Showing 99001 words to 102000 words out of 130520 words

Chapter 34 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8019

kalaman rabuwa suke yi.
Ta yi magana da turanci ta ce, ''Sagir ka taya ni
cikawa Umaimah alkawarin da zan daukar mata
idan na haifi mace zan saka mata suna Umaimah,
saboda kauna da zaman amanar da muka yi.
Sagir ya gyada kai ya ce, ''Na amince miki Yah
Habitti.
Umaimah ta fashe da kukam farin ciki ta ce ''Na
gode muku, nima insha Allah kafin in bar duniya
inda rabon nayi aure na haihu zan saka sunanki.
Zasu sake kankame juna su sake bude wani
sabon shafin kukan sai Sagir ya janya Faduwa ya
ce Umaimah ta shiga mota ta tafi, kukan ya isa
haka zasu sakawa kansu ciwon kai.
Basu daina dagawa juna hannu ba har sai da
suka yi nisa suka daina hango juna.
Allah Sarki sabo, turken wawa. Ko da rabon a
sake haduwa ko kuwa rabuwar ce har abada?
Allah ne kadai Ya sani.
Amma dai sun yiwa juna alkawari zasu ziyarci
juna Egypt da Nigeria ba nisa sosai.
***
Ba Umaimah kadai ce me himilin kaya ba dalibai
da dama sun lodi kaya da yawa musamman ma
matan.
Ai kuwa ansha dogon turanci a tsakanin wakilan
Gwamna da ma'aikatan Egypt air saboda himilin
kayan da dalibai suka loda yayi yawa ainun. Duk
da alafarma da rangwamen da suka yarda suka yi
amma sai da aka biya makudan kudin awo. Su
Umaimah suna gefe kamar ba akan kayansu ake
hayaniya ba, suka yi lukus a gefe. Ka ga *yan
gatan gwamnati, sai da aka gama komai aka
miko musu
'tag label' din kayansu, suka wuce abinsu zuwa
cikin jirgi, daga su sai *yar jakarsu ta ratayawa
da jakar Laptop dinsu.
Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal ne suka
shigo cikin jirgi sanye da riga da wando (jeans)
sai suka dora bakar abaya akai, zo kaga farar
fata a cikin bakin kaya yadda suka haska.
Kananan hijabai ruwan madara masu kwalliyar
fulawa baka suka dora akansu, suka saka takalmi
masu tsini da kalarsa ruwan madara, suka dora
farin gilasai a idanuwansu.
Rigiji-gafji!
Wani kaya sai amale.
Kowa sai da ya dago ido ya dube su, dan su ne
suka shigo daga karshe kasancewar sun bata
lokaci a wajen awo aka dade ana ta hayaniya
akan kayansu, sun yi kyau sosai, sai suka zama
tamkar *yan tagwaye masu kama daya, kallo
daya zaka yi musu ka tabbatar sunyi kama da
masu digiri digirgir. Su na tafe suna hirarsu suna
ta tuntsira dariya har suka shigo ciki, suka fara
duba inda lambar kujerarsu take kamar yadda
take a rubuce a jikin 'Bording pass' din kowanne
fasinja. Dama tsakiyar jirgin lambarsu take dan
haka suka
wurwuce mutane da yawa kafin su isa
mazauninsu.
Tunda suka shigo suke aikin gaishe da iyayen
kawayensu irin su Baban Hanif dan su tuni sun
shisshigo.
Tana juyawa gefenta Abdul-Basi da Tanimu ta
gani suna zazzaune, sai ta duka ta gaishe su
cikin girmamawa, nan da nan suka yi caraf suka
amsa abunka da daman jira suke. Ta gaggauta
wuce zuwa can baya inda kujerunsa suke tana
tafe tana mamakin irin wannan isa da girman kai
na Abdul-Basi, ta shiga addu'a kada Allah Ya sa
*ya*yanta su biyo halinsa.
Sai yanzu ta sake curewa da jinjinawa Abdul-
Sabur, sai da ya shekara yana bin ta yana yi
mata magana tana share shi bai taba gajiya ba
ya daina.
''Na yi rashin masoyi Abdul-Sabur. Ta fada a
zuciyarta.
