Showing 54001 words to 57000 words out of 130520 words
Chapter 19 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
hau kan benci na zauna, jikina sanyi
kalau.
Daya daga cikin ma'aikatan ce ta yi min tsawa
wai na zo na karbi abinci na mika ciki, ina ganin
masu siya suna ta shiga ciki na sami waje na
zauna.
Sai na tashi jikina yana rawa na karbi farantin
abincin na shiga ciki ba tare da na san wanda zan
ba wa ba, maza ne dankar a ciki. Kallona suke
sama da kasa, duk da na yafa gyale. Amma sai
duk na tsargu. Nan da nan na juya waje na koma
wajen matar da ta aiko ni na ce wa zan ba wa?
Ta harare ni ta ce, ''Ki ce ina Ali Ali mai
mangyada?
Sai na koma ciki muryata na karkarwa na
tambaya,
sai ya yi dariya ya ce, ''Zo nan *yar shila, ga ni
nan. Zagayo nan. Na je na ajiye a gabansa sai na
ga ya kawowa hannuna cafka, na yi sauri na
zame, sai suka kwashe da dariya shi da
abokansa. Su ka ce,
''Wannan sabuwar zuwa ce dai ko? Shi yasa ba
ta san dawan garin ba.
Ali Ali ya ce, ''Haka ne, bakuwa ce dan ko jiya ma
na zo ba ta nan. Ke yarinya ki saki jikinki da mu,
mune
masu yi muku ciniki, gara ma ki saba da mu don
a jikinmu zaki sami abin duniya, don shi kika fito
nema. Idan kuwa kina bukatar manda sai ki
bayar da gishiri.
Yana maganar yana kanne min ido kamar tsohon
maye.
Na shiga zargin anya kuwa ban fada mugun
hannu ba?
Anya ba a cikin karuwai nake ba?
Ai kuwa sai na tsinkayo maza suna kaiwa mata
cafka, duk wacce ta zo ajiye abinci sai na ga
maza suna wawurarta. Da aka ce na zo na kai
abinci a karo na biyu sai na sake lullube jikina na
dauki farantin abincin na mikawa wani Alhaji mai
katon ciki da gemu, ga shan taba.
Yana ganina sai ya zabura ya ce, ''Wai Allah!
Wannan halittar fa daga ina? Lallai Hajiya ta yi
tsintuwa mai kyau. Ta zo mu yi magana ko nawa
ne zan biya don na samu wannan yarinya.
Ya dinga dagamin gira alamar iskanci tsan-tsa a
kansa.
Rana ta yi aka ce na je na zubo abinci da zai ishe
ni na zo na ci akan baranda. Ina kusa da Hajiya
babba ta shiga yi min nasiha da lallashin cewar,
na kwantar da hankalina na saki jiki da abokan
cinikayyarmu. Na kasa gane me ta ke nufi, in bari
maza su ringa taba ni yadda suke tattaba sauran
ko
me...?
Abdul-Sabur ya girgiza kai yayin da takaici ya
hana shi magana, sai cika yake yana batsewa kai
ka ce shirin dambe yake yi.
Faduwa kuwa salati ta ke yi tana zabura tana
dafe kirji.
Umaimah ta langwabar da kai, ta ce, ''Da na idar
da sallar la'asar sai na rataya jakata na zo na
durkusa a gaban Hajiya babba.
Na ce, ''Ki ba ni kwatancen gidanki zan je na
sanarwa uwar dakina cewar na sami aiki a
wajenki''
Ta girgiza kai ta ce, ''Mai zai hana ki bari sai
gobe ki je da wuri zai fi sauki. Na girgiza kai na
ce, ''To, bari na yi sauri na je na dawo kafin ku
tashi a nan kusa ne unguwar.
Ta ce, ''To ajiye jakarki mana, tunda yanzu za ki
je ki dawo.
Na rasa wannan wayo na matar nan, ko da yake
bai kamata na yi mamakin gogewarta akan
hikimomi irin haka ba, tunda ta manyanta, kuma
gashi idanunta a bude suke tas!
