Showing 96001 words to 99000 words out of 130520 words
Chapter 33 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
da namiji wadanda
bata taba zaton
zata gansu a wannan waje ba kuma bata addu'a
ta gansu din, dan basu rufa mata asiri ba a
lokacin da take neman sutura, suma a hotuna
suke daukarta
basu daina ba har ta koma kujerarta ta zauna
suma sannan suka koma suka zazzauna. Sun ga
alamar ta razana da ganinsu kuma ba tayi farin
ciki da ganinsu ba saboda tana ganinsu yanayinta
ya canja, duk da kuka take yi daman amma tana
dariya a cikin kukan, ganinsu yasa ta fashe da
kukan takaici hade da fushi.
Babu abunda yake yi mata zillo a zuciyarta sai
sunayensu ta dinga fada tana maimaitawa.
''Abdul-Basi, Lamijo. Me ya kawo ku wajena?
Me yasa zaku zo inda na ke?
Me yasa zaku dawo cikin rayuwata, alhali rashin
ku ne ya sa na tarki tafiya na rabu na bar *yan
uwana da *ya*yana?
Sai abubuwan da suka yi mata a baya na rashin
kyautatawa suka yi ta dawo mata a jejjere,
hawaye ya gagara tsayawa daga idanunta.
Ana kiran dalibai suna tasowa a layi suna karbar
takardar sakamakonsu. Aisha Bingyal ma ta
karbo nata, dukkansu sun karba suna tsalle suna
murna saboda kowa yayi kokari dan babu wanda
bai fito da sakamako mai kyau ba daga cikin *yan
garinsu.
Sai dai Umaimah ce kadai baqa data sami 1st
slass a wannan shekarar a makarantarsu.
Tunda Umaimah ta ga Lamijo da Abdul-Basi bata
sake fahimtar abubuwan da ake cewa ba a wajen.
Hankalinta ya kada can yayi hanyar waje babu
abunda ta fi so irin tabar wajen kada ma su sake
haduwa. Ai kuwa babu damar fita dole sai
angama sannan kowa zai tashi, ta kagu ma a
gama dogayen jawaban nan da ake ta faman yi a
tashi. Ta kasa kurbar ko ruwa balle ta figi naman
kaji da abinci iri-iri da aka yi ta jerawa kowa a
gabansa. An ci, an sha, kamar yadda aka yi a na
su Abdul-Sabur.
Da aka kammala taro sai kowa ya tashi ya nufi
wajen *yan uwansa, tafiya Umaimah take tamkar
wacce kwai ya fashewa a ciki bata son ta karasa
wajen *yan uwanta, badan mutuncin Baban Hanif
ba da arcewa zata yi a neme ta a rasa sai dai su
hadu a filin jirgi ranar da zasu tafi.
Ta ci sa'a Faduwa ta zo ta figo hannunta daga
cikin yuyar mutanen da suka baibaye ta suna
tambayarta adireshinta da lambar wayarta. Ta
cika da mamakin dalilin da yasa mutane suke
tambayarta adireshi da lambar wayarta alhali duk
fararen fata ne turawa, Indiyawa da kuma *yan
Maley. Tabbas haka ake yi a turai wanda Allah
Ya bawa wata baiwa ta daukaka zasu dinga
tururuwar son yin mu'amala da shi. Abun
burgewa ne a gansu da shi sun yi hoto ko ya
rubuta sunansa a cikin wani abu nasu hankicin ko
dan littafi.
Da Faduwa ta figo hannun Umaimah bata dire ta
a ko ina ba sai tsakiyar *yan Nigeria a gaban
Hanif da Babansa, sai ta durkushe ta gaishe da
Baban Hanif.
Ya yi mata addu'a mai kyau ya yabe ta sosai
kuma ya jinjina mata ya ce ta burge shi yana
alfahari da
ita.
Lamijo ce a gefensa mowarsa kenan, da ita ya
zo. Sai kallon Umaimah take kasa-kasa amma
bata yi mata magana ba. Darajar mijinta ya sa
Umaimah ta ambaci sunanta sannan ta gaishe ta,
gami da tambayarta lafiyar Ummarta.