Gaba daya *yan tawagar su Umaimah su dari
biyu ne, jirgi kuwa mai cin mutane dari biyar ne
dan haka aka batse da farar fata masu zuwa
Cairo su dari uku. Bayan kowa ya zauna, sai aka
kwararo addu'ar nan ta tafiya.
Jirgi ya zabura ya tashi sama ya luma cikin
gajimare yayin da Umaimah ta runtse
idanuwanta, babu wanda take hangowa daga
Abdul-Sabur sai Faduwa, hawaye mai zafi ya
kwararo mata. Ta sake tunowa da kawayenta
*yan Malaysia da *yan India, da malamanta da
suka saba sun rabu da wuya su sake ganin juna
kuma har abada.
Ta dade tana ta kuka bata daina ba duk da
lallashin da Aisha ta dinga yi mata dakyar ta
daina. Tana cike da farin ciki dan zata je taga
Baffanta, *ya*yanta da *yan uwanta amma ta san
yanzu zata hadu da ce-ce-ku-ce da kananan
maganganu, da masu shiga sharo ba shanu,
masu fada ba'a tambayesu ba.
Africa kenan sabanin nan da ba ruwan wani da
wani.
Sai wata rana Malaysia!!!
CAIRO Tafiyar kwanaki biyu zasu yi sai da suka
shafe awanni goma sha hudu a sama sannan
suka isa Cairo da misalin karfe shida na asuba
agogon Cairo,
sannan aka kwashe su a motoci aka rarraba su a
Hotels. Saboda yawansu ma a Hotel daban-
daban
aka rarrabasu, dan sai sun shafe awanni goma
sha biyu sannan zasu taho Nigeria. Duk daki
daya mutane biyu aka rarraba, Umaimah da
kawarta Aisha dakinsu daya, bata ga Abdul-Basi
ba daman ba nemansa take ba. Bata ga Lamijo
da mijinta ba amma taga Hanif shi da abokinsa
Bashir Wada, a kusa da dakinsu ma suke. Burinta
kawai ta shiga dakin ta kwanta saboda gajiya da
bacci, sai bayan data yi bacci ya ishe ta sannan
suka yi wanka da salloli suka sauko suka ci
abinci. Saida yamma karfe biyar aka kawo motoci
aka kwashe su zuwa jirgi
da karfe shida na yamma jirgi ya tashi zuwa
Abuja,
tafiyar ba nisa sosai awanni uku da rabi ne kacal,
suka isa Abuja da karfe goma na dare a birni
tarayya ta yi musu.
MAKWABTAKA 43
ABUJA, NIGERIA
Suka ci sa'a kuwa suka sauka da kayansu gaba
daya kafin su iso dogayen motocin gidan
gwamnatin garinsu sun zo sun jeru reras suna
jiransu a filin jirgi, suna fitowa sai suka duru a
ciki su da kayansu a ka zarce dasu katafaren
Hotel. Aka rarraba su mata dakunansu daban,
maza ma dakunansu daban, mutane uku-uku.
Daliban ne kadai aka kai wannan Hotel din sauran
kowa ya
tafi ya kama nasa da kudinsa masu gidan *yan
uwa ko abokai suka tafi can.
Ta san Abdul-Basi gidan Yayansa ya tafi wato
Abdul-Badi.
Washi gari da sanyin safiya suka shirya suka
shiga motocin suka nufi garinsu Gombe, nan
danan suka
isa, abinka da motoci masu lafiya.
GOMBE, NIGERIA Suna shiga garin sai suka gan
shi kamar anyi gobara haka mutanen garin duk
sun yi baki-kirin,
amma ba baki suka yi ba haka garin ba ayi
gobara ba, illa sun saba ganin jajayen fata da
dogayen
gininnika kamar gidajen tangaran.
Gidan Gwamna aka zarce da su sai suka iske
gidan a cike da masu taryarsu, Umaimah bata
damu da duba nata *yan uwan ba ta san babu
mai zuwa mata duk da dai su Baffa sun san tana
tafe amma ba suyi da ita za su zo ba.
