Showing 84001 words to 87000 words out of 130520 words

Chapter 29 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8048

ta ce, ''Lallai
wannan hadin ya yi kyau. Amma Yaya ya kamata
ka zabi daya naga duk suna da kirki, kuma ga su
masu ilimi, kyawawa. Amma ni na fi yi maka
sha'awar babbar, wato Faduwa.
Abdul-Sabur ya katse hammar da yake yi, ya
ajiye cokali ya dade yana kallon Khausar don
mamaki,
can ya daure ya yi magana.
Ya ce, ''Me yasa kika ce haka?
Ta ce, ''Za ku fi daidaitawa saboda ta manyanta
zata fi sanin rayuwa da hakurin zaman aure, ga
ta da
fara'a da sakin fuska. Ita ma karamar ba laifi
tana da kirki, amma wani lokacin kamar tana da
jan aji da ji da kai.
Wai shin ba ita ba ce muka hadu da ita a Ka'aba
ba, ta harare mu ta tafi?
Shamsuddin Ya girgiza kai, ''Ai gara ya auri
karamar za su fi dacewa, saboda Faduwa zata ga
kamar sa'anta ne ba zata yi biyayyar aure ba.
Amma karamar, yarinya ce karama budurwa za
su fi daidaitawa.
Abdul-Sabur ya yi murmushi kawai ba tare da ya
sake cewa komai ba, har suka yi surutun su suka
bari.
Kwanakin su Kausar biyar a Malaysia, Abdul-
Sabur na dawainiyar kai su wuraren shakatawa
kala-kala. Idan suka fita tunda safe sai tsakar
dare suke
dawowa.
Yawanci da Faduwa ake tafiya kasancewar
Umaimah na zuwa makaranta kullum.
Sau daya ne suka je 'Langkawi Beach' da
Umaimah shi ma don bata taba zuwa ba tana so
ta je ta gani,
idan ba ta bi su ba yanzu zuwan zai yi mata
wuya nan gaba, musamman idan lecture ta
kankama.
'Langkawi Beach' teku ne babban gaske wanda
aka kawata shi fiye da sauran tekunan da suke
kasar.
Garin yana da nisa sosai a mota, don haka wasu
suke hawa jirgin sama. Abdul-Sabur ne ya saya
musu tikitin jirgin sama su dukka biyar din, suka
isa garin ranar alhamis da rana. Ba su baro
wajen ba sai karfe goma na dare, su dukka sun
kunshi nishadi marar adadi.
Ranar da Kausar da mijinta zasu tafi Abdul-Sabur
ya rako su gidan Faduwa suka yi mata sallama,
sannan suka dunguma gidan Umaimah ita ma
suka yi mata sallama. Umaimah ta rako su har
bakin lift suka tafi, tayi musu fatan alkhairi da
fatan Allah Ya kaisu gida lafiya sannan ta koma
gida ta ci gaba da karatu. Kasancewar wannan
semester bata samu ta
zauna ta yi bita ba sosai, tana ta biyewa su
Abdul-Sabur suna yawon shakatawa don haka ta
yiwa
kanta fada ta zauna a gida tayi karatu.
Faduwa kuwa da ita aka yi rakiya har filin jirgi.
Kafin su Kausar su wuce zuwa wajen screening
sai ta jawo hannun Abdul-Sabur gefe suka kebe,
a zatonsa wata magana zata fada masa mai
muhimmanaci.
Sai ya ji ta ce, ''Zan fadawa Faduwa kana sonta
zaka aure ta in ka kasa fada. Don gaskiya ta
damu dakai
fiye da Umaimah, ba ka ganin Umaimah ko rako
mu bata yi ba, Faduwa ce ta katse baccinta da
tsakar daren nan ta taso ta zo.
Ya ji tamkar ya kifa mata don takaici, ya harare
ta ya yi tsaki. Ya ce, ''Wai ke me yake damunki
ne? Kada ki kuskura ki fadawa Faduwa wata
magana, naga kin karbi lambarta wallahi idan na
ji wata magana sai na bata miki rai. Babu
ruwanki da wannan maganar.
