Showing 45001 words to 48000 words out of 130520 words
Chapter 16 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
yi tsuru-tsuru, kana ganinsu kasan a
takure suke.
Ita kadai ce a gidan yaranta duk sun tafi
makaranta.
Na yi sallama sam ba ta amsa min ba, na wuce
kai tsaye na dauki Bilal na kama hannun
Babangida na ja, ai kuwa sai ta rike shi ta ja.
Ta ce, ''Ki tafi da danki, wannan dai ba ke kika
haifa ba, kuma ba ke kika ba ni ba, Kakarsa ce ta
ba ni da
ubansa, don haka sai a bar min dana.
Na auna mata harara, na ce, ''Kin manta wace ce
ta haife shi? Idan kin manta ki tuna, dana ne, dan
yayata ne uwa daya uba daya, don haka ni na fi
cancanta na rike shi ba ke ba.
Sai ta sake shi ta gyada kai, ta ce, ''dauke su ki
tafi da su, na ji *ya*yanki ne amma ki sani
daukar
*ya*yan nan da kika yi daga wajena zai zai janyo
miki bacin ran da za ki dauwama da shi bai
gushe ba. Ni Haj. Zulayha ba a ja da ni, yaro bai
san wuta ba sai ya dafa ta. Idan kin san wata ba
ki san wata
ba, da sannu za ki banbance zuma da madaci.
Na sake auna mata harara na ce, ''Allah Ya fi ki
ai, duk abin da ya same ni daga Allah ne ba dai
mutum ba. Ta rike baki tana mamaki, sai ta
gyada kai, ta ce,
''Au har kin yi baki? Kin yi wayon yi min rashin
kunya? Tabbas sai na zame miki duhu a cikin
rayuwarki, sai kin yi da-na-sani da ba ki zage ni
ba.
Na ja wani dogon tsaki ba tare da na tanka mata
ba, na fice da *ya*yana muka shiga gidana. Sai
na ji sanyin kasurgumin bacin ran da nake ciki da
na ganni da yarana suna taya ni hira.
Amma ina mai tsananin mamaki da takaicin kawo
Babangida a dalilin Zulayha ba a dalilina ba. Babu
irin magiyar da ban yiwa Abdul-Basi ba tun
farkon aurenmu ya dawo da Babangida wajena,
amma fur! Ya ki sai ga shi yanzu ya dauko shi
tun kafin ma ya aure ta ya damka mata shi.
Na san halin kissa da kisisinar Zulayha ta yi
musu dadin baki ne shi yasa suke ganin ita zata
iya rike
su alhalin nan gaba wahalar da su zata yi.
Na san zata fadawa Abdul-Basi zai yi fushi da ni
amma ban zaci har zai yanke min irin wannan
hukuncin ba....
Sai ta dafe kai ta surnano da hawaye.
Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Ba dai dukanki ya yi
ba akan haka?
Kafin ta amsa Abdul-Sabur ya amshe da cewa.
''Ba dai saki ya baki ba?
Umaimah ta sharce hawaye mai hade da majina,
''Ina fita tayi masa waya wajen azahar sai ga shi
a
gida. Na yi mamaki da ganinsa dai-dai wannan
lokacin. A fusace ya fado mana cikin falon, muna
cin abinci. A gigice muka mike don tsorata, ya
daka min tsawa ya tambaye ni.
''Me ya kai ki gidan Zulayha kika zage ta?
Na ce, ''Ban zage ta ba, ni karya ta ke yi min''
Ya dakamin tsawa, ya fada cike da fusata, ''Ita ta
ke yi miki karya? Sa'ar ki ce? Daman ta ce kin
zama
fitsararriya, don haka ki kwashi yaran nan ki
mayar da su, amma ki durkusa ki ba ta hakuri
kada ki sake shiga gidanta.
Na tambaye shi har Bilal din ma a wajenta zai
zauna? Ba saboda rashin lafiya ba ne aka ba ta
ba,
yanzu kuwa ai na warke ni zan rike dana.
Sai na ji ya kwashe ni da mari dau! Na durkushe
na rike kunci. Ya fada cikin kakkausar murya.
''Daga yau idan ina magana kina yi sai na saba
miki.
Banza! Ballagaza, saunar mata. Yaushe aka
gama rainonki da zaki iya rainon wasu? Yaushe
kika
gama sanin ciwon kanki balle ki san ciwon wani?
To tunda bakyajin maganata ki shirya kayanki
gobe na saki a mota ki koma Dugge can ki zauna
a gidanku, sai ki yi musu fitsarar a kauye, ba a
nan ba. Dama tsiyar bakauye ke nan, ya zo birni
ya sha
jar miya ya nuna maka ya fi ka iya tafiya a kan
tiles.