Gagarumar liyafa aka shirya musu a gidan
Gwamna, aka yi dafe-dafe iri-iri aka zazzauna
akan kujeru da suke babban dakin taron da yake
gidan gwamnati, tare da mai girma Gwamna aka
ci. Da aka ci, aka sha, sai ya yi musu jawabin
maraba gami da yaba musu bisa kokarin cin
jarabawa da kowannensu yayi sannan ya gode
musu da cika masa alkawarin da suka yi suka je
can basu yi wani abu na rashin da'a ba.
Dalibai uku maza biyu, mace daya suka tashi
suka yiwa mai girma gwamna godiya bisa
dawainiyar da
ya sha yi da su har suka kammala karatunsu na
tsawon shekara uku bai taba gajiyawa ba.
Daga karshe aka umarci kowannensu ya dauki
kayansa ya tafi gida, za'a neme su nan da wata
daya da rabi zasu tafi bautar kasa. Abuja za su
yi bautar kasarsu dan haka acan zasu karbo
takardunsu wato 'Call up letter.
Umaimah Bello ce ke tsaye a farfajiyar gidan
gwamnati tana kallon kawayenta da abokananta
suna ta tururuwar shiga cikin tsala-tsalan
motocin iyayensu.
Allah Sarki, ita kuwa bata da kowa da ya zo
daukar ta a mota, ta na tsaye tana ta zulumin
yadda zata yi. Shawara take ko dai ta fita ta je
ta samo tasi ta zo ta kwashi kayan akaita har
Dugge,
amma anya kuwa jami'an tsaro zasu bar dan tasi
ya shigo wannan gida?
Gashi kayan kuma ba zasu dauku ba da sai ta
kinkima zuwa bakin titi ta hau mota amma
saboda yawansu da nauyinsu ba zata iya ba.
Tana cikin wannan tunani sai ta ga Hanif a
gabanta.
Ya ce "Ke muke neme tun dazu, Baba ya ce ki zo
ki shiga mota mu tafi gidanmu ki kwana gobe sai
a
kai ki gida.
Sai ta ji gabanta ya fadi nan da nan muryarta ta
dauki rawa dan ba zata iya zuwa gidan Lamijo ta
kwana ba har abada.
Ta ce, "A'a na gode, yanzu nake so in tafi gida,
Hanif ka taya ni yiwa Baba bayani dan ya
fahimce ni, ba kin bin ku nayi ba.
Hanif ya ce, "To ina motar da zata kai ki gida?
Umaimah ta ce, "Yanzu nake tunanin ko bakin titi
zan fita in nemo tasi?
Ko kuma kayan zan baka ka tafi min da shi ni
kuma sai in tafi tasha in dauko mota in zo
gidanku in dauka amma gidanku ba gidan Lamijo
ba zaka kai min dan gidanku ya fi kusa da tasha.
Hanif ya ce, ''Nifa bana so in ji kina maganar
motar haya, ke fa babbar yarinya ce. Kina da
mota a Malaysia taki ta kanki a kasar ku a ganki
a motar haya. Ki zo mu je gidanmu kawai ki
kwana gobe da wuri zan tashi in kai ki Dugge da
kaina.
Umaimah, ta girgiza kai alamar bata amince ba,
wani takaici ya rufe ta data ji wannan bayanai na
Hanif, kai da jin bayanan Hanif ka san da sauran
kuruciya a kansa, da kuma gata da yayi masa
yawa bai san wahala ba, shi dai magiya yake yi
mata.
Tabbas tun yanzu Umaimah ta san ta fara
tozarta a kasarsu.
Kamar daga sama ta ji wata murya ta kira
sunanta,
muryar ta yi mata kama da muryar data sani
tana kuma matukar kewar mai muryar, amma
bata zaton bayyannar mai muryar a halin yanzu
kuma adaidai wannan lokaci. Ta waiga da sauri
ta dubi
inda sautin yake fitowa tabbas mai muryar da
take tunani ne. Baffanta ta gani a tsaye, Sabitu
da kuma
Ilah cikin yagulallun rigunansu, kai kace daga
bakin kura aka kwato kayan jikinsu, basu yage ba
amma sun kode sunyi yaushi. Daman ta san za'a
rina wai an saci zanin mahaukaciya, duk da ta
aiko musu da makudan kudi ta san ba zasu saki
jiki su ci ba, boyewa zasu yi su cigaba da wahala
daman ita suka saba yi. Ta ji hankalinta yayi
matukar tashi data gansu cikin wannan hali dan
ma wai sun yi wanka sun caba ado zasu shigo
birni taryar babbar bakuwa daga kasar waje.