Kausar ta tabe baki, ta ce, ''Allah Ya huci
zuciyarka ba ruwana, daga yau ma na daina yi
maka maganar aure ma balle na yi laifi.
Ya ce, ''Da kin hutawa kanki kuwa.
Haka suka yi sallama baram-baram ba ta
walwala.
Har mijinta da Faduwa suka fuskanci hakan,
amma ba a shiga tsakanin dan uwa da dan uwa,
babu wanda ya tambaye su me ya faru. Sai karfe
biyu na dare Abdul-Sabur da Faduwa suka dawo
gida.
Suka yiwa juna sallama kowa ya shiga gida.
Asuba ta gari Abdufaduwa.
*
Sai bayan tafiyar su Kausar ne Abdul-Sabur ya
samu yake yin isasshen bacci kwana biyu, amma
da su Uncle Hamza suka dawo Malaysia daga
Singapore sai aiki ya dawo masa sabo fil. Saboda
yana tashi da safe yake zuwa ya same su a hotel,
daga nan su nausa cikin kasuwa. Daman dai
Uncle Hamza dan kasuwa ne don haka duk kasar
da ya je sai ya nemi abin da zai sara, wani ya
aika shagonsa na London, wani kuma ya tura
shagunansa na
Ghana.
Ba dare ba rana Abdul-Sabur yana tare da Uncle
Hamaza har sai da suka shafe kwanaki goma a
haka, sannan ya kai su filin jirgi shi da Emeke
suka koma London. Don haka Abdul da su
Faduwa ma ba a haduwa ko a waya ba sa
samunsa. Bayan tafiyar bakinsa da ya dawo gida
ma sai da yai kwanaki uku bai kunna waya ba,
bacci kawai yake
yi, sai dai ya tashi ya yi sallah ya koma bacci,
bai cika fita masallaci ba ma abinci ma jifa jifa
yake ci. To me zai yi tunda ya gama karatu?
Sai da ya tabbatar ya huta sosai ya kunna
wayarsa missed call ya fi guda dari ya tarar daga
kasashe daban-daban. Missed calls din Faduwa
guda ashirin da biyu. Na Umaimah guda biyar sai
na Kausar guda talatin da uku, ta damu tana ta
kiransa a tunaninta saboda ita ya kashe waya,
don ta bata masa rai ta yi masa maganar
Faduwa, don haka duk ta bi ta damu.
Ya dinga bin su daya bayan daya yana kira yana
yi musu bayanin yana nan lafiya kalau, baccin
gajiya
ne kawai. Ya cewa Umaimah da Faduwa in ba sa
komai ranar asabar da yamma su hadu a wajen
shakatawa na 'Sunway Pyramid' su yi hira,
dukkansu suka ce ba
damuwa za su je.
Ranar asabar misalin karfe biyar da rabi suka
gama hallaruwa a cikin *yar rumfar da suka saba
haduwa, kowanne daban-daban ya zo. Ba daga
gida suke ba, Umaimah daga makaranta ta ke
gidan su Aisha Bingyal.
Faduwa daga Hotel din wasu kawayenta da suka
zo daga Cairo, Abdul-Sabur ne ya fito daga gida.
A jere suka jera motocinsu a wajen da aka tanada
don yin 'parking'.
Ka'ida ne daga ka zauna a cikin rumfunan
ma'aikata su kawo maka littafin abinci da abin
shan da ake siyarwa, ka zaba ka saya, don haka
sai kowa ya zabi abin da ya ke so. Faduwa da
Umaimah a koshe suke dam! Kasancewar sun ci
abinci a wajen kawayensu. Lemo kadai suka
zaba.
Abdul ne yake jin yunwa sosai don ko karyawa
bai yi ba shi ya zabi shinkafa da kaza.
Suna shan lemo suna hira, wasa da dariya Abdul-
Sabur ya kammala cin abinci ya goge baki da
hankici, ya juya ya kalle su ya yi murmushi. Ya
ce, ''Na tara ku anan don mu yi zaman karshe,
kuma hirar karshe.
