Showing 81001 words to 84000 words out of 130520 words

Chapter 28 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8017

hadu sun dahu luguf
sai
kamshi suje yi.
Dogon kofi (Jug) daya, kunun aya ne sannan daya
kofin markadaddiyar kwakwa ce da abarba aka
tace aka zuba (coconut da pineaple) aka zuba
dan sukari a ciki. Tabbas Yau Umamaimah ta yi
musu komai, saboda ta dafa musu abun da suke
so. Sai ga Faduwa da ta ke son alala kawai ta
buge da cin shinkafa da danwake. Haka Abdul-
Sabur da yake son dan wake ya hau cin alala da
shinkafa gami da farfesu da dankalin da aka
jejjefa a cikin romo. Suka ci suka sha gami da
yiwa Umaimah doguwar godiya da jinjina bisa iya
dafa zazzakan girki. To meye matsalar da zaisa
abinci ya ki yin dadi?
Da suka gama ci Umaimah ta kwashe kwanuka
ta kai kicin ta wanke, sannan ta dawo suka
matsar da tebur din da yake tsakiya (center table)
suka zazzauna akan kafet suka buda kur'anai.
Izufi ashirin-ashirin suka rarraba, Umaimah zata
fara daga kasa, Faduwa daga sama, yayin da
Abdul-Sabur ya dauki tsakiya.
Faduwa ta yi hamma gami da yin doguwar mika
ta dubi Abdul-Sabur da Umaimah, ta ce, ''Anya
kuwa ba zamu bar saukar nan ba sai gobe da
safe ba, da na ci abincin nan sai jikina ya mutu
bacci kawai nake ji.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ba ki isa ba, sai kin yi
karatunan, kina gyangyadi ruwan sanyi zan watsa
miki. Kina so ki bari shaidan ya yi miki huduba,
idan abun Allah ne sai ki dinga rauni, amma da
party ne ko za a kwana ba kya gajiya.
Faduwa ta dauki dogon salati, ta ce, ''Har haka
na zama? Irin wannan shaidar zaka yi min?
A'uzubillahi minal shaidanir rajim, mu fara karatu
na kori shaidan. Umaimah ta sha tuntsira dariya,
suka yi salati goma gafiyayyen halitta (S.A.W)
sannan suka fara karatu babu wanda ya sake yin
magana a cikinsu . Ayar Allah kawai suke ta
ragargazowa. Ba su sauke ba har sai da suka kai
asuba.
Allah Ya amsa mana addu'o'inmu, Ya biya mana
bukatunmu na alkhairi, amin!!
***************
Ranar lahadi da yamma Abdul-Sabur Faduwa da
Umaimah suna zaune a wajen shakatawa na
jenting high land, wani gari ne mai nisa 51km
daga KL. Wajen yin wasanni ne iri-iri da
shakatawa, wajen akan tsauni yake babu abinda
kake hangowa daga sama sai fulawowi da ruwan
teku.
Ga liluka wasu akan tsauni wasu a can kasa.
Yawancin mutanen da suka fi yawa a wajen
turawa ne masu zuwa kasar musamman dan
shakatawa.
Su Umaimah na zaune akan kujeru da tebur
shake da kayan ciye-ciye kamar; gasassun kaji,
meatpie,
cake, gogguru, lemuka kala-kala. Tun daga karin
kumallo na safe babu wanda ya kara cin abinci a
cikinsu, saboda haka yunwa ce take ta
addabarsu,
suna zuwa sai suka hau yin maganinta. Abdul-
Sabur ba ya kiwar kashe kudi komai ya tashi
saya sai ya jifgo da yawa, yadda zai ishe su, su
ci har su bari.
Don haka har nauyi da kunyarsa suke ji wani
lokaci su yi kokarin fitar da kudi za su biya sai
ya hana su.
Ransa yana baci da duk wacce ta aikata hakan
daga cikinsu, don haka ma suka daina damuwa
da sai sun dauko jakar kudi don babu abin da zai
bari su saya da kansu. Sannan ya gargade su da
su daina yi masa godiya duk abin da ya yi musu
yana yi musu ne saboda Allah.