Na ji kamar almara, na kasa kuka, na kasa
magana.
Ya ja hannun yaran suna ta tsala kuka, har da
ihu ya kai su wajen Zulayha, sannan ya shiga
motarsa
ya koma ofis. Sai a lokacin na fara rusa kuka ni
kadai a daki, amma na tsorata da maganar kora
ta da ya yi, na san tonan asirina ya zo idan ya
sake ni na koma Ruga da zama.
Har dare jikina rawa ya ke yi, ina ta addu'ar Allah
Ya huci zuciyarsa kada ya dawo da fushi ya sake
ni. Ya dawo tunda magruba, na ga tsayuwar
motarsa amma ba gidana ya shigo ba, gidan
Zulayha ya shiga inda ya ci lafiyayyen abincin da
ta dafa masa.
Ni kuwa da yake bai bar min kudin abinci ba, sai
na dafa shinkafa da wake da mai da yaji, dan na
ga yana sonsa. Na kakkalato kudi na aika aka
siyo min salad da tumatir da *yar albasa na
yayyanka masa don na burge shi. Bai shigo gidan
ba sai sha dayan dare.
Na durkusa na gaishe shi ya yi banza da ni
kamar bai san da wanzuwata a gurin ba, na
yunkura zan je na dauko abinci, sai ya ce dawo
nan, bana son abincinki munafuka.
Na tsorata da jin wannan kalma da ta fito daga
bakinsa. Na dawo na durkusa, sai ya fara
zayyano min maganganu kala-kala na tsakani na
da shi,
amma ya ji maganar nan a waje a ofis ma aka
fada masa. Sai jikina ya hau rawa na ce, ''Ni ban
fadawa kowa ba.
Ya daka min tsawa ya ce, ''Ki fada min da wacce
ku ke hira a gidan nan idan bani nan, ko kuma
yanzu
na yi kasa-kasa da ke, bakar makira kina tafiya a
sum-sumke, amma sai tsabar bakin munafurci da
tozarci.
Can na tuno aminiyata Bara'atu ce kadai nake irin
wannan hirar da ita. Sai na ce, ''Na san dai mu
kan
yi hira da Bara'atu.
Ya ce, ''To zamana da ke ya kare tunda ba kya
iya boyemin sirrina. Bara'atu kike fadawa ita
kuma ta ke kwashewa ta fadawa mijinta, shi
kuma ya je ofis yana yadawa ga abokan aikinmu.
Na yi ta ba shi hakuri, na ce, ''Ba zan kara ba.
Ya yi banza da ni, ya shiga daki sai ya fito min
da farar takarda mai kunshe da bakin sako. Na
bude
na karanta tun a gabansa, saki daya ya rubuta
min, wanda tunda nake a rayuwata ban taba jin
tashin hankali ba sai irin na ranar. Allah Ya sa
ban manta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un ba. Na yi ta fada ina mai-maitawa kamar
yadda malamin islamiyyarmu ya ce mu dinga yi
da zarar mun hadu da bala'i. Ya damke gashina
ya kai ni dakina ya ce, na fara hada kayana gobe
da safe zai saka ni a mota na tafi garinmu.
Ina makyarkyata ina hada kayana a lokacin na
nemi hawaye na rasa, saboda masifa ta yi
masifa, tashin hankalina rabuwa da karamin dana
Bilal ga Babamgida da aka dauko shi daga gidan
tarbiyya,
wajen rufin asiri aka kawo shi wajen wahala, inda
za a iya gurbata masa tarbiyya, shi ma zan fi so
da an bar shi a Gombe ya fi komai a gare ni.
Yana ta zagina ta uwa ta uba, yana ambaton
albasa ba ta yi halin ruwa ba, ban yi halin Nasiba
ba, ba don albarkacin Nasiba ba ai da tuni ya
sake ni.
Alhali na fi yi masa biyayya ma akan Nasiba, na fi
ta wayewa da sanin tattalin miji...
Abdul-Sabur ya kumbura ya yi suntum kai ka ce
Abdul-Basi ne a gabansa, ko Zulayha sai harare-
harare yake zuciyar nan na ta tafasa don takaici.
Faduwa kuwa sai girgiza kai ta ke, kira ta ke,
''Lahaula wala kuwwata illah billah.