Sai duka suka zura masa ido suna yi masa duban
rashin fahimta. Yayin da mummunar faduwar
gaba ta addabi zukatansu.
''Wacce irin magana kake yi Abdul? Idan ka ce
hirar karshe zaman karshe, ai sai mu yi zaton
mutuwa zaka yi. Inji Faduwa.
Umaimah ta ja dogon numfashi ta dire bata iya
cewa komai ba.
Abdul-Sabur ya yi shiru kansa a kasa kamar mai
tunani, sannan ya dago ya dube su ya yi
murmushin karfin hali.
Ya ce, ''Kin yi gaskiya Faduwa, banda Allah babu
wanda Ya san abin da zai faru a gaba amma
Allah
Ya kadarto rabuwarmu wanda ba na tunanin zan
sake waiwayar Malaysia kuma idan na tafi.
Sai suka ji tamkar an dire aradu a kahon
zuciyoyinsu, suka zazzare ido suna dubansa.
Ya ci gaba da cewa, ''Na kammala karatuna, na
so in dan zauna da ku saboda sabo, amma Uncle
Hamza ya ce in tattara in koma gida. Don haka
zan tafi gobe har na cike takardar sakin gidana
sun dawo min da ragowar kudina don ban cika
shekara ba.
Yana rufe bakinsa sai Faduwa ta dora hannu aka,
Umaimah ta cije yatsa suka kame tamkar wasu
gumaka, idanuwansu a sunkuye a kasa.
Da ya ambaci sunayensu suka dago suka dube
shi, sai yaga hawaye sharkaf na zubowa daga
idanuwansu.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?
Suke karantowa su duka ukun a bayyane.
Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Amma Abdul
zaka tafi ka ki yi mana sallama da wuri, sai da
ya rage saura awanni? Ya girgiza kai, ya ce, ''Ku
yi hakuri na san zafin da
zaku ji na rabuwarmu, bana so in tayar muku da
hankali da wuri. Ku yi hakuri don Allah ba boye
muku na yi ba. Ku yafe min idan na bata muku
rai,
ko na kuskure muku ban sani ba, kun san mutum
ajizi ne. Ni ma na yafe muku idan kun yi min laifi
a fili ko a boye, balle ni babu wacce ta yi min laifi
a cikinku.
Ku yi min alkawari za ku ci gaba da zumunci a
junanku ko ba na nan, ku ci gaba da mutunta
kanku da kare mutumcinku a kasar nan har ku
kammala karatunku. Umaimah ina rokonki da
zarar kin kammala karatu ki koma gida ki zauna
kusa da iyayenki ko a cikin garin Gombe ki kama
aiki har Allah Ya ba ki wani mijin ki yi aure,
saboda kin yi kankanta ace kin zauna a wata
kasar ba a gaban iyayenki ba. Ki manta komai da
ya faru da ke a
baya, ki bude sabuwar rayuwa Allah zai taimake
ki.
Kuka ya ci karfin Umaimah, sai ta gyada kai don
ba zata iya magana ba.
Hawaye mai zafi ne ya fara zubowa daga
idanunsa shi ma kasancewar ya ga halin da suka
shiga na kuka. Bai zaci zasu ji radadin rabuwa da
shi haka ba. Ya goge hawaye ya juya ya dubi
Faduwa, ta kifa kai akan tebur tana kuka ta ki
dagowa har sai da ya
ambaci sunanta ba adadi, sannan ta dago ta
dube shi idanunta sun yi jawur.
Ya ce, ''Faduwa ki yi hakuri da duk yanayin da
kika tsinci kanki, Allah Yana tare da ke, zai yaye
miki damuwarki insha Allah, ki rike aikinki ki
dinga ziyartar *yan uwnaki na Cairo da Nigeria.
Kada ki
yanke zumunci da su don Allah ba Ya bada
rahama ga mai yanke zumunci, haka zumunci
yana kai
bawa aljanna.
Faduwa ta gyada kai cikin shesshekar kuka, ta
ce, ''Na ji zan yi amfani da shawararka insha
Allah.
