Showing 90001 words to 93000 words out of 130520 words
Chapter 31 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
ya tashi a wurin musamman da
suka ga kato yana kuka, kuma gashi a durkushe a
kasa yana neman gafara. Umaimah ta rike
Faduwa tana tambayarta a gigice cikin harshen
Hausa "Me
yake faruwa ne Anti Faduwa?
Faduwa ta sharce hawaye magana take yi cikin
kakkausar murya, amma cikin harshen turanci
take
bawa Umaimah amsa yadda kowa zaiji. Ta ce,
"Umaimah wannan shine mutumin da ya fara jefa
rayuwata cikin kunci da musiba. Shine wanda ya
tozarta ni a lokacin da nake neman mafaka. Shi
ne wanda yayi min tsirara a lokacin da nake
neman sutura, yaki share min hawaye a lokacin
da nake kwararar da hawaye
"Waye kenan? Umaimah ta tambaya
Faduwa ta matse hawaye ta nuna shi da hannu.
Ta ce, "Wannan shine Sagir wanda nake baku
labarinsa.
Da yake jama'a da dama sun san labarinta da
Sagir,
bata iya boye zafi da radadin kunar da ta yi masa
a baya kuma ya rabu da ita ya guje ta.
Sagir ma ya dawo yana magana cikin harshen
turanci dan kowa ya fahince shi kuma ya tausaya
masa.
Ya ce, "Ku taya ni rokar Faduwa ta saurare ni, ta
ji abun da nake tafe dashi. Abun da ya faru a
baya ta yafe min ba laifi na ba ne, takanas daga
Cairo na zo wajenta dan na samu labarin yau ne
ranar Graduation din ta, da magana mai
muhimmanci na zo mata da ita. Faduwa, ban
yaudare ki ba a baya,
yanzu ma ban zo da niyyar yaudararki ba, kin fi
kowa sanin abunda ya raba mu a baya. Bayan
rabuwarmu dai-dai da sakon daya ban taba
mantawa dake ba, ban taba yini guda ban tuna
da ke ba. Ki ji tausayina Faduwa, ke ce farin cikin
rayuwata..
Bai rufe baki ba sai kuka ya kece masa, jama'a
da dama sai da suka yiwa Sagir da Faduwa
hawaye saboda irin ruwan hawayen da yake
shatata daga idanuwansu, musamman ma
Umaimah wacce ta
rushe da kuka daman kiris take jira daman ciwon
rabuwa da nata masoyin ya addabe ta.
Ahmad dan asalin kasar Malaysia ne, daya daga
cikin abokan Faduwa shi ne yaje ya kama hannun
Sagir, ya tasheshi tsaye gami da karkade masa
kurar daya kwasa a jikinsa, yana mai yi masa
albishir da ya kwantar da hankalinsa za su taya
shi rokar Faduwa har sai ta saurare shi. Aka
zagaye Faduwa ana bata hakuri, daga ta dubi
Sagir sai ta
sake barkewa da kuka daga dukkan alamu tana
tuna tsiyar daya kulla mata a baya.
A lokacin ne kawayenta da zasu kawo mata kati
suka karaso da saurinsu kuma a gigice, sun zaci
ba lafiya ba. Suna tambayar me yake faruwa,
bayan an kora musu bayani sai suma suka shiga
bawa
Faduwa baki akan ta yi hakuri ta yafewa Sagir.
Daga karshe dai aka rarrabawa kowa katinsa a
hannu har da Sagir, sannan suka shiga ciki aka
zazzauna aka fara gudanar da bikin yaye dalibai.
Tabbas suma na su yayi kyau matuka amma bai
kai na su Abdul-Sabur haduwa ba. Anci, an sha,
an
gyatse, aka yi ta hotuna ba adadi a lokacin da
dalibai suke ta karbar satifiket din shaidar
kammala karatunsu a hannu.
