da kai.
Wannan magana ta Umaimah da alama ta yiwa
Abdul-Basi dadi sai ya kwashe da dariya ya buga
kafa.
Abdul-Sabur ya sake fusata ya juya ya dubi Baffa
da Dagaci. Ya ce "Allah shine shaidata, kuma ku
ne shaidata,
kun san irin zaman da na ke da Umaimah da
kuma burinta da nake shirin cika mata. Iyayena
dana turo
garin nan suka nema min aurenta, ko kuma kudin
aure da muka kawo, nan da wata daya za'ayi
bikinmu shine cin amanar da nayi mata?
Sai Umaimah ta gigice ta dago da sauri ta kalli
Baffa da Dagaci ta juyo ta dubi Abdul-Sabur duba
na
rashin fahimta.
"Baffa da gaske ne maganar da yake fada kun
karbi kudinsa na aure amma ba'a fada min ba,
har
an saka ranar daurin aure nan da wata guda
babu wanda ya fada min?
Umaimah ta tambaya.
Baffa ya gyada kai ya ce "Yanzu kika dawo
Umaimah ko hutawa baki yi ba daman yau zan
fada miki.
Abdul-Basi da yake jingine a jikin motarsa ya
hada hannayensa biyu ya makale a jikin kirji ya
cije baki sai huci yake dan tsananin fushi, ji yake
tamkar ya hada Abdul-Sabur da *yan garin kakaf
ya kone su kowa ya mutu a bar shi da Umaimah
yaga ta tsiya dole ta aure shi ai.
A fusace ya dakawa Baffa tsawa ya tafi har
gabansa da Dagaci yana nuna su da hannu, bai
raga musu ba ko kadan magana yake yi musu
kamar yana magana da *ya*yan cikinsa.
Ya ce "Munafincin nan daga gare ku yake, babu
abin da kuka sani sai kwadayi. Wato kunga mai
kudi daya fi ni kudi wanda ma baku san asalinsa
ba. Ku ka dauki *ya kuka bashi. To ina mai dada
fada muku sai na takura muku a rayuwarku
yadda kuka musguna min dan ba'a ja dani..
Bai rufe bakinsa ba sai ya ji an fisgo kafadarsa
yana juyowa sai ya ga Abdul-Sabur ne, nan da
nan Abdul-Basi ma ya fusata ya daga hannu zai
mari Abdul-Sabur sai ya ji an rike hannunsa yana
juyawa ya ga Umaimah ce.
Ta fada a fusace kada ka sake ka ce zaka mare
shi dan ya hana ka zagin tsofaffi, tunda kai baka
san girma da darajar tsofaffinka ba to mu mun
sani kuma talauci ba hauka ba ne. Baka da
kunya, dan da kana da kunya da ka san akwai
wani abu mai suna kunya da ba ka yi min korar
kare ba kuma yanzu ka dawo kana bina ba.
Baffa ya roke ni in koma wajenka haka mai girma
Dagaci, ni ce naki
komawa dan haka kada ka ga laifinsu. Ni kuma
yanzu kaina ya waye, babu mai yi min dole.
Abdul-Basi ya dunkule hannu kamar zai kai mata
naushi sai Abdul-Sabur ya ce ta matsa, ya matso
daf da Abdul-Basi.
Ya ce "Idan dan kudi su Baffa zasu bi da sai sun
baka auren Umaimah tun kafin in zo saboda ka
zo biko kuma ka basu kudin basu karba ba. Na
baka dama ta har tsawon shekara, na fada maka
yadda zaka sami Umaimah ka kasa. Abinda nake
nufi kuwa yau kowa zaiji maganar da muka yi da
shi.
Ina son Umaimah amma bana so na aure ta ban
sani ba ko tana son wani, ina so in tabbatar tana
sona son da duk duniya babu wanda take so iri
na kamar yadda na ke sonta shine yasa nayi
mata sallama na tafi a matsayin zan koma Ingila
in yi aure amma ba da gaske nake yi ba. Bayan
nan na dawo Malaysia amma ban yarda ta ganni
ba ina so in ga ko ta sami wani da take so
wanda ya fini kamar yadda Faduwa ta karbi Sagir,
amma ban ga Umaimah da kowa ba. Da muka yi
waya da Abdul-Basi sai ya nuna min haryanzu
yana son Umaimah sai na bashi shawara na ce
ya lallaba ki ko zaki yarda ku koma amma na
sanar masa Umaimah bata son takama, bata son
talastawa, dole sai ka lallaba ta ka nuna mata ka
canja kuma ka yi kuskure akan abun da ka yi
mata a baya. Ni na fada maka ranar da zata yi
graduation kuma na baka shawara ka je wajenta
watakila idan ta ganka zata yarda da kai. Amma
kaje wajenta ka
dinga fadin rai tayaya zata yarda da kai?
Daman na shaida maka ina sonta sosai amma na
fi so ta zabe ni da kanta bana so na aure ta da
son wani.