Cike da mamaki gami da farin ciki mabayyani ta
ruga da sauri kai tsaye wajen Baffanta ta nufa ta
kankame shi su dukka suna kukan murna, ta rike
hannun Sabitu shima
hawayen murna yake, sannan ta juya ta kalli Ilah
duk ya tsufa saboda talauci ga *ya*ya, ga
masifar Matawata.
A sanyaye ta ambaci sunansa ''Hamma Ilah, ina
wuni.
Ya yi murmushin dadi, yayi caraf cike da murnar
ganin amaryarsa ya ce, ''Lafiya Umaimah, sannu
da dawowa. Sai suka ji ana ta matsa 'horn' din
mota a bayansu nan da nan suka waiwaya, mota
dankareriya kirar BENZA suka sake tabbatarwa da
su mai motar yake, amma ba su gane ko waye ba
saboda gilashin motar a rufe kuma bakin-kirin
basa ganin cikin motar. Ko daya sauke gilashin
motar, ya zare bakin gilashin da yake fuskarsa
sai suka shaida shi.
Abdul-Basi ne ya bayyana muraran a gaban su.
Ta dukar da kai kasa ya ce, ''Baffa, ina wuni. Ku
shigo mota in kai ku gida.
Baffa, Sabitu da Ilah sai suka zubawa Umaimah
ido suna jiran su ji abunda zata ce. Ta kuwa sha
kunu tana harararsa zuciyarta cike da tsantsar
tsanarsa,
ta cije baki ta juya ta dubi Baffa ta girgiza kai.
Ta ce ''Kada ku shiga motarsa tunda ba shi ya
kawo ku ba.
Aka yi carko-carko na kallon-kallo tsakanin
Umaima da Abdul-Basi daga dukkan alamu yana
mamaki yadda Umaimah ta waye har ta fara yi
masa musu. Sai ya sauke gilashin kujerun bayan
motarsa,
sai ga Babangida da Bilal sun bayyana. Su ma
aka hau kallon-kallo da su da su Umaimah, da
farko
yaran basu shaida ta ba. Sai ta ji wani farin ciki
ya lullubeta, ta runtse ido dan ta tabbatar ba'a
mafarki take ganinsu ba sannan ta bude ido ta
tabbata zahiri take ba'a mafarki ba, ta yi
murmushi ta
ambaci sunayen yaran.
''Baku gane Anti Umaimah ta Malaysia, ba na
fada muku a waya nace zan zo ba?
Sai suka gasgata ita ce suka fara tafa hannu da
ihu suna tsalle, yayin da suka yunkura zasu bude
kofa su rugo wajenta, Babansu ya dakatar da su.
Ya ce ''Ku koma ku zauna zata zo.
Yana so ya nuna mata idan ta isa da Baffanta
shima ya isa da *ya*yansa. Aka jima ana kallon-
kallon,
har yanzu su Umaimah na tsaye a inda suke haka
Abdul-Basi da *ya*yanta suna zaune a cikin
mota.
Sai fullanci ya hargitse tsakanin Baffa da Sabitu
suna rokarta data manta da abubuwan da yayi
mata a baya ta dubi albarkacin yara ta yafe
masa.
Wanne miji take da shi yanzu a duniya wanda ya
wuce shi, mutumin da ya rike ta tun tana karama,
ya dauki nauyin karatunta har ta zama mutum.
Ba dan tubalin karatu (firamare da sakandire)
daya bata ba ada a ina za ta sami ilimin da har
zata sami damar tafiya kasar waje ta yi karatu?
Ita kuma tana fada musu irin wulakanci da korar
karen da yayi mata a lokacin daya tabbatar bata
da kowa din sai shi.