Umaimah ta goge hawayenta ta tashi tsaye
cimak ta dube su, ta ce, ''Zan koma makaranta,
dama group assignment muke yi a gidan Aisha
Bingyal na taho zan koma mu karasa.
Abdul-Sabur ina maka fatan Allah Ya kai ka gida
lafiya, kuma Allah Ya saka maka da alkhairi a
bisa dawainiya da kulawar da ka yi mana. A da
rayuwata tana cikin kunci har sai da ka bi duk
yadda zaka yi na sami sauki. A da farin ciki ya
kaurace min, kai ka taimaka ya dawo. Ina gudun
mutane ka sa na shigo cikin mutane. Ina cikin
kuskure na dawo hanyar Allah madaidaiciya.
Yanzu na san tawakkali na nemi wadanda na
kauracewa a baya. Da jikinka da dukiyarka babu
abin da baka yi mana ba, tsakaninmu da kai sai
addu'ar Allah Ya kaddara saduwarmu ko ba a
duniya ba ranar gobe kiyama, Allah Ya hada mu a
aljanna..
Kuka ne ya hana ta karasa maganarta, sai ta
juya da sauri ta tafi. Ta ki dawowa duk kwalla
kiran
sunanta da Faduwa ke yi. A guje ta shiga wajen
da ta ajiye motarta ta bude ta zauna ta dora kai
a sitiyari ta sharbi kukanta har ta godewa Allah.
Ita kanta ta rasa dalilin yin wannan kukan
saboda Abdul-Sabur din nan a kasar nan ta san
shi kwanan nan, to me don ya ce zai tafi zata
damu kanta?
''Mutumin da na ki jini a da na tsana, na tsani in
hadu da shi a hanya? Ya aka yi ya zama abokina
har na ke jin ciwon rabuwa da shi? Sabo turken
wawa in ji masu iya magna.
Abdul yana da kirki, yana da kyautatawa, kuma
zuciya tana son mai kyautata mata wannan ita ce
kadai amsar. Inji zuciyar Umaimah.
Tana tuki tana tafe tana tunani, hawaye kuwa ya
ki kafewa sai shatata ya ke.
Faduwa ta zabura ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ya
na ga ka saka kafa ka shure maganar da muka yi
da kai?
Ya fada cikin sanyin jiki, ''Wacce ke nan?
Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Maganarka da
Umaimah ta aure.
Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya gyara
zama, ya ce, ''Daman na amince, na yi miki
alkawari zan aure ta ne?
Ai ban taba amsa miki ba ke kadai kike
maganarki. Abinda kika kasa fahimta shi ne,
babu maganar soyayya tsakanina da Umaimah,
yadda nake mutumci da ke haka nake yi da ita..
Faduwa ta katse shi cikin kuka ta ke magana, ta
ce,
''Amma ni naga kun dace na hada ku, ka ce kana
tausayinta, maganin tausayi sai ka aure ta. Kai
ma
ka san zaku dai-daita da ita don ba ta tsane ka
ba, ta saba da kai, ta shaku da kai, ga ta da
ladabi da kunya da tarbiyya..
Abdul-Sabur ya dafe kai, ji yake tamkar tana
daka tabarya a kwakwalwarsa.. Ya daga hannu
da sauri ya dakatar da ita.
Ya ce, ''Ya isa haka Faduwa, ba ki fahimce ni ba,
ba za ki taba fahimtata ba kuma. Ni kadai na san
halin da nake ciki yanzu, zuwan da Uncle Hamza
ya yi, ya zo min da magana kuma ba zan iya
ketare ta ba, ya ce in zo in auri *yarsa..
Bai rufe baki ba Faduwa ta dafe kirji don fargaba
da tashin hankali.
Ta ce, ''Shi yasa kake yi mana sallama irin wacce
har abada ba zaka sake waiwayarmu ba?
Ta girgiza kai yayin da hawaye ya ci gaba da
surnanowa daga idanunta.
Ta ji ba zata iya ci gaba da zama tare da shi ba,
saboda zuciyarta kamar zata burme. Nan da nan
ta mike, ta suri mukullin motarta. Ta ce, ''Abdul
Allah Ya kiyaye hanya, Allah Ya kaddara
saduwarmu. Ni ma zan tafi ana jirana Putra
Jaya'. Ta tafi da sauri hawaye yana zuba.