Bayan karbar satifiket din Faduwa da kwana biyu
sai ta kaura rikunin gidajen da aka tanada dan
ma'aikatan asibitin, a nan sabon babban birnin
Malaysia wato Putra Jaya Dankareren gida mai
dauke da dakuna har guda uku da faluka biyu
gami da bandakai guda hudu,
aljannar duniya sunan gidan nan dan ya kayatu
da kayana alatu. Kamar su gadaje na alfarma,
kujeru, dinnin table, kafet, gass cooker, firij, injin
wanki da dai sauransu. Duk abunda ake bukata a
gida na amfani an zuba ko cukali bata shiga da
shi ba daga ita sai
akwatinan kayan sakawarta.
Dadin-da-dawa aka hada mata da tsaleliyar mota
dan haka waccan sai ta barwa wata kawarta
kyauta. Aka zo aka shato mata makudan kudi
duk wata za'a dinga bata a matsayin albashinta.
Tabbas Faduwa ta zama babbar likitan mata
(gyanae consultant) wacce aka ji da ita a wannan
gari, shi yasa aka wadata mata kayan more
rayuwa wanda zata samu nutsuwa wajen aiwatar
da aiyukanta yadda ya kamata. Sai Faduwa ta ji
kamar a mafarki ba a ido biyu ba saboda canjin
rayuwa da ta samu nan da nan.
Allahu akbar Allah mai iko, sarki mai kyauta a
duniya.
Dr. Faduwa Ahmad ke zaune a cikin katafaren
ofishinta da yake cikin babban asibitin Putra
Jaya. Ta jawo wayarta ta kira aminiyarta
Umaimah Bello.
Bugu daya Umaimah ta dauka cike da farin ciki
ko gaisawa basu yi ba.
Faduwa ta ce "Umaimah yaushe zaki zo Putra
Jaya?
Ki zo kiga yadda Allah Ya canjawa Dr. Faduwa
rayuwarta a cikin lokaci kankani. Umaimah ta
gyara zama dan ta ji dadin labarin sosai gami da
jawo remote din talabijin ta rage maganar data
cika mata kunne. Saboda tabbas labarin da
Faduwa take bata ya sanya ta nishadi tana kuma
taya ta murna.
Faduwa ta lumshe ido ta ci gaba da cewa. "Ni
Faduwa yanzu ni ce nake da katon gida, mota
mai tsada, albashi mai tsoka, mai gadi, mai aiki a
cikin gida da direba mai tuka ni. Haka nake da
*yan hidimata daban a cikin ofishina na asibiti,
kananan likitoci, manyan nurses, masu gadi duk
sai sun duka suke gaishe ni. Addu'ar da Abdul-
Sabur yayi min Allah Ya amsa daya ce insha Allah
kafin ma na karbi satifiket dina a hannu zan sami
nijin aure.
MAKWABTAKA 39
Kinga kuwa haka Allah Ya yi ikonSa ya jeho min
da sagir ba zato ba tsammani. Ya zo nema na
ido rufe,
maganar aure ya zo min da ita.
Umaimah ta lumshe ido don farin ciki ta shafa
kirji ta ce "Alhamdulillah, na taya ki murna Dr.
Faduwa.
Allah Ya tabbatar muku da alkhairi, Sagir din yana
nan ko ya koma Cairo?
Dr.Faduwa ta yi dariya ta ce, "Satinsa biyu a
garin nan sannan ya tafi, ya sha koke-koke da
magiya da tuba, dakyar na fara sauraransa na
fuskanci abun da yake tafe da shi maganar aure
ya zo min da ita kuma a cikin dan kankanin
lokaci yake son ayi. Na
ce masa ya je zan yi shawara ko zan iya aurensa
koma ba zan iya ba.
Umaimah ta zabura ta rike haba ta ce, "Dan
Allah, da gaske?
Ina mahaifiyarsa ko ta mutu?
Faduwa ta girgiza kai ta ce, "Bata mutu ba tana
nan a raye Allah ne Ya nuna mata ishara. Tana
raye tana ji tana gani za ayi, da wuya ta yi wuya
ma dakanta ta ce ya nemo ni ta amince ya aure
ni.
"Ikon Allah" Umaimah take ta fada tana
maimaitawa cike da mamaki yayin da take jin
dadin sauraran wannan labarai masu abun
alajabi.
Dr. Faduwa ta yi fari da ido ta kyalkyale da
dariya ta ce, "Ai bala'i kala-kala ne ya saukar
mata tun bayan data hanashi aure nan Allah ya
dinga nuna mata ishara har ta gwammace da tun
farko ni ta bari ya aura.