Umaimah ta zubo da hawayen takaici, ta ce, ''Na
kwana ban runtsa ba a zaune, ina ta sake-saken
inda zan nufa don ba zan iya zama a tsakiyar
Matawata da Ilah ba, ga gulmar gari, ga
tsangwamar matan uba, ga talauci da rashin
lafiyar mahaifina babu kudin magani.
Daman Abdul-Basi ne mai siya ya aika masa, ni
ma na tara dan kudi na kunshe idan na je na ba
shi, yanzu duk babu mai ba mu.
Gari ya waye na tashi na yi wanka na yi sallah
tun da asubah. Sai da na jima da kimtsawa
sannan na ji
Abdul-Basi ya shiga wanka, misalin karfe shida
da rabi, bakar abaya na saka a jikina sai na
zindimo bakin hijabi na fice da sauri na nufi gidan
Bara'atu zuciyata tana ta tafasa. Ba su bude gida
ba ma ni na kwankwasa, na san sun tashi tunda
mijinta ma Ma'aikacin Banki ne. Ta yi mamaki da
ganina, gami da hawaye face-face a idona.
''Lafiya Umaimah? Ta tambaye ni a dan duburce
Na ce, ''Na zo ne na yi miki sallama na kuma yi
miki godiya. Na ji abin da duk kika fadawa mijinki
shi kuma ya je ya yada a ofis har Abdul-Basi ya
zo ya sake ni a dalilin haka. Amma wallahi
Bara'atu kin ba ni mamaki, ban taba tunanin
MAKWABTAKA takan iya komawa cuta ba. Yanzu
duk yadda na dauke ki a gurina ki rasa abin da
zaki saka min da shi, sai ki kwashe duk maganar
da muka yi da ke ki fadawa mijinki, shi kuma don
rashin lissafi kamar shi namiji wai ya buge da
kwasar maganar mata yana kaiwa gurin aiki.
Sai ta hau fada da daga murya don mijinta ya ji
ya fito. Ta na cewa, ''Kamar yaya, me kike nufi?
Ni da mijina munafukai ne ke nan? To mun fada
din ke dai kawai kishi ne ya dame ki za a auro
miki wayayyiya *yar birni, kin tsorata za ki gudu,
amma mu ina ruwanmu? Idan ma na fada ni na
gayyatoki kizo ki fada min?
Surutai dai da cin mutunci ya yi ta fitowa daga
bakin Bara'atu, na yi kasake ina kallonta cike da
tsananin mamaki, makwabciyar da na amincewa
ce yau ta ke min wannan tonan sililin.
MAKWABTAKA 20
Na tuno cin amanar da Matawata ma ta yi min
na hado da cin amanar da Zulayha ta yi min, sai
na ji a raina na tsani duk wani MAKWABCINA. Na
kudira a raina har abada ko gaisuwa babu
tsakanina da MAKWABTANA, haka na dai na ba
da hakkin MAKWABTAKA..
Umaimah ta fashe da kuka mai cin rai.
Abdul-Sabur ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya
gyara zama ya ce, ''Ke wanne sirrinsa ne kika
barbaza a
waje wanda ya ba shi haushi haka har da saki?
Kin san fa maza ba sa son kananan maganganu
irin na mata, amma shi ma ai duk wannan bai kai
ga saki ba.
Umaimah ta ci gaba da kuka, abin da kuwa ba ta
sani ba, kukanta yana tayar da hankali ga duk
mai raunin zuciya. Sai suka shiga rarrashinta
suna mika mata toilet paper tana ta sharcewa.
Sai can ta nisa ta ci gaba da magana, ''Allah
Sarki kuruciya mai dadi, rashin sani ya fi dare
duhu. Ba
wani abu na fada ba wanda ya wuce hirar da
nake ba ku yanzu. Hirar garinmu na ba ta, ta
kuruciyarmu da waken dandali. Da hirar yanda
Abdul-Basi ya hadu da yayata Nasiba har aka yi
aure, dawowata wajensu da zamana a wajensu,
da shiga makaranta. Don ita bata san Nasiba ba
a lokacin ba a yi mata aure ba, ba sa gidan,
wadan da suka zauna da Nasiba sun bar gidan.
Kuma da bakinta ta tambaye ni wai wacece
Nasiba
da ta ke jin su Haj. Bishra suna ta maganarta,
wai an ce yayata ce? Shi ne na bata labari, na
hada mata da labarina da Ilah da Matawata sai
kuma labarinsa da Zulayha a lokacin da maganar
cin amanar da ake yi min ban sani ba. Ita ma
Bara'atun ta ke karamin da abubuwan da
idanuwanta suka gani, ko wanda mijinta ya jiyo a
ofis ya fada mata.