''Faduwa, Faduwa zo ki ji. Inji Abdul. Ta ki
waiwayowa ma balle ta dawo, ta dade a zaune a
mota tana kuka, sannan ta tuka ta tafi, don kada
ma ta kwana a gidan ta ga tafiyarsa sai ta wuce
garin 'Putra Jaya' zata kwana a gidan kawarta.
Umaimah ma ma a gidan kawarta Aisha ta yi
niyyar kwana.
Karfe dayan dare kowa yana bacci yayin da
Faduwa da Umaimah suke murkususu a cikin
duhu saboda damuwa.
Abdul-Sabur ya damu kwarai da ya je gidajensu
ya iske ba sa gidajensu, ke nan babu me yi masa
rakiya. Yana filin jirgi ya kira Faduwa ya sake yi
mata sallama ya tabbatar mata yana filin jirgi zai
tafi,
ta rushe da kuka, ta yi masa fatan alkhairi da
fatan Allah Ya kiyaye hanya.
Ya tambaye ta laifin me ya yi suka gudu daga
gidajensu suka ki raka shi filin jirgi.
Ta ce bai yi musu komai ba, saboda tashin
hankali ba zasu iya ganinsa zai tafi ba.
Irin wanna tambayar ya yiwa Umaimah da ya kira
ta a waya, irin amsar da Faduwa ta ba shi ita
Umaimah ta bayar, sai ya shaida mata yana filin
jirgi nan da awa guda za su tashi.
MAKWABTAKA 37
ya shaida mata yana filin jirgi nan da awa guda
za su tashi.
Ta tambaye shi ina zai je? Ya amsa mata Ghana
zai je. Ta yi masa tambayar data ba shi mamaki,
irin
tambayar da Faduwa ta yi masa dazu.
Umaimah ta ce, ''Yayana ba ka ji shawarar da na
baka ba ko wacce na ce ka auri Dr. Faduwa?
Idan ka duba maganata baku da matsala saboda
kun shaku, ka san halinta ta san naka, mace me
fara'a da son mutane. Me zai hana ka share mata
hawayenta ka aure ta?
Sai ya ji kansa ya yi masa gingirim ya ji tamkar
zai fasa ihu. Wai shin me yake shirin faruwa da
shi ne a rayuwa? Tabbas ya gasgata ba bakinsu
daya ba da sai ya ce hada baki suka yi don su
gwada shi. Ya
fuskanci kowacce magana take yi masa tsakani
da Allah. Lallai suna kaunar junansu, kuma
kowacce
na tausayin *yar uwarta. Umaimah ta ji shirun
yayi yawa, sai ta zaci wayar ta katse fadi ta ke,
''Hello! Hello kana jina?
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi gyaran murya
ya ce ''Umaimah, ban ki shawararki ba, amma ina
so ki gane wani abu guda daya. Babu soyayya
tsakanina da Faduwa ko kusa a matsayin kanwa
ko kawa na dauke ta, kamar yadda na dauke ki.
Sannan Uncle Hamza ya zo min da maganar
auren *yarsa wanda
ba zan iya bujire masa ba.
Umaimah ta dafe kirji ta runtse ido yayin da
hawayen takaici ya surnano mata. Sai ta yi masa
fatan alkhairi da fatan Allah Ya ba su zaman
lafiya da zuri'a dayyiba.
Ya amsa mata da ''Amin, na gode.
Suka kashe wayar babu wanda ba ya hawaye a
cikin su ukun.
Da ya shiga jirgi ma ya zauna sai da ya kikkirawo
su ya shaida musu ya shiga jirgi ya zauna, nan
da *yan mintuna za su tashi don haka zai kashe
wayarsa.
Suka sake yin bankwana da fatan Allah Ya kai shi
gida lafiya.
Jirgi ya lula da Abdul-Sabur, ya bar Umaimah da
Faduwa cikin gagarumar damuwa da kewarsa.