Sai bayan dana tabbatar bata yarda ta koma
wajenka ba sannan na fito ta ganni na isar ba
sakon zuciyata ta san ba zan yi mata dole ba,
haka iyayenta ba zasu yi mata dole ba.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya na jin dadi ta harari
Abdul-Basi sai ta dawo bayan Abdul-Sabur ta
tsaya, wannan ya nuna baro-baro ga wanda ta
zaba ba sai ta fada ba.
Abdul-Basi ya girgiza kai ya juya ya kalli jama'ar
da suke tsaitsaye.
Ya ce "Ba dai kun dauko bare kun rike ba, to a
daura auren Umaimah da Abdul-Sabur din in
gani. Wallah sai na tashi garin nan duk ranar da
aka taru za'ayi daurin auren nan sai dai in bana
numfashi a duniya.
Ya juya a fusace zai shiga motarsa sai Dagaci ya
ambaci sunansa ya ce "Abdul-Basi baka yi mana
adalci ba, ka fi kowa sanin yadda muka karbe ka
muka ba ka auran marigayiya Nasiba ba tare
damun sanka ba ko wani naka ba, da Nasiba ta
rasu muka musanya maka mu ka baka Umaimah
ba tare da tana so ba muka tilasta mata ta aure
ka.
Baka ji nauyinmu ko kunyarmu ba ka sake ta ka
koro mana ita a lokacin da ka sami wata, baka
biyo baya ba balle ka ji ko ta iso gida lafiya ko ta
bata a hanya har sai da kafi shekara sannan ka
zo bayan
can ta kwabe maka.
Da kazo biko aka ce ka turo magabatanka
wadanda suka nemar maka auren ka ki kawo su.
Sannan yarinya ma ta ce ba zata
koma ba har tana ikirarin sai dai akai maka
gawarta.
To ma yayi zafi da zamu tilasta mata, ka sani
babu abinda zaka iya yiwa kowa komai a garin
nan. Da izinin Allah za'a daura auren nan
kuma a wanye lafiya.
Sai samarin garin suka fara fito da sandina suna
damewa nan fa *yan shadi da *yan farauta suka
hau karkarwar jiki suna yiwa kansu kirari suna
fada suna sake fada yayi takatsantsan da su,
muddin rigima ce take kawo shi garisu kada ya
kara shigowa idan ba haka ba zasu lahanta shi,
tun kafin yaga bayansu.
Abdul-Basi ya harare su sama da kasa ya ja
dogon tsaki ya shiga motarsa a fusace ya fisga
da gudu ya tayar da kura, ya tafi.
Ilah fa ya samu masoyiyarsa anan page din ita ce
...
Matawata fa wa mai so na aura masa?
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 51
Abdul-Basi ya harare su sama da kasa ya ja
dogon tsaki ya shiga motarsa a fusace ya fisga
da gudu ya tayar da kura, ya tafi.
Umaimah ta juya a fusace ta fara tafiya har ta
gifta sai ta dawo da baya ta zo gaban Matawata
da mahaifiyarta suna tsaye ta dube ta sama da
kasa.
Ta ce "Matawata, gari ya waye tunda safiya ta yi,
haske ya bayyana yayin da duhu ya kauce. Ina
fatan kin fahimce ni dan da yaren fulatanci na ke
miki magana ba da Hausa ba ko turanci. Kada
ma ki wahalar da kan ki wajen zuwa gaban
Dagaci dan yi mana sulhu idan kina so kada ki
fasa daukar matakin da kika yi niyya. Ki sani
shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, na yi
hakuri a baya bana nufin hakurina ya kare amma
ina mai tabbatar miki nan gaba ba zan kara
daukar abin da na dauka a
baya ba. Na fuskanci sai na nuna miki rashin
kunyar baki iya ba. Na bar miki Ilah tuntuni babu
hadina da shi Allah Ya musanya min Ya kawo
mijin da ya fi kowa a wajena shine Abdul-Sabur.
Kada ki sake shiga harkata, bana nufin ina gaba
da ke amma zagi da habaici ba zan sake dauka
ba.
Umaimah ta gyada kai ta wuce ta bar Matawata
a tsaye tana kallonta tamkar an zare mata laka.
Kowa ya fara fadar albarkacin bakinsa yana fadin
tabbas Umaimah ta yi gaskiya ta yi hakuri da
wulakanci da cin amanar da Matawata ta yi
mata.
Aliya budurwar Sabitu da kawayenta su ne suke
yiwa Matawata habaici suna fada mata Umaimah
ta fi karfinta ba sa'ar yin ta ba ce.
Da Matawata ta hau zaginsu sai suka zamar da
ita shiri-shiri su da yara suka hau rero mata
wakar da aka rere mata a lokacin da ta yi
kwartanci, har kofar gida aka rako ta dan ma
iyayenta suna duka suna rarraka yara gida a guje.
Abdul-Sabur ya koma cikin motarsa ya zauna
yayi shiru yana tunani ransa ya sosu a yau
musamman da ya ga fushin Umaimah har ta fara
zaton yana cin amanarta.
Bayan da Sabitu, da su Baffa sun raka Dagaci
fada ya zauna sai Sabitu ya dawo da sauri wajen
Abdul-Sabur ya iske shi har yanzu a cikin mota,
ba kowa a wajen duk *yan kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login