Baffa yana hawaye a zuciye ya jawo hannunta ya
tura ta cikin mota kusa da *ya*yanta ta rushe da
kuka ta rungume su. Baffa ya shiga kusa da
Umaimah ya zauna, Sabitu ya zauna kusa da
Baffa,
dukkansu a gidan baya, yayin da Ilah ya ja burki
ya tsaya cak. Baffa ya leko ta windo ya ce da
Ilah ya
shiga gaban mota ya zauna. Ilah ya ce su tafi
kawai ba zai shiga motar ba zai taho a motar
haya.
Da alama dai kishi ne ya ke zakularsa, wannan
shi ake kira da 'ta leko ta koma kenan' har da ya
fara murna Umaimarsa ta rabu da Abdu-Basi
zasu daidaita gashi ya dawo, har su Baffa sun
fara goyon bayansa. Aka hau galle-gallan harara
a tsakanin Ilah da Abdul-Basi yayin da Umaimah
ke
tsakiya tana kallon ikon Allah da mamaki marar
adadi.
Kishi kumallom maza!!!
Baffa dai har yanzu magiya yake yiwa Ilah don ya
shigo motar, ya ce in dai ka dauke ni uba kamar
yadda ka dauki Jani to ka shiga mu tafi.
Umaimah ta ce, ''Hamma Ilah, yi hakuri ka shiga
mu tafi kada ka damu.
Nan da nan ya ji sanyi a ransa. Sai yayi amanna
da maganarsu, har da tafiyar takama yake yi
saboda ko a yanzu Umaimah ta gwada wanda ta
fi so a cikinsu shi ta zaba, ya zo ya bude gidan
gaba ya zauna basu daina gallawa juna harara ba
har
yanzu.
''A ina kayanki suke?
Abdul-Basi ya tambayi Umaimah a gadarance ba
tare da ya juyo ya kalle ta ba.
Ta turo baki tayi masa nuni da hannu ba tare da
tayi masa magana ba, ya ja mota ya tafi kusa da
kayan. Da yake babbar mota ce tana da katon
but yana daga zaune bai fita ba sai ya bude but
ya kira wasu kartai ma'aikatan gidan gwamna
masu jidar kaya a cikin but. Nan da nan suka
dinga cicciba
suna sakawa har suka gama, ya zaro naira dubu
ya basu.
Abdul-Basi ya yi addu'ar tafiya, ya zaro bakin
gilashi daga aljihunsa ya saka, ya daga gilashin
windunan mota sama, ya kunna Ac gami da
sautin kida a hankali, ya fisgi mota ya kama
hanyar Dugge.
Gudu yake ba kakkautawa, bai sake
magana ba kuma babu mai yin magana a cikin
motar, sai muryar Babangida da Bilal ne ke tashi,
suna ta yiwa Umaimah hira kala-kala, tana biye
musu suna hira amma gaba daya hankalinta a
tashe yake. Ganin Abdul-Basi da tayi ya ruguza
mata lissafi gaba daya amma ta ji dadi ya kawo
mata *ya*yanta, tun daga cikin mota ta fara
zakulo musu tsarabarsu ta alawoyi masu dadi da
tsada sai suka ji sun kara sonta dan suna kaular
alewa sosai.
Suna shiga Dugge sai Umaimah taga yara da
samarin garin kacokan sun firfito waje suna daga
mata hannu daga dukkan alamu taryarta kowa ya
fito yi sai farin ciki ya rufe ta, tausayinsu ya
kamata saboda ta gansu har yanzu a gidan jiya
babu wani ci gaba a tare da su. Sai taga garinsu
ya zama tamkar wanda aka cisu a da yaki, bututu
da su a cikin yashi. Amma bada yaki aka ci garin
ba tsabar talauci ne daman can ma haka suke,
dan ta saba ganin titina dodar da kwalta, fitulu da
dogayen
gininnika, a garin fararen fata garau-garau. Ta
dinga addu'a a zuciyarta Allah Ya taimaki Africa
da garinsu Dugge, su sami ci gaba suma su ji
yadda a ke ji a kasashen da suka ci gaba. Amin.