To amma ka san magana idan ta zamana ta
koma ta gulma, to yadda za'a jujjuya ta sai ka ji
ba iri daya ba ce da yadda ta ke tun fil'azal.
Yadda Kamal mijim Bara'atu ya je yake fada a
ofis cewa ya yi, Abdul-Basi dan birni ne, dan
masu kudi da sarauta a Gombe, amma saboda
neman kyau ya shiga Ruga ya auro mai tallar
nono Nasiba Yayata
ke nan, wai don ta haifa masa kyawawan *ya*ya.
Da ta rasu ya koma nacewa kanwar bayan shi ya
rike ta ya ce sai ya aure ta, ba ta sonsa, tana ta
wulakanta shi ya yi ta cusa kudi aka raba ta da
saurayinta da ta ke matukar so mai suna Ilah, ta
zo
gidan ba ta sonsa. To burinsa ya cika ya sami
fararen *ya*ya, amma fa duk maza ne ya fi son
*ya mace don ta kawo masa jari.
Kun ji yadda aka juya zancen, kuma dai shi ma
ya tsane ni ya fasa zama da ni akan Zulayha shi
ne ya sa ya yi saki, amma ba don maganar nan
kadai ba.
Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas haka ne,
nima abin da zan fada kenan kika riga ni.
Abdul-sabur ya kurbi lemo ya ce, ''Haka ya ke
yanzu na fuskanci maganar. Ya dai so ya sake ki
ne ya rasa dalili, kuma ba ya so ace ya sake ki a
dalilin zai yi aure.
Umaimah ta langwabe kai gefe, ta ce, ''Sai na ji
Kamal yana magana da Abdul-Basi a waya, wai
ya zo gidansa ya fitar da ni ga shi nan na zo
gidansa ina ta takalar matarsa da fada. To shi ba
ya son tashin hankali, ya za a yi na zo gidansa
na tayar musu da hankali da sassafen nan?
Sai na ji muryar Abdul-Basi yana kwalla min kira
a bakin matattakalar gidan. Na fito da sauri jikina
yana rawa. Bayanai nake yi masa cewar ni ba
fada
na zo na yi da ita ba, sallama zan yi mata.
Ai kuwa ban rufe bakina ba na ji ya rufe ni da
duka ta ko'ina, yana zagi yana jana ya wurga ni a
cikin mota. Da gudu MAKWABTA suka kawo min
agaji,
amma ina! Har ya kulle ni a mota. Haj. Bishra har
da hawayenta ta shiga yi masa fada tana cewa,
''Haba Abdul-Basi kashe yarinyar na kake so ka
yi bayan cin amana da cin mutuncin da Zulayha
take mata a gidan nan tana hakuri, kuma har da
duka da zagi?
Sai ya balbale ta da rashin kunya, wai babu
ruwanta da iyalansa. Ina daga cikin mota na bude
mata takardar sakin da ke kunshe a cikin rigata.
Ta gilas ta karanta, sai ta fashe da kuka ta shiga
gida.
Kalmar karshe da ta fada kafin ta tafi ita ce, ''Ki
yi hakuri Allah Zai musanya miki da miji mafi
aikhairi.
''Insha Allah''. Inji Abdul-Sabur.
Faduwa ta ce, ''Kayanki fa, ya bari kin koma kin
dauko? Ta ce, ''Eh, gidan amaryarsa ya shiga ko
in ce
farkarsa don ba a yi auren ba suke holewarsu. Ta
lalata shi, salihin mutum ne Abdul-Basi, ban taba
jinsa da neman mata ba, amma sai ga shi kowa
ya san abin da suke aikatawa da Zulayha
Senegal.
Yana shiga na bude kofar da gudu na hau
samana Allah Ya sa bai kulle ba na jawo katuwar
akwatina da na shirya ta tun cikin dare na ratayo
jakata mai dauke da tarkacen kayan kwalliyata
na fito, har nazo matattakala zan sauka na tuna
takarduna na firamare da sakandire, da na
diploma da na yi akan na'ura mai kwakwalwa
(computer) suna cikin akwatin da yake ajiye
muhimman takardunsa na garzaya da gudu na
dauko a cikin ambulan na cusa su a cikin riga
don idan ya gani zai kwace tunda ya yi niyyar yin
mugunta, baya son ci gabana.
Ina saukowa sai na ji an ambaci sunana, wata
*yar karamar murya daga kan barandar Zulayha.
Na daga kai da sauri sai na ga Bilal dina ne ya
tashi daga barci daga shi sai pampers.