Na ce, ''Ai kayanta ne zan mayar mata na debo
nawa, ban zaci zan sami aikin ba zuwa dai na yi
na tambaya, yanzu da na samu shi ne zan je na
sanar mata.
Ta ce, to na je na dawo da wuri, na sauke ajiyar
zuciya da na ji ta ambaci haka, na tashi jikina
yana
bari kai ka ce cafko ni za a yi, sai sauri nake yi
kamar zan kifa ina yi ina waiwayen baya.
Na haye acaba don ina tunanin kudin jakata zai
ishe ni na biya shi.
''ina za ki je?
Inji Faduwa.
Umaimah ta ja fasali, ta ce, ''Wallahi ban sani ba,
sai da mai acaba ya fara tafiya yana tambayata
ina zai kaini?
Fiye da sau uku sannan na fara tunanin inda zan
je.
Can na ce, ''Ka kai ni ma'aikatar ilimi (ministry of
education). Koda ya tambaye ni wacce unguwa
ban sani ba.
Sai ya ce, ''Koda yake ita ce dai guda daya, bari
na kai ki can...
Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Me zaki
yi a ministry of education?
Tambayarsu zancen tafiya zaki yi?
Ta girgiza kai, ta ce, ''Na san mijin Lamijo a can
yake aiki, sannan ne ina fadar sunansa za su san
shi,
wajensa zan je na tambaye shi ranar tafiya.
A bakin get dan acaba ya ajiye ni na biya shi na
shiga ciki a tsorace, ina tsoron kada a koro ni ko
ace min ba nan yake ba.
Har kasa na durkusa na gaishe da masu gadi,
daga dukkan alamu sunji dadin gaisuwar da na yi
musu,
suka amsa cike da fara'a. Na tambaye su shi da
cikakken sunansa Alhaji Nasir Nafada.
Sai suka ce ''yana ciki ga motarsa ma bai tashi
daga aiki ba.
Na ce, ''Ina ne ofisshinsa?
Suka fara kwatanta min da hannu, sai suka
fuskanci ban gane ba, daya ya taso da sauri ya
ce na biyo shi a baya zai kai ni can.
Akan bene yake can ciki, ya kai ni har cikin
ofishin gami da sanar masa, ''Alhaji ka yi
bakuwa.
Yana dago ido sai ya ga ni ce, don haka sai na
ga ya dan firgita kuma ya cika da mamaki.
Ya ambaci sunana, sannan ya ce na shigo ga
kujera na zauna. Na yi wa maigadi godiya ya fita
ya rufo mana kofa. Maimakon na zauna sai na
durkushe a gabansa na barke da kuka mai
tsanani ina magana, amma kuka ya hana ni ya
fahimce ni. Ya tausaya min matuka, hankalinsa
ya tashi, har kwalla ta cika masa ido. Rokona
yake na tashi na zauna, na daina kukan na
nutsu..
Da kyar na tsagaita da kukan na tashi na zauna,
shi ma ya zauna a tasa kujerar yana ta ba ni
hakuri
cikin Fulatanci muke magana, shi ma bafillace ne.
Da kansa ya ce, ''Duk na san halin da kike ciki
Umaimah, wannan abu da ya faru da ke kulalliya
ce aka hada miki, kawarki Lamijo zuga ta aka yi
amma ita ai mai sonki ce.
Na sharce hawaye na ce, ''Ummarta ma ta kore ni
daga gidanta shi ne na zo na shaida maka bana
gari zan koma Rugarmu Dugge, ga shi babu waya
balle na ji ranar tafiyarmu. Ko zaka fada min
takamaimai ranar da zamu tafi na dawo, ko kuma
na karbi lambarka idan har ba zai zama matsala
ba na dinga fitowa daga Dugge na zo Dukku na
dinga kiranka ina jin labarin tafiya?