Wai! Wai! Wa ya ga garabasa?
Tabbas cikin *yan watannin nan Umaimah da
Faduwa sun yi kiba sun kara jawur saboda ciye-
ciye da kwanciyar hankalin da suka samu.
Abdul-Sabur din ma a dalilinsu yana samu ya ci
abinci sosai sabanin da da yake ci shi kadai ba
ya iya ci da
yawa.
Mutum rahma ne inji masu iya magana, hira suke
yi sosai ta shakuwa. Umaimah ta dubi Faduwa ta
juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Wani lokaci ma
sai in ji farin ciki ya yi min yawa, saboda na
duba, na hanga a halin yanzu
babu abin da yake damuna na kuncin rayuwa ko
akwai abin da na rasa ma kadan ne, shima ban
daukesa a matsayin damuwa ba. Allah Shine abin
godiya, shi kadai Ya cancanci a godewa a koda
yaushe.
KU DAN HUTA ANAN SAI ZUWA GOBE DA YARDAR
ALLAH A KWAI CI GABA
INA GAYYATAR KU XUWA SHAFINA NA FACEBOOK
DOMIN SADA XUMUN TA DA FADAKAR DA JUNA
MAKWABTAKA 35
Faduwa da Abdul-Sabur suka yi murmushi,
Faduwa ta ce, ''Gaskiya ne kanwata babu abin da
yake damuna ni ma yanzu a duniya. Iyayenmu da
suka
rigamu gidan gaskiya muna yi musu addu'a Allah
Ya kai rahma kabarinsu, amma na cire damuwa
da bakin ciki daga cikin zuciyata.
Son Sagir da talauci da yake addabata a baya
sun gushe. Saura watanni uku in kammala
karatuna, a take ina da upper ta aiki. Albashi mai
tsoka, gida da motar hawa duk
kyauta za a ba ni. Miji kuwa na hakura da
nemansa, idan Allah Ya yi zan yi aure, in lokaci
ya yi zan yi,
idan kuwa ba ni da rabon aure a duniya ina
addu'a Allah Ya tayani tsare kaina da kama
mutuncina har
karshen rayuwa.
Tausayinta ya rufe Abdul-Sabur da Umaimah. Ya
girgiza kai ya ce, ''Ki ma daina irin wannan
magana za ki yi aure insha Allah ki hayayyafa,
fatana ace kafin ma ki karbi takardar aikin naki a
hannu ki
sami mijinki a hannu kin ga dai-dai ke nan.
Faduwa da Umaimah suka amsa da, ''Amin, amin
Ya rabbi.
Abdul-sabur ya gyara zama ya yi murmushi ya
dubi Faduwa, ya ce, ''Ai ni da ina so ki ba ni
adireshin Sagir idan na je Cairo in neme shi mu
zauna inji yadda za'a yi a yi komai in dai zai
yiwu.
Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ka ji shi da tsokana
ko,
shekaru nawa da rabuwarmu ya taba nemana? Ai
in mahaifiyarsa na raye auren nan da kyar zai
yuwu, sai dai ikon Allah. Nasan ma ya yi aurensa
ya manta da ni. Don ni ma gaskiya da kyar zan
iya zama da Sagir yanzu, saboda na sake
wayewa nasan daraja da martabar kaina yanzu,
ba wai na fi karfinsa ba ne, a'a na ga yadda ake
kula da
tarairayar mace, bana tunanin Sagir zai iya yi min
irin wannan tarairayar dana gani.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A ina
kika ga tarairayar mace? Ai matan Malaysia su
suke fita su nemo abincinsu, yaransu da
manyansu kowa aiki yake yi dan ya ciyar da
kansa. Kin manta sai kiga mata da miji da
*ya*yansu sun je cin abinci restaurant kowa ya ci
ya biya nasa?
Faduwa ta ce, ''Na san da wannan amma ni
yanzu na ga inda namiji yake tarairayar matarsa,
sai ya
burge ni haka nake fata in auri irinsa.
Abdul-Sabur ya tabe baki ya ce, ''Ke kike leke-
lekenki har kika hango wannan daman shegen
yawo gare ki, gidajen kawaye iri-iri.
''Eh anyi yawon, Faduwa ta fada a fusace.
Umaimah ta kyalkyale da dariya, daman ita ba ta
da aiki sai dariya idan ta ji sun fara irin wannan
fadan nasu.
Abdul-Sabur ne ya katse dariyar da take
kyakyatawa, nan da nan dariyar ta koma fushi.
Da ya ce, ''Ke kuma Umaimah idan na je Nigeria
zan je har Kaduna mu zauna da Abdul-Basi idan
kuma Ilah kika fi so zan je Dugge mu gana. Kada
ki ji tsoron Matawata, zan yi mata nasiha ku
zauna lafiya.
Faduwa ta kyalkyale da dariya, har da tsugunawa
yayin da Umaimah ta ji wani kululun takaici ya
dira
a cikin zuciyarta, kuma ba ta sha'awar auren Ilah
ko kadan balle Abdul-Basi. Sabuwar rayuwa ce ta
bude don haka ba ta so ta waiwayi baya. Takaici
ne sabo fil ya ke dirgo mata a kahon zuci har ta
tuna dacin da suka dandana mata a rayuwarta ta
baya su dukka biyun.
Abdul-Sabur ma ya yi ta dariya daga karshe ya
shiga lallashinta yana ba ta hakuri, don yaga da
gaske take ta yi fushi, har ta daina cin abincin.
Dariyar da Faduwa ta ke kyakyata mata ita tafi
tunzura ta sai da Abdul-Sabur ya roki Faduwa ta
daina yi mata dariya kada ta sa ta kuka. Da
faduwa ta ki dainawa sai ya ce, ''Zan je Nigeria
in hada ki da
Alhajin Birni.
Nan dai aka rincabe da Faduwa da Abdul-Sabur
suka hau zolayar juna. Umaimah ta sami abin
dariya, tana ta kyakyatawa.
Abdul-Sabur ya saka hannu a aljihun wandonsa
ya ciro wasu kananan katina guda biyu masu
kyawu da kyalkyali kai ka ce da ruwan gwal aka
yi rubutun. Ya mikawa Faduwa daya, Umaimah
ma guda daya. Sai suka yi sauri suka karba suka
karanta, daga dukkan alamu ba su fahimci ko
katin mene ne ba. Ba na gayyatar aure ba ne,
haka ba na liyafa ba ne. Abin da za su iya gani
shi ne 'Graduation Ceremoney.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya gyada kai a lokacin
da ya ga duk sun zuba masa ido suna neman
karin bayani daga gare shi.
Ya ce ''Me ye ba ku gane ba? Katin gayyata ne
na bikin yaye mu mun gama karatun PhD za a
bamu satifiket. Lokaci ga shi nan an rubuta karfe
goma na safe, waje ga adireshin nan da sunan
hotel din 'J.W MaRRIOTT HOTEL'. A bukit Bing
Tang. Sai kun nuna katin nan za a barku ku
shiga, shi ne ya sa na
karbo muku. Ku yi kokari ku fito da wuri gobe,
tara da rabi ta yi muku a can. Tafiyarmu ba zata
zama
daya ba saboda ni a cikin makarant zan kwana,
tun karfe bakwai na safe zamu shiga taro
(meeting),
sannan a raba mana riguna da huluna (graduation
gown) a zuba mu a doguwar motar makaranta a
kawo mu can.
*Yan uwa da abokan arziki za su zo daga
kasashe daban-daban, ni dai ku ne *yan uwana
kuma dangina, in kuka makara ba ku zo ba
shikenan na zama ba ni da kowa, babu mai
daukana a hoto a lokacin da ake mika min
satifiket.
Faduwa da Umaimah suka zabura suka hada
baki, ''Ah haba zamu zo mana.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce, ''Tsokanarku
nake, na san zaku zo, ai na yarda da ku kannena.
Na so
ace Ummana Fuse ta zo itama, amma sai na
kyale ta ban gayyace ta ba saboda nisa, Malaysia
ta yiwa tsoho nisa tun daga Ghana zuwa
Malaysia, zata sha wahalar zuwa. Amma kanwata
Kausar da maigidanta sun ce min za su zo ban
dai tabbatar da zuwan nasu ba, don nasan
shiriritarsu. Jiya dai da
muka yi waya suna London sun ce min za su
taho nasan ko za su iso sai yau da tsakar dare.
Na kira
su dazu na ji wayarsu a kashe, ban sani ba ko
suna hanya in sun iso na san za su kira ni, ga dai
katinsu
a hannuna in sun zo in ba su su shiga.
Faduwa da Umaimah suka yiwa su Khausar fatan
Allah Ya kawo su lafiya. Sai da suka yi sallar
isha'i sannan suka sha hawan lilo da tsalle-tsalle,
sannan suka fara haramar tafiya.
A motar Umaimah aka zo ita ake tukawa. Abdul-
Sabur ya so ya karbi tukin saboda garin da nisa,
kuma ga dare ya yi, Umaimah ta ce ya bari zata
tuka, ya shiga gidan baya ya zauna Faduwa da
Umaimah a gaba suka tafi.
A 'Sabang Jaya' ya ce su sauke shi cikin
makarantarsu da suka sauke shi sai suka yi
masa sallama akan sai goben idan sun hadu a
can.
Umaimah ta fisgi mota sai unguwarsu wato
'MAHARJALELA' Allah Ya ba mu alheri!!
****************
Tsabagen kwalliya mai suna kwalliya an caba ta a
wannan rana da kaya na karya, sai a wajen ma
su
Umaimah suka taba ganin wata suturar. Gwala-
gwalai da lu'u-lu'u a wuyan wasu matan, abun
sai a rike baki. Hausawa, Inyamurai, Yarbawa,
Larabawa da Turawa duk sun hallara a wannan
katafaren
hotel da ake ji da shi a Malaysia, wato 'J.W
Marriott',
kowa sai ya nuna kati za'a bar shi ya shiga, yana
shiga sai ya sami waje ya zauna a cikin katafaren
dakin taron da yake cikin hotel din. Babu abin da
yake tashi a wajen sai sautin kida a hankali gami
da sanyin A.C da kamshi na alfarma. Kowanne
tubur an zagaye da kujeru hudu, abubuwan sha
ne kala-
kala a gaban kowa.
Faduwa, Umaimah da wasu Turawan Spain mata
da miji ne suka zauna a teburi daya. Kan ka ce
kwabo Faduwa ta saba da su suna ta hira, suka
shaida musu su ma sun zo jiya daga Spain wajen
dan
uwansu. Umaimah da Faduwa suka shaida musu
su a nan kasar suke zaune suna karatu, amma
asalinsu *yan Africa ne suma dan uwansu suka
zowa.
Su umaimah sun yi kwalliya, amma ba su zaci irin
wannan caba adon za a yi ba, yadda suke hango
dakakkun leshina da dakakkun riguna (English
wears) a jikin mata sai suka raina shigarsu. Sun
saka wando jeans, da riga mai dogon hannu,
gami da kananan hijabai da takalma masu tsini
da jakunkuna ratayawa masu tsada. Hannayensu
a jere da zobuna English gold. To me ye laifin
shigarsu?
Ba ta yi muni ba, kuma sun fi wasu kyau duk da
su ma da yawa sun fi su.
Har yanzu dai ana jiran isowar manyan kasar da
manyan furofososhin makarantar da kuma dalibai
masu fita wato su Abdul-Sabur.
Har yanzu dai shigowa ake ta yi hall dai sai
hadidiyar mutane yake yi, kowa ya shigo ba ya
rasa wajen zama, saboda girman wajen da kujeru
rututu.
Karfe goma saura minti goma sha biyar aka
sanar da shigowar dalibai da malamansu. A bun
gwanin ban sha'awa sai ga su Abdul-Sabur nan a
jere a layi suna shigowa sun yi anko da riguna da
huluna iri daya (Graduation gown).
Abdul-Sabur yana daga baya-baya kasancewar
mata ne gajeru daga gaba, shi da yake dogo ne
sosai a mazan ma yana daga kusan karshe.
Umaimah da Faduwa sai zare ido suke suna
hange ba su ga nasu ba alhali yawanci kowa ya
ga dan
uwansa yana murna, yana dauka a hotuna.
Can suka hango gogan nasu ya zuba kyau kuwa
a cikin kayan fiye da fararen fatar ma. Nan da
nan kowaccensu ta tashi da kyamararta a hannu
suna daukarsa a lokacin da yake tafiya a cikin
ayari. A lokacin da suke daukarsa a hotuna sun
fahimci wata mata da mijinta su ma sun ta so da
sauri suna daukarsa a hoto. Ko tantama babu
kanwarsa ce Kausar tare da mijinta, sai suka hau
kallon-kallo tsakanin su Kausar da su Umaimah.
Da yake Umaimah ta taba ganin Kausar a Makka
sai nan da nan ta shaida ta. Ba su yiwa juna
magana ba har kowa ya koma mazauninsa ya
zauna, yayin da su Abdul-Sabur suka isa
bangaren da aka tanadar
musu na musamman suka zazzauna daga gaba.
Bayan kowa ya zauna ne aka fara bayanai cikin
harshen Nasara (turanci). Daga karshe aka fara
kiran sunayen dalibai guda goma da suka fi kowa
cin jarabawa, ana ba su satifiket dinsu a hannu.
Ihu, tafi da murna marar misaltuwa *yan uwan
wadannan bayin Allah suke yi. Allah cikin ikonSa
kwatsam aka kira sunan Abdul-Sabur shi ne na
hudu, nan da nan Faduwa da Umaimah, Kausar
da mijinta suka dau murna da tafi
raf-raf-raf, hotuna kuwa sun kyasa masa ba
adadi.
Sarkin rawar kai har kan stage ta haye tana
daukarsa a hoto, kai ka ce ita ce zata mika masa
satifiket din, wato Faduwa.
Banda dariyar farin ciki sai dagawa jama'a hannu
da Abdul-Sabur yake yi. Dalibai suna da yawa
don haka an kai karfe daya da rabi ana abu daya.
Abinci kala-kala masu dadin gaske ake ta jerewa
akan teburan kowa. Suka ci suka sha suka gyatse
ba tare da ko sisinsu ba.
Da aka gama rufe taro da jawabi sai taro ya fara
watsewa. A lokacin ne su Abdul-Sabur suka sami
damar tunkaro inda *yan uwansu suke dauke da
kwalinsu a hannu. Ana ta rungumar juna ana
murna. .
Allahu Akbar, sai ya karaso inda su Umaimah
suke cike da murna, Kausar da mijinta suka taho
suma aka taru waje daya. Bai ankara ba
yana juyawa sai ga Uncle Hamza a bayansa shi
da babban yaron da ya ke mai aiki a shago na
London wato Emeka. Hade da El-Abdullahi dan
Indonosia ne daya daga cikin shugaban kamfanin
da suke saro kaya a wajensu, takanas ya zo taya
shi murna.
Nan dai murna ta hautsine yayin da Abdul-Sabur
ya shiga gabatar da kowa da kowa. Yawanci sun
san
junansu, Umaimah da Faduwa ne basu sani ba.
Ya gabatar da su matsayin MAKWABTANsa,
kuma
aminansa, sannan ya juya ya gabatar da *yan
uwansa ga su Umaimah. Aka gaggaisa aka dinga
daukar hotuna daban-daban.
Faduwa da Umaimah suka yi musu bankwana
suka kama hanyar gida yayin da Abdul-Sabur ya
tafi ya
raka su Uncle Hamza da tawagarsa masaukinsu.
Kausar da mijinta kuwa su ma hotel dinsu ba shi
da nisa da kafa ma suka karasa anan cikin Bukit
Bing Tang.
Abdul-Sabur ya yiwa su Kausar alkawarin daga
ya raka su Uncle Hamza zai zo hotel dinsu ya
samesu.
Faduwa ce ke tuka motarta Umaimah na zaune a
gefenta babu abin da suke sai hirar kayan jikin
Kausar, leshine tsadadden gaske kuma ya yi
kyau,
ruwan dorawa da fulawar ruwan bula (blue),
dinkin riga da siket matsattse ga lu'u-lu'u yana
ta
kyalli a wuyanta. Shaddar da ke jikin mijinta ta
hadu sosai fara sol. Tabbas kudi ya zauna musu
ko
ba'a fada ba, Allah Ya yarda da su Ya amince su
yi arziki.
Haka ai rayuwa ta ke, babu abin da yake
dauwamamme, talauci ko wadata.
Sun jinjina tsohon nan da ya yi kara ya yi
zumunci ya zo, wato Uncle Hamza, shima ya sha
babbar riga
da hula da wani hadadden filted, bai bar
al'adarsa ba bawan Allah.
'Allah Ya azurtamu duniya da lahira da alfarmar
Annabinmu (S.A.W). In ji Faduwa yayin da
Umaimah ta cafke salatin suka dire tare.
Taro ya yi taro, haduwa takai haduwa yadda baki
ba zai iya lissafa wasu abubuwan ba sai dai ayi
kurum!
Farin ciki da nishadi babu irin wanda ba su shaka
ba a yau. Haka babu wani abun dadi da ba
su ci ba a yau. Don haka sai hamdala ga uwa
uba wanda suka je dominsa ya burge, ya fito da
sakamako mafi daraja.
Da yamma Abdul-Sabur ya iso gidan Faduwa shi
da Kausar suka ci sa'ar iske Umaimah a gidan,
don haka aka hadu a kasha hira. Babu abin da
Kausar ke yi sai lura da Yayanta da *yan matan
nan ta ke yi
idan suna hira, tana so ta tantance wace ce
budurwar a ciki. Don ta kula Yayanta yana ji da
su alhali bata taba ganin in da ya saba da mata
haka ba, har yake shiga cikinsu yana musu hira
haka.
Ta kasa tantancewa wani sa'in sai ta ga kamar
yana shisshigewa Umaimah idan aka jima sai ta
ga ya fi kula Faduwa. Ta shiga gaggawar su kebe
ita da shi ta jero masa tambayoyi game da
matan nan.
Sai da aka kira sallar magruba suka watse,
Umaimah ta koma gidanta, Abdul-Sabur da
Kausar suka tafi gidansa. Da ya bude mata kofar
gidan ta shiga, sai ya sauko ya tafi masallaci.
Daga masallaci ya je ya dauko mijin kanwarsa
daga hotel ya ce su kauro gidansa dakuna biyu
ne. Kafin su iso Umaimah da Faduwa duk sun
kawowa Kausar abinci kala-kala.
Da Abdul-Sabur ya dawo Kausar ta nuna masa
abin arzikin da kawayensa suka kawo mata, ya ji
dadi kwarai. Sai suka jere akan dinnin table suka
zauna cin dadadan abinci, aka bude shafin hira.
Kausar ta dubi Yayanta tayi dariya ta ce, 'To wai
a cikinsu wacece Yayar tawa don nasan dai akwai
guda daya da aka yarda da ita.
Abbdul-Sabur ya harareta ya bata rai, don baya
so ta dinga masa shisshigi game da maganar
aure.
A'a ka ga ka daina hararar min mata, ai gaskiya
ne,
ka fada mana kawai, in ita kanwarka ce ba zaka
bata amsa ba, ni ai abokinka, ne, kuma yayanka
idan aka bi ta shekaru. Malam ka fada mana
kawai.
Inji mijin Kausar.
MAKWABTAKA 36
Suka kyalkyale da dariya su duka ukun. Abdul ya
kai lomar abinci, ya ce, ''Idan na fada muku wani
abu za ku yarda?
Babu guda daya a cikinsu da muke soyayya. Sun
dauke ni tamkar yayansu, na dauke su tamkar
kannena na jini. Su duka rayuwarsu abar tausayi
ce, marayu ne kuma ba su da miji a kasar da ba
su da dangi. Ina jin tausayinsu matuka shi yasa
na yi kokari mu hada kai mu zauna lafiya. Kuma
kun san wani abin mamaki?
Gaba dayansu *yan asalin Nigeria ne har Faduwa
Balarabiya, mahaifinta mutumin Sokoto ne,
Umaimah kuma bafilatanar Gombe ce, *yar asalin
wani kauye Dugge.
Kausar ta yi dariya ta gyada kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login