Showing 72001 words to 75000 words out of 130520 words

Chapter 25 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8052

ba zata
yi magana da Abdul-Basi ba. Ta ci gaba da
addu'a Allah Ya sa ya canja layi a kasa samunsa,
kuma daman layinsa daya na MTN din nan.
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya gyada kai, da
alama dai ya ci nasara lambar ta shiga sai ya
katse.
Ya dubi Umaimah, duba na tausayi ya girgiza kai,
ya juya ya dubi Faduwa.
Ya ce, ''Ki lallashe ta ta daina kuka, ki fadakar da
ita manufata.
Ya juya da sauri ya fice bai sake waiwayowaba.
Faduwa ta karaso kujerar da Umaimah ta ke
zaune,
sai ta zauna a hannun kujerar ta rungume ta.
Ta ce, ''Yi shiru kanwata, na san zaki tsane mu
yanzu, amma nan gaba zaki yabe mu. Mu masu
sonki ne, kuma masu son inganta rayuwarki ne.
Zo mu je gidana mu yini saboda ki sami saukin
bacin
ran.
Umaimah ta fizge jikinta tana magana cikin
shasshekar kuka ta ce, ''Kaina ne yake ciwo
magani zan sha na kwanta. Faduwa ta ce, ''Allah
Ya sauwake, mu je gidana in ba ki magani in
kisha ki kwanta.
Umaimah ta sake turo baki gaba don takaici, ta
ce ''Ina da magani a daki.
Faduwa ta ce, ''To ki je ki sha ki kwanta. Bari in
tafi in barki, ki huta sai mun hadu gobe. Faduwa
ta tashi ta fice fuskarta har yanzu cike da
murmushi, don ita ba ta fushi. Yayin da Umaimah
ta bita da harara don tsana.
Fitar Faduwa ba jimawa Umaimah ta tashi a
fusace ta banko kofar gidan ta ta datse da
mukulli gami da karawa da sakata. Ba don
jarabawa ta ke zanawa ba da sai ta shafe sati
guda a cikin gida bata fita ba,
kuma ba zata kunna fitila ba balle a san tana ciki.
Tsananin takaicin da take ji bata ki a wayi gari a
ganta a mace ba don ta huta.
Kalmar 'La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu
minal zalimin. Ta yi ta karantowa a ranta, sannan
ta fara jin sa'ida a zuciyarta.
Don ma bacin rai ba ya hana ta yin karatu da a
yau ba zata yi karatuba. To daga anzo maganar
karatu tana iya jingine damuwa ta lura da
littafinta har sai ta gane.
Allah Ya yi mana maganin duk wata masifa,
Aamiin!!
MAKWABTAKA 31
Sati ya zagayo Umaimah ta kammala jarabawarta
babu abin da ya yi mata saura sai shirin tashi
daga gidan nan. Har ta fara cigiyar gidajen haya a
unguwa mai nisan gaske yadda su Abdul-Sabur
ba zasu sake ganinta ba.
Amma fa ta fara jin dadin wayarta saboda Hanif
kullum sai ya yi mata waya sun sha hira. Haka
jifa-jifa babansa yana kiranta su gaisa ya tambayi
lafiyarta da karatunta. Ita ma in aka kwana biyu
sai ta yi masa flashin in dai ba ya aiki, ko baya
tare da Lamijo sai kaga ya kira ta su gaisa. Don
ba ta son ta
kira shi lokacin da yake tare da iyalinsa, kada su
zarge shi da wani abu. musamman Lamijo da
tuni ta
zarga.
Lambobin mutane tara gare ta a wayarta, a kalla
a kowacce rana mutane biyar suna kiranta su
jima suna hira. Mutanen kuwa sune Hanif, Baban
Hanif, Faduwa, Aisha Bingyal, Binta Hamisu, Tahir
Aliyu
duk *yan Gombe ne *yan ajinsu. Sai kuma sauran
ukun kuwa malamanta ne na makaranta matan
nan biyu da suka yi zaman jinyarta a asibiti *yar
India da *yar Malaysia Mrs. Sonia, da Mrs.