Sai ya girgiza kai don tausayi, ya yi shiru yana
kallona, har tsawon wani lokaci mai tsawo. Can
ya dauko wayarsa ya buga, sai na ji ya ambaci,
''Ranka ya dade permanent sectery na kira ne
game da maganar tafiya karatun yaran nan
Malaysia. Ka ce a cikin satin nan ne wacce ce
takamaimiyar ranar tafiyar? Saboda akwai
yarinya daya a nan *yar Dugge ce, zata koma
Ruga ba su da waya balle ta sani ta fito. Sai ya
ce, ''Rana ita yau ne tafiya, talata, amma ranar
ake so su hallara a Gombe za a dibe su a mota a
kai su Abuja su kwana litinin a sake tantance su
a can, sannan talata su wuce.
Da ya gama wayar ya yi min duk wadannan
bayanai, sai naji sanyi a zuciyata, kamar zanyi
tsalle. Sai a lokacin ya ga fara'ata shi ma da
alama ya ji sanyi a ransa.
Ya miko min lemo da ruwa ya ce, na sha ya shiga
tambayata me ye takamaiman tarihin rayuwata?
Na langwabe kai na ba shi tarihina kakaf da inda
na hadu da matarsa har zuwa rana irin ta yau da
muka rabu da ita, wanda bansan dalilin
rabuwarmu ba. Sai ya girgiza kai ya ce, ''Na
tausaya miki Umaimah, ki yi hakuri Allah Yana
bayan mai
gaskiya. Ki yi min alkawarin idan kin je wannan
kasar zaki kama kanki, ki rike mutuncinki, ki yi
abin da ya kai ki, ki dawo gida lafiya. Idan kika yi
haka insha Allah sai kin fita daban da *yan
rugarku. Sai kin zama abar kwatance a garinku,
zaki zama abar alfahari ga gwamnatin garinmu.
Idan kika yi min wannan alkawari zan ji dadi,
kuma zan taimake ki kamar yadda dolena na
taimaki
dana na cikina Hanif.
Sai na sulalo na durkusa a gabansa. Na ce,
''Allah Shine shaidata, idan na tafi can ba ka
ganina Allah Yana ganina, na yi alkawarin zan
kama mutumcina,
abin da naje yi shi zan yi insha Allah Baba ba zan
ba ka kunya ba.
Sai ya ji dadi ya yi murmushi, ya ce na tashi na
zauna.
Na mike tsaye na duka na ce, ''Dare ya fara yi
zan tafi garinmu don ba ni da inda zan kwana a
nan.
Ya ciro bandir din kudi mai yawa ya miko min, sai
hannuna ya hau karkarwa don razana da yawan
kyautar. Na yi godiya na fito akan ranar lahadi in
fito da wuri na zarto gidan gwamna a nan zamu
taru a yi mana jawabin karshe.
Da na fito daga ofishin na duba kudin *yan naira
dari-dari ne dubu goma ke nan. Tasi na hau ban
kula masu acaba ba, na nufi Dukku daga Dukku
na hau motar garinmu. Daga bakin garin acaba
ne dole zai shiga da kai cikin rigagenmu. Ban isa
Dugge ba sai bayan sallar isha'i, sai *yan gida
suka yi mamaki da ganina a dai-dai wannan
lokaci. Ba su firgita ba don sun ganni a nutse na,
cikin farin ciki da tsarabata kala-kala. Sai da
garin Allah Ya waye sannan labari ya kai ko'ina
aka ce na iso. Masu zuwa sannu da zuwa suka yi
ta shigo min, ina ta rabon lemon bawo da biredi,
yara kuwa suna ta karbar alewa.
Na zauna na korawa Baffa da matansa bayanan
karyar cewar, an tura mijina Abdul-Basi aiki kasar
Turawa da ni zai tafi, wani satin ne tafiyar. Dama
idan kun tuna can baya na fada masa zamu kaura
daga kasar nan.