Ta sauke gilashin kasa ta leko da kanta tana ta
daga musu hannu, sai yanzu suka hangota dan
da duhun gilas yasa basa ganin komai suna
ganinta sai murna ta karu. Yara suka biyo motar
a guje har kofar gidansu suna fadin ''ga Umaimah
daga turai'' tana fitowa daga mota sai suka
ganta ta juye jar fata ta zama tamkar balarabiya
jajawur a cikin bakar abaya, ta yi kyau, ta yi kiba,
sai kamshin turare take. A haka ta dinga
rungumar yara kaca-kaca da su, duk wacce ta ci
sa'a Umaimah ta taba ta sai ta ji tamkar an yi
mata gafara dan ta sami babban rabo a duniya,
sai ka ji
suna cewa kamshinta ya shafe ni, su dinga
shinshina kayan su.
Mata suka dinga leke ta saman katangu ko zana
suna kallon Umaimah, sai rike baki ake saboda
mamakin wannan canjawa da ta yi. Har sai da ta
gaji da gaisawa da jama'a ta shiga gida, yuu!
Kungiya guda aka bita ciki.
Nene da Inna da murna suka fito suka rungume
Umaimah tabbas yau sun san ba karamar
daukaka
Allah Ya yi musu ba da Ya sa suka auri Baffa
wanda ya haifi wannan galleleliyar yarinya
Umaimah, ba
karamin abun alfahari ba ne a ga Umaiman ta
wuce kowanne gida ta shigo gidan da suke.
Subhan Allah,
sai Umaimah taga gidansu tamkar turken shanu,
dakinta tamkar kejin kaji wai dan ma saboda
zuwanta Baffa yasa an yabe shi da jar kasa, an
share, an shinfida sabuwar leda da sabuwar
katifa karama, ga sabon labule. Su Sabitu suka
dinga jidar manyan jakunkunanta suna saka mata
a daki.
Babangida da Bilal suka rirrike Umaimah wai ba
za su shiga dakin nan ba itama ba zata shiga ba
sai dai ta zo su tafi gidansu, dadi ya rufe Abdul-
Basi yadda zata ji zuciyarta ta karaya saboda
yara ta koma gidansa.
Nene tana rawar jiki ta yiwa Baffa da Abdul-Basi
shimfidar tabarmar kaba a zaure, ta kawo musu
dakwalkwalin ruwan sha a kwanan
sha, ko ba'a fada ba Abdul-Basi ba zai iya shan
wannan ruwa ba da ruwansa na roba a mota.
Umaimah ta dinga lallashinsu yaran dakyar suka
shiga dakin a bisa sharadin ana jimawa zasu fito
su tafi da ita.
Mata, yara da manya kowacce ta wanko kafa ta
zo yiwa gimbiya Umaimah sannu da zuwa har da
masu guzurin abinci, wasu dafaffiyar kaza, wasu
fura da nono aka jere mata a gabanta, sai godiya
take tana ta gaisawa da mutane har sai da ta ji
ba dadi, kanta ya fara ciwo saboda ta dade
rabon data ji rin wannan hayaniya, gida ya cika
dankar kai ka ce gidan biki ne.
Kowacce mace a dangi da MAKWABTAN Umaimah
sun hallara a gidan amma banda Matawata, ta
kulle kanta a daki ita da *ya*yanta ta hana su
fitowa, sai cizon yatsa take tana kai kawo daga
wannan
bango zuwa wancan bango, zama balle kwanciya
sun gagare ta saboda bakin cikin dawowar
Umaimah musamman Ilah ya shirya ya je har
Gombe taryar ta. Daman ta san da wanan
maganar
har yanzu yana son Umaimah, ya fada da
bakinsa ba zai daina sonta ba har abada. Ko
bayan ransa yana fatan Allah Ya hada su a
aljanna su zauna tare.
Duk da ta rufe kanta a daki babu abinda bata
jiyowa daga gidan su Umaimah, shewa kawai ake
yi ana yiwa Umaimah kirari ana yabawa da
kyawun da ta tsatso a can, har ma ana
kwatantata da ta zama tsoka daya a miya dan ita
ce *yan asalin garin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login