Umaimah ta ce, "Tunda ki ka rabu bai yi aure ba?
Faduwa ta ce, "Yayi aure-aure ma tunda mata
uku ya aura daban daban suna rabuwa, a
sanadiyyar
rashin son su da yake da kuma azabtar da
mahaifiyarsa da matan suke yi. Mata daya ce ta
haifa masa *ya daya aka saka sunan
mahaifiyarsa. In takaice miki har da wacce take
zuwa gabanta suyi zage-zage.
Dayar barauniya ce ta je ta sacewa
mahaifiyarsa gwala-gwalanta tatas masu yawan
gaske wadanda ta ke da su tun na gadon
mahaifiyarta data rasu ta bar mata, dana aurenta,
da wadanda danta ya dinga saya mata da yayi
kudi, shi kuma ta yashe masa kudinsa kaf daya
ajiye a gida ta gudu daman ba sonsa take yi ba,
abun da ya kawota kenan. Jinin mahaifiyarsa
yahau sosai dan takaici ta fadi rabin jiki ya
shanye.
Dakyar dai aka dinga yi mata magani sannan ta
fara warkewa ta fara takawa da sanda. Da kanta
ta tambaye shi wai a ina nake yanzu? Ya ce ina
Malaysia banyi aure ba, ta ce ta amince ya zo ya
aure ni. Umaimah, nasan basu kyauta min a baya
ba amma ina son Sagir so na hakika kuma na
tsakani da Allah, tun bani da komai shima bashi
da
komai muke son juna, ki duba ki ga tsawon
shekarun da muka yi tare. Kuma ko alokacin da
ya rabu da ni na san ba ra'ayinsa bane tilasta
masa akayi.
A rashin Sagir ne nake jin son wani amma da zan
same shi babu zancen in so wani ma.
Umaimah ta fada a cikin zuciyarta ta ce, "Ashe ni
ce nake son Abdul-Sabur ba Faduwa ba, rashin
Sagir ne yasa take son Abdul-Sabur daman. Ashe
ma da ya aure ta idan Sagir ya dawo zata iya
rabuwa da
shi ta koma wajen Sagir. Ni kuwa yadda nake son
Abdul-Sabur, Abdul-Basi da Ilah baza su sa in
rabu da son sa ba.
Faduwa ce ta katse tunanin da Umaimah ta ke yi
ta ce, "Yanzu dai hira a waya ba zata yiwu dukka
ba.
Yaushe za ku yi hutu in dauke ki? Ki zo gidana
kiyi sati biyu mu dade muna hira. Allah Ya sa
lokacin
bikinmu a cikin hutunku ne ki zo mu je Cairo ki
ga yanda larabawa suke kashe kudi idan suna
shagalin biki. Bikina ya zo dai dai da kudi ya zo,
Sagir ma ya samu mukami babba a aikin dan
sanda,
yanzu haka baya tafiya shi kadai sai da *yan
rakiya a bayansa yake yawo don haka yanzu kudi
ya zauna masa. Yaya kika ga cashewa da
rakashewa a wajen bikinmu? Kai! Inama Abdul-
Sabur zai kira in
gayyace shi bikin nan, na san idan na fada masa
zai zo har Cairo.
Umaimah ina miki addu'a da fatan ke ma Allah
Ya fito miki da miji na gari kuma wanda zuciyarki
ta ke so wato Abdul-Sabur.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali yayin da ta
ji kamar ta barke da kuka ta dai daure ta
amsawa Faduwa da amin sannan ta yi mata
alkawarin zata je gidanta idan suka yi hutu. Su
ka yiwa juna sallama da fatan alkhairi. Suna ajiye
waya Umaimah ta fashe da kuka ta sulale ta
kwanta tana fadin
"wayyo Abdul-Sabur ina ma ka zo a lokacin da
bana zaton zuwanka, da maganar aure kamar
yadda Sagir ya zowa Faduwa. Ina sonka, na kasa
daina sonka. Allah Ka agaje ni, Ka taimake ni in
samu abunda zuciyata take so.