Baffa ya yi murna ya yi mana addu'ar fatan
alkhairi,
yayin da matansa suka nuna hassadarsu kiri-kiri
a fuska ba haka suka so ba. Labari ya cika gari
cewar Umaimah da mijinta za su kaura Turai da
zama, har zuwa kallona suke yi har da masu
shafa jikina wai suma su kwashi albarka.
Allah Ya sa suma wataran su je.
Bakin ciki ya rufe Matawata, kawayenmu suka
dinga fada min irin mugayen fatan da ta ke yi
min, wai dama ace mijina ya sake ni ya fasa
tafiya Turai da ni na dawo rugar nan na zauna na
ganta da Ilah
bakin ciki ya kashe ni.
Na sake godewa Allah da Ya sa na rufe bakina
ban fadi aurena ya mutu ba, masu jin dadin suna
da
yawa.
Sabitu ne da ni a cikin dakinmu mun saka fitilar
kwai a gaba da littafi kai ka ce karatu muke
biyawa,
nan kuwa hira muke yi ta sirri. Na ba shi labarin
zamana a Gombe tas da duk yadda aka yi. Na ba
shi
labarin tafiyata nan da *yan kwanaki. Sai ya fara
hawaye ya tausaya min akan kunci da na shiga
da kazafi da aka yi min. Sai ya nuna fargabarsa
akan wannan tafiya da zan yi kasar da ban san
kowa ba,
kuma ba ni da kowa. Yana tsoro kada na je na
fada hannun muyagu su cutar da ni, ko halin
mutuwa a rasa *yan uwana.
Na roke shi da ya kwantar da hankalinsa insha
Allah zan je lafiya na dawo lafiya. Ina so ya
rufamin asiri, kada ya fadawa kowa gaskiyar
magana,
saboda idan Baffa ya ji ni kadai na tafi hankalinsa
zai tashi, ga shi da hawan jini.
Ranar lahadi da sassafe na shirya tafiya na fito
na fara sallama da *yan cikin gida, sannan na
lelleka MAKWABTA har wajen mahaifiyar Ilah na
shiga da yake har goben tana sona. Ta rungume
ni ta fashe
da kuka.
Matawata ta kama kugu tana ta girgiza ta cika
taf don fushi kamar zata fashe wai don na shigo
gidan.
Tun zuwana sai a ranar na ga Ilah, sai dai na jiyo
muryarsa daga cikin gidanmu. Ya kalle ni sau
daya nima na kalle shi mu dukkanmu sai muka
sunkuyar da kai kasa, tsoron matarsa ya hana ya
yi min magana.
Na fice na bar ta a nan ni kyankyami ma ta ba ni,
duk ta kazance da wani kodadden zani daurin
kirji, ba riga. Kanta buyaya ba dankwali ba kitso,
gashin nan duk ya kakkarye, bututu jikinta da jar
kasa don babu sumunti, haihuwa kawai ta ke yi
ciki da goyo. A lokacin ma tsohon ciki ne da ita.
Baffa da Sabitu ne suka rako ni har kofar fita
daga gari, idan Sabitu ya kalle ni sai idanuwansa
ya cika da kwalla.
Ya ce da ni, ''Adda Umaimah za ki je lafiya ki
dawo lafiya ki same mu lafiya a cikin izinin
Ubangiji. Kada
ki manta kin tafi kin bar ni ba ni da kowa sai
tsohon nan, ba Yafindo, ba Nasiba yanzu ke ma
babu ke....
Muka rushe da kuka mu dukka har Baffa. Can
Baffa ya ce, ''Umaimah fatana a gare ki shi ne ki
je ki dawo lafiya, Allah Ya kare ki daga sharrin
makiya, idan kin dawo kin same ni a raye to
Alhamdulillah, amma idan kin dawo kin iske na
mutu to ki yi min addu'a, Allah Ya jikaina. Tsufa
ya zo min, lafiya ta yi karanci a gare ni, don haka
ina daf da tafiya.
Na yafe miki duk abin da kika yi min a duniya.