Yana murna yana tsalle yana fadin, ''Ga Umma''
Sai Babangida ya fito da gudu ya ce, ''Aunty
Umaimah ina za ki je na ga kin dauko akwati?
Kar ki tafi ki bar mu, ni ma zan bi ki Gomben. Sai
ta fashe da kuka cikin rurin kukan ta ci gaba da
magana, ta ce, ''Sai na daga ido na dube su na yi
musu addu'a, na ce ''Allah Ya kare ku, Ya raya ku
na ba wa Allah amanarku.
Na ja akwatina da sauri na tafi, suna ganin na
tafi sai suka fashe da kuka suna kiran sunana.
Na tsugunna a bakin motar Abdul-Basi na toshe
kunnuwana da hannayena biyu saboda sautin
kukansu tamkar darmar wuta ake caka min a
dodon kunnena....
Kuka ya ci karfinta sosai, yayin da ta kifa kai
akan dinning table din da ta ke ta yi ta rusawa.
Hawaye mai yawa ya yi ta zubowa daga
idanunwan Abdul-Sabur da Faduwa su ma
saboda tausayi.
Lokaci mai tsawo suka dauka kowa ya kasa
magana. Umaimah ta dago da kanta ta sa toilet
peper ta goge hawayen da ya bata mata fuska,
yayin da idanuwanta suka yi jajawur ta ci gaba
da cewa.
''Har yanzu wani lokacin sai na ji kamar kukansu
ne a cikin kunnuwana, sai na yi ta tunanin ko a
wanne hali suke ciki?
Na san Allah ba zai bari su wulakanta ba insha
Allah. Ya fito a fusace na yi sauri na mike tsaye
kada ya sake dukana, ya harari akwatina ya bude
bayan mota ya wuce ya shiga mota ya kunna. Sai
na kinkimi akwatina na saka a cikin bayan motar
na mayar na rufe. Na sake daga ido na dubi su
Bilal har yanzu ba su gushe daga wajen ba, ba su
daina kallona ba suna kuka suna kiran sunana ba.
Na sake daga kai na dubi wundon kicin sai ga
Zulayha a labe ita da *yarta suna nuna ni suna
dariyar mugunta.
Na yi sauri na bude gidan baya na zauna don na
san gidan gaba ya haramta a gare ni yanzu a
wajensa. A fusace ya fisgi motar sauran
MAKWABTA sun fito sun jeru suna daga min
hannu suna nuna
min jimami a gare ni, har da kabilun mazan nan
da suke zaune a gidan su ma sun tausaya min
har da
yi min hawaye.
Ya kai ni tasha ya fito ya bude bayan mota ya
kira masu lodi ya ce su saka kayan a motar
Gombe,
daga Gombe zai biya direba ya wuce da ni Dugge,
ya kai ni har gida ya damka ni a hannun
mahaifana.
Da suka ji ciniki sai suka rugo suka kira direban
ya garzayo da kansa don ya caski kudi. Nan da
nan ya
amince da bukatun Abdul-Basi, kudi mai yawa ya
ba shi ya juya ya tafi ya bar ni da dirobobi a
tsaye.
Bai ma sake waigowa ba balle ya ga na shiga ko
ban shiga ba. Ko sisi bai ba ni ba, bayan kuma ya
san ba ni da ko sisi a jakata.
Na yi ta rusa kuka a motar ana kallona, wasu na
ba ni hakuri, wasu na tambayar me aka yi min.
Har mota ta tashi muka tafi ban daina kuka ba,
idanuwana kamar za su zazzago su fado don zafi
da kumburi ga ja da suka yi, sai na yi tawakkali
na zaro carbi na yi ta jan ''Lahaula wala kuwwata
illa billahil alaihil azim.
Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan
minha''.
Ba adadi har muka isa Gombe.
Na yi kamar na ki wucewa garinmu na tafi gidan
iyayensa na sanar musu ko za su sa ya mayar da
ni,
sai na ga gara na hakura da shi tunda ya daina
sona, so yake ya rabu da ni ta kowanne hali.
Direba ya kai ni Dugge da misalin karfe biyar na
yamma, sai yara suka hau murna da ihu sun zaci
na taho musu da tsaraba kamar yadda na saba
zo musu da su alewa, biskit, cingam, biredi, lemo,
ayaba. Har na tafi kullum sai na rabawa yara
alewa kwali-kwali nake saya. Wannan karon babu
komai, nima makoshina a bushe yake ba ci ba
sha a hanya, pure water guda
daya wata mata da ta zauna a kusa da ni ta ba
ni na sha, bayan shi ban ci komai ba ina ji ina
gani, ina jin