Rabi'at, sai lambar Mr. Cheu HOD department
dinsu.
Wasu daman tana da lambobinsu a rubuce rashin
waya ne ya sa ba ta kira su ba, kamar
Malamanta.
Dalibai *yan uwanta kuwa da suka ga waya a
hannunta sai suka karbi lambarta, idan ta dawo
gida sai ta ji suna kiranta sai ta yi saved number
masu hankali cikinsu.
Tabbas Umaimah ta fara ganin canji a rayuwarta
don a yanzu daga safe zuwa lokacin da rana zata
fadi zata yi hira da bil'adama ta yi murmushi, ta
yi dariya har ta kyakyace, musamman idan Hanif
ya
kira ta baya gajiya da magana, baya kuma jin
tsoron katin waya don yana da ishasshen kudi.
Kawayenta suna kiranta su fada mata halin da
makaranta ta ke ciki, duk ranar da bata fito da
wuri
ba haka malamanta tana kira ta tambaye su
abubuwan da ta ke bida ta ji na game da
sakamakon jarabawar da suka gama jarabawa.
Ta ji shin an gama dubawa (making) ko ba a
gama ba, da dai suaransu.
Ta fara jinta ta dawo cikin duniya tsundum don a
da tana ganin kamar ba a raye ta ke ba, ita kadai
sai ta yi kwana uku ba ta yi ko tari ba a cikin
gida,
komai ba ya mata dadi, ko abinci ta dafa sai ta
kasa ci.
Allah Ya kauta.
*******************
Ranar litinin ce da misalin karfe goma na safe da
yake ba makaranta zata je ba, don haka ko
wanka ba ta yi ba, tana sanye da rigar baccinta.
Shayi da lifton ne kawai ta ke kurba, ko madara
babu yayin da ta mike kafa a tsakiyar falo akan
kafet tana kallon talabijin tashar MBC 4 suna
shirin 'The Doctors'. Tana jin dadin yadda ake
jero abincin da masu kiba zasu ringa ci don su
rage kiba. Ita da ta
kekashe ba kibar ta kudiri niyyar shi zata dinga ci
don ta yi kiba, sai dai kash ! Ko ta sissiyo ma ba
iya
ci zata yi ba, saboda rashin kwanciyar hankali.
Ta yi ajiyar zuciya mai karfi ta fada a bayyane.
''Allah kai ne jagorana ka kawo min agaji a bisa
al'amurana. Ka musanya min damuwar nan ta
koma farin ciki a rayuwata. Sai ta girgiza kai ta
zubo da kwalla. Kwankwasa kofar da ta ji ana yi
ita ce ta ba ta mamaki a dai-dai
wannan lokaci. Mamaki bai tsawaita ba saboda
tana kyautata zaton Faduwa ce. Ana ta
kwankwasawa kofa gami da danna kararrawa duk
lokaci guda. Ta taso a hankali ta leka ta jikin
hudar kofa. Faduwa ta gani, don haka ba ta damu
da neman hijabi ko dankwali ba, amma fa sai da
ta yi dan siririn tsaki, sannan ta bude kofar a
sanyaye.
Faduwa ta yi sallama ta shigo sai ta rada mata
cewar su biyu ne da Abdul-Sabur, ta je ta sako
hijabi. Umaimah ta arta cikin daki da gudu don
kada ya sako kai ya ganta a haka. Har yanzu
Abdul-Sabur
yana tsaye daga waje bai shigo ba sai da Faduwa
ta sake lekowa ta yi masa iso ya shigo.
Sun jima a zaune akan kujera, Umaimah ta ki
fitowa bayan ta saka dogon hijab ta daura zani,
sai ta yi zamanta a gefen gado ta cika ta yi fam!
Kamar zata fashe. Da zata iya datse kofar
dakinta zata yi ta ki fitowa in sun gaji sa tashi su
tafi. Tana ganin girmansu har yanzu haka kuma
wulakanta mutum babu dadi shiyasa ba zata yi
hakan ba.
Ta fito falo yayin da ta dan kirkiro wani
bushasshen murmushi tana yi, ta duka ta gaishe
su ta koma gefe ta sami kujera ta zauna tana
sauraron abin da za su fada.
Ko ba ta fada ba sun san ba ta farin ciki da
zuwansu.
Abdul-Sabur ya jawo wayarsa ya matsa wata
lamba ya kara a kunne, ba jimawa sai ya taso da
sauri ya mikawa Umaimah, nan da nan ta ji
kirjinta ya buga ta kura masa ido, kallo irin na
tsana ta ke yi masa.
Ya yi dan murmushi, ya ce, ''Karbi waya
Umaimah,
kada ki damu amsawa kawai za ki yi.
Huci kawai ta ke yi tamkar zuciyarta zata fice,
nan da nan hannayenta suka dau karkarwa ta
karba ta dora wayar a kunnenta ba tare da ta yi
magana ba.
Kamar a mafarki, kamar daga sama ta ke jiyo
muryar wanda ba ta taba zato zata sake ji a
duniya
ba. Ta dafe kirji ta lumshe ido, yayin da ta rushe
da kukan dadi amma fa dariya take yi. Ta tashi
da gudu ta shiga daki ta fada akan gado, har
yanzu wayar na makale a kunnenta.
Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta cika da mamaki,
ta ga ya sami kujera ya zauna babu abin da yake
sai murmushi yake yi kasa-kasa.
Faduwa ta matso kusa da shi ta zauna ta
zungure shi, ta ce, ''Da wa ka hadata a waya ta
fashe da kuka daga jin muryarsa, Abdul-Basi ne?
Abdul-Sabur ya ce, ''A'a, danta ne Bilal da dan
yayarta Babangida. Sai da na roki Abdul-Basi
kada ya ce zai yi magana da ita ya hada ta da
yaran kawai. Na sami Abdul-Basi a lokacin da
yake tsakiyar cigiyar Umaimah, gari-gari, gida-
gida yake zuwa nemanta. Ya rasa ta a ko'ina
wanda daga karshe ya sami labarin Umaimah
tana daya daga cikin daliban da suka sami zuwa
Malaysia, amma ya yi iyakacin bincike ya rasa
lambarta ta nan. Allah cikin ikonSa sai ya ji na
kira shi kuma har na ambata masa ina tare da ita
anan.
Da farko ya tsorata yana tunanin ni mijinta ne, ko
kuma saurayinta na shaida masa ni malaminta
ne,
kuma yayanta, dan uwanta a musulunci, me
niyyar taimakonta ta fita daga kunci. Ya roke ni
alfarma da yawa wasu na masa alkawari zan iya,
wasu ban yi masa alkawarin zan yi ba. Wani
abun kuma na ce kada ya yi garaje, ya yi addu'a,
Allah Zai iya mana.
Na ce ba zan ba shi lambarta ba har sai ta yi min
izinin yin hakan sannan ba zan hada su a waya
su
yi magana ba har sai ta yarda da kanta. Alfarma
daya na roke shi ya dinga hada ta da *ya*yanta
a waya suna gaisawa ba sai ya ji muryarta ba.
Nan da nan ya amince min da haka, don ya yi
nadama yana tsakiyar yin dana sanin abubuwan
da ya yi mata a baya.
Faduwa ta ce ''Ina matar da ya aura Zulayha
Senegal?
Abdul-Sabur ya ce ''Ban tambaye shi wannan ba,
don ba layina ba ne. Fatana kawai ta ji muryar
*ya*yanta don ta sami nutsuwa. Je ki kiji ko ta
gama wayar ki dauko min wayata idan tana son
lambar ta dauka ta saka a wayarta ta dinga kira
suna gaisawa. Idan ta ki karbar lambar kada ki
dame ta ki kyale ta kawai. Don ba lambar da ta
ba ni ba ce wannan. Ina jin lambar mamar Abdul-
Sasi ce, don shi ya ba ni lambar ya ce in kira za
a ba ni yaran suna Gombe.
Faduwa ta tashi ta shiga dakin Umaimah akan
gado ta iske ta tayi sharkaf da hawaye, tana ta
hira da yaranta a waya. Kukan ya yi kama da
kukan farin ciki don tana kuka tana dariya. Babu
abin da ta ke
ambata sai sunan Bilal da Babangida.
''Ka sanni kuwa Bilal? Ni ce mama da ka santa a
da can. Shi kuma yana ta tsalle yana mata
gwaranci.
Babangida ne bai mance da ita ba, sunanta yake
kira, ''Aunty Umaimah yaushe za ki dawo? Jiya
mun ga hotonki, Bilal bai manta ki ba sai ya ce
ga anti.
Umaimah ta dafe kai hawaye ya kasa kafewa
daga idanunta. Fadwa ta dafa kafadarta, ta ce,
''Ya kamata ace a yau kin yi sallama da kuka,
kusan duk wadanda kika rasa a baya sun dawo.
Ki godewa Allah
Umaimah tunda Allah Ya sa *ya*yanki suna raye
suna cikin koshin lafiya.
Umaimah ta katse waya ta rungume Faduwa tana
kuka, ta ce, ''Anti Faduwa na ji muryar
Babangida, na ji muryar Bilal ya fara magana bai
manta ni ba.
Faduwa ta ce, ''To Alhamdu lillah, ai shi ke nan
tunda kinji lafiyarsu ki daina kuka. Ki dauki
lambarsu ki saka a wayarki koda yaushe sai ki
dinga kira kuna gaisawa. Tunda an ce suna
Gombe ba lambar Abdul-Basi ba ce.
Umaimah ta dauki wayar Abdul-Sabur ta duba
lambar da ta yi magana yanzu an rubuta Gombe,
amma ba lambar Abdul-Basi ba ce, sai ta ji sanyi
a ranta ta dauko wayarta ta dauki lambar ta saka
a
wayarta. Ta mikawa Faduwa wayar Abdul-Sabur
ta sharce hawaye ta ce, ''Na gode ki ce ina masa
godiya shi ma.
Faduwa ta yi dariyar jin dadi, ta ce, ''Fito mu je
falo ki yi masa godiya ya ji da kunnensa.
Umaimah ta yi murmushi kadan ta girgiza kai
alamar a'a, ta koma ta kwanta akan gado. Ta
sake matso lambar *ya*yanta, Babangida ya
dauka.
Ya ce, ''Anti Umaimah yanzu muke cewa Hajiya
ta saka kudi a wayar mu kirawo ki.
Sai aka hau kokawa shi da Bilal shi ma yana so
ya karbi waya ya yi magana da mahaifiyarsa.
Da da uwa sai Allah, zai yiwu bai tuna ta ba
saboda yana yaro sosai suka rabu sai dai ana
yawan nuna masa ita a hoto amma wannan
soyayyar da Allah (S.W.T) Ya saka a zuciyar uwa
da danta tana nan.
Shiyasa yana jin muryarta ya ji yana sonta, yana
jin dadin hira da ita.
Umaimah ta ce, ''Babangida kai fa yaya ne, ba
wa kaninka wayar mu gaisa, kada ya yi kuka.
Sannan ya ba shi wayar, tana jin muryarsa yana
kiran Antina, sai ta ji hawayen dadi ya surnano
mata.
Faduwa ta dade a tsaye a kanta tana kallonta
yayin da tausayinsu ya rufe ta babu abin da ta
tuna sai soyayyar da mahaifiyarta ta nuna mata a
lokacin tana raye, ta tuna dan uwanta Ibrahim.
Hawaye ne
ita ma ya surnano mata ta yi sauri ta fice daga
dakin tana mai gaggawar gogewa don kada
Abdu-Sabur ya gane ita ma ta yi kuka.
Ta mikawa Abdul-Sabur wayarsa, sannan ya
tashi suka dunguma suka fito daga gidan.
Labarin abin da ya faru a daki ta ke ba shi gami
da isar da sakon da Umaimah ta bata zuwa gare
shi na godiya.
Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya ji dadi da jin
sakon Umaimah, hankalinsa ya kwanta, da ya ga
na Umaimah ya kwanta. Sun dade a tsaye a
farfajiyar gidan suna ta
tattaunawa game da matsalolin Umaimah,
sannan daga karshe suka yi sallama ya nufi
hanyar
gidansa, Faduwa tai sama ita ma ta shiga
gidanta.
Yayin da Umaimah ta dade tana waya da
*ya*yanta har sai da katinta ya kare. Aiki ya
sami Umaimah ta yi firgigit ta tashi ta shiga
wanka, ta saka doguwar riga abaya ta fita neman
katin waya, don hirar ba ta ishe ta da su ba.
Umaimah ta sami abun yi ita kadai a cikin gida,
koda yaushe tana waya da jama'ar da ta ke da
lambobinsu a wayarta, musamman ma *ya*yanta
na Gombe. Duk wannan hirar da ta ke yi da su
Babangida bata taba jin muryar wani babba da
daga cikin *yan gidan. Ita dai in ta buga
Babangida ne yake dauka, haka idan ba ya kusa
sai ta ji ba a
dauka ba idan aka jima sai ta sake kira, in yana
kusa sai ya dauka su yi hira ya kira mata Bilal
shi ma ya zo ya yi mata gwarancinsa.
Labaru kala-kala Babangida yake yi mata, wani
abun idan ya fada sai tayi mamaki, musamman
da
ta ji radau yana bata labarin Zulayha Senegal
matar Babansa irin fadan da suka yi ita da
Babansa, kuma daga karshe suka rabu ya dawo
da su Gombe shi yana Kaduna har yanzu.
Ta tambaye shi an taba kai su Dugge?
Ya ce, ba a taba kai su ba, su ma *yan Dugge ba
sa zuwa. Sai ta ji ba ta ji dadi ba da aka ki
nunawa
*ya*yanta danginta. Idan suna hira sai ta ji
tausayinsu har wani lokaci su sakata kuka, ko su
saka ta dariya har da kyakayatawa.
Allah Sarki, haka rayuwa ta ke.
********************
A satin ne Hanif ya shaida mata zai je gida
Najeriya hutu, ta rokeshi da kafin ya wuce ya zo
ya karbi sako ya kai mata rugarsu Dugge. Ya yi
mata alkawari zai zo, amma ita fargaba ta ke,
kada ya manta ya wuce bai zo ba, don haka
wayar safe daban, ta rana daban ta ke yi masa
tana sake nanata masa.
Duk da haka ta ji ta matsu ta damkawa Hanif
sakonnin nan da ta shiryawa *yan gidansu. Ta
zuba kayanta kala biyu a jaka. Ta yi wanka tsaf
ta ci ado da wata riga da siket blue gyalenta baki
da
takalmi baki ta rataya jakarta baka a kafadarta,
ta rufo gidanta ta fito. A gidan Faduwa ta tsaya
ta iske
gidan a datse daga dukkan alamu ta fita unguwa,
makaranta ko asibitin da ta fara cuku-cukun
neman aiki, ko kuwa gidan kawayenta don tana
da kawaye rututu iri-iri mata da maza.
Ta dade a tsaye a bakin kofar ta rasa wanda zata
ba wa sako a fadawa Faduwa cewar zata yi
tafiya zuwa garin 'Mantin' makarantar su Hanif
wato Legenda zata kwana daya ko biyu a can.
Sai can ta tuna ashe fa yanzu tana da waya babu
sakon da waya ba ta isarwa cikin sauki da
gaggawa. Nan da nan ta zaro wayarta ta nemo
sunan Faduwa ta kira ta. Ta yi mamaki da ganin
kiran Umaimah, ta amsa cike da fara'a sannan
Umaimah ta shaida mata ga ta a kofar gidanta,
amma ba ta nan daman sallama zata yi mata
zata Mantin makarantar Legenda wajen Hanif da
sauran kawayenta mata *yan Gombe.
Faduwa ta yi farin ciki da jin haka, ta kuma yi
mata fatan Allah Ya kiyaye hanya. Daga karshe ta
tambaye ta, ''Kin yiwa Abdul-Sabur sallama
kuwa?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ai ba ni da
lambarsa.
Faduwa ta ce, ''Amma ai yana gida ki shiga ki yi
masa sallama.
Umamai ta ce, ''Ban san ta inda zan bi in je
gidansa ba, kasancewar ban taba hawa block
dinsu ba, sai dai ki turomin da lambarsa.
Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kuna gida iri daya ki
ce ba ki san yadda za ki hau samansa ba? Ai
kina ma
yin kokari a hakan kin fi da. To bari na turo miki
lambarsa.
Umaimah ta sauka kasa tana daf da zata fita
daga get sakon Faduwa ya shigo wayarta. Tana
dubawa ta ga lambar Abdul-Sabur ce. Nan da
nan ta kira duk da sai da ta ji faduwar gaba kafin
ya dauka. Ba ta sani ba ko ba ya so ta kira shi
shiyasa bai karbi lambarta ba bai taba kiranta ba.
Ina fatan nacika Alkawari.?
Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu da rai da
lafiya...
MAKWABTAKA 32
yana daga wayar ta ya gyara zama ya ce, ''da
wa nake magana ne?
Wannan karon mamaki ne ya kama ta, don a
zatonta yana da lambarta kira ne bai taba yi ba.
Ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Sunana Umaimah Bello
Gombe.
Sai ya bude ido da baki don mamaki, amma bai
fallasa mamakinsa a fili ba.
Ya ce, ''Barkanki da safiya Umaimah. Kina lafiya?
Ta amsa, ''Lafiya kalau. Yayin da ta fara
gaggauta fadar sakon da zata fada. ''Zan je
Mantin makarantar Legenda wajen Hanif, zai je
Nigeria a cikin satin nan, zan ba shi sako ya kai
Dugge shine zan kai masa. Zan kwana daya ko
biyu a can saboda akwai kawayena su Zainab a
makarantar, sai in zauna a wajensu. Shi ne na
kira in yi maka sallama, na yiwa Anti Faduwa ma,
ita ce ta turo min lambarka.
Sai ya yi mamaki da wannan sauyi, ya kuma ji
dadi sosai.
Ya yi murmushin dadi ya ce, ''Lallai kin yi tunani,
kuma kin yi dubara kin kuma kyauta. Yanzu har
kin shirya kin sauko ne?
Kina waje ko?
Don na ji karar motoci.
Ta ce, ''Na fita, har na kusa isa bakin titi.
Ya ce, kin san inda za ki je ki hau mota zuwa
Mantin daga can ki hau mota zuwa Legenda?
Ta ce, ''A'a, yanzu in mun gama wayar nan zan
kira Hanif ya kwatanta min inda zan je da inda
zan jira idan na isa Legenda ya je ya dauke ni.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ki tsallaka gada sai ki jira ni
zan zo in kai ki har Mantin.
Ta ce, ''A'a, ka bar shi kawai, zan iya zuwa da
kaina,,,
Ba ta rufe bakinta ba ya kashe waya, sai ta ji
kamar ta fasa zuwa Legenda saboda Abdul-Sabur
ya ce zai bi ta. Ba ta so a dinga ganinta da shi,
saboda ba al'adarmu ba ce, a yawaita ganin
mace da namiji
tare alhali ba mijinta ba ne kuma ba dan uwanta
ba,
ai sai ayi musu wata fassarar.
Nan da nan ta ji hankalinta ya tashi, ta fara
tafiya cikin sauri, burinta ta yi sauri ta bace masa
ya zo ya rasa ta. Ta tuna ai yana da lambar
wayarta zai kira ta kuma ba dadi ta kashe
wayarta bayan yanzu suka gama yin waya. Tana
matukar ganin girmansa yanzu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login