*
Haka kuwa aka yi da su Umaimah suka yi hutu
Faduwa ta turo direbanta ya zo ya dauke ta da
*yar
akwatin kayanta ta yi shirin yin sati guda.
Tabbas bata zaci daukakar da Faduwa ta ke fada
ta kai haka ba, ta sha mamaki da ganin wannan
daula ta gidan Faduwa. Suka hadu suka dinga
murna da alama Faduwa ta fara koya mata
wannan halayyarta ta hayaniya.
Faduwa da me aikinta ce suke ta layin jerawa
Umaimah abinci da abubuwan sha iri-iri a
gabanta wanda suka dafa musamman dan ita a
matsayin karrama babbar bakuwa.
Umaimah ta ji dadi da ganin irin wannan
karramawa ta yi godiya ta ci, ta sha har ta
barshi. Daki na musamman Faduwa ta mallaka
mata da bandakinsa ita kadai ta baje har ta
gama kwanakin da zata yi ba tare da takurawa
ba.
Idan Faduwa ta tafi aiki da sassafe Umaimah sai
ta ci gaba da mimmikewa tana shirgar baccinta
babu abin da ya dame ta, sai ta yi ya isheta
sanna ta farka. Wanka kawai take yi da kanta
sannan ta fito falo ta iske mai aiki ta shirya mata
abin karya kumallo iri-iri sai wanda take so ta ke
ci tabar wanda bata so.
Da daddare Faduwa take dawowa
gida sannan su zauna zaman hira har zuwa karfe
dayan dare koma fiye da haka.
Umaimah tana kirgawa a iya wanda ta gani ban
da wadanda bata nan, Sagir yakan kira Faduwa
sama da sau ashirin a rana, bayan turo sakonni a
jejjere duk bayan mintuna saboda so da kauna.
Samun waje wai *yar caca da yado in ji masu iya
magana.
Faduwa sai share shi take tana ja masa aji tana
cewa ya rage kiran nan saboda tana da aikin yi.
Wani lokaci yana bawa mahaifiyarsa waya su
gaisa da Faduwa, tsohuwa sai rawar jiki take har
tana kiran Faduwa da ''Yah Faduwa Yah Habbitti.
Ma'ana masoyiyarta.
Tabbas ashe kiyayya tana iya komawa soyayya!!!
Sagir da mahaifiyarsa sun fi so ayi bikin nan da
watanni biyu, Faduwa ce ta ki amincewa dan ta
san ba za'a bata hutu a cikin wannan kankanin
lokaci ba a wajen aiki saboda bata dade da
farawa ba
amma akalla bayan watanni shida za'a bata hutu.
Sai ta je Cairo ta shafe wata biyu ayi hidimomin
biki a tsanake. Har Sagir ya bi dukka danginta ya
gaggaishe su ya shaida musu sun gama
daidaitawa da Faduwa zasu yi aure. Kowa ya yi
murna da jin
haka. Kwatsam sai dai Faduwa ta ji tsofaffi sun
kira ta a waya suna surfa mata zagi wai ta gama
shirya
aurenta bata fada musu ba dan ba su suka haife
ta ba.
Ta yi musu bayani tana bada hakuri wasu su
gamsu wasu su ki yarda sunyi fushi kenan.
Kullum tana gargadin Sagir ya daina yadawa har
sai zance ya kankama amma ina doki ya hana
shi dainawa. A
dole Faduwa ta shiga fadawa *yan uwa da
kawayenta cewar zata yi aure.
Da Umaimah ta lissafa lokacin da Faduwa ta ke
so ta dauki hutu ayi bikin a lokacin sungama
jarabawar 1st semester a level 3 dan haka ta
kudiri niyyar zuwa biki har Cairo. Kudin jirgi ba
matsala ba ne zata biyawa kanta ko Faduwa bata
biya mata ba.
Balle ma ta ji Faduwa ta jerowa Sagir sunayen
kawayenta guda goma da zai dauki nauyin siyan
tikitin zuwansu Cairo daga Malaysia, da sunan
Umaimah a ciki.