Allah Ya tsare ki Ya ba ku zaman lafiya ke da
mijinki da zuri'a ta gari.
Sai muka sake fashewa da kuka, na kankame
Baffa na ji kamar na fasa tafiyar. Da kyar na sake
shi na juya na fara tafiya zuwa bishiyar da masu
acaba suke tsayawa.
Ina waiwayensu suna tsaye a inda na bar su,
kowannensu yana sharce hawaye yana daga min
hannu..
Umaimah ta rushe da kuka yayin da ta kasa ci
gaba da labarin. Hawaye ya cika idanun Abdul-
Sabur da Faduwa su ma.
Ta ci gaba da cewa, ''Na hau acaba ina ta rusa
kuka, ban daina ba har na isa garin Dukku na
shiga motar Gombe. Na isa gidan gwamna a
kurarren lokaci har an yi nisa a taro da kyar aka
bar ni na kutsa cikin masu tafiya.
MAKWABTAKA 24
Mai girma gwamna ya yi mana jawabai masu
dadi gami da nasihohi masu ratsa jiki cewar mu
yi karatu sosai mu ci jarabawa, babu ruwanmu da
shiga kungiyar *yan iska, mu kama kanmu mu
rike mutuncin garinmu da kasarmu.
Sannan ya yi mana yayyafin albishir cewa
kowanne dalibi daga
cikinmu mu dari daya cur maza tamanin mata
ashirin ya biya mana zunzurutun kudin makaranta
har na tsawon shekaru ukun da zamu yi mu
kammala karatun digiri dinmu. Sannan an
budewa kowannenmu account a banki duk
karshen wata za a dinga turo mana da kudin
abinci da gidan haya, har dalla dari biyar.
Sannan aka raba mana na'ura mai kwakwalwa
(laptop) kowa daidaiya kauta.
Iyayen yara suka yi jawabin godiya, yayin da aka
yi addu'a aka tashi kowa ya je ya yi sallama da
iyaye da *yan uwansa, yayin da ni da Hanif muka
yi wajen Babansa.
Ya ji dadi sosai da isowata, amma ya tambaye ni
ina akwatin kayana, sai na nuna masa jakata a
rataye a
kafadata na ce, ba ni da jaka sai wannan kaya
kala uku ne a ciki, sai tarkacen kayan kwalliyata
da hotunana da takardun makaranta.
Sai ya tausaya min, ya ce ni idan muka isa Abuja
zai fadawa abokinsa wanda su ne jami'an
Gwamnatin da za su raka mu har can Malaysia
zai ba shi kudi ya sissiya min akwati mai taya
karama, wacce ake ja da suturu na tsukewa
wadanda ba atamfofi ba,
don kada na fita daban.
Sannan ya kara da cewa, 'iyaye sun karawa
*ya*yansu kudi da zasu dinga kashewa, don haka
zan baki kudi dai-dai da yadda zan ba wa Hanif
ku dinga kashewa har shekara.
Ku bude account a banki daban ku turo min da
account number zan sakawa kowannenku naira
miliyan daidaiya, zan canja muku zuwa dallar.
Sai na durkushe a gabansa ina kuka ina ta godiya
Hanif ma sai ya durkusa ya yi godiya.
Abdul-Sabur ya buda baki don mamaki, ya ce,
''Allah Sarki bayin Allah ba sa karewa a duniya.
Faduwa ta ce, ''Lamijo matarsa kuwa ta sani?
Umaimah ta goge hawaye ta ce, ''Ba ta sani ba,
don tun lokacin da ta fara nuna kishi da zargi ya
nuna ya cire hannunsa daga kaina, ya nuna mata
Hanif ne kawai zai tafi. Ya gargadi Hanif kada ya
fada mata da ni za a tafi.
Alhaji. Rabi'u ya hadamu da abokinsa Alh. Sani
ya dinga kula da mu, daga Abuja har Malaysia.
Ya ba
shi kudi mai yawa ya rike muma ya ba mu dallar
dari bibbiyu mu rike a hannunmu kafin mu gane
gari mu fara kashewa.