''Lafiya kalau''. Kawai Lamijo ke cewa.
Umaimah ta san dai ba dan ita Lamijo ta zo ba
saboda Hanif ta zo bata zaci zata ganta ba dan
tana yi mata kallo irin na takaici da bakin ciki.
Umaimah ta gaggauta barin wajen iyayen
kawayenta da wakilan gwamna. Zubewa a kasa
kawai take yi tana kwasar gaisuwa cikin ladabi da
biyayya.
Amsawa suke yi cikin kulawa da kaunarta game
da jero mata addu'oin alkhairi.
Daga karshe aka jeru aka dinga yin hotuna iri-iri
ita da su.
Abun mamaki sai ta nemi Abdul-Basi ta rasa a
wurin, bata san inda ya kutsa ba, haka bata damu
da ta gan shi ba daman.
Da suka fito daga ciki sai aka taru a waje daya
aka tsayar da shawarar kowa ya koma
masaukinsa sai bayan kwanaki uku za'a hadu a
'Royal Bingtang Hotel' da karfe goma na safe in
da makarantar su
Hanif wato 'Legenda' za su gudanar da nasu
bikin suma.
Faduwa an sami abunda ake so, dan ita babban
burinta shine ta ganta cikin *yan uwanta *yan
Nigeria ta shiga cikinsu tayi ta yaren Hausa suna
mamaki, sai ta hau basu labarin cewa itama *yar
Nigeria ce Babanta dan Sokoto ne. Ta dinga hira
da su kamar wacce ta shekara da saninsu, kowa
ya ji
yana sonta ya na so ya saba da ita har da
musayar lambar waya suka dinga yi. Umaimah ta
kagu su tafi ta san halin surutun Faduwa bata ki
a kwana ana yi ba, dakyar ta jawo ta suka tafi.
Umaimah ta bi Faduwa a motarta suka tafi dan
bada motarta ta zo ba a motocin makaranta aka
kawo
su, Faduwa tana tuki ta juya ta dubi Umaimah
wacce taga alamar damuwa a tattare da ita sai
ta zungureta ta tambayeta.
''Lafiya? Yau ranar farin cikinki, kowacce zata yi
fatan ta zama ke. Me yasa kika shiga damuwa?
Na
ga alamar bayan kukan murna kina cikin damuwa
kuma.
Umaimah ta sake barkewa da kuka, cikin
shesshekar kuka take magana.
Ta ce, ''Abdul-Basi da Lamijo na gani a wajen.
Shine na ji duk raina ya baci, tunanin abubuwan
da suka
yi min a baya ya dawo min.
Faduwa ta zabura ta ce, ''Haba dan Allah? Ai
abun farin ciki ne ke a wajenki, ba shikenan ba
sai ku shirya da aminiyarki, ta daina zarginki da
mijinta ba.
Ga mijinki uban danki shima ya dawo kuje a
daura muku sabon aure ku yi zamanku.
Umaimah ta girgiza kai ta ce ''Ba saboda ni
Lamijo ta zo ba kuma na san bata zaci zata
ganni ba anan, ko
ma dai menene ya kawo ta bata yi min magana
ba, albarkacin mijinta ni na gaishe ta.
Abdul-Basi kuwa zai yiwu shi dan ni ya zo amma
bana jin bayan gaisuwa zai ga fuskar yi min wata
maganar. Babu zancen kome a tsakaninmu, dan
ni ba zan iya zama
da shi ba kwata-kwata, shima haka yanzu zai
sha wahala idan ya ce zai zauna da ni. Saboda
zaman da muka yi ada zama ne da yake yi mana
mulki, son nuna isa, takama da son girma. Ya kira
mu kauyawa, ya daka mana tsawa, duk abunda
yake so dole shi za mu yi, ba mu da zabin
kanmu. Haka yayi mana ni da Nasiba musamman
ma ni da ba
zabinsa ba kuma ya ganni yarinta sosai.
Zamansa da Zulayha Senegal kuwa ita take
sonsa, take binsa, take kashe masa kudinta, daga
lokacin
da ta gama gulmar ta daina yi masa biyayyar,
bayan ta samu ta aure shi kenan, na san daga
lokacin
masifa ta kunnu. Ya fito mata da halinsa na
rashin mutunci itama daman ta fi shi iyawa suka
babe.
Dr. Faduwa ba zan iya auren kowa ba yanzu a
duniya in ba mai irin halin Abdul-Sabur ba.
Halayensa sune: Hakuri, kulawa, damuwa da
halin da mutum ya ke ciki, tattali, karamci,
kyauta, tausayi, nasihohi masu taushi, ga
lallausan lafazi, wasa da dariya, iya hira, amfani
da hankalinsa baya taba damunka idan kana cikin
fushi ya san yadda zai zauna da kai a duk
yanayin da kake ciki.
Faduwa ta dade tana kallonta sai ta kasa yin
magana, can tayi ajiyar zuciya.
Ta ce ''Ni yanzu ba gashi na hakura nayi aurena
ba tunda nasan ba zan same shi ba.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ce
''Amma kina son Sagir sosai, kuma a rashinsa ne
ma har
Abdul-Sabur ya burgeki. Ni kuwa bana son
Abdul-Basi tun farko ma, Abdul-Sabur na fara so
a duniya,
ban tantance ba har sai da na rasa shi, sannan
na tabbatar duk duniya babu mai yimin kulawar
da yake min alhali ada na tsane shi akan ya
damu da ni.
Faduwa ta ce, ''Gara ki auri wanda yake hannunki
Umaimah, kada ki yi biyu babu.
Umaimah ta yi *yar siririyar dariya ta ce, ''Anti
Faduwa, daman sauri ne aure?
Bana sauri ko yanzu da babu Abdul-Sabur babu
dalilinsa, na tabbatar na
rasa shi ba zan same shi ba, ba zan koma wajen
Abdul-basi ba dan bashi da kirki. Ya kore ni a
lokacin da nake tsananin son zama dashi, a
lokacin da babu in da zan zauna inji sanyi sai
gidansa. Sai yanzu da na zama mutum, nake da
yadda zan yi sannan zai dawo min.
Ba Abdul-Sabur nake jira ba amma ba zan auri
Abdul-Basi ba. Zan ci gaba da yin addu'a Allah
Ya turo min da miji na gari.
Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Allah Ya turo miki
Kamal kika ki shi, kullum ni da Sagir yake damu
ya ce yana ta kiranki bakya amsawa. Ashe
Umaimah ba za kiyiwa kanki fada ba ki auri dan
larabawa ba, ga kyau ga kudi. Zai kula da ke
sosai dan mazanmu suna da rikon aure.
Umaimah ta yi dan murmushi ta ce, "Yi hakuri
Antina, ba zan iya auren shi ba, kema kinsan
dalili.
Daidai lokacin Faduwa ta ja ta tsaya a kofar
gidan Umaimah ta ce, "Kin san nayi nauyi yanzu
bana yawo, saboda ke ne ma na fito yau. Ba zan
iya hawa sama ba yanzu, zan je gidan kawata in
jira direbana ya zo ya mayar da ni 'Putra Jaya'
dan ba zan iya dogon tuki ba.
Umaimah ta ce, ''Allah Ya sa ki haihu a cikin
satin nan kafin na tafi in ga babyn ki.
Faduwa tayi dariya ta ce, "Amin Umaimah, hakan
zai iya faruwa saboda watan haihuwana ya
kama.
Umaimah ta bude kofar mota ta fito, ta yi mata
godiya gami da yi mata fatan sauka lafiya.
Tunda Umaimah ta shiga gidanta bata sake
fitowa ba sai bayan kwanaki uku wato sai ranar
bikin yaye su Hanif, Umaimah ta shirya tsaf, ta
ce kwalliya ba ta kadan ba saboda ta ga yadda
ake tsala ado
idan za'aje bikin Graduation.
Tana Allah.. Allah yasa taga dan Aunty a wajen
ko xataji sanyi a xuciyar ta..
hmm.
To Alhamdulillah.
Allah yayi na cika alkawari.sai kuma gobe da
yardar Allah xaku jini da cigaban kayattaccen,
kasai taccen wannan littafin na Mashahuriyar
marubucia wato Jamila Umar Tanko..
Naku a kullun mai kaunar nishadin ku. Abbas
MAKWABTAKA 42
Umaimah ta shirya tsaf, ta ce kwalliya ba ta
kadan ba saboda ta ga yadda ake tsala ado idan
za'aje bikin Graduation.
Ta saka daya daga cikin tsala-tsalan shaddojinta
data dinko daga Dubai. Ta dauki wayarta da
mukullin motarta sai digital camera data rataya a
wuyanta, ta nufi 'Royal bingtang Hotel' a cikin
motarta, tana tafe tana sauraron wakarnan da
take so ta mutumin Ghana 'Akuri Afomsa' wacce
yake yi
cikin yaren 'Asanti, wacce Abdul-Sabur ya bata.
Babu abinda take tunawa sai Abdul-Sabur dinta
ta tuna ranar da ya kaita Mantin wakar suka yi ta
ji yana fassara mata. Ta ci karo da su Aysha
Bingyal a bakin Hotel din,
tana isowa kawayenta mata da maza suka yo
kanta caa! Su na ta yabawa da tsananin kyawun
da ta yi har suka ce basu gane ta ba da farko sai
da tayi magana suka gane. Anya kuwa wannan
kwalliya
da Umaimah ta yi ba kwalele take yiwa Abdul-
Basi ba?
OHO!
Wato a lokacin da ta nufo cikin Hotel din a cikin
motarta sai da kowa ya zuba mata ido yana
kallon
halittar Ubangiji, sai kowa ya kagu da ya tantance
ko wacece wannan, ashe Umaima Bello ce sai da
ta fito aka shaidata.
Umaimah ta dade a tsaye tana hira da kawayenta
sai daga baya ta gane ashe Abdul-Basi ne a
tsaye a
gefensu shi da abokinsa Tanimu Wada. To ai ba
dan ita su ka zo Malaysia ba saboda kanin
Tanimu
Wada suka zo wato Bashir Wada, ajinsu daya da
Hanif.
Tanimu ya karaso inda Umaimah take a tsaye ita
da kawayenta cike da fara'arsa, yayin da itama ta
juyo
ta kalleshi tayi murmushi sai suka gaisa.
"Shin ba ki gane mu ba ne?
Tanimu ya tambaye ta.
Sai ta cika da mamakin wannan tambaya tasa.
Itama ta tambaye shin kamar yaya?
"Naga da kika shigo kin kalle mu sanna kika
watsar.
Ta tabe baki ta kawar da kai dan taga alamar rai
yake so ya bata mata.
Ya nisa ya ce, "Ki zo ki gaishe shi mana.
Ta dube shi duba irin na takaici ta kasa bashi
amsa, har ya gaji da surutu ya yi mata sallama
ya koma in da ya fito. Yana ta mamaki a
zuciyarsa dan ya zaci Umaimar daya sani a da
ce, da take zuwa ta
durkushe a gaban abokan mijinta, ta kudindine a
cikin hijabi ta shige lungu, ko me zata mika musu
sai ta durkusa har kasa. Yanzu ya tantance ya
gane akwai banbanci, dan shima Abdul-Basin
daga dukkan alamu ya zaci irin ta da ce shiyasa
yake daddakewa. Sai da ta juya taga Tanimu ya
bace,
acan ta hango shi yana bawa Abdul-Basi labarin
abin da ya faru.
Tanimu ya ce da abokinsa Abdul-Basi "Umaimar
daka sani ada ba irin ta ba ce yanzu, akwai
bambanci sosai. In har kana tunanin Umaimah
zata zo ta gaishe ka yanzu to ba zata zo ba.
Tunda biko ka zo to ka zo mu je kayi *yar murya
ko Allah Zai sa ta amince maka dan na lura bata
marmarin son zama da kai kuma.
Abdul-Basi ya girgiza kai ya ce, "Haba nawa
Umaimah take da za'a ce ni zan je in gaishe ta.
Ai tana kallona bata zo ta gaishe ni ba tayaya ni
zan je wajenta?
Za ta kawo kanta ka kyale ta, guguwar digiri ne
yake kwasar ta sai ta sake ta sannan, kasan *yan
jami'a da ji da kai.
Tanimu ya ce "a'a abokina ka cire girman kai ka
zo mu gwada, ka san halin mace da jan aji balle
ace ita
aka yiwa laifi, kai ne fa me nema. Kai kake
tsananin son ta dawo, kai kake kasa bacci
dominta, kai kake
hana ni sakat da hirarta, gara ka zo mu je tunda
wuri.
Abdul-Basi ya ce ba zai je ba sai dai ta zo ta
gaishe shi.
Girman kai rawanin tsiya ne!
Su Umaimah ne suka fara shigowa ciki, suka
sami waje mai kyau suka zauna daga gaba dan
suga komai radau.
Su Abdul-Basi ma suka shigo amma daga baya
suka sami waje suka zauna suna hango su
Umaimah da kwayenta, da lama babu abin da ya
dameta, harkarta da kawayenta kadai take yi,
suna ta wasa da dariya suna ta daukar junansu a
hotuna.
Da su Hanif suka shigo, sai aka hau tafi ana ta
dasa musu hotuna kala-kala. Umaimah tabi Hanif
tana dauka a hoto har saida ya zauna sannan ta
dawo ta zauna itama. Babu abinda Lamijo da
Abdul-Basi suke yi sai mamakin Umaimah, suna
kallon irin wannan kyau da tayi, da wayewa.
Tabbas yanzu Umaimah tayi musu zarra tafi su
komai, dan haka ta girmi wulakancinsu.
Abunda ya fi tsayawa Lamijo a rai shine yadda
taga Umaimah a Malaysia har tukin mota, ko ma
dai menene a ransu basa gaban Umaimah ko
kallon inda suke bata yi ba bayan farin ciki bata
da wani
abun yi.
Taro yayi kyau, an rabawa su Hanif sakamakon
jarabawarsu a hannu, sannan aka yi ta dogayen
jawabi, aka ci, aka sha, sai aka watse. Sai kuma
gobe war haka wani sabon bikin za'a yi na
wadanda suka fita daga jami'ar 'Intii Nilai' su
kuma
a 'Radius International Hotel' za'ayi, tabbas gobe
za'a sake wata sabuwar haduwar.
Cancadi! Za'a kece raini da suturu da gwala-
gwalai.
Washe gari ma haka Umaimah Bello ta caba ado
kai kace tarwada ce wacce take sheki, santsi,
sulbi, yadda take karairaya idan tana takawa. Ta
zama tamkar tauraruwa mafi haske a cikin *yan
iwanta taurari wato 'Zahra'. To ko ita zata maye
sunan kawarta wato 'MATAWATA?
OHO!
Ta hadu da Abdul-Basi da Lamijo a sanda ta je
ta gaida Baban Hanif, basu yi mata magana ba
dan sunga haduwar data yi ta wuce tunaninsu, da
suka ganta sai suka kawar da kai gefe, sai ita ta
je gare
su ta duka ta gaishe su. Dan ta tuna kadan daga
cikin irin halayyar Abdul-Sabur, idan ka gan shi
ka
share sai kaga shi ya zo yayi maka sallaman
bawan Allah kenan me koyi da halin Manzon Allah
(S.A.W).
Ta gaggauta kaucewa daga bangarensu ta ta fi
wajen masu kaunarta. Aka gudanar da biki yadda
ya kamata kowa yana murna, da aka gama kowa
ya watse.
Daga nan ba'a sake yin bikin yaye dalibai ba sai
da aka shafe kwanaki biyar, baki suka dinga cika
dogayen motoci aka yi ta zagaye gari da su, suna
kallon wuraren shakatawa iri-iri.
Umaimah bata bi su ba saboda Lamijo da Abdul-
Basi, babu yadda kawarta bata yi da ita ba akan
ta zo su je su dinga raka su, ta ce ba zata je ba
a gida zata zauna. Bata fito daga gida ba sai a
ranar bikin yaye dalibai na jami'ar 'Subang Jaya'
shi kuma a Capitol Kaula Lumpur Hotel ake yi.
Me za'a fasa mutuwa ko tonar kabari?
Inji masu iya magana.
Ado ne dai Umaimah bata daina caba shi ba,
kuma a dole sai ta zuba
kyau, idan ta fito fili sai kowa ya kalle ta kuma
sai ta burge, suturu ne Allah Ya hore mata kala-
kala.
Saura makaranta daya ce ta rage basu yi ba, su
ba yanzu zasu yi ba saura wata guda, dan haka
aka
bawa dalibai hakuri dan ba zai yiwu a jira su ba
saboda ba dole bane yin bikin. Abu mai
muhimmanci dai shine karbar sakamako kuma
za'a kawo musu har gida Nigeria idan ya
kammala.
Daliban makarantar basu ji dadi ba dai amma
dole tasa suka hakura suka tarkato dan a taho
gaba daya a tare. Dole ne a tafi sabida viser sati
bibbiyu ce kacal aka bawa su Baban Hanif.
****
gobe su Umaimah zasu tafi, tunda sanyin safiya
ta dinga bin duk jama'ar data sani tana yi musu
sallama, daga nan ta wuce gidan Faduwa a cikin
motarta a inda zata yi mata sallama sannan
kuma za'a sayi motarta, wata kawar Faduwa mai
suna Salma ita ma *yar Egypt ce tana so zata
saya. Bayan da aka gama cinikin mota, salma ta
biya ta kudinta cif a hannu, da Dallar ta biya ta
kamar yadda Umamai ta bukata dan ta canja
gaba daya kudinta ya zama Dallar, saboda ta fi
saukin canzuwa a nan gida Najeriya.
Umaimah tana ji tana gani Salma ta
haye motarta ta tafi, tana tsananin son motarta
dole ce tasa ta rabu da ita.
Faduwa ce ta hana ta tafiya da wuri, acan suka
yini har zuwa yamma, Sagir ma ya zo daukar
matarsa zai tafi da ita Cairo acan zata haihu
koma a ce kacokan zata kaura ta bar Malaysia,
har ta yi
sallama da wajen aikinta suma saura kwanaki
uku su tafi. Da Umaimah ta tashi tafiya direban
Faduwa ne zai mayar da ita gida sai Faduwa da
Sagir suka yi mata rakiya har bakin mota suka
mika mata babbar leda a cike da alawowi iri-iri
masu tsadar gaske
suka ce ta kaiwa yaranta tsaraba,
.
Umaimah ta karba ta yi godiya sai kuma ta rushe
da kuka ta rungume Faduwa itama tuni daman
Faduwa ta fara kuka. Suka yi ta rusa kuka ba na
wasa ba. Sagir ne ya dinga lallashinsu dakyar
kukan ya tsagaita.
Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Ada na tsani
MAKWABTAna, bana sonsu, nayi zaton dukka
MAKWABTA haka suke basa bada hakkin
MAKWABTAKA ashe ba haka ba ne. Anti Faduwa,
daga kanki ke da Abdul-Sabur na fara son
MAKWABTAna kuma daga yanzu duk inda zama
ya hada ni da mutane zan zauna da
MAKWABTAna
lafiya.
Kun yi jahadi da ku ka fahimtar da ni na san
hakkin MAKWABTAKA. Allah Ya saka muku da
gidan aljanna, ba zan manta da ku ba har abada.
Faduwa ta sharce hawaye ta ce ''Ada na tsani
*yan Najeriya saboda yadda *yan uwana suka
musguna min, amma zamana da ke yasa na
fahimci ashe wasunku kuna da kirki. Ke ce *yar
Nijeriyar dana fara sani mai kamun kai, hankali,
kunya da ladabi.
Ke ce wacce kika sadaukar min da abunda kike
so kika hakura da shi dan in samu. Ina jin ki a
zuciyata
tamkar kanwata uwa daya uba daya, saboda bani
da kanwa ko daya a duniya....
Kuka ne ya ci karfin Faduwa ta kasa karasa
bayananta suka sake kankame juna, ji suke kamar
kar su rabu.
Faduwa ta sake sharce hawaye ta juya ta dubi
Sagir wanda shima sun saka shi hawaye dan
tausayi duk da ba Hausa yake ji ba amma ya
san