Umaimah da ta zo da shirin sati daya a gidan
Faduwa sai gata ta zarce tayi sati biyu saboda
zaman gidan Faduwa ya yi dadi, duk da haka ma
dakyar Faduwa ta bar da zata tafi wai sai ta
gama hutunta dukka a gidan, hutun kuwa har na
tsawon watanni biyu ne. Umaimah taki saboda
tana so ta dawo gidanta zata fi samun nutsuwa
yin tilawar karatu. Gashi zasu shiga shekarar
karshe dan haka karatu ya karu dole sai ta sake
zagewa.
Duk sanda Umaimah ta ji Faduwa da Sagir suna
waya suna hirar so da kauna sai taji jikinta yayi
sanyi saboda sai ta tuno nata masoyin wato
Abdul-Sabur.
Allah Sarki soyayya gamon jini ce!!!
**
Rana bata karya sai dai uwar *ya taji kunya' inji
masu iya magana.
Watanni shida kamar kwana shida ne a wajen
Allah, sai ga bikin Faduwa ya rage saura sati uku.
A lokacin Faduwa da kawayenta
suka shirya tafiya biki Cairo. Sai dai kash a
lokacin Umaimah bata gama jarabawa ba saura
sati guda ta gama, dan haka ba zata yiwu tare
ba. Sai Faduwa ta damka mata tikitinta a hannu
da zarar ta gama jarabawa sai ta hau jirgi ta je.
Kullum akwai Egypt air wanda yake tasowa daga
Malaysia kai tsaye zuwa Cairo.
Bayan su Faduwa sun tafi da kwanaki goma
sannan Umaimah ta yi shirinta a nutse, ta kira
waya ta yiwa Hanif, Babansa, Baffanta, Kaninta
da kwayenta su Aisha Bingyal sallama ta shaida
musu
cewar zata je Cairo bikin aminiyarta Faduwa,
dukkansu sun yi amanna ta je saboda sun san
yadda ta ke da Faduwa. Suka yi mata fatan
alkhairi
da fatan ta ji lafiya ta dawo lafiya. Bata dauki
wasu kaya masu yawa ba sai dai ta dauki kudi
masu yawa saboda ta sayi kaya a can,
dan ta ji Faduwa tana cewa in ta zo har Dubai
zasu shiga su yi kwanaki suyi siyayyar auren.
Kudi masu gidan rana. Allah Ya bamu na halak.
Sanda Umaimah zata baro Malaysia sai ta kira
Faduwa a waya ta shaida mata gata nan a filin
jirgi
zasu taso, tafiyar awanni goma sha hudu ce a
jirgi daga Malaysia zuwa Egypt, dan haka
Umaimah ta zaunu har taji babu dadi duk da
daman ta taba dandana nisan tafiyar shekaru
biyu da rabi da suka shude, a lokacin da suka zo.
Faduwa tana kirga awanni dan haka daidai sanda
jirgin su Umaimah ya sauka a filin jirgin Cairo,
Faduwa da angonta Sagir sun baiyana suna
jiranta. Tana fitowa daga ciki sai ta gansu sai
suka hautsine da murna suka rungume juna, suka
ja jakarta zuwa inda suka ajiye motarsu.
Umaimah ta iske Faduwa a cikin babban gida
inda danginta kakaf suke, bangare-bangare, iyaye
da
kakanni, mata da maza, yara da *yan mata.
Kyawawan gaske jajur-jajur da su, larabawan
asali,
tabbas da dangin Mahaifiyarta Faduwa tayi kama,
basa jin wani yare a duniya wanda ya wuce
larabci sai dan kadan da suka yi makaranta suke
jin turanci.
Umaimah ta ji tamkar a wata duniyar take ba'a
wacce take ciki ba ada. Da ta tuno da danginta
na
ruga inda ta taso sai ta tabbatar da da kuma
yanzu ba daya bane. Tabbas ta sami ci gaba a
rayuwarta, Larabawan da take gani a hoto ko a
talabijin yau ga su a gabanta tana cikinsu
tsundum suna ta gaggaisawa. Ashe ba Faduwa
ba ce kadai mai son
mutane da fara'a duk danginta haka suke, lallai
sun yi dace da hali na gari hade da shaida mai
kyau.
Hakika sunyi farin ciki da ganin Umaimah gata
dukka ilahirin wadanda suka zo bikin nan ita
kadaice bakar fata, sai itama ta saki jiki dasu
kamar yadda taga sauran bakin da suka taho
daga
Malaysia sun ware sun zama *yan gida kuma
*yan gari.
Ana ta yawatawa da su Umaimah waje-waje na
tarihin Egypt kasancewar Misra tana daya daga
cikin manyan kasashe da suke da asali da
dimbun kayan tarihi.
A nan ne kasar da Annabi Musa (AS)
ya yi rayuwarsa shida fir'auna.
An kai su sun ga gawar fir'auna, gawar matansa
da *yan fadarsa.
Sun ga gawawwakin sarakuna daban daban da
suka mulki Egypt shekaru dubunnai a baya. Sun
ga kayayyakin da suka yi amfani da su kamar su:
dutsen nika, duwatsu da aka fafe aka yi tukwane
da su, sun je wannan tsaunin da ake kira Pyramid
da dai sauransu.
Sanda bikin ya rage kwanaki takwas Faduwa,
Umaimah da kawayenta guda uku suka yi visar
Dubai domin sake yin sayayyar da amarya da
kawayenta suke bukata. Umaimah ta damu da
taga
wannan kasa da take yawan jin labarinta a cikin
duniya 'United Arab Emarate' wato Dubai. Ta
kagu
da taga wannan kasa me dumbin arziki da yalwar
kasuwanci wanda ta ji labarinta a cikin wani
littafi
mai farin jin wato' ADON DAWA''
Hakika taga Dubai sosai ta je Daira, ta ga Bur
Dubai,
ta tsallaka ruwan har take hange-hange ko Allah
Zai sa taga gidan Kaltum da Mambela.
Kwanansu hudu a Dubai suka sha yin siyayya iri-
iri, Umaimah ta samu atamfofi super holland,
shaddoji da materials kala-kala ta bayar a dinka
mata, dinkin surfani masu kyawun gaske riga da
zani, dogayen riguna da dan kwalayensu, ta sayi
gayaleluwa,
takalma da jakunkuna wadanda suka shiga da
kayan. Suka koma Cairo inda aka fara gudanar da
harkokin biki sai da aka shafe sati guda cur a na
ta shagulgula. Party na zamani a manyan hotel
na
cikin garin Cairo aka dinga yi kala-kala sannan
aka yi na gargajiya a wasu wuraren tarihi na
kasar.
Abun ya bawa su Umaimah sha'awa sosai,
makadan larabawa kala-kala aka gayyato suka
wake amarya da ango aka sha raye-raye. Kaya na
alfarma amarya da ango suke ta canzawa masu
kyalkyalin gaske,
Umaimah da sauran kawayen amarya shigar
kayan larabawa suka dinga yi kala-kala, irin
dogayen rigunan nan masu dan kwali sannan aka
jera wasu sulalla masu kyalli suna kara kacau-
kacau, haka ake daura sulillikan a kugu da
kafafuwa, an sha hotuna da bidiyo ba adadi.
Tunda Allah Ya halicci Umaimah bata taba ganin
bikin da ya kayatar da ita ba irin na Faduwa, ta
shaki farin ciki irin wanda bazai misaltu ba. Har
ta yi katarin haduwa da santalelen saurayi mai
suna Kamal daya daga cikin abokan ango, ya ce
yana sonta. Ya ji duk duniya bashi da matar da
ya ji yana so ya aura sai Umaimah.
Hidindimu iri-iri yake ta yi mata yana ta kashe
mata makudan kudi daman kuma akwaisu dan
har ya fi Sagir kudi, hamshakin dan kasuwa ne
kuma dan gidan dan kasuwa, a
wajen mahaifinsa ya gada. Ita dai baya gabanta
so take ta gama biki ta juya kasar da ta fito
wato Malaysia.
Aka kai amarya wannan katafaren gidan na Sagir
wanda ya gina da sunan Faduwa. Zamani ya
canja dan haka ya rushe fiye da rabin gidan ya
sake yi masa sabon fasali, ya zuba kaya irin na
zamani a ciki. Al'adar larabawa mace daga ita sai
kayan jikinta zata shiga gidan miji shine