Muka dunguma cikin birnin tarayya a cikin
zungura-zunguran mota (bus) mai sanyin A.C ta
gidan gwamnati. A hadadden hotel aka sauke mu
a Abuja, mata dakunansu daban mu uku-uku,
maza ma dakunansu daban.
Washe gari aka kai mu Embassy inda aka sake
tantance mu kowa da takardunsa (original) a
wajensa, da takardunmu da aka turawa kowa
daga makarantarsa a Malaysia (admission letter),
babu wanda ya sami matsala, aka mayar da mu
hotel muka sake kwana.
''Kin yi kawaye amma daga cikin *yan matan nan
dai ko, kuna hira?
Faduwa ta tambayi Umaimah.
Murmushi Umaimah ta yi, ta ce ''Ai tuni na sawa
raina babu ni babu duk wani bil'adama a duniya,
mace ko namiji, yaro ko babba.
Abdul-Sabur ya tuntsire da dariya ya ce, ''Ba ke
babu bil'adama sai jinnu?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gara na hadu da
jinnu da na hadu da bil'adama don sun wahalar
da ni.
Don haka ba na kula kowacce kawa, na girmi
wasu, wasu sun girme ni, wasu shekarunmu
daya.
Sun shisshige min sun ga babu fuska har sun
rabu da ni. Mai girman kai suka dauke ni, *yar
wulakanci, suna tunanin ni *yar wani hamshakin
mai kudi ne, musamman da suka ga Alhaji Sani
yana ta kula da ni da Hanif.
A Abuja Alhaji Sani ya yi min siyayyar kaya
kamar riga da siket kala biyu, riga da wando
(jeans) kala biyu, abaya kala biyu, *yan kananan
gyaleluwa,
takalma da jaka kala biyu. Ya zuba a cikin
dandatsetsiyar akwati *yar madaidaiciya dai dai
ta shiga jirgi ya kawo min. Ai tuni na yi wurgi da
zannuwana kala daya na dauko wata super
holland sabuwar riga da zani, kacokan na bawa
wata miskina sadakar kayan da jakar.
Abu kamar wasa ranar litinin da daddare sai
gamu a jirgi Egypt air ne, da ya kwashe mu daga
Abuja sai birnin Cairo. Wannan shi ne karo na
farko da na taba hawa jirgin sama a rayuwata,
don haka
maganar kauyanci ma an san dole ne na yi shi.
Faduwa ta hau tafa hannu tana murna ta ji an
hau jirgin kasarsu, an sauka a garinsu. Ta ce,
''Ya ya
kika ga Cairo?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Airport ya yi, kuma
an dibe mu a mota an kai mu wani hotel a cikin
gari mai suna Novotel aka bamu daki mutum
bibbiyu, ga abincin safe da na rana, sai yadda ka
ga dama zaka diba.
Awannai goma sha biyu muka yi daga shida na
safe zuwa shida na yamma. Tun karfe biyar aka
dawo da mu filin jirgi muka shiga muka fara
lulawa doguwar tafiya daga Egypt zuwa Bounkok
awa goma sha daya, daga Bonkok (Thailanda)
zuwa Malaysia awa biyu.
Abdul-Sabur ya ce, ''Au sai da kuka tsaya a
Bonkok sannan kuka taho?
Umaimah ta ce, ''Eh, mun yi transit na awa biyu
an sauke fasinja kuma an debi wasu fasinjoji
zuwa Malaysia.
Mun iso Malaysia daf da magruba, ba mu sha
wahalar binciken immigration ba saboda a
tawagar gwamnati muka taho ga jami'an
gwamnati wadanda suka san gari ga takardun
kowa tsaf-tsaf.
Kai tsaye cikin Kaula Lumfur (KL) aka shigo da
mu wani babban hotel ni har yau na ban san
wanne ne ba muka kwana.
Washe gari aka hau rarraba mu, ashe ba mu
dukka