Allah Ya kiyaye hanya!!!
*
Faduwa da Umaimah su kan hadu jifa-jifa, amma
ba koda yaushe ba, tabbas Abdul-Sabur shi ne
ginshikin hada wannan shakuwa tasu. Babu
wacce take jin dadin zaman gidanta a cikinsu,
kullum da sassafe Umaimah sai ta fito kan
baranda ta tsaya babu abin da ta ke gani a
idanuwanta kamar inuwar Abdul-Sabur a lokacin
da yake tsayawa yana kallonta yana yi mata
murmushin nan na sa.
Nan da nan sai ta ji hawaye ya surnano mata, sai
ta jawo doguwar kujerarta ta zauna don kada jiri
ya kwashe ta ta fadi. Ta duba dukka wundunan
gidansa, ta ji kamar za ta ji motsinsa, amma ta
ga wayam.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Ta ke ta karantawa a bayyane.
Ta tashi ta shiga gida ta kudundune akan kujera
ta dora filo a kanta babu abin da ta ke hange sai
Abdul-Sabur.
''Me yake shirin faruwa da ni ne? Inji Umaimah ta
ke tambayar zuciyarta.
Wayarta ce ta yi ruri nan da nan ta tashi ta suri
wayar addu'a ta ke, fata ta ke Allah Ya sa Abdul-
Sabur ne. Amma kash! Sai ta ga sunan Faduwa.
Ta amsa a sanyaye.
Bayan sun gaisa Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur
kuwa ya kiraki bayan tafiyarsa?
Umaimah ta ce, ''Bai kira ni ba.
Faduwa taja dogon tsaki, ta ce, ''Ni ma bai kira ni
ba, kinga duk lambobinsa na London da Ghana da
nake da su na kira a rufe.
Umaimah ta ce, ''Baki da lambarsa ta Nigeria?
Ina jin can ya tafi.
Faduwa ta ce, ''Bai taba kirana da lambar
Najeriya ba. Suka yi sallama suka kashe waya,
yayin da kowacce ta shiga mamakin damuwar da
dayar ta shiga a sanadiyyar rashin Abdul-Sabur.
Kwana da kwanaki Abdu-Sabur bai kira
kowaccensu ba, har suka fara irga satittika, har
ya tafi wata guda shiru. A daddafe kowacce ta ke
gurgurawa ta tafi makaranta, a dole suke
daurewa suke yin karatu
don babu yadda zasu yi, abin da ya kawo su
kasar kenan, amma tabbas rashin Abdul-Sabur
ba
karamin gibi ba ne a rayuwarsu ta Malaysia ba.
Sai su yi sati ba su hadu ba, haka sai su kwana
uku ba su yiwa juna waya ba. Wani sa'in sai dai
su hadu a titi, kowacce a cikin motarta su yiwa
juna fitila su daga hannu.
Shin ko shi wanda suke yi dominsa ya san suna
yi?
Watakila ma yana can ya mike kafa ya bude
sabuwar rayuwarsa ya manta da ya taba saninsu
a duniya. Ko kuwa har ya fi su shiga halin
damuwa, saboda kewarsu? Oho! Allah ne kadai
Ya sani.
*
Umaima ce ta ke juyi akan gadonta cikin dare
tana tambayar kanta da kanta, wai shin me yake
damunta ne ta damu haka da yawa don Abdul-
Sabur ya tafi? A wanne dalili ta ke kasa cin
abinci, barci da kuka mai hawaye?
Ta fada a bayyane, yayin da ta yi zumbur ta tashi
zaune, ta sauko daga kan gado da sauri ta shiga
ban daki ta dauro alwalla ta zo ta fara sallah
tana addu'a kada Allah Ya dasa mata son
mutumin da ba zata taba samu ba a rayuwarta.
Faduwa ce a zaune a falonta da sassafe, barcin
safe ya kauracewa idanunta, yayin da shara ta
gagari hannayenta saboda sanyin jiki. Babu abin
da ta ke fata da bege irin ta gani sai Abdul-Sabur
ko a waya
ne. Ta shiga tantance sakamakon da zuciyarta ta
ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login