Showing 69001 words to 72000 words out of 130520 words

Chapter 24 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8038

ce, ''Haka yake, ta ba
ni labari. To amma ai duk ya wuce, Allah Ya
masanya mata rayuwa mafi alkhairi. A tunanina
ta warware
ta fitar da waccan matsalolin da suka addabi
rayuwarta. To ashe in dai damuwa zata saka a
ranta ba ta iya yin karatun ma daya kai ta kenan
kudi ake kashewa a banza.
Abdul-Sabur ya duka ya ce, ''Ranka ya dade tana
karatu sosai ma kuwa, ba ta da matsala. Ga ta
ku fara gaisawa tukunna. Umaimah ta dafe kirji
tun sanda Abdul ya fara waya da Baban Hanif,
saboda tashin hankali. Hawaye ne kawai yake
zubowa face-face tana jiyo duk abin da suke
cewa.
Ta yi sallama cikin girmamawa da shesshekar
kuka,
sannan ta duka ta gaishe shi cikin harshen
fulatanci. Ya amsa gami da tambayarta lafiyarta
da kuma karatunta. Ya dora da nuna mata rashin
kyautawarta da rashin tunani akan hukuncin da ta
yankewa kanta na fita daga harkar kawaye da
*yan uwa. Ba ta neman kowa ta yi dif! Kamar
wacce ba ta duniyar. A matsayinsa na uba ya
dade yana yi mata fada, nasiha da jan kunne
busa kuskuren da ta tafka cikin harsunan nan
uku, Hausa, Turanci da Fulatanci yarensu.
Kalmar, ''I am sorry sir, Alhaji yi hakuri, Baba
mutubi'am. Amsar da ta ke ta ba shi ke nan har
ya yi mata sallama ya kashe waya.
Da alama Baban Hanif ya yi fushi da Umaimah,
amma hawayen nadama, tuban da ta ke yi da
hakurin da ta dinga ba shi ya sanyaya masa
zuciya matuka. Har ya dora mata doguwar
addu'a kafin ya ajiye wayar. Wannan karon kukan
dadi da samun sauki daga kullutun da ya dankare
mata a zuciya ta ke fitarwa.
Hakika yau Umaimah ta dan ji sanyi daga
tsantsar damuwar da ta dade tana addabarta.
Abdul-Sabur ya dauko wayarsa ya dauki lambar
Hanif da ta babansa sannan ya mika mata
wayarta. Kalmar da ya fada mata ta karshe
wacce daga ita ya mike tsaye ya fice ita ce,
''Umaimah ki yi hakuri ki
daina kuka, don ba zai yi miki maganin
matsalarki ba. Ki yi addu'a sannan ki yi hakuri
sai kuma ke da kanki ki gyara lamuranki da
jama'a. Idan kika yi haka za ki inganta rayuwarki,
kuma ki ji dadinta duniya da lahira. Sai
anjimanku.
Ya fice ya bar su a zaune,
Umaimah ba ta daina kuka ba, sabon shafi ma ta
bude na kuka. Yayin da Faduwa ta rungume ta
tana lallashi tamkar wata *yar jaririyar goye.
Umaimah ta kasa tafiya gida a gidan Faduwa ta
yini, suka dafa abincin rana suka ci, suka yi sallar
azahar da la'asar, suka yi kallon talabijin suka yi
ta hira.
Hakika Faduwa ta zauna ta bawa Umaimah
shawara game da yadda zata yi mu'amala da
jama'a. Ta gargade ta da ta canja halayenta,
domin shi mutum rahma ne. Dole ta canja
wannan ra'ayin nata na kin kula mutane da
gudun danginta da *yan kasarta.
Ya zama dole ta bi Abdul-Sabur a hankali har ya
samar mata mafita. Amma ko da wasa Faduwa
ba ta
sako mata maganar soyayyar da ta ke shirin
kullawa a tsakaninta da Abdul-Sabur ba, saboda
kada Umaimah ta zaci da wata manufar yake
kula da ita.
Kuma tana gudun bacin ran Abdul-Sabur kada ta
furta wata kalma da zai yi fushi da ita. Umaimah
ta
fara saduda, a yau ta fuskanci rashin kyautawarta
baro-baro a zahiri, wacce ta yiwa Alh. Nasir da
dansa Hanif.
''Tabbas na san Abdul-Sabur mutum ne mai
fadar gaskiya komai dacinta, haka yana kokarin
kwatantawa. Ba ya fushi, kuma bai damu da duk
bakar maganar da za a fada masa ba. Umaimah
take fada a ranta. Umaimah ta sake yiwa Faduwa
sha'awarsa don tabbas zata yi dace da miji na
gari idan har hakan ta kasance.
*******************
Tsakar dare misalin karfe uku Umaimah na zaune
a tsakiyar gadonta, ta mike kafa don bacci ya
kauracewa kwayar idanunta. Ta fuskanci kuka ma
ba zai yi mata wannan magani ba, sai addu'a.
Tana ta jan carbi tana karanto 'hailala da
istigfari,
sannan lahaula wala kuwwata illa billahil azim.
Fitilar dakin Abdul-Sabur ce aka kunna nan da
nan taga hasken ya hasko mata daki, don haka
sai ta tsurawa dakin ido. Da alama ya tashi daga
barci, shi yasa ya kunna fitilar. Ta tashi a hankali
ta je jikin
windo ta daga labule tana duban inuwarsa yana
ta kai kawo a cikin dakinsa. Ba ta ankara ba sai
ganinshi ta yi a jikin windonsa yana kallon
windon dakinta, sai ta yi sauri ta durkusa tana
kyautata zaton ya ganta. Sai ta ga ya gyara
labule ya sake rufewa, ya koma ciki da alama
magana yake yi a waya. Ya wuce zuwa falonsa
sai ta ji motsi ya bude kofar kicin ya shiga. Tana
jin karar bude firij ya zuba lemo a kofi ya sha, ya
bude kofar barandar waje ya fito baranda duk
tana sanda tana hango shi. A halin yanzu in ta yi
sa'a zata iya jiyo abin da yake cewa, saboda dare
ne kuma harshen Hausa ya ke magana.
Tana tsaye a cikin kicin a makale a jikin kofa, sai
dai kash, ba zata iya bude kofar baranda ta fito
ba,
saboda zai ganta. Babu tantama ta ji ya ambaci
sunana Baban Hanif daga dukkan alamu da Alh.
Nasir yake waya. Kwatsam sai ta ji ya ambaci
sunanta baro-baro.
Ya ce, ''Alh Umaimah tana da hankali, amma tana
neman taimako wajen kula da ita don kada ta
shiga wani hali na bakin cikin rayuwa, Allah ma
dai Ya kiyaye.
Ta yi wuki-wuki ta rasa yadda zata yi ta jiyo
sauran abin da ya ke fada, don ya koma cikin
gida ya rufo
kofar. Tana hango inuwarsa a zaune akan dinning
table yana hada shayi har yanzu wayar na sakale
a kunnensa yana magana. Tabbas sun shafe fiye
da awa guda cur suna maganarta.
Ta jawo wayarta ta duba tsaf, babu lambar
Abdul-Sabur a cikin lambobin da ta ke da su,
lambobin
mutane uku ne kacal a ciki, daga ta Faduwa,
Hanif sai ta Babansa.
Ta ji duk ta damu kanta, sai ta ji abin da suke
fada amma kuma babu hanyar da zata ji don
haka ta
cirewa kanta damuwa, tasan koma me za su fada
alkhairi ne. Duk laifin da ta yiwa Alh. Nasir tasan
Abdul-Sabur yana da wayon da zai kare ta. Dole
ma Alh. Nasir ya ji sanyi a ransa in dai Abdul-
Sabur ya jawo masa hadisai da ayoyin alkur'ani.
Jikinta ya yi sanyi ta tashi ta dauro alwala ta
hau nafilfili har aka kira assalatu, ta yi sallah ta
sha ragargazo addo'i akan Allah Ya yaye mata
duk wani abu da yake damunta na kunci a
rayuwarta.
MAKWABTAKA 30
Washe gari litinin ce amma ita ba ta da jarabawa,
don haka ba zata je makaranta yau ba.
Ta fito ta tsaya akan baranda tana shakar
sanyayyiyar iskar da ta ke kadawa. Abdul-Sabur
ne ya hango ta, ya yi kamar zai fito su gaisa sai
ya fasa ya fuskanci ba ta son a cika shisshege
mata. Ya shirya tsaf cikin bakar riga da wando na
suit ya fice
kasa.
Tana daga sama ta hango giftawarsa ya sauko,
sai ya wuce zuwa gareji ya dauko motarsa. Bai
dago da kansa ba balle tasan ya ganta a
tunaninta bai san tana tsaye akan baranda tana
kallonsa ba alhali ya sani.
Tana tsaye tana leke har ya fita daga get din ya
figi motar ya hau titi, daga dukkan alamu sauri
yake yi yana da jarabawa da sassafen nan.
''Tabbas ka yi dace da hali na gari, Allah Ya ba
ka mace ta gari Abdul-Sabur. Umaimah ta fada a
cikin zuciyarta, yayin da hamma ta hana ta sakat
saboda baccin da ta ke ji, ta kwana idonta biyu.
Sai yanzu baccin ya zo. Hawaye ne yake
kwararowa daga idanunta da zarar ta yi hamma,
sai yinta take ba kakkautawa, mafita daya ce ta
je ta kwanta ta yi bacci, amma sai ta cika
tumbinta zata yi bacci daga
dukkan alamu tabahuwa zata iya hana ta baccin.
Kan ka ce kwabo ta shige kicin ta jona butar
ruwan zafi (kettle), nan da nan ta tafasa ta hada
shayi ta
sha da biskit. Daman yawancin abincinta ke nan,
ba ta cika cin abinci mai nauyi ba, shi yasa har
yanzu kiba ta gagare ta.
Da kyar ta ke takawa ta shiga daki, da rarrafe ta
hau gado saboda tsananin baccin da ya yi mata
nauyi a ido. Abu na farko da ta fara tunawa
shine:
''Shin ko yaya Abdul-Sabur ya ke ji shima da ya
kwana yana yawo yana waya bai runtsa ba?
Da safe bai yi bacci ba ya fita zuwa makaranta.
Ta fada a bayyane ''Ka ga bayin Allah masu
kaunar *yan uwa musulmai, matsalar wani ta
zama
matsalarsu. Allah Ya saka masa da alkhairi.
Daga nan ta rufe ido bacci mai dadin gaske ya
rufeta, sai ta dora da mafarkai masu dadi.
Umaimah ta yi mafarki Alh. Nasir ya zo yana
fara'a yana ambaton sunanta har ya ce da ita
tare muke da kawarki Lamijo zo mu je inda ta ke
ku gaisa.
Umaimah ta hau murna a cikin mafarkin tana
fadin, ''Alhamdulillah da Lamijo ta fahimce ni ta
bar zargina.
Sai taga Abdul-Sabur ma a mafarkin ya yi
murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Dauki takalmanki
sababbi ki saka ki je ku gaisa da kawarki.
Ta yi zumbur ta bude ido, sai ta ga ashe mafarki
ta ke yi. Hakika mafarkin nan ya bata mamaki
matuka. Sai ta tofa addu'a Gabas da Yamma,
Kudu da Arewa ta canja yanayin kwanciyarta ta
ci gaba da barci.
Mafarkai makamantan wadannan dai ta ci gaba
da yi.
Bacci ya yi bacci abu kamar wasa, har karfe uku
saura mintina na rana sannan Umaimah ta farka
daga baccin nan da ta ka yi, shi ma a sanadiyyar
wayar da Hanif ya rangado mata ne ya tashe ta,
ba
don baccin ya ishe ta ba.
Ta yi sauri ta mika hannu ta wawuro wayar ta
duba sai ta ga sunan Hanif ne, nan da nan ta
amsa.
Hanif ya gaishe ta cikin ladabi, ''Anti fal bakinsa
haka yake kiranta kamar yadda ya ke kiran
Lamijo matar Babansa.
''Anti ya makaranta? Ya ya karatun jarabawar,
koda yake fa Anti ba kwa tsoron jarabawa na ji
labari irin pionts din da kike ja. Ance 4pointer ce
ana kyautata zaton da first class za ki fita. Ashe
ba'a banza ba da ba kya kula mutane boko ne
kadai a gabanki.
Ta tuntsure da dariya da bata shirya ba, sai ta
nemi baccin da ya ke idanuwanta ta rasa.
Ta ce da shi, ''Kai Hanif wa ya fada maka haka?
Kai ne dai ka kirkiro hakan don ka tsokane ni. Ya
ce, ''Wallahi an fada min, ba daga bakin mutum
daya na ji haka ba, *yan ajinku ma sun fada min.
Ke
ki rantse in ba haka ba ne kamar yadda na
rantse.
Umaimah ta kyalkyale da dariya, ta ce, ''To meye
abun rantse-rantse tunda ka ce haka ne, to
abarshi
a hakan. Hanif ya ce, ''Kin san haka ne ke ma.
Amma ai abun alfahari ne ma a wajenki, ni da zan
sami haka ai da na dinga dagawa ina alfahari a
kasar nan da ma Nigeria gaba daya.
Tanadi na musamman fa gwamna ya yiwa wanda
ya fito da first class a cikinmu, kuma ya yi
alkawarin zai biyawa wanda ya fita da first class
kudin karatun master da PhD a kowacce kasa ya
ke so yayi a duniya. Bayan babban aiki da za a
bashi a gwamnatin garinmu. Ina ga ku biyu ne za
ku sami wannan garabasar ke da wani Abba
Ahmad dan makarantarmu.
Umaimah ta yi murmushin farin ciki, ta lumshe
ido ta ce, ''Alhamdu lillahi, kai ma fa idan ka dage
zaka
iya kamo mu ka fito da first class.
Hanif ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A yaushe
kuma bayan saura shekara daya da kadan mu
gama, an cinye rabin karatu ina zan iya kamo ku?
Mu dai ki barmu a second calass upper ko lower
ma ai kwakwalwar ma ba iri daya ba ce. Baba ya
ce kun kira shi jiya, ya yi farin ciki sosai, ya ce
idan an
yi hutu in dinga ziyartarki muna gaisawa. Kuma
idan an yi hutu in tambayeki in kina so ki zo ki ga
gida zai aiko mana da kudin tikiti. Sai ta ji kamar
ya daba mata wuka a kirji, ta dafe kirji ta yi
firgigit ta tashi ta zauna.
Ta ce, ''A'a bazan je gida ba, sai na gama sai dai
ka tafi kai kadai.
Hanif ya ce, ''Ba ga irinta ba, mu ne masu yin
nisa da littafi ku masu kokarin nan ba kwa yin
nisa da littafinku, boko ya hana.
Suka yi dariya su dukkansu, daga karshe suka
yiwa juna fatan alkahairi da sallama suka kashe
waya.
Umaimah ta ji dadin hira da Hanif, yaro mai kirki
da ladabi, sai ta ji sanyi a ranta tamkar ta ji
muryar dan uwanta rabin jiki Sabitu. Tana duba
agogo ta ga lokaci ya ja azahar har ta gota, sai
ta yi wuf! Ta diro daga kan gado tana fadin,
''Astagfirullah! A'uzu billah, na makara azahar ta
wuce ban yi sallah ba.
Gaskiyarki Umaimah, sallah ita ce gaba da komai.
Allah Yana hukunta masu aikata tarikul salat.
Allah Ya mana jagora, Ya shiryar da mu hanya
madaidaiciya, amin!!!
**************
Faduwa ce a tsaye a gaban kofar gidan Umaimah
da yammacin ranar juma'a, Umaimah na bude
kofa sai ta ga bakuwarta. Farin ciki ne ya duro
mata mabayyani a fuskarta. Ta yi sauri ta
rungume ta gami da ruko hannunta suka zo suka
zauna a cikin falo akan kujerun nan nata na
alfarma. Faduwa ta dube ta ta yi murmushi, ta
ce, ''Ya na ga kin rame ko
jarrabawa ce?
Umaimah ta taba kashin wuyanta, ta ce,
''Jarabawa ce Anti, bana iya cin abincin kirki
kullum.
Faduwa ta ce, ''Bayan jarabawar fa, meye yake
ramar da ke?
Sai Umaimah ta yi kasake tana kallonta ta kasa
amsa wannan tambayar.
Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kin saka damuwa a
ranki da yawan tunani, ga kuka kullum. Ki daina,
babu kyau ko don lafiyarki ma, mu likitoci ba ma
son haka.
Nan da nan idanuwanta suka ciko da kwalla da
alama da wani kukan zata fashe.
Faduwa ta ce, ''Au tuno miki ma na yi?
Shi ne za ki bude min sabon shafin kuka? A'a
kada ki tayar min da hankalina, na zo mu yi hira
wasa da dariya kuma zaki fashe da kuka?
Umaimah ta yi sauri ta goge idanunta, ta yi
murmushin karfin hali, ta ce, ''To na goge
hawayen na daina kukan, mu yi hirar.
Faduwa ta shafi kuncinta ta ce, ''Yauwa kanwata,
ko ke fa rayuwa ma yanzu za ki fara. Nawa kike
da zaki nemi kashe zuciyarki? Ki sakawa ranki
damuwa. Abdul-Sabur ya aiko ni wajenki, ya ce in
ce ki ba shi lambar Abdul-Basi...
Faduwa ba ta rufe bakinta ba Umaimah ta zabura
ta mike tsaye gami da dafe kirji. Ta ce,
''Subhanallahi, ina zan sami lambar Abdul-Basi?
In ina da ita ma me zai yi da ita da yake nema?
Me ye hadina da Abdul-Basi?
Me Abdul-Sabur yake nufi da yake neman in ba
shi lambar Abdul-Basi?
Kada ya sake ya ce zai dai-daita ni da shi don in
koma gidansa a matsayin matarsa, da in yi haka
gara a dauki gawata a kai masa.
Faduwa ta mike tsaye cike da damuwa, da kuma
mamaki, ta dafa kafadar Umaimah.
Ta ce, ''Ya naga hankalinki ya dugunzuma daga
kiran sunan Abdul-Basi? Mijinki ne fa uban danki
ya aka yi kika zamar da shi makiyi? Umaimah ki
fahimci Abdul-Sabur shi mutum ne mai son
shirya alkhairi, me son ya ga hankalin kowanne
musulmi a kwance, musamman mu mata da muke
kasar da babu dangin iya babu na Baba. Ki bada
lambar tasa ki zuba masa ido ki ga wacce hikima
zai bullo da ita...
Umaimah ta katse ta kafin ta rufe bakinta, ta
dakatar da ita da hannu sannan ta zame
kafadarta daga hannun Faduwa, hawaye ya yi
mata face-face a fuska. Ta fada cikin kakkausar
murya.
''Anti Faduwa, ba zan boye miki ba Abdul-Sabur
yana yawan takura min a rayuwa yana saka ni a
cikin wani hali, yana saka ni aikata abubuwan da
ba na ra'ayi. Wannan karon dai sai dai ya yi
hakuri bazan aiwatar da abin da yake so na yi ba.
Sai dai in a kashe ni amma ba zan yi magana da
Abdul-Basi ba. Kada Abdul-Sabur ya ga na yarda
na gaisa da Hanif da Babansa ya zaci zan yarda
in yi magana da abdul-Basi.
Faduwa ta yi dan murmushi, ta ce, ''Abdul-Sabur
ne ya aiko ni ya ce in kin ki bani inyi masa waya
ya zo
da kansa.
Umaimah ta ce, ''Ko ya zo da kansa ba zan iya
ba shi lambarsa ba balle ma ban san lambarsa
ba.. Ba ta rufe baki ba sai ga Abdul-Sabur a
gabanta.
Nan da nan ta zabura ta yi wuki-wuki da ido
kamar ba ita ba ce take fiffikala ba yanzun nan.
Ya zura
mata ido yana kallo, sai ta yi sauri ta sunkuyar
da kanta kasa. Daga dukkan alamu daman a
kusa da
kofar ya ke, ya ji dun abin da ta fada. A sanyaye
ta sami kujera ta zauna ta rike kai, yayin da
hawaye zazzafa ya dinga digowa daga idanunta.
Zuciyarta ta yi ta tafasa, wani sabon tashin
hankalin matsalar rayuwa ne suka zubo
mata.
Malaysia ta yi mata zafi, ta ji dama ba ta zo
unguwar nan ba balle tasan Abdul-Sabur. Ta ji ta
tsane shi tsanar da ba ta yi masa irin ta ba a
baya. Tabbas yana yawan shigar mata hanci da
kudundune amma a yau ta shirya tsaf zata fyeto
shi. Ta kuduri niyyar tashi daga gidan nan a cikin
satin nan, kuma har abada ba zai taba sanin inda
zata koma ba, balle ya takura mata. Ina ruwansa
da rayuwarta da zai saka mata ido ya damu da
sai ta shirya da mutanen da ba ta bata da su a
baya? A mutanen har da Abdul-Basi mutumin da
ya shayar da ita ruwan madaci, ya wahalar da
ita, ya ci amanarta, ya rabata da abin kaunarta a
duniya *ya*yanta. Tana cikin wannan tunani da
murkusun takaici,
kanta a sunkuye a kasa yayin da hawayen takaici
ya ci gaba da bulbulowa daga matse-matsin
yatsunta na hannu data dafe fuskarta da su.
Ya rasa kalmar da zai fara furta mata, saboda bai
zaci har wannan abun da ya nema ba zai sakata
a cikin wannan tashin hankali ba.
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya sunkuyar da
kansa kasa ya dauki lokaci mai dan tsawo a
tsaye a kanta,
sannan ya zaro wayarsa ya nanika mata a cikin
hannayenta.
Ta zabura ta dago da jajayen idanunta ta dube
shi, duba irin na rashin fahimta da takaici.
Ya fada cikin sororuwar murya mai cike da
tausayawa gami da lallashi, 'Saka min lamabar
Abdul-Basi a wayata na ce, ba a wayarki ba.
Kuma ni bance zan kira shi don ku yi magana ba,
haka bance zan sasantaku ba don ku koma. Na
miki alkawari babu wani abu da zan yi don in
jawo ranki ya baci, ko hankalinki ya tashi.
Tsakani na da
ku sai fata na gari da dimbin alkhairi.
Ta dube shi, ta juya ta dubi Faduwa wacce ke
gefe sai kifta mata ido ta ke, tana yi mata nuni
da hannu
alamar ta rubuta masa lambar wayar. Umaimah
ta zamo tamkar wacce kwakwalwarta ta zare,
kamar ba ta da wata dubara ko tunanin kanta sai
yadda suka yi da ita. Ta karbi wayar ta zurawa
wayar Abdul-Sabur ido tana jujjuyawa. Ta ci gaba
da zubo da wani sabon baiti na hawaye mai
radadi wannan karon hawayen tuno da takaicin
da Abdul-Basi ya guma mata a rayuwa ta ke yi.
Ta shiga danno lambarsa a hankali, yayin da
zuciyarta ta ke rababbaka, bata taba zaton akwai
ranar da zata zo da har zata danno lambar wayar
Abdul-Basi ba.
Abdul-Sabur ya cuci rayuwarta da
ya tursasa mata take yin abn da ba ta so, amma
yau komai zai kare saboda a bisa sharadin barin
gidan nan ta ba shi lambar shi ne dai bai sani ba.
Ta mika masa wayarsa ya kurawa lambobin ido,
da alama dai kirgawa yake yi sai da ya tabbatar
sun cika. Sai ya matsa code number Nageria ya
kira lambar, yana dannawa ta shiga ya tabbatar
tana aiki ko ba ta yi.
Yayin da numfashin Umaimah ya ke kokarin
daukewa saboda tashin hankali, amma ta kuduri
niyyar ko me Abdul-Sabur